فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

DA NAMIJI KO MACE 254

                                           

DA NAMIJI KO MACE              

al'umma ta kasance ta na karkata ga `ya`ya maza a zamanin jahiliya kafin zuwan muslunci don su kasance makomarsu a gobe kan yaqe yaqe da hare hare, sannan sun kasance suna binne `ya`ya mata halin suna raye saboda aqidarsu kan cewa su `ya`ya mata abin kunya ne kansu, sannan suna zama ganimar abokan gaba a fagen yaqi da dalilansu daban daban.

Muslunci ya zo don daukaka matsayin `ya mace, sannan muslunci ya kasance ya na zargin ayyukan jahiliya da motsa zukatansu da alqur'ani:

  وَإذَا المَوْؤُدَةُ سُئِلَتْ * بِأيِّ ذَ نْب قُتِلَتْ[1] 

idan aka tambayi   wadda aka binne ta da ranta * da wanne laifa ne a kasheta.

Muslunci na zargin wadannan da suka kasance idan anyi musu bushara da `ya mace sai fusakensu su turbune  suyi baqi suna halin danne baqin ciki kamar yanda qur'ani ya bamu labarin haka cikin fadinsa madaukaki:

وَإذَا بُشِّرَ أحَدُهُمْ بِالاُ نثَى ظَلَّ وَجْهُهُ مُسْوَدّاً وَهُوَ كَظِيم[2]ٌ 

  idan aka yiwa dayansu bushara da diya mace sai fuskarsa ta yini baqin qirin halin ya na cike da baqin ciki.

 annabin rahama ya zo don shelanta juyin juya halinsa na kawo gyara cikin munanan al'adu na jahiliya, ya ruguje gumakan bauta da qarya qaidoji da sarkokin don `yantar da dan adam daga bautar kansa da bautar wanin ubangiji zuwa bautar ubangiji matsarkaki ya kuma shiryar da shi zuwa tafarkin shiriya da hanya miqaqqa, da bautawa Allah daya tal rak wanda bai haifa ba'a haife shi ba wani tsara bai kasance gareshi ba.

Muslunci ya zo da koyarwa don ya baiwa mace haqqinta da bayyana matsayinta madaukaki cikin al'ummar muslunci da iyali masu riqo da addini.

Muslunci ya zo ya bayyana cewa manufar daukar ciki da haihuwa da abin da za'a haifa ya kasance da qoshin lafiya shi da mahaifiyarsa, babu banbanci cikin kasantuwa abin da aka haifa mace ko namiji muhimmi shi ne nauyaya kan qasa da masu fadin kalmar la'ilaha illallah mace saliha ta fadi kalmar ko namiji salihi babu banbanci sune jigon tarbiyya ingantatta da hukumar addini da taqawa da ayyuka nagari da ilimi mai alfanu cikin dangi da al'umma.

Cikin wannan ma'ana akwai nassosi masu tarin yawa zamu dan kawo kadan daga cikinsu don gudun tsawaitawa:

عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : البنات حسنات والبنون نعمة ، والحسنات يثاب عليها ، والنعمة يُسأل عنها

1 – an karbo daga imam sadiq (as) ya ce: su `ya`ya mata kyawawan ayyuka ne, su kuma maza ni'ima ne , kyawawan ayyuka ana bada lada kansu, ita kuma ni'ima ana tambaya kanta.

بُشّر النبيّ (صلى الله عليه وآله) بابنة ، فنظر في وجوه أصحابه فرأى الكراهية فيهم ، فقال  : ما لكم  ؟ ريحانة أشمّها ورزقها على الله

2 – an yiwa annabi (saw) bushara da `ya mace sai ya kalli fusaken sahabbansa sai ya ga ba sa son abin da aka yi masa bushara da shi, sai ya ce: me ya same ku ne ? fure ne da na ke shaqar qamshinsa arziqinta na wurin Allah.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : نعم الولد البنات المخدّرات ، من كانت عنده واحدة جعلها ستراً له من النار ، ومن كانت عنده اثنتان أدخله الله بهما الجنّة ، وإن كنّ ثلاثاً أو مثلهن من الأخوات وضع عنه الجهاد والصدقة

