فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

29 – GODIYA 246

29 – GODIYA

 daga cikin dabi'ar dan adam yin godiya ga wanda ya kyautata masa, mai kyautata da ni'imatawa na fari shi ne Allah matsarkaki, saboda haka wajibi ne godewa wanda ya yi ni'ima, dukkanin ni'momi na tukewa gareshi matsarkaki shi ne mafi canacata da godiya da yabawa, sai dai cewa daga godiya gareshi godewa abin da ya halitta idan ya kyautata maka, duk wanda bai godewa mutum ba bazai godewa mahaliccinsa ba, ya zama dole godiya ta kasance tsakanin ma'aurata da rayauwar iyali, miji ya godewa matarsa bisa sadukar da qoqarinta  wajen dafa abinci da tsaftace tufafi da gida da tarbiyyar yara da makamantan haka daga nauyi da ayyuka da suke kanta, sannan ya zama tilas miji ya ji cewa wannan falala ce daga matarsa da kyawaunta dabi'a  ba wai don ya zama wajibi kanta ko da ranta bai so haka ita ma mace wajibinta ta godewa mijinta bisa sadaukarwarsa wajen yin aiki tuquru  don jin dadinta da na `ya`yanta sai dai cewa abin ban takaicin shi ne galibin mata ba su godiya da yabawa mazajensu sannan suna butulcewa ayyukan alherinsu da suke ke musu.

أَتَتِ امْرَأَةٌ إِلَى النَّبِيِّ ص فَقَالَتْ مَا بَالُ الْمَرْأَتَيْنِ بِرَجُلٍ فِي الشَّهَادَةِ وَ الْمِيرَاثِ فَقَالَ لِأَنَّكُنَّ نَاقِصَاتُ الدِّينِ وَ الْعَقْلِ قَالَتْ يَا رَسُولَ اللَّهِ ص وَ مَا نُقْصَانُ دِينِنَا قَالَ إِنَّ إِحْدَاكُنَّ تَقْعُدُ نِصْفَ دَهْرِهَا لَا تُصَلِّي وَ إِنَّكُنَّ تُكْثِرْنَ اللَّعْنَ وَ تَكْفُرْنَ الْعِشْرَةَ تَمْكُثُ إِحْدَاكُنَّ عِنْدَ الرَّجُلِ عَشْرَ سِنِينَ فَصَاعِداً يُحْسِنُ إِلَيْهَا وَ يُنْعِمُ عَلَيْهَا إِذَا ضَاقَتْ يَدُهُ يَوْماً أَوْ خَاصَمَهَا قَالَتْ لَهُ مَا رَأَيْتُ مِنْكَ خَيْراً قَطُّ وَ مَنْ لَمْ تَكُنْ مِنَ النِّسَاءِ هَذَا خُلُقَهَا فَالَّذِي يُصِيبُهَا مِنْ هَذَا النُّقْصَانِ مِحْنَةٌ عَلَيْهَا لِتَصْبِرَ فَيُعَظِّمَ اللَّهُ ثَوَابَهَا فَأَبْشِرِي

47 – wata mata ta zo wajen annabi (saw) sai ta ce masa: me yasa mata biyu ke matsayin namiji guda cikin ba da shaida da raba gado ? sai ya ce mata: saboda ku kuna da tawayar addini da hankali, sai ta ce: ya manzon Allah meye tawayar addininmu ? sai ya ce: lalle dayarku zata zauna rabin zamaninta ba tare da sallah ba, lalle ku kuna da yawan tsinuwa da kafircewa mu'amala, dayarku zata zauna wajen mijinta tsawon shekaru goma ko fiye  da haka ya na kyautata mata da ni'imta ta, da zarar hannunsa ya dan quntata wata rana ko kuma sun sami sabani da ita sai ta ce masa: ni koda sau daya ban taba ganin alheri daga gareka ba, duk macen da ba ta da irin wannan halayya ta `yan uwanta mata to ta dauki wannan tawaya da ta sameta cikin addini da hankali matsayin jarrabawa kanta sai Allah ya girmama ladanta, kiyi bushara.[1][1] Biharul anwar m 100 sh 259