فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I 267

MUQAMI NA 5

TASIRIN ABINCI KAN MATA MASU CIKI DA YARA DA JIMA'I

Lalle abinci na da tasiri matuqa cikin jiki dan adam da ruhinsa kamar yadda dabi'a da ilimin likitanci ya yi shaida kan haka da kuma abubuwan da suka zo daga hadisai masu daraja, ga kadan daga cikin abincin da ke da tasiri kebantacce ga masu dauke da ciki da yara kamar yadda ya zo a hadisi:

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : كلوا السفرجل وتهادوه بينكم ، فإنّه يجلو البصر وينبت المودّة في القلب ، وأطعموه حبالاكم ، فإنّه يحسّن أولادكم ، وفي رواية  : يحسّن أخلاق أولادكم

1 – manzon Allah (saw): ku ci safarjal ku yi hadayarsa tsakaninku lalle shi yana ya ye gani ya na kuma tsirar da qauna cikin zuciya, ku baiwa matanku masu ciki, lalle ya na kyawunta `ya`yayenku, a wata riwayar: ya na kyawunta dabi'un yaranku.

عن الصادق (عليه السلام) ، أ نّه نظر إلى غلام جميل ، فقال  : ينبغي أن يكون أبو  هذا أكل سفرجلا ليلة الجماع

2 – daga sadiq (as) : yayin da ya kalli wani kyakkyawan yaro, sai ya ce: da gani baban wannan yaro ya ci safarjal a daren da ya kusanci iyalinsa.

الكافي عبد أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : قال أمير المؤمنين (عليه السلام)  : خير تموركم البرني فأطعموه نساءكم في نفاسهن يخرج الولد ذكيّاً حليماً ، وفي خبر آخر  : حكيماً .

3 – alkafi daga baban Abdullah (as) ya ce: sarkin muminai ali (as) ya ce: mafi alherin dabinonku barrani ku ciyar da matanku kwanakin nifasinsu yaro zai zamanto mai kaifin basira da haquri.

عن أمير المؤمنين (عليه السلام) قال  : قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : ليكن أوّل ما تأكل النفساء الرطب فإنّ الله تعالى قال لمريم  : (  وَهُزِّي إلَيْكِ بِجِذْعِ النَّخْلَةِ تسَاقط عَلَيْكِ رُطَباً جَنِيَّاً  ) قيل  : يا رسول الله فإن لم يكن أوان الرطب  ؟ قال  : تسع تمرات من تمرات المدينة ، فإن لم تكن فتسع تمرات من تمر أمصاركم فإنّ الله تعالى يقول  : وعزّتي وجلالي وعظمتي وارتفاع مكاني لا تأكل نفساء يوم تلد الرطب فيكون غلاماً إلاّ كان حليماً وإن كانت جارية كانت حليمة

4 – daga sarkin muminai ali (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: ya kamata ace farkon abin da mai nifasi za ta fara ci ya kasance danyen dabino lalle ubangiji na cewa:

 ( kuma ki girgiza kutturen dabino zuwa gareki ya zubar da `ya`yan dabino kanki nunannu.

 sai aka ce ya manzon Allah idan kuma bai kasance yana da dan dabino nunanne ba fa? sai ya ce: ta ci busashshen dabinon madina kwaya tara, akace idan kuma ba a samu na madina ba fa, sai y ace: ta ci kwaya tara daga busashshen dabinon garuruwanku, lalle Allah madaukaki na cewa na rantse da izzata da girmana da daukakar matsayina mai nifasi ba za ta ci nunannen dabino ranar da za ta haihu ba kuma ta haifi da namiji face ya kasance mai haquri idan mace ce ta kasance mai haquri.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : كلوا التين الرطب واليابس ، فإنّه يزيد في الجماع ...

5 – manzo Allah (saw) :  ku ci danyen baure da busashshe, lalle shi ya na qara qarfin jima'i.

عن الصادق (عليه السلام)  : في البصل ثلاث خصال  : يطيّب النكهة ، ويشدّ اللثّة ، ويزيد في الجماع

6 – daga sadiq (as) cikin albasa akwai abubuwa uku: tana kyawunta qamshin baki, qarfafa dadashi, qara qarfi cikin jima'i.

عن داود بن فرقد ، قال  : دخلت على أبي عبد الله (عليه السلام) وبين يديه جزر ، قال  : فناولني جزرة وقال  : كل . فقلت  : إنّه ليس لي طواحن ، فقال  : أما لك جارية . قلت  : بلى . قال  : مرها أن تسلقه وكله ، فإنّه يسخن الكليتين ويقيم الذكر .

