فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

AQIQA 281

MUQAMI  NA 10

                                                    AQIQA

daga cikin ladubban muslunci akwai aqiqa, yanka dabba saboda yaron da ka haifa, cikin wannan fage akwai riwayoyi masu tarin yawa da suke ishara kan cewa aqiqa ta na da wani tasiri a rayuwance duniya da lahira, malamai sun samu sabani kan hukuncinta cikinsu akwai wanda suka tafi kan cewa wajibi ce wasunsu kuma suka zabi kasantuwarta mustahabbi da aka qarfafa aikata shi kamar yanda hakan shi ne mafi rinjaye.

 ya zo cikin littafin alfaqihu  da isnadinsa ya ce: (yanka aqiqa wajibi ne idan akai maka haihuwa  sai dai cewa abin da ake nufi da wajibi anan shi ne musatahabbi mai qarfi mai littafin kifaya ya ce: malamai sunyi sabani kan wajabcin aqiqa da mustahabbancinta, sayyid murtada alamul huda da dan junaidu sun tafi kan wajabci, sayyid ya yi da'awar ijma'in malaman imamiya kan wajabcinta sakamkon abin da ya zo daga zahirin umarni daga riwayoyi masu tarin yawa da suka tabbatar da wajabcinta, sai dai cewa wadannan riwayoyi na buqatar duba isnadinsu da dilala.

shaik da malaman da suka zo daga bayansa sun tafi kan mustahabbancita sakamakon raunin riwayoyin da suke ishara kan wajabci, ya zo cikin wasu riwayoyin cewa aqiqa ta fi layya zama wajibi, ita layya mustahabbi ce wajen galibin malamai.

ya zo cikin muwassaqatu ammar sabadi daga littafin alfaqihu cewa: idan bai yanka ma abin haihuwar aqiqa ba har  lokacin layya to layyan ya isar, abin da zamu fa'idantu daga wannan riwaya shi ne cewa: ita aqiqa mustahabbi ce saboda da ba ta kasance mustahabbi ta da yankan layya ba ta isar daga gareta ba.

ga jumla daga riwayoyin da suka yi magana kan aqiqa:

عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : كلّ امرئ يوم القيامة مرتهن بعقيقته ، والعقيقة أوجب من الأضحية . أي أهمّ منها

 

1 – an karbo daga baban abdullah (as) : duk wani mutumin ranar alqiyama ya jingine da aqiqarsa, aqiqa ta fi zama wajibi daga layya.

وعنه (عليه السلام) ، قال  : كلّ إنسان مرتهن بالفطرة ـ  فإنّ كلّ مولود يولد على فطرة التوحيد والإيمان الكامل  ـ وكلّ مولود مرتهن بالعقيقة

2 – daga gareshi (as) ya ce: duk wani mutum na jingine da halittarsa, duk wani da ana haifarsa kan halittar tauhidi da kammallen  imani, duk wani da jingine ya ke da aqiqa.

عن عمر بن يزيد ، عن أبي عبد الله (عليه السلام) ، قال  : قلت له  : إنّي والله ما  أدري أكان أبي عقّ عنّي أم لا  ؟ فأمرني فعققت عن نفسي وأنا شيخ .

3 – daga umar dan yazid, daga baban abdullah (as) ya ce: na ce ma imam ni wallahi ban sani ba shin babana ya yi mini aqiqa ko bai ba? sai imam ya umarce ni na yi aqiqa alhalin na riga na tsufa.

عن عليّ بن أبي حمزة ، عن العبد الصالح (عليه السلام) ، قال  : العقيقة واجبة إذا ولد للرجل ولد ، فإن أحبّ أن يسمّيه في يومه فليفعل

4 – daga ali dan baban hamza daga baban salihu (as) ya ce: aqiqa wajibi ce idan aka yiwa mutum haihuwa, idan ya na sha'awa da ya rada masa suna tun ranar da aka haifi yaron to ya akata hakan.

عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : العقيقة لازمة لمن كان غنياً ، ومن كان فقيراً إذا أيسر فعل ، فإن لم يقدر على ذلك فليس عليه ، وإن لم يعقّ عنه حتّى ضحّى عنه فقد أجزأته الاُضحية ، وكلّ مولود مرتهن بعقيقته

5 – an karbo daga sadiq (as) ya ce: aqiqa wajibi ce ga wanda ya ke da wadata, wanda ya ke talaka kuma idan ya samu budi to ya yi, idan kuma bai samu iko ba to ta sauka daga kansa, idan kuma bai yi aqiqa har ya yanka layya to layyan ta isar masa, dukkanin abin haihuwa na jingine da aqiqarsa.

وقال (عليه السلام) في العقيقة  : يذبح عنه كبش ، فإن لم يوجد كبش أجزأ ما  يجزئ في الأضحية وإلاّ فحَمَل ، أعظم ما يكون من حملان السنّة .

6 – imam (as) yana cewa: cikin aqiqa: ana yankawa yaro rago, idan kuma ba'a samu rago to a yanka dukkanin abin da ake yankawa cikin layya idan kuma ba'a samu ba to ana iya yanka dan tunkiya, mafi girman abun shi ne dan tunkiya guda biyu.

وعنه (عليه السلام) ، سئل عن العقيقة  ؟ قال  : شاة أو بقرة أو بدنة ـ  الجمل أو  الناقة  ـ ثمّ يسمي ويحلق رأس المولود يوم السابع ، ويتصدّق بوزن شعره ذهباً أو فضّة ، فإن كان ذكراً عقّ عنه ذكراً وإن كانت اُنثى عقّ عنه اُنثى

7 – an tambayi imam (as) game da aqiqa? sai ya ce:  akuya ko sanuwa ko raqumi, sannan a radawa yaro suna a yi masa aski rana ta bakwai da haihuwarsa a auna nauyi gashinsa a ba da sadaka da zinari ko azurfa gwargawadon nauyin gashin, idan namiji a yi masa aqiqa da dabba namiji idan mace ce ayi mata da dabba mace.

وعقّ أبو طالب عن رسول الله (صلى الله عليه وآله) يوم السابع فدعا آل أبي طالب ، فقالوا  : ما هذه  ؟ فقال  : عقيقة أحمد ، قالوا  : لأي شيء سمّيته أحمد  ؟ فقال  : ليحمده أهل السماء والأرض

8 – abu dalib ya yiwa manzon Allah (saw) aqiqa rana ta bakwai da haihuwa, sai mutane suka ce meye wannan sai ya ce musu: aqiqar ahmad, suka ce saboda me ka rada masa suna ahmad, sai ya ce musu saboda don mazauna sama da qasa su yi masa godiya.

daga cikin mustahabbin aqiqa shi ne a baiwa unguwar zoma wani kaso daga ciki ragowar kuma a ciyar da shi ga masoya ahlul baiti (as)

عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : يعطى للقابلة ربعها ، فإن لم تكن قابلة فلاُمّه تعطيها من شاءت وتطعم منها عشرة من المسلمين ، فإن زاد فهو أفضل

9 – daga sadiq (as) ya ce: ana baiwa unguwar zomo kashi daya cikin hudu daga  aqiqar da aka yanka, idan kuma babu unguwar zoma to ya rage ga uwar yaro ta iya baiwa duk wadda ta so sannan kuma ta ciyar da mutane goma daga musulmai idan kuma sun haura goma hakan aka fi so.

وعنه (عليه السلام) ، قال  : يسمّى الصبيّ يوم السابع ويحلق رأسه ويتصدّق بزنة الشعر فضّة ويعقّ عنه بكبش فحل ، ويقطع أعضاءه ويطبخ ويدعى عليه رهط من المسلمين ، فإن لم يطبخه فلا بأس أن يتصدّق به أعضاء ، والغلام والجارية في ذلك سواء ، ولا يأكل من العقيقة الرجل ولا عياله ، وللقابلة رجل العقيقة ، وإن كانت القابلة اُمّ الرجل أو في عياله فليس لها منها شيء ، فإن شاء قسّمها أعضاء ، وإن شاء طبخها وقسّم معها خبزاً ومرقاً ولا يطعمها إلاّ لأهل الولاية ...

