فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240

20 -  MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA

daga ciki dalilai muhimmai da ke sanya dawwamar rayuwar aure da samun nasara da nutsuwa da tabbatatuwar qaunar da rahama shi ne mace ya zamanto cikin kowanne ta na jin cewa girmanta da mutuncinta kadai na tabbatuwa ne da tsayuwar mijinta da mutuncinsa, girman mijinta shi ne girmanta alfaharinsa shi ne alfaharinta ita inuwa ce shi kuma haske, shi bishiya ne ita kuma reshe, duk matar da tunaninta ya kasance haka babu shakka ta na tsare mijinta da mutuncinsa, za ta kasance mai bada kariya ta fari gare shi, ta kuma shimfida hanya saboda daukaka kalmarsa cikin jama'a, da wannan masu Karin Magana ke cewa : babu wani mutum ma'abocin girma face ka samu mace bayansa, ita ke tanadar hanyar daukakarsa da bayyanarsa da shahararsa ya zamanto tauraro mai haskaka  a fagen rayauwa.

عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : انصرف رسول الله (صلى الله عليه وآله) من سرية كان اُصيب فيها كثير من المسلمين ، فاستقبلته النساء يسألن عن قتلاهن ، فدنت منهن امرأة فقالت  : يا رسول الله ، ما فعل فلان  ؟ قال  : وما هو منكِ  ؟ فقالت  : أخي . فقال  : احمدي الله واسترجعي فقد استشهد ، ففعلت ذلك ثمّ قالت  : يا رسول الله ، ما فعل فلان  ؟ فقال  : وما هو منكِ  ؟ قالت  : زوجي ، قال  : احمدي الله واسترجعي فقد استشهد  . فقالت  : وا ذلاّه . فقال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : ما كنت أظنّ أنّ المرأة تجد بزوجها ( هذا كلّه ) حتّى رأيت هذه المرأة  

36 – an karbo daga imam sadiq (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya dawo daga yaqi wadda da yawan musulmi suka samu raunka da shahada, sai mata suka tarbeshi suna tamabayarsa kan yaqinsu, sai daya daga cikinsu ta matso kusa ta ce: ya manzon Allah wacce bajinta wane ya yi ? sai yace mata : me ye matsayinsa daga gareki ? sai ta ce : dan'uwana ne, sai ya ce : ki godewa Allah ki karanta innalillahi wa'inna ilaihi ….. lalle shi ya samu shahada, sai ta aikata haka sannan ta ce: ya manzon Allah me wane ya yi ? sai ya ce mata ? me ye matsayinsa gareki ? sai ta ce mijina ne, sai ya ce mata ki godewa Allah ki karanta innalillahi … lalle shi ma ya yi shahada, sai ta rusa ihu ta na fadin wayyo wayyo qasqantata. sai manzon Allah (saw) ya ce: ban taba zato cewa mace za ta ji haka kan mijinta ba har sai da na ga wannan matar.