7 – daga dauda dan farqad, ya ce: na shiga wajen baban Abdullah (as) sai ya bani dan itaciyar karas sai na ce bani da masu niqe shi, sai ya ce  ba ka da kuyanga, sai nace ina da ita, sai ya ce ka umarce ta da dafama ka ci, lalle shi yana dumama qoda ya na qarfafa da tsayar da azzakari.

وقال (عليه السلام)  : الجزر أمان من القولنج والبواسير ويعين على الجماع .

8 – manzon Allah (saw) ya ce: karas aminci ne daga ciwon qarzuwa da basir ya na kuma taimakawa lokacin jima'i.

ـ عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : كلوا البطّيخ فإنّ فيه عشر خصال مجتمعة  : ... ويزيد في الباه

9 – sadiq (as) ya ce : ku ci kankana, lalle cikin akwai abubuwa goma daga ciki ya na qara qarfin da namiji.

قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : أطعموا نساءكم الحوامل اللبان ، فإنّه يزيد في عقل الصبي .

10 – annabi (saw) ya ce : ku ciyar da matanku masu dauke da ciki qaro lalle shi ya na qara kaifin hankalin yaro.

 عن الرضا (عليه السلام) ، قال  : أطعموا حبالاكم اللبان ، فإن يكن في بطنهن غلام خرج ذكيّ القلب عالماً شجاعاً ، وإن يكن جارية حسن خَلقها وخُلقها وعظمت عجيزتها وحظيت عند زوجها ـ  أي سعدت به ودنت من قلبه وأحبّها ، واللبان  : الكندر 

11 – an karbo daga rida (as) ya ce: ku ciyar da matanku masu dauke da ciki qaro, iadan ya kasance akwai yaro a cikinsu to zai fito daga cikinsu yna mai basira zuciya saduki masani, idan kuma mace ce za ta kasancemai kyawun halitta da dabi'a , za ta azurta da mijinta ta kusanci zuciyarsa ya kuma dinga sonta.

قال أبو الحسن (عليه السلام)  : لا تدع العشاء ولو بكعكة ، فإنّ فيه قوّة الجسد ولا أعلمه إلاّ قال  : وصلاح للزواج بل للجماع

12 – baban hassan (as) ya ce: ka da ku bar cin abincin dare ko da cake  lalle cikinsa akwai qarfin jiki da gyara ga miji da jima'i.

قال أبو الحسن (عليه السلام)  : من أكل البيض والبصل والزيت زاد في جماعه ، ومن أكل اللحم بالبيض كبر عظم ولده

13 – baban hassan (as) ya ce : duk wanda ya ci kwai da albasa da mai zai qaru cikin jima'insa, duk wanda ya ci kwai da nama qashin dansa zai girma.

عن بعض أصحاب أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال له  : جعلت فداك ، إنّي أشتري الجواري فاُحبّ أن تعلّمني شيئاً أتقوّى به عليهن  ؟ قال  : خذ بصلا وقطّعه صغاراً صغاراً وأقله بالزيت ، وخذ بيضاً فافقصه في صفحة وذر عليه شيئاً من الملح فاذرره على البصل والزيت وأقله شيئاً ثمّ كل منه ، قال  : ففعلت فكنت لا اُريد منهن شيئاً إلاّ وقدرت عليه

14 – daga ba'arin sahabban baban abdullah (as) dayansu ya ce masa raina fansarka ., lalle ni ina sayen kuyangu ina son ka sanar dani wani abu da zan qarfafa da shi kansu? sai ya ce: ka nemi albas aka yayyanka ta qanana ka soya da mai , sannan ka nemi kwai ka gutsitstsirashi cikin akushi ka zuba masa gshiri sannan ka zuba kan albasa da mai ka dan soya shi kadan sannan ka ci , sai ya aikata haka , ya ce sai na kasance ba neman wani daga garesu face na samu iko kai.

نهى النبيّ (صلى الله عليه وآله) عن الأكل على الجنابة ، وقال  : إنّه يورث الفقر

15 – manzon Allah (saw) ya yi hani daga cin abinci a halin janaba, ya ce : ya na gadar da talauci.

Da wani likita zai dauki wannan riwayoyi ya duba da idon basira da ya gano abubuwa da wani bai gabace shi ganowa ba , ko da ya ma ya gabace shi to zai san cewa abin da waninsa  ya gano tuntuni akwai shi cikin riwayoyin a'imma (as) fiye da daruruwan shekaru da suka gabata , wannan al'amari mai ban sha'awa na girmama matsayin muslunci cikin zukata musammam cikin wannan zamani da muke ciki da ake qiyasin abub

uwa da qiyasin zahiri tsantsa.