فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

SHAYARWA 270

MUQAMI NA 7

                                             SHAYARWA

Daga al'amarin da muslunci ya himmatu da shi matuqar himmatuwa cikin rayuwar aure da cikin tarbiyya shi ne batun shayarwa, muslunci ya sanya masa iyakoki da ladubba da muqaddimomi da natijoji, daga abin da ke jawo hankalin mai karatu da mai kasa kunne da zurfafawa cikin batun da ba da kaso mai girma daga himmatuwa da damuwa da shi  cikin rayuwarsa, ya kamata ya kiyaye batun shayarwa tun gabanin yin aure sakamkon abubuwan da ke biye da ita daga kyawawan tasiri na yanayi da munana.

mai ya fi yawa daga hadisai masu daraja da qissoshin tarihi cikin wannan babi.

عن الإمام الصادق (عليه السلام) ، عن أبيه (عليه السلام) ، قال  : إنّ علياً (عليه السلام) كان يقول ـ  وهذا يدلّ على الاستمرار ، أي كان دائماً يقول  ـ  : لا تسترضعوا الحمقاء ، فإنّ اللبن يغلب الطباع .

1 – daga imam sadiq (as) daga babansa (as) ya ce: lalle ali (as) ya kasance ya na cewa ka da ku bawa mata wawaye shayarwa, lalle shi ne nono na galaba cikin dabi'a.

وقال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : لا تسترضعوا الحمقاء ، فإنّ الولد يشبّ عليه

2 – manzon Allah (as) ya ce: ka da ku baiwa wawaye shayarwa lalle shi yaro ya na girma kansa.

وقال (صلى الله عليه وآله)  : توقّوا على أولادكم من لبن البغية والمجنونة ، فإنّ اللبن يعدي

3 – manzo Allah (saw) ya ce : ku kiyaye `ya`yanku daga nonon karuwa da mahaukaciya lalle shi ne na cira daga muhalli zuwa muhalli.

Allah madaukaki na cewa:

وَالوَالِدَاتُ يُرْضِعْنَ أوْلادَهُنَّ حَوْلَيْنِ كَامِلَيْنِ لِمَنْ أرَادَ أنْ يُتِمَّ الرَّضَاعَةَ وَعَلَى المَوْلُودِ لَهُ رِزْقُهُنَّ وَكِسْوَتُهُنَّ بِالمَعْرُوفِ لا تُكَلَّفُ نَفْسٌ إلاَّ وُسْعَهَا لا تُضَارَّ وَالِدَةٌ بِوَلَدِهَا وَلا مَوْلُودٌ لَهُ بِوَلَدِهِ وَعَلَى الوَارِثِ مِثْلُ ذَلِكَ فَإنْ أرَادَا فِصَالا عَنْ تَرَاض مِنْهُمَا وَتَشَاوُر فَلا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا وَإنْ أرَدْتُمْ أنْ تَسْتَرْضِعُوا أوْلادَكُمْ فَلا جُنَاحَ

عَلَيْكُمْ إذَا سَلَّمْتُمْ مَا آتَيْتُمْ بِالمَعْرُوفِ وَاتَّقُوا اللهَ وَاعْلَمُوا أنَّ اللهَ بِمَا تَعْمَلُونَ بَصِير[1]ٌ 

  uwaye mata suna shayar `ya`yansu shekaru biyu kammalallu ga wadanda suka so cika shayarwa * a kan wanda aka haifa masa da ciyarwarta da tufafinta da alheri ba a dorawa rai face abin da ta ke iko kai ba'a cutar da mahaifiya game da danta haka nahaifi game da dansa  akan magaji akwai misalin wancan idan suka nufi yayewa a kan yarda da shawartar juna babu laifi kansu idan kun yi nufin ba da shayar da `ya`yanku babu laifi kanku idan kuka miqa abin da kuka zo da shi da alheri kuji tsoron Allah ku sani Allah na ganin abin da kuke aikatawa.

وَفِصَالُهُ فِي عَامَيْنِ[2] 

 (yaye shi shekaru biyu)

وَحَمْلُهُ وَفِصَالُهُ ثَلاثُونَ شَهْرا[3]ً 

  ( cikinsa da yaye shi watanni talatin )

فَإنْ أرْضَعْنَ لَكُمْ فَآ تُوهُنَّ اُجُورَهُنَّ وَأتَمِرُوا بَـيْنَكُمْ بِمَعْرُوف وَإنْ تَعَاسَرْتُمْ فَسَتُرْضِعُ لَهُ اُخْرَى * لِـيُـنفِقْ ذُو سَعَة مِنْ سَعَتِه[4] 

(idan suka shayar muku ku basu ladansu, kuyi shawara tsakaninku da sananne al'amari idan kuka nuna tsanani to wata za ta shayar saboda miji  ma'bocin yalwa ya ciyar daga yalwarsa.

