فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

TAYA MURNA DA SAMUN DA 279

MUQAMI NA 9

                                                                               TAYA MURNA DA SAMUN DA  

daga cikin ladubba da al'adun zamantakewa wanda muslunci ya tabbatar da su shi ne taya murna, ya kamata `yan'uwa makunsanta da abokai da makota su taya iyali murna samun azutuwa da haihuwa , wannan al'adace mai kyawu wadda ke gudana dukkanin garuruwa , kadai akan samu dan banbanci cikin yanayi yadda kowacce al'umma ta ke yin nata taya murnar ta hanyar amfani da lafuzza da kalmomi mabambanta .

muslunci ya zo ya ladabtar da wadanda suka rungume shi da ladubban zamantakewa daga cikinsu yadda ake taya murna da amfani kalmomi da suke tattare da ma'anoni da ke bayyana aqida da qa'idoji, ya zama dole amfani da lafuzzan muslunci  wadanda suke labartar da aqidar da imanin mai magana.

عن الإمام الصادق (عليه السلام) ، قال  : هنّأ رجل رجلا أصاب ابناً ، فقال  : أهنئك الفارس . فقال له الحسن بن عليّ (عليهما السلام)  : ما أعلمك أن يكون فارساً أو راجلا  ؟ ـ  أي هذا من المستقبل المجهول لعامة الناس  ـ فقال له  : جعلت فداك فماذا نقول  ؟ قال  : تقول  : شكرت الواهب وبورك لك في الموهوب وبلغ أشدّه ورزقت برّه

1 – ankarbo daga imam sadiq (as) ya ce: wani mutum ya taya abokinsa da ya samu qaruwa da da murna sai ya ce: ina taya ka murnar samun jarumi mahayin doki sai hassan dan ali (as) ya ce: me ya sanar da kai cewa mahayin doki ne ko kuma mai tafiya da qafafuwansa ne, sai mutumin ya ce : to qaqa za mu ce : imam ya ce : ku ce: na godewa ma'abocin kyauta Allah ya sany maka albarka cikin abin da ya ba ka ya isar da girmansa ya kuma azurtaka da biyayyarsa.

Da wannan ne imam ya koyar da mu cewa da fari mu fara godiya ga Allah bisa ni'imominsa masu tarin yawa daga cikinsu wannan yaro sabo da a ka haifa , sannan ranar fari muyi masa addu'a da Allah ya sanya masa albarka  cikin aryuwarsa ta ilimi da aiki ya kasance dan da aka haifa kayautace da Allah ya bashi kamar yadda ya zo cikin fadinsa:

يَهَبُ لِمَنْ يَشَاءُ إنَاثاً وَيَهَبُ لِمَنْ يَشَاءُ الذُّكُور[1] 

 ya na ba da kyautar `ya`ya mata ga wanda ya so, ya ba da `ya`ya maza ga wanda ya so.

albarkantacce wanda rayuwarsa za ta tsawaita har zuwa girmasa da cikar hankalinsa, haka Allah ya zaurta shi da`arsa ya kasance mai da'a ga iayaensa bai kasance mai  girman kai shaqiyyi ba da sabawa iyayensa.

Mai ya fi kyawu daga muslunci mai girma, tabbas kalaman imam jagoran kalamai, lalle kalaman imamai tsarkaka (as) haske ne da ake haskaka da su cikin kowanne fage a rayuwa duniya da lahira.[1] Shura:49