10 – daga imam sadiq (as) ana radawa yaro suna rana ta bakwai da haihuwar yaron sannan a aske gashin kansa ayi sadaka da nauyin a yanka masa aqiqa daga riqaqqen rago, a daddatsa naman a dafa a gayyaci musulmi, idan ma ba'a dafa ba babu laifi cikin yin sadaka da gabobin abin da ka yanka, babu banbanci  cikin kasantuwar dan mace ko namiji, uban yaro da iyalansa ba za su ci wani abu daga aqiqar ba, a baiwa unguwar zoma qafa daya daga abin da aka yanka idan kuma uwar yaron ce ta kasance unguwar zoma  to ba ta da komai daga aqiqa, idan ya so ya karkasa aqiqa idan yaso ya dafa dukkkaninta ya raba hade da gurasa da miya ka da ya ciyar da kowa daga naman face masu riqo da wilayar iyalan annabi (as)

Daga cikin mustahabban aqiqa akwai addu'ar yankan aqiqa:

عن الباقر (عليه السلام) ، قال  : إذا ولد لأحدكم ولد فكان يوم السابع فليعقّ عنه كبشاً وليطعم القابلة من العقيقة الرجل بالورك ، وليحنّكه بماء الفرات ، وليؤذّن في اُذنه اليمنى وليقم في اليسرى ويسمّيه يوم السابع ، ويحلق رأسه ويوزن شعره فيتصدّق بوزنه فضّة أو ذهباً ، فإنّ الله ينزل اسمه من السماء ، فإذا ذبحت فقل  : ( بسم الله وبالله والحمد لله والله أكبر إيماناً بالله وثناءً على رسول الله (صلى الله عليه وآله) وشكراً لرزق الله ، وعصمةً بأمر الله ، ومعرفةً بفضله علينا أهل البيت ) ، فإن كان ذكراً فقل  : ( اللهمّ أنت وهبت لنا ذكراً وأنت أعلم بما وهبت ، ومنك ما أعطيت ولك ما صنعنا ، فتقبّله منّا على سنّتك وسنّة رسولك (صلى الله عليه وآله) وأخسئ عنّا الشيطان الرجيم ، لك سفكت الدماء لا شريك لك ، الحمد لله ربّ العالمين )

11 – daga imam baqir (as) ya ce: idan aka haifa ma dayanku da rana ta bakwai da ta zagayo ka yanka masa aqiqa a baiwa unguwar zoma cinyar aqiqar,  a digawa jaririn ruwan furat cikin saman bakinsa, a kira sallah a kunnensa na dama a yi iqama a na hagu  sannan a rada masa suna a aske gashin kan yaron a auna nauyi a ba da sadakar zinariya ko azurfa gwargwadon nauyin, lalle Allah zai saukar da sunansa daga sama, idan ka yanka aqiqa ka ce: ( bismillah wabillah wal-hamdu lillah Allahu akbar imanan billah wasana'an ala rasulillah (saw) wa shukran lirizqillah  wa'ismatul  ba'amrullah wama'arifatan bifadlulihi alaina ahlul baiti) idan yaron namiji ace:(Allah kaine ka bamu shi da namiji kai ne mafi sani daga abin da ka bayar )ka karbe shi daga garemu kan sunnarka da sunnar manzonka (saw) ka qasqantar da shaidani jefaffe  ga barin mu, Allah saboda kai na zubar da wannan jini babu abokin tarayya gareka, dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talaikai.