Zancen mu kan shayarwa ba bisa la'akari da hukunce hukuncenta ba na fiqihu da shari'a kamar haramcin wadda kuka sha nono tare da wadda ta shayar da dai makamancin haka, bari dai bisa la'akari da bangare kyawawan dabi'u da ma'anawiya, kamar misalin ka da ku baiwa wawaye shayarwa  lalle shi ne nono na tasiri da yaduwa ya taso daga wawiya zuwa yaron da ta shayar.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : ليس للصبيّ لبن خير من لبن اُمّه

5 – manzon Allah (saw) ya ce: yaro bai da nonon da ya fi na mahaifiyarsa.

Wannan ma'ana hatta cikin ilimin likitanci ta tabbata.

قال أمير المؤمنين عليّ (عليه السلام)  : ما من لبن يرضع به الصبيّ أعظم بركةً عليه من لبن اُمّه[5]

6 – sarkin muminai ali (as) y ace: babu wani nono da za'a shayar da yaro da ya fi nonon mahaifiyarsa albarka gareshi.

الكافي بسنده عن محمّد بن العباس بن الوليد عن أبيه عن اُمّه اُمّ إسحاق بنت سليمان قالت  : نظر إليّ أبو عبد الله (عليه السلام) وأنا أرضع أحد ابني محمّداً أو إسحاق فقال  : يا اُمّ إسحاق ، لا ترضعيه من ثدي واحد وارضعيه من كليهما يكون

أحدهما طعاماً والآخر شراباً

7 – alkafi da isnadinsa daga muhammadu dan abbas dab walid daga babansa daga babarsa ummu is'haq `yar sulaiman, ta ce: baban abdullah (as) ya kalle ni yayin da na shayar da daya daga cikin `ya`yana, sai ya ce: ya ummu is'haq ka da ki dinga shayar da shi daga nono guda ki shayar da shi daga duka biyun, daya zai kasance abinci gareshi daya ruwan sha.

عن أبي عبد الله (عليه السلام)  : الرضاع واحد وعشرون شهراً ، فما نقص فهو جور على الصبي

8 – an karbo daga baban abdullah (as): shayarwa watanni ishirin da daya ya ke duk abin da ya shallake haka to zai zama zalunci kan yaro.

الفقيه عن سعد بن سعد عن أبي الحسن الرضا (عليه السلام) قال  : سألته عن الصبي هل يرضع أكثر من سنتين  ؟ فقال  : عامين . قلت  : فإن زاد على السنتين هل على أبويه من ذلك شيء  ؟ قال  : لا

 9 – alfaqihu – daga said dan baban hassan arrida (as) ya ce:  na tambaye shi game da yaro shin ya na halasta a shayar da shi fiye da shekaru biyu ? sai ya ce: shekaru biyu, sai na ce : idan ya wuce haka  shin iyayensa na da haqqin yin haka ? sai ya ce: a'a.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : سألته عن مظائرة المجوسي  ؟ قال  : لا ولكن أهل الكتاب

10 – daga baban Abdullah (as) na tambaye shi kan  baiwa bamujusiya shayarwa sai ya ce : a'a , sai dai ma'abota littafi.

عن الحلبي قال  : قلت لأبي عبد الله (عليه السلام)  : امرأة ولدت من الزنا اتّخذها ظئراً 2؟ قال  : لا تسترضعها ولا ابنتها

11 – daga halabi ya ce: na cewa baban Abdullah (as) mace ce aka haifata daga zina shin zan iya bata shayarwa? sai ya ce: ka da ka bata shayarwa haka ma ka da ka baiwa `yar da ta haifa.

قال رسول الله (صلى الله عليه وآله)  : لا تسترضعوا الحمقاء والعمشاء فإنّ اللبن يعدي وإنّ الغلام ينزع إلى اللبن يعني إلى الظئر في الرعونة

12 – manzon Allah (as) ya ce: ka da ku baiawa wawiya da mai  raunin ido shayarwa, lalle shi nono na yaduwa shi yaro na fusguwa zuwa ga nono da ya sha da dabi'un mai shayarwa.

عن أبي جعفر (عليه السلام)  : استرضع لولدك بلبن الحسان وإيّاك والقباح فإنّ اللبن قد يعدي

13 – daga baban jafar (as) ka shayar da danka da nonon kyawawan mata na haneka da shayar da shi daga munana, lalle shi ne nono ya na yaduwa.

وقال (عليه السلام)  : عليكم بالوضاء من الظؤورة فإنّ اللبن يعدي

14 – manzon Allah (saw) : na umarce ku da kyakkyawa daga mai shayarwa lalle shi nono ya na yaduwa.

قال الصادق (عليه السلام)  : يحرم من الرضاع ما يحرم من النسب ، ولا يحرم من الرضاع إلاّ رضاع خمسة عشر يوماً ولياليهن ليس بينهن رضاع

15 – sadiq (as) ya ce: duk abin da ya haramta cikin nasaba ya haramta cikin shayarwa, sannan haramci bai tabbata cikin shayarwa sai idan shyarwa ta kasance sau goma shabiyar  dare da rana sannan kuma ka da wata shayarwa ta shiga tsakani.[1] Baqara:233

[2] Luqman:14

[3] Ahqaf:15

[4] Addalaq: 6 7

[5] Alwafi m 2 sh 1363