فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

MATAKAN TARBIYYYAR YARA 292

MUQAMI NA 13

MATAKAN TARBIYYYAR YARA

sakamakon kasantuwar mutum da gangar jiki da ruhi, haqiqa an sanyawa kowanne daya cikinsu wanda zai tarbiyantar da shi da qara masa girma da lura da shi, akwai wasu abubuwa da ke sanya  tarbiyya ga ruhi, haka akwai na gangar jiki, sannan ita kanta tarbiyya tare da dukkanin kasha kashenta ta na da lokaci n agama gari da kebantacce, sakamakon kasuwar ilimi zuwa kasha biyu: ilimin zukata (wanda ba ta koyo ake samunsa ba) da wanda ake tsiwirwira (koyo ) kashin farko shi ne wanda riwaya ke cewa: ilimi baI kasance daga yawan koyo ba, kadai dai ilimi haske ne da Allah ke sanya cikin zuciyar wanda ya so ya shiryar da shi.

Koyo da tarbiyya ta hanyar ilimin zuciya da ruhi kadai dai na kasancewa tsawon rayuwa ba ya kebanta da zamani koma bayan wani zamani ya na kasancewa tun daga zani shimfidarsa bayan haihuwa har zuwa kabari, amma ilimin koyo lalle koyansa ga yaro qarami kamar zane ne kan dutse koyansa kuma bayan an rigaya an girma to kamar zane ne kan teku, akwai wasu sunnoni na musammam ga koyo da tarbiyyar ruhi da ta jiki kamar misalin wasannin motsa jiki, sannan waccan magana ta cewa karatun babba kamar zane kan teku hakan ba ya nufin cikin kowanne hali sai dai galibin lokuta haka al'amarin duk da cewa an samu wasu mutane da su kayi karatu a shekarunsu na qarshen rayuwa sannan suka kai manya-manyan  muqaman ilimi.

malaman tarbiyyar ruhi sun ambaci wasu kebantattun daurori, shi mutum ana iya yi masa tarbiyya har zuwa kai wa shekaru arba'in, sannan ana far tarbiyyarsa tun ya na shekaru bakwai.

muslunci na batu da kebantacciyar mahanga kan haka , a bayyane yak e duk sanda wani abu ya yi karo da abin da muslunci ya zo da shi ana gabatar da abin da muslunici ya kawo kan wancan, lalle abin da wahayi ya zo da shi a fadake yak e da dukkanin sirrinka dan adama da badininsa, Allah ne ya halicce shi kuma ya san haqiqaninsa da dukkanin abin da zai amfanar da shi da wanda zai cutar da shi da yadda ya kamata tarbiyyarsa da koyansa su kasance, annabi (saw) ya zo don ya tsarkake dan adam ya kuma koyar da shi littafi da hikima. sannan dangane da tarbiyyar yara haqiqa ya sanya marhaloli uku:

na farko: a kyale yaro ya dauki duk abin da yak e sha'awa matuqar dai baza cuatar da shi ba domin shi yaro a daurar yarintarsa jin kansa kamar basarake, sai a dinga ba shi abin da dukkkanin ransa ke so matuqar dai babu cutarwa da asara, ya zama tilas abar masa `yancinsa  ya yi yadda ya ke so, sannan  shi yaro idan ba'a bashi damar nuna mulkinsa ba da sannu cikin marhala mai zuwa zai nuna dagawarsa da ya boye cikin zuciyarsa.

ta biyu: da'a a ladabtarsa shi wannan lokaci ya zama ya na jin magana da da'a gadukkanin abin da aka sashi saboda a banshi dukkanin damar yin yadda ya so a marhalarsa ta farko yanzu kuma lokaci yay i shi da zai zama bawa ya kuma zama tilashinsa yay i da'a ga babban malamin sa mai yi msa tarbiya wato uba.