3 – manzon Allah (saw) ya ce : madalla da `ya`ya mata masu suturce kansu, duk wanda ke da kwaya daya Allah zai sanya ta gareshi hijabi daga wuta, wanda kuma ya ke da biyu Allah zai shigar da shi aljanna albarkacinsu, idan sun kasance uku ko misalinsu daga `yan'uwa mata Allah zai dauke jihadi da sadaka daga kansa.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : خير أولادكم البنات

4 – manzon Allah (saw) ya ce : mafi alherin `ya`yayenku `ya`ya mata.

قال عمر بن يزيد للإمام الصادق (عليه السلام)  : إنّ لي بنات ، فقال له  : لعلّك تتمنّى موتهن ، أما إنّك لو تمنّيت موتهن ، ومتن لم تؤجر يوم القيامة ، ولقيت ربّك حين تلقاه وأنت عاص

5 – umar dan yazid ya cewa imam sadiq (as) lalle ni ina da `ya`ya mata, sai imam ya ce masa: ta yiwu kana fatan mutuwarsu, idan suka mutu Allah ba zai baka lada ba ranar qiyama, sannan zaka gamu da ubangijinka alhalin ka na mai sabo.

وروي عن حمزة بن حمران ، بإسناده ، أ نّه أتى رجل النبيّ (صلى الله عليه وآله) وعنده رجل فأخبره بمولود له فتغيّر لون الرجل ، فقال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : ما لك  ؟ فقال  : خير . قال  : قل . قال  : خرجت والمرأة تمخض ـ  أي تريد وضع حملها  ـ فاُخبرت أ نّها

ولدت جارية ـ  أي بنتاً  ـ فقال له النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : الأرض تقلّها والسماء تظلّها والله يرزقها ، وهي ريحانة تشمّها ، ثمّ أقبل على أصحابه فقال  : من كانت له ابنة واحدة فهو مقروح ، ومن كان له ابنتان فيا غوثاه ، ومن كان له ثلاث بنات وضعه عنه الجهاد وكلّ مكروه ، ومن كان له أربع بنات فيا عباد الله أعينوه ، يا عباد الله أقرضوه ، يا عباد الله ارحموه

 

6 – an rawaito daga hamza dan hirana da isnadinsa, cewa wani mutum ya je wajen annabi (saw) dai dai lokacin da annabi (saw) ya ke tare da wani sai wannan wanda ya zo ya baiwa wanda ke zaune labarin haihuwar matarsa take fuskarsa ta turnuke ta canja, sai annabi (saw) ya tambaye shi me ya faru da kai ? sai ya ce babu komai, sai annabi (saw) ya ce masa ka fada, sai ya ce na fito alhalin mata ta tana naquda to shi ne yanzu aka bani labarin cewa ta haifi mace, sai annabi (saw) ya ce: `ya mace qasa na daukarta sama na lullubeta da inuwa Allah na azurta ta, ita fure ce da zaka dinga shaqar qamshinta, sai ya fuskanci sahabbansa ya ce: duk wanda ke `ya guda daya ya na da ciwo, wanda ya ke da guda biyu ya na buqatar tallafi da kawo masa dauki, wanda ke da guda uku an dauke masa jihadi da dukkanin abin qi, wanda kuma ya ke da guda hudu ya ku bayin Allah ku tausaya masa ku taimake shi ku bashi rance.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : من عال ثلاث بنات أو ثلاث أخوات وجبت له الجنّة ، قيل  : يا رسول الله واثنين  ؟ قال  : واثنين ، قيل  : يا رسول الله وواحدة  ؟ قال  : وواحدة

7 – a wani wajen kuma (saw)  ya ce: duk wanda ya ciyar da `ya`ya mata uku aljanna ta wajaba gareshi, sai aka ce ya manzon Allah wanda ya ke da guda biyu fa ? sai ya ce: shi ma ta wajaba gareshi, aka qara cewa wanda ke da guda daya fa ? ya ce: shi ma ta wajaba gareshi.

