فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

19 – HANKALTA 239

19 –  HANKALTA

tafiyarda sha'anin iyali na hannun mai gida, shi ne tsayayye kan iyali da al'amuransu. dole ya dinga sanya hankali cikin al'amura, ya aje komai a muhallinsa, duk sanda ya qara girma ya zamanto hankali na qaruwa qarqashin ilimi da gogayyarsa ta yau da gobe, ya san dabi'un matarsa  da haqiqanin mata, tilas ya yi mu'amala da ita da yanayin da zai tsare da kiyaye zaman lafiyarsa gidansa da nutsuwar iyalinsa.

عن أبي جعفر (عليه السلام) ، قال  : إنّ المرأة إذا كبرت ذهب خير شطريها وبقي شرّهما  : ذهب جمالها ، وعَقُم رحمها ، واحتدّ لسانها ، وإنّ الرجل إذا كبر ذهب شرّ شطريه وبقي خيرهما  : ثبت عقله ، واستحكم رأيه ، وقلّ جهله

34 – an karbo daga baban jafar (as) ya ce: lalle ita mace idan ta tsufa sai biyun rabin mafi alherinta su tafi mafi sharrrinsu su wanzu: kyawunta ya tafi mahaifarta ta rufe ta daina haihuwa, harshenta ya kaifafa, lalle namiji idan ya girma biyun mafi sharrinsa su tafi mafi alherinsa su wanzu: hankali zai tabbata, ra'ayinsa ya qarfafa, jahilcinsa ya qaranta.

ومن ثمّ لا يسلّم زمام الأمر بيدها لأ نّه ورد عن أمير المؤمنين (عليه السلام)أ نّه قال  : كلّ امرئ تدبّره امرأته فهو ملعون ، أي بعيد عن رحمة الله سبحانه . ومن كان بعيداً عن رحمة ربّه كيف يسعد وكيف تسعد اُسرته 

35 – sannan kuma kada miji ya kuskura ya miqa ragamar al'amura hannuta ba saboda hadisi ya zo daga sarkin muminai ali (as) : dukkanin mutumin da matarsa ke juya shi tsinanne ne, ma'ana ya nesanta daga rahamar Allah, sannan duk wanda ya kasance nesa daga rahamar Allah ta qaqa zai samu farin ciki da azurta ta qaqa iyalansa za su azurta da farin ciki?