ta uku : wazirci bawa ya nade marhaloli biyu ya tsiwirwiri ilimi da gogewa kwakwalwarsa ta bude hankali ya girma, lalle zai zamanto cikin hukuncin waziri ga mahaifinsa, saboda haka kamata mahaifi ya dinga neman shawara daga gareshi cikinal'amuran rayuwar yau da gobe da batutuwan iyali, har da ya zma ya na dogaro da kankin kansa ya zma ya na jin knsa cikakken mutum  da cewa shi ma ya na da samuwa cikin iyalin da zma ana karbar shawararsa ta gari, da wannan wazirci zamu gane cewa rayuwa a wannan lokaci ta koma ryuwar demoqaradiyya, ka da uba ya zama dan mulkin fin qarfi da kama karya da nuna fin ikonsa cikin kowanne hali, bari dai kamat ya yi ya dinga shawartar iyalinsa misali idan ya nufi yin tafiya tare da iyali don shaqatawa ko kuma wata ziyara to sai ya bijiro da batun garesu  ya ji ra'ayin kowa da ga cikinsu da yadda  ya kamata ace tafiya ta kasance da tsawo lokacin da zata ci da dukkanin abin da ya rataya da ita, wannan marhala ta wazirci da in shawara da iyali ba ta kore matsayinsa da tsayuwarsa kan mata kamar yadda bayanin haka ya gabata, hakan shine ma'ana tsayuwa kan mata da kula nauyin da yah au kansa daga iyali.

قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : الولد سيّد سبع سنين ، وعبد سبع سنين ، ووزير سبع سنين . فإن رضيت أخلاقه لإحدى وعشرين ، وإلاّ فاضرب على جنبه ، فقد أعذرت إلى الله تعالى

1 – annabi (saw) ya ce: da shugaba ne na shekaru bakwai, bawan shekaru bakwai, wazirin shekaru bakwai, idan ka gamsu da dabi'unsa a shekaru ishirin da daya idan kuma ba ka gamsu ka doki kan kwibinsa, lalle ka sauke nauyin da ya hau kanka wurin Allah.

 ma'ana idan kayi aiki da abinda nauyin da ke kanka na tarbiyyarsa cikin wadannan shekar ishirin da daya cikin marhaloli uku ta kuma ka gamsu da kyawun dabi'arsa to madallah, idan kuma baka gamsu ba to dai ka riga ka sauke nauyin da yahau kanka wurin Allah.

عن الصادق (عليه السلام)  : دع ابنك يلعب سبع سنين ، ويؤدّب سبعاً ، وألزمه نفسك سبع سنين ، فإن فلح ، وإلاّ فلا خير فيه

2 – an karbo daga sadiq (as) ka kyale danka ya yi wasa  zuwa  shekaru bakwai, a kuma ladabtar da shi shekaru bakwai, ka lazimce shi shekaru bakwai zai rabauta idan kuma bai rabuta ba to babu alheri cikinsa.

وقال (عليه السلام)  : احمل صبيّك حتّى يأتي عليه ستّ سنين ، ثمّ أدّبه في الكتاب ستّ سنين ، ثمّ ضمّه إليك سبع سنين فأدّبه بأدبك ، فإن قبل وصلح ، وإلاّ فخلّ عنه

3 – imam (as) : ka kyale danka zuwa shekaru bakwai, sannan ka ladabtar da shi cikin littafi shekaru shida, sannan ka jawo jiki shekaru bakwai ka ladabtar da shi da ladabinka, idan ya karbi ladabinka gyaru ya ladabtu  idan kuma bai ladabtu ba to kayi watsi da shi.

ورد في حديث أمير المؤمنين (عليه السلام)  : أدّبوا أولادكم بآداب زمانهم ، فإنّهم خلقوا لزمان غير زمانكم

4 – abin da aka rawaito daga sarki muminai al (as) bai buya ba cikin fadinsa: ku ladabtar da yaranku da ladubban zamaninsu, lalle su an halicce zamanin da  ba na ku ba.

 ita wannan riwaya ba kore yiwa yaro tarbiyya da da tarbiyyarka sai dai z aka yi masa ne gwargwadon yadda ta da ce da zmanin da yak e ciki, lalle ladubban muslunci tun daga zamanin annabi (saw) har zuwa ranar alqiyama ladubba ne guda daya, sune ladubban da tauhidi da sunnonin annabta ke tajalli ciki, yaro ya girmama babba na tsaye ya yiwa na zane sallam, a wanke hannuwa gabanin cin abinci da dai makamantan hakadaga ladubba da sunnonida halayyar annabta mai daraja, lalle it aba kebanta da wani zamani banda wani, na'am koyarwa a zamanin da ana yinta kan allo amma yanzu kan injin komfuta, tarbiyya da koyarwa sune cikin kowanne zamani sai dai hanyar koyar da su ta kan dan banbanta cikin kowanne zamani.

muslunci ya yi wasicci kan tarbiyyar yara matuqar wasicci.

عن النبيّ (صلى الله عليه وآله) ، قال  : لأن يؤدّب أحدكم ولