فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

KAMANCECENIYAR DA DA MAHAIFINSA 290

MUQAMI NA  12

            KAMANCECENIYAR DA DA MAHAIFINSA

A dabi'ace uban na son ya ga dansa ya yi kama da shi cikin surarsa, don ya zama da zarar matne sun ganshi sai su tuna da babansa, mutum zai dinga jin cewa kamar ta hakan zai zama ya samu wanzuwa kenan, ya kuma cika naqastuwarsa ta rashin kasantuwarsa wanzazze ko da kuwa cikin wahami ne saboda dan adam a dabi'ance na son wanzuwa wadda daya ce daga halittarsa.

Ya zo a riwaya cewa kamanceceniya da mahaifi siffa ce mai kyawu, sai dai cewa rashinta ba ya nufin naqastuwa ga da, gaskiya ne cewa duk wanda ya yi kama da mahaifinsa bai yi laifi ba, sai hakan bay a nufin cewa wanda bai yi kama da mahaifinsa ba ya yi laifi  , babu wani lazimci cikin haka, saboda tabbatar da haka ne muka samu riwaya mai daraja na nassanta al'amura biyu, kamanceceniya duk da kasantuwarta abu mai kyawu sai dai rashinta bai nuni ga muni ko ha'inci da dai makamantansu.

عن الصادق (عليه السلام)  : من نِعَم الله عزّ وجلّ على الرجل أن يشبهه ولده

1 – sadiq (as) daga cikin ni'imar Allah ga mutum dansa ya yi kama da shi.

وعنه (عليه السلام) ، قال  : إنّ الله تبارك وتعالى إذا أراد أن يخلق خلقاً جمع كلّ صورة بينه وبين آدم ، ثمّ خلقه على صورة إحداهن ، فلا يقولن أحد لولده هذا لا يشبهني ولا يشبه شيئاً من آبائي

2 – daga gareshi (as) ya ce: Allah madaukaki idan ya yi nufin halittar halitta sai ya tattara  dukkanin sura tsakaninsa da tsakanin adam, sai ya halicce shi kan sura daya daga ciki, ka da wani ya sake ya cewa dansa wannan bai kama da ni bai dauko kamar komai daga iyayena.

وسأل رجل عن النبيّ (صلى الله عليه وآله) فقال  : ما لنا نجد بأولادنا ما لا يجدون بنا  ؟ قال  : لأ نّهم منكم ولستم منهم

3 – wani mutum ya tambayi annabi (saw) me ya sa muke samun daga `ya`yan mu abin da su ba sa samu cikin mu ? sai ya ce masa: saboda su daga gareku suke amma ku ba daga garesu kuke ba.

من كتاب المحاسن ، عن الصادق (عليه السلام) ، قال  : من سعادة الرجل أن يكون الولد يعرف بشبهه وخَلقه وخُلقه وشمائله ـ  وهذا يعني أنّ الوالد لا بدّ أن يكون متخلّقاً أوّلا بأخلاق الإسلام وله شمائل أهل الخير والصلاح 

4 – daga littafin almahasin, daga imam sadiq (as) ya ce: daga cikin azurtar mutum ya zma dansa ya yi kama da shi cikin halittarsa da dabi'unsa.

Wannan na nufin kenan ya zama dole uba ya yi ado da kyawawan dabi'u.

عن أبي عبد الله (عليه السلام) قال  : إنّ الله عزّ وجلّ خلق للرحم أربعة أوعية فما  كان في الأوّل فللأب وما كان في الثاني فللاُم ، وما كان في الثالث فللعمومة ، وما كان في الرابع فلخؤولة                                  

5- an karbo daga baban Abdullah  (as)  Allah mai girma da daukaka ya halicci wurare hudu cikin mahaifar mace, na farko zai zama ga uba, na biyu uwa, na uku ga baffanu, na hudu ga `yan 'uwan uwa.

ta yiwu abin da ake nufi da wadannan mazubai shi ne digon maniyyi idan ya zauna a matsuguni na farko to yaro zai kama da mahaifinsa, haka al'amarin ya ke ga ragowar.

عن أبي الحسن (عليه السلام) قال  : سمعته يقول  : سعد امرؤ لم يمت حتّى يرى خلفاً من نفسه

7 – daga baban hassan (as) ya ce: na ji shi ya na cewa: mutumin da ya ga magajinsa gabanin mutuwarsa ya azurta.