فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

SON `YA`YA DA QANAN YARA 252

MUQAMI NA   FARKO

                    SON `YA`YA DA QANAN YARA 

soyayya shi ne karkata zuciya da kwadayi na badini zuwa ga masoyi soyayya wata alaqa ce tsakanin masoyi da abin da ya ke so, ta kan sabawa da sassabawa dalilai da abin da suka ta'allaqa da ita, wani lokaci soyayya ta na kasancewa abin yabo wani sa'ailin kuma abar zargi da kyama, soyayyar alheri abar yabo ce, soyayyar sharri abar zargi da kyama kamar yadda sharri ya ke abin kyama da zargi, daga cikin soyayya da ake yabawa shi ne wanda halitta lafiyayya da hankali ke tabbatuwa kanta, ana qirga ta cikin dabi'ar `yan adamtaka shari'a ta tabbatar da ita ta kuma sanya lada cikinta, itace  soyayya ga qananan yara da soyayyar da mutum kewa `ya`yansa.

Cikin shari'a da ta zo daga samaniya ana qirga  son qananan yara daga mafifitan ayyuka.

من كتاب المحاسن ، عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : قال موسى (عليه السلام)  : يا  ربّ ، أيّ الأعمال أفضل عندك  ؟ قال  : حبّ الأطفال ، فإنّي فطرتهم على توحيدي ، فإن أمتّهم أدخلتهم جنّتي برحمتي

1 – daga littafin almahasin, daga baban Abdullah (as) ya ce: annabi musa (as) ya ce: ya ubangiji wanne aiki ne mafificin aiki wajenka? sai ya ce: son qananan yara lalle ni na halicce su kan tauhidi idan na yi naso sai in shigar da su aljanna ta da rahama ta.

 dukkanin yaro ana haifarsa kan tauhidi, kadai dai muhallin da ya taso da iyayensa suke mayar da shi yahudu ko bamajuse ko banasare, wannan na nufin hatta `ya`yan kafirai bisa la'akari da halittar da aka haliccesu kan ta tauhidi za su kasance ababen so, lalle mumini mai tauhidi  wanda ke ganin Allah cikin kowanne abu, ba zai ga wani abu face ya ga Allah gabaninsa  tare da shi da bayansa, babu shakka zai kasance ya na son qananan yara da qaunarsu bari ma dai zai dinga yi musu addu'ar shiriya da taufiqi cikin rayuwa.