فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248

TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS)

mafi darajar tarihin tarbiyyar iyali shi ne tarihin rayuwar ali (as) da matarsa Fatima (as) haqiqa tarihin rayuwarsu tarihin rayuwa ne na ma'asumai biyu wadanda zancensu da ayyukansu da abubuwan da suka zartar  dukkaninsu na daga cikin sunna mai daraja, ba zaka taba samun iyali da suke dauke da ismar zati da dukkanin sasanninta da bangarorinta sai gidan ali da fatima (as) rayuwarsu ta aure ita ce mafi alherin misali da kasantuwa abar kwaikawayo, cikin rayuwarsu akwai wani abin tsintuwa da ke yada haske da kyawu da rayuwa da nishadi, za mu koyi yanda ya kamata mu rayu qaqa zamu dinga tunani a matsayinmu na ma'aurata da sukayi sa'a cikin rayuwar aure da duniyar iyali da tarbiyya da koyarwa.

daga cikin ababen tsinta:

yayin da abubakar da umar suka yi niyyar ziyartar fatima (as) lokacin rashin lafiyarta sun nemi izinin ali (as) sai ya shiga wajenta ya ce mata: ya ke `yantacciya haqiqa wane da wane suna qofar gida suna jira suna son gaishe ki amma me kika gani ? sai tace gida gidanka ne sannan `yantacciya taka ce matarka ce, kana iya yin yadda ka so.

wannan tsintuwa na da matuqar qayatarwa cikin rayuwar aure, lalle wannan tsintuwa na ishara ga ma'aurata ta yaya fuskantar juna zai kasance tsakaninsu da kuma yanda za su yi mu'amala da juna, ga wanda ya nufi shigar da baqo cikin gida kan wani batu na siyasa  ya kamata ya nemi izinin matarsa ya bata labari ya ji ra'ayinta kan batun saboda ta na da haqqi kan gida da abin da ke gudana cikinsa, sannan ita kuma ya kamata ta girmama matakin da zai dauka ka da ta kalli kanta bakin komai gaban mijinta, ta ce masa gidanka ne ni kuma mallakarka ce ka aikata dukkanin abin da ka ga ya dace,

daga cikin kyawawan tsintuwa daga gidan ali da Fatima {as} shi ne abin da ya zo cikin wasiyyar zahara (as) lalle ita ta bayyana rukunan asasi cikin rayuwar aure ta koyar da dukkanin mutane da matan duniya yaya mace za ta kasance cikin gidan mijinta da menene aikinta a addinnance da mutunce, lalle da mace za ta yi ado da wadanan siffofi da ta rayu cikin arziqi ta mutu cikinsa da soyayya qauna da tausasawa sun zama jagaba cikin rayuwarta, rabuwa da ita ya girmama wajen mijinta.

lokacin da Fatima ta yi rashin lafiya mai tsanan  ta zauna tsawon kwanaki arba'ain cikin rashin lafiya, yayin da ta debe tsammani daga rayuwa, sai ta cewa da ali (as) ya dan baffana lalle raina ya sanar da ni mutuwa ta, lalle ni ina ganin babu abin da ya rage gareni face riskar babana cikin kowanne lokaci, ina maka wasiyya da wasu abubuwa da ke cikin zuciyata, sai ali (as) ya ce mata: kiyi wasiyya da dukkanin abin da ki ke so ya `yar manzon Allah (saw) sai ya zauna kusada kanta ya fitar da mutanen da suke cikin gidan, sannan ta ce: ya dan baffana ba ka sameni maqaryaciya ko maha'inciya tun lokacin da ka aureni, sai ali (as) ya ce muna neman tsarin ubangiji daga haka  lalle ke kimfi kowa sanin daga Allah da biyayya da karamci da tsananin tsoron Allah daga kasantuwar ace na zargeki da saba mini, lalle rabuwa da rashinki na da tsanani gareni sai dai cewa al'amari ne da babu makawa daga gareshi, wallahi musibar zafin rabuwa da manzon Allah (saw) ta qara sabunta gareni haqiqa rashinki da rabuwa da ke ya girmaa gareni, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un daga musiba me ya fita girma da radadi da zartuwa da baqin ciki, wannan wallahi wata musiba ce da ba ta ta'aziyyarta, sai suka fashe da kuka zuwa dani wani  lokaci.

haqiqa Fatima (as) ta tattare rayuwar aure cikin wannan tattaunawa ta malakutiyya zuwa rukunai uku:

1 – rashin qarya 2 – rashin ha'inci 2 – rashin sabawa miji.

sai ta tunatar da sarkin muminai ali (as) da'arta da tsarkakarta da sallamawarta ga mijinta, shi kuma imam (as) ya yi godiya ga kiyaye alqawarinta  ya kuma yi yabo kan tsarkakarta da juriyarta da taqawarta, ya bayyana mata soyayyarsa da qaunarsa da ratayarsa gareta, haqaia kalmominsa gareta kalmomine da suke motsa  soyayya da girmama ga matarsa wacce babu wata mace kamar ta dukkanin fadin duniya.

bayan sun gama kuka sai ali (as) ya kama kanta ya sanya shi kan qirjinsa ya rungume sannan ya ce: kiyi mini wasiyya da dukkanin abin da ki ke so, tabbas za ki sameni mai zartar da wasiyyarki kamar yanda ki ka umarce ni, ki zabi al'amarinki kan al'amarina.

na'am haka rayuwar aure azurtacce ta ke ka ga miji ya zabi fifita abin da matarsa ke so kan abin da zuciyarsa ke so matuqar matarsa na tsoran Allah, kamar yadda zaka samu mace ta na fifita abin da mijinta ke so kan abin da ta ke so matuqar mijin na ta mai da'a ne ga Allah  mai tsarkake niyya, zuwa misalin wannan rayuwar ma'aurata muke kiran baki dayan mutane tabbas za su samu arziqin gida biyu duniya da lahira.