فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244

27 – WATSI DA BOKANCI DA TSAFE TSAFE :

Ya na daga abin ban takaici ace har ya zuwa yanzu mata ba su gushe ba suna zuwa wajen bokaye don samun waraka daga matsalolinsu na cikin gida, za ka same su suna ba da kudade masu yawan gaske don ganin sun mallake zukatan mazajensu ko kuma don qoqarin ganin auren kishiyarsu ya mutu da dai makamancin haka, ire iren wadannan abubuwa sun fi afkuwa cikin qauyuka da karkara cikin dangin da suke fama da qarancin ilimi da wayewa, kai hatta cikin wasu lokuta  zaka samu wadanda suke da karatu da wayewa idan hanya ta kure musu sai su koma gurin wadannan bokaye da matsafa don neman mafita, muslunci mai girma yanyi inkarin wannan mummunan aiki matukar inkari.

قال عليّّ (عليه السلام)  : أقبلت امرأة إلى رسول الله (صلى الله عليه وآله) فقالت  : يا رسول الله ، إنّ لي زوجاً وله عليّ غلظة وإنّي صنعت به شيئاً لأعطفه عليّ، فقال رسول الله (صلى الله عليه وآله): اُفٍّ لكِ ، كدّرت دينكِ لعنتكِ الملائكة الأخيار ، لعنتكِ ملائكة السماء ، لعنتكِ ملائكة الأرض . فصامت نهارها وقامت لياليها ـ  بالعبادة والصلاة  ـ ولبست المسوخ ، ثمّ حلقت رأسها ، فقال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : إنّ حلق الرأس لا يقبل منها إلاّ أن يرضى الزوج[1]

45 – ali (as) ya ce: wata mata ta fuskanci manzon Allah (saw) sai ta ce: ya manzon Allah lalle ni ina da wani miji wanda ya ke kausasa mini, lalle ni nayi wata `yar dabara don samun tausasawarsa, sai manzon Allah (saw)ya ce: Allah wadaranki, kin gurbata addininki mafi alherin mala'iku sun la'ance ki mala'ikun sama da qasa sun la'ance ki, sai wannan mata ta dinga azumce yininta da kuma tsayuwar dare da ibada,ta aske gashin kanta, sai manzon Allah (saw) ya ce : aske gashin kai ba zai sa a karbi aikinta ba har sai ta nemi yarda mijinta.[1] Biharul anwar m 100 sh 250