Wannan duka cikin falalar `ya`ya mata kenan, don a san cewa muhimmi bawai kasantuwar abin da ka Haifa ya zama na miji ba shi ne kawai abin buqata ba, muhimmi shi ne abin da ka Haifa ya zamanto cikin qoshin lafiya kamar yanda ya zo cikin littafin almahasin:

كان عليّ بن الحسين زين العابدين (عليه السلام) إذا بُشّر بولد لم يسأل أذكر هو أم اُنثى ، بل يقول  : أسويّ  ؟ فإذا كان سويّاً ـ  أي لا عيب فيه ويخرج بسلامة  ـ قال  : « الحمد لله الذي لم يخلقه مشوّهاً

8 – ali dan husaini zainul abidin (as) ya kasance idan an yi masa bushara da abin haihuwa ba ya tambayar shin namiji ko mace ce, kadai dai ya na tamabayar shin ya na cikin qoshin lafiya bai da wata naqasa? idan aka ce masa na'am, sai ya ce: godiya ta tabbata ga Allah wanda bai halicce shi da muni ba.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : إنّ الله تعالى على الإناث أرأف منه على الذكور وما من رجل يدخل فرحة على امرأة بينه وبينها حرمة إلاّ فرّحه الله يوم القيامة

9 –  manzon Allah (saw) ya ce: lalle Allah madaukaki ya na tausayawa `ya`ya mata fiye da yadda ya ke tausayawa maza, babu wani namiji da zai farantawa mace wadda tsakaninsu akwai haramcin aure face Allah ya faranta masa ranar alqiyama.

الكافي  : عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : نِعمَ الولد البنات ملطفات مجهّزات ـ  أي مهيّات الاُمور  ـ مؤنسات مباركات مفليّات

10 -  alkafi : daga baban abdullah (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: madalla da `ya`ya mata masu tausayi, masu shirya al'amari, masu debe haso masu albarka.

عن الجارود بن المنذر قال  : قال لي أبو عبد الله (عليه السلام)  : بلغني أ نّه ولد لك ابنة فتسخطها ، وعليك منها ريحانة تشمّها وقد كفيت رزقها وقد كان رسول الله أبا بنات

11 – daga jarud dan munzir, ya ce: baban Abdullah (as) ya ce mini : labari ya iso mini cewa ka na da `ya mace amma ka na baqanta mata rai, ka na da fure daga gareta wanda zaka dinga shaqar qamshinsa kuma haqiqa waninka ya dauke maka arziqinta haqiqa manzo Allah ya kasance uba ga `ya`ya mata.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : إنّ إبراهيم (عليه السلام) سأل ربّه أن يرزقه ابنة

تبكيه وتندبه بعد موته

12 – an karbo daga baban Abdullah (as) ya ce: lalle Ibrahim (as) ya roqi ubangijinsa da ya azurta shi da `ya mace wadda za ta dinga kukan rashinsa bayan mutuwarsa.

الكافي بنسده عن الكرخي عن ثقة من أصحابنا قال  : تزوّجت بالمدينة فقال لي أبو عبد الله (عليه السلام)  : كيف رأيت  ؟ قلت  : ما رأى رجل من خير في امرأة إلاّ وقد رأيته فيها ولكن خانتني ، فقال  : وما هو  ؟ قلت  : ولدت جارية ، قال  : لعلّك كرهتها إنّ الله تعالى يقول  : (  آباؤُكُمْ وَأبْناؤُكُمْ لا تَدْرونَ أ يّهُمْ أقْرَبُ لَكُمْ نَفْعا[3]ً

