فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

21 – KISHI 240

21 – KISHI

Lalle Allah madaukaki mai kishi ne kuma ya na son kishi sai dai cewa daga maza koma bayan mata, lalle mumini na da kishi kan addininsa kamar yadda ya kasance mai kishi kan  danginsa da iyalinsa  musammam matarsa, mace kadai ta na samun aminci da kwanciyar hankali da ni'ma idan ta kasance ta na rayuwa qarqashin miji mai kishi, bai yarda da wulaqanci da qasqanci kan matarsa ba, da wannan ne zaka fahimci cewa mutuncin mace da daukakarta da wanzuwarta  shi ne miji.

mumini na da kishi kuma kishinsa daga imani ya ke sai dai cewa ita mace kishinta na cikin addininta da dabi'unta, amma kan mijinta ba ta da haqqin yin kishi saboda Allah ya sanya daga haqqin miji ya na iya auren mata hudu cikin aure dawwamamme amma qayyadaddde ya na iya aurar adadin da ya so daga mata, kishin mace kan mijinta ta wannan babi kafirci ne saboda hukuncin Allah da sauqaqawarsa, sai dai mata basa lura da wannan  al'amari mai hatsarin gaske.

قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : كان إبراهيم (عليه السلام) أبيّ غيوراً وأنا أغيَر منه ، وأرغم الله أنف من لا يغار من المؤمنين

37 – annabi (saw) ya ce: babana ibrahim (as) ya kasance mai tsananin kishi amma ni na fushi tsananin kishi, Allah turbude hancin wanda bai da kishi daga muminai.

عن الباقر (عليه السلام) ، قال  : غيرة النساء الحسد ، والحسد هو أصل الكفر ، إنّ النساء إذا غِرْنَ غضبن ، وإذا غضبن كفرن ، إلاّ المسلمات منهن .

38 – an karbo daga baqir (as) kishin mata hassada ne, hassada kuma hassada ita ce asalin kafirci, lalle su mata idan suka yi kishi  sai su fusata, idan suka fusata sai su kafirce face musulmai daga cikinsu.

روى جابر عنه (عليه السلام) ، قال  : قال (عليه السلام) لي  : إنّ الله تبارك وتعالى لم يجعل الغيرة للنساء ، وإنّما جعل الغيرة للرجال ، لأنّ الله قد أحلّ للرجال أربع حرائر وما  ملكت يمينه ، ولم يحلّ للمرأة إلاّ زوجها وحده ، فإن بغت مع زوجها غيره كانت عند الله زانية ، وإنّما تغار من المنكرات ، وأمّا المؤمنات فلا

Jabir ya rawaito daga gareshi (as) ya ce imam ya gaya mini cewa: lalle Allah madaukaki da albarka bai sanya kishi ga mata ba, kadai dai ya sanya shi ga maza, saboda Allah ya halasta ma maza aurar mata hudu `yantattu da kuma abin da hannun damansu ta mallaka daga kuyangu, amma bai halasta ma mace fiye mijinta kwaya daya rak ba  idan ta je ta yi lalata da wanin mijinta ta kasance mazinaciya gurin Allah, kadai dai ta na haqqin yin kishi daga lalatattun mata amma kan muminai ba ta da haqqin kishi.

أمير المؤمنين لولده الحسن (عليه السلام)  : وإيّاك والتغاير في غير موضع غي

رة ، فإنّ ذلك يدعو الصحيحة إلى السقم ، والبريئة إلى الريب[1]

39 – bai buya ba kan cewa kowanne irin abu idan ya shallake iyaka sai ya zama kishiyarsa, kishi wanda ya ke abin yabo ya na da haddinsa da iyakarsa, duk wanda ya wuce wannan iyaka sai kishinsa ya zama abin kyama kamar yadda ya zo cikin wasiyyar sarkin muminai ali (as) ga dansa hassan (as) na haneka da yin kishi wajen da ba muhallinsa ba, lalle hakan na jawo lafiyayye abu ya koma mai ciwo, barrantacce ya zama abin kokwanto.

 

daga cikin abin da ke saurin ruguje yali shi ne mummunan zaton ga matar da kake aure , lalle wannan muguwar halayya na rusa mafi girman rukuni daga rukunan iyali shi ne siqa da yarda, alaqa ba za ta taba kulluwa ba tsakanin mutane biyu ba idan babu yarda tsakaninsu.[1] Biharul anwar m 100 sh 252