فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

23 – DADADAWA IYALI 243

23 – DADADAWA IYALI

قال أبو عبد الله (عليه السلام)  : ثلاثة هي من السعادة  : الزوجة المؤاتية ـ  أي السمحة السهلة وأن لا تكون صعبة الفراش والمراس  ـ والولد البار ، والرزق يرزق معيشة يغدو على صلاحها ـ  أي رزق واسع يصلح به حياته ومعيشته  ـ ويروّح على عياله[1]

42 – baban Abdullah (as)ya ce: abubuwa uku na daga azurta: mace mai saqin kai mai miqa wuya, da mai biyayya, arziqi mayalwaci da zaka gyara rayuwarsa da shi ya dadadawa iyalinsa.

Zahiri al'amari shi dadadawa qari ne kan ciyarwa da ta wajabta kansa a shari'ance, lalle mustahhabi ne mutum ya jiyar da iyalinsa dadi.

عن الباقر صلوات الله عليه أ نّه قال  : « أنفقوا ممّـا رزقناكم ) قال  : ممّـا رزقكم الله على ما فرض الله عليكم فيما ملكت أيمانكم واتّقوا الله في الضعيفين النساء واليتيم ، فإنّما هم عورة[2]

43 – an karbo daga baqir (as) cewa cikin fadin madaukaki: ( ku ciyar daga abin da muka azurta ku ) sai imam ya ce: daga abin da Allah ya  azurta ku kan abin da ya farlanta kanku cikin abin da hannayen damanku suka mallaka: kuji tsoron Allah cikin raunana biyu mata da marayu, lalle su al'aura ne.

عن النبيّ (صلى الله عليه وآله) ، قال  : إنّ أكمل المؤمنين إيماناً أحسنهم خلقاً ، وخياركم خياركم لنسائهم[3]

-44 – an rawaito daga annabi (saw) ya ce: lalle mafi cikar imanin muminai shi ne wanda ya fi su kyawun dabi'a, sannan mafi alherin cikinku sune wadanda suke mafi alheri wajen matansu.

24-KYAWUNTA KYAUTATAWA:

Taimako da dadadawa iyali kyautatawa iyali da abin da ya yi kama da haka dukkaninsu subna nuni zuwa ga soyayya namiji ga iyalinsa wadda ta na masadiq gwargawadon sassabawar zamani da mahalli dda yanayi, idan ka kau da kai daga haka to dukkaninsu daga gundari guda suke  shi ne fadin Allah madaukaki:

وَجَعَلَ بَـيْنَكُمْ مَوَدَّةً وَرَحْمه[4]

Ya sanya qauna da rahama tsakaninku.

Daga cikin rahama cikin rayuwa zama da iyali shi ne mijiya kyautata musu ka da ya wulaqanta ta su cikin hana su abin da ya zama lazimi y aba su daga wajibai na addini da mutumtaka.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : من صدق لسانه زكا عمله ، ومن حسنت نيّته زاد الله في رزقه ، ومن حسن برّه بأهله زاد الله في عمره[5]

45- daga baban Abdullah(as) ya ce: duk wanda harshnsa ya gasgata ayyukansa za su tsarkaka. Duk wanda niyyarsa ta kyawunta  Allah zai qara masa arzikqi, duk wanda ya kyawunta kayutatawarsa ga iyalinsa  Allah zai qara masa tsawon kwana.

Daga tasirin kyatatwa iyali a ryuwance shi ne samun tsawon rai.

 

25- TAFIYAR DA GIDA NA HANNUN MIJI.

Cikin ilimin zamntakewa  da dangataka ya zuwa shugaba cikin iyali maganganu da wayewa sun sassaba , wasu na ganin tafiyar da gida na hannun uwa mace , wasu kuma na ganin na hannun uba namiji , wasu kuma na ganin kamata yayi ace su biyun ne suke shawarta juna don gudanar da harkokin gidan, ka da ya zamanto danniya da kama karya dayansu ke tafiyar da gidan .

Sai dai  kuma shi muslunci na ganin mazaje ke da haqqin tsayuwa kan mata sannan gabadayan harkokin tafiyar da gida na hannun da namiji, amma al'amuran da suka nshafi cikin gida kamar  tsaftace shi  da dai sauransu.

Haka al'amarin tafiyar da gari dole ne ya kasance hannun namiji, dukkanin mazajen da mata ke mulkarsu sun nesanta daga rahamar Allah.

قال أمير المؤمنين (عليه السلام)  : كلّ امرئ تدبّره امرأة فهو ملعون[6]

46- sarkin muminai Ali(as) na cewa: duk mutumin da mace ke mulkarsa Allah ya tsine masa.

 

26-BOYEWA MATA HARKOKIN KUDADENKA:

Lalle netsinkaye na rayuwar yau da gobe ya tabbatar da cewa idan mace tsinkayi abin da mijinta yak e da shi da al'amuransa na kankin kansa da rayuwarsa cikin al'umma to za ta yi qoqarin  ta ga ita ke juya shi da al'amarunsa, ta dunga yi masa katsalandan cikin kebantattun al'amuransa  da abubuwa da suka shafi maza kadai. Za ka samaeta ta na wuce iyakar ta ta diya mace ta rikirkita al'amura. Ya zama dole namiji ya zage dantse da yin damara wajen tafiyar da al'amuran gidansa ta yadda zai aje komai a muhallinsa.

قال أمير المؤمنين (عليه السلام)  : لا تطلعوا النساء على حال ، ولا تأمنوهنّ على مال ، ولا تثقوا بهنّ في الفعال ، فإنّهن لا عهد لهن عند عاهدهنّ ، ولا ورع لهن عند حاجتهن ، ولا دين لهن عند شهوتهن ، يحفظن الشرّ وينسين الخير ، فالطفوا لهن على كلّ حال ، لعلّ يحسن الفعال

47- sarkin muminai Ali(as) y ace: ka da ku tsinkayar da mata kan halin da kuke ciki, ka da ku amince musu kan kudadenku, ka da ku dogara da taimakonsu cikin aikinku, lalle al'amrin yadda ya ke su mata ba su da alqawari yayi da akayi alqawali da su , bas u da tsntseni yayi buqatunsu , ba su da kula  addini yayin da suke cikin has'awa, suna da riqon sharri suna da manta alheri, amma duk da haka ku tausasa musu cikin kowanne hali.

 

27-KYAWUNTA MIJINTAKA:

Daga cikin sabubban dawwamar aure ma'abocin nasara shi ne kyawunta mijintaka, ma'ana mata ta kiyaya abubuwa da mijinta yake da wadanda ba ya so domin yin haka gareta na da matsayin jihadi cikin tafarkin Allah kaga kenan na daga cikin abubuwa masu wahala gaske wanda  za ta cancanci girmamawar ubangiji da samun lada mai girama, kyawunta mijintaka na nufin tausayawar mace da taushinta yayin da ta ke mu'amala tare da mijinta  wanda ke cikin qishirwar wayawarta don ta kasance mace ma'abociyar nasara.

قال أمير المؤمنين (عليه السلام)  : جهاد المرأة حسن التبعّل

48-sarkin muminai Ali(as) ya ce: jahadin mace shi ne tya kyawunta zmatakewarta da mijinta.

وقال  : لتطيب المرأة المسلمة لزوجه[7]

ا49- a wani wajen kuma ya ce: lalle mace musulma ta sanya turare don mijinta.

Kasantuwar himmar mace na da rawar da ke take muhimmiya wajne jawo hankalin miji zuwa gareta to ita macen na  kulawa da tsaftarta don ta kasance mai kyawun gani da dadin mu'amalada dadin lafadi kowacce rana ta zama sabuwar budurwa mai kyawun gani.

 [1] Biharul anwar m 100 sh 219

[2] Biharul anwar m 100 sh 226

[3] Amali dusi :226

[4] Rum:21

[5] B anwar m  100 sh 225

[6] Biharul anwar m 100 sh 228

[7] Biharul anwar m 100 sh 245