13 – alkafi da isnadinsa daga karaki daga yardaddu daga sahabban mu ya ce: na yi aure a madaina sai baban Abdullah (as) ya ce mini: ya ya ka gani ? sai n ace: banga wani alheri daga namiji face na ganshi cikin mace sai dai cewa ta ha'ince ni, sai imam ya ce: menene ? sai na ce ta haifi `ya mace, sai imam ya ce: ta yiwu kai baka sonta lalle Allah madukaki na cewa:

babanninku da `ya`yayenku ba ku san wadanda su ka fi kusa da  alfanu gareku ba.

 ma'ana iyayenku da `ya`yayenku ba ku san gwargwadon alfanunsu gareku ba kuma baku san cikinsu wanene ya fi alfanu ba, haka al'amarin ya ke cikin `ya`ya maza da `ya`ya mata ta yiwu mace ta fi amfani ga iyayenta daga da namiji, ta yiwu da namji ya fi cutarwa ga iyayensa daga `ya mace, ya kamata miji da mata su yarda da abin da ubangiji ya zaba musu ya azurta su da shi mace ne ko namiji babu banbanci.

 الكافي بسنده عن الحسن بن سعيد اللحمي قال  : ولد لرجل من  أصحابنا جارية فدخل علي أبي عبد الله (عليه السلام) فرآه متسخّطاً فقال له أبو  عبد  الله (عليه السلام)  : أرأيت لو أنّ الله أوحى إليك أن أختار لك أو تختار لنفسك ما  كنت تقول  ؟ قال  : كنت أقول يا ربّ تختار لي ، قال  : فإنّ الله قد اختار لك ثمّ قال  : إنّ الغلام الذي قتله العالم الذي كان مع موسى (عليه السلام) وهو قول الله عزّ وجلّ  : (  فَأرَدْنَا أنْ يبدلهما ربّهما خيراً منهُ زكاةً وأقرب رُحماً  ) أبدلهما الله به جارية ولدت سبعين نبيّاً

14 – alkafi – da isnadinsa daga hassan dan said   ya ce: an haifarwa daya daga cikin sahabban mu `ya mace, sai ya shiga wajen  baban abdullah  (as) sai imam ya ganshi cikin fushi sai imam ya ce masa: shin da Allah zai aiko maka da wahayi kan ya zabar maka ko kuma kai ka zaba da kanka me za ka ce? sai ya ce: zance ya ubangiji ka zabar mini, imam ya ce: lalle yaro nan wanda wannan malami da  ke tare da annabi musa (as) cikin tafiyarsu ya kashe, cikin fadin Allah madaukaki:

sai mu ka nufi ubangijinsu ya sauya musu ga  mafi alheri daga gareshi da zai zama tsarkakuwa  da mafi kusanta da tausasawa.

 sai Allah ya sauya musu da `ya mace wacce ta haifi annabawa har guda saba'ain.

الفقيه عن الصادق (عليه السلام) قال  م من عال ابنتين أو اُختين أو عمّتين أو خالتين حجبتاه من النار ـ  من أعال أي أنفق وتكفّل بحياتهما المعيشيّة  ـ

15 – alfaqihu  daga sadiq (as) wanda ya ciyar da `ya`ya biyu mata ko `yan'uwansa mata biyu ko goggwaninsa biyu ko `yan'uwan mahaifiyarsa biyu za su yi masa hijabi daga wuta.

الفقيه  : قال (عليه السلام)  : إذا أصاب الرجل ابنة بعث الله عزّ وجلّ إليها ملكاً فأمرّ جناحه على رأسها وصدرها وقال  : ضعيفة خلقت من ضعف ، المنفق عليها مُعان[4]

16 – alfaqihu sadiq (as) ya ce: idan aka haifawa mutum `ya mace Allah ya na aiko da mala'ika zuwa gareta ya shafa fuffukensa kanta da qirjinta ya ce rarrauna an halicceta daga rauni, duk wanda ya ciyar da ita Allah zai taimake shi.[1] Takwir:9-8

[2] Annahl:58

[3] Baqara:216

[4] Alwafi m 12 sh 1306