وعنه (عليه السلام) ، قال  : إذا أردت أن تذبح العقيقة فقل  : ( يا قوم إنّي بريء ممّا تشركون ، إنّي وجّهت وجهي للذي فطر السماوات والأرض حنيفاً وما أنا من المشركين ) ( إنّ صلاتي ونسكي ومحياي ومماتي لله ربّ العالمين لا شريك له وبذلك اُمرت وأنا من المسلمين ) اللهمّ منك وإليك بسم الله والله أكبر اللهمّ صلّ على محمّد وآل محمّد ، تقبّل من فلان بن فلان ) ويمسّي المولود باسمه ثمّ يذبح ( باسم الله ) .

12 – imam (as) : idan ka nufi yanka aqiqa ka ce:

ya ku mutane lalle ni ina barranta daga abin da ku ke tarraya lalle ni na fuskantar da fuskata ga wanda ya halicci sammai da qassai ni kuma ba na daga mushirikai. lalle sallah ta da ibada da rayuwa ta da mutuwa ta na hannun Allah ubangijin talikai bashi da abokin tarayya da wancan ne aka umarce ni lalle ni ina daga musulmai ) Allah daga gareka zuwa gareka da sunan Allah, Allah akbar Allah kayi tsira da aminci ga muhammadu da iyalan muhammadu, ka karba daga wane dan wane.

a ambaci sunan yaron da za'a yankawa aqiqar sannan a yanka da bismillah.

عن أبي عبد الله ، عن آبائه (عليهم السلام) ، قال  : عقّ رسول الله (صلى الله عليه وآله) عن الحسن والحسين (عليهما السلام) كبشاً يوم سابعهما وقطعه أعضاء ولم يكسر منه عظماً ، وأمر فطبخ بماء وملح وأكلوا منه بغير خبز وأطعموا الجيران

13 – daga baban abdullah (as)  daga babanninsa (as) ya ce: mazon Allah (saw)  ya yankawa  hassan da husaini (as)  rago rana ta bakwai da haihuwa ya yanka gabobin abin da aka yanka ba tare da ya qarya qashi ba ya dafa shi da ruwa da gishiri suka ci daga naman ba tare da gurasa ba suka kuma ciyar da maqotansu.

وقال (عليه السلام)  : سبع خصال في الصبيّ إذا ولد من السنّة  : اُولاهنّ يسمّى ، والثانية يحلق رأسه ، والثالثة يتصدّق بوزن شعره ورقاً ـ  الدراهم المضروبة من فضّة  ـ أو ذهباً إن قدر عليه ، والرابعة يعقّ عنه ، والخامسة يلطخ رأسه بالزعفران ، والسادسة يطهّر بالختان ، والسابعة يطعم الجيران من عقيقته

14 – imam (as) ya ce: abubuwa bakwai ga yaro idan an haife shi ta hanyar sunna : na farko rada masa suna, na biyu aske gashin kansa, na uku auna nauyin gashin da yin sadaka da kerarren dirhami daga   azurfa  gwargwadon nauyin ko kuma zinariya, na hudu a yanka masa aqiqa, na biyar a shafe kansa da za'afaran, na shida a tsarkake shi ta hanyar yi masa kaciya, na bakwai a ciyar da maqota daga naman aqiqarsa.

سئل أبي عبد الله (عليه السلام)  : ما الحكمة في حلق رأس المولود  ؟ قال  : تطهيره من شعر الرحم

sai ya ce: tsarkake shi daga gashin mahaifa.

وسأل عليّ بن جعفر أخاه موسى (عليه السلام) عن مولود لم يحلق رأسه يوم السابع  ؟ فقال  : إذا مضى سبعة أيام فليس عليه حلق

16 – ali dan jafar ya tambayi dan'uwansa musa (as) game da jinjirin da ba'a aske kansa ba ranar suna? sai ya ce: idan kwanaki bakwai daga haihuwarsa suka wuce babu tilashin aski kansa.

15 – an tambayi baban abdullah (as)  me ye hikimar aske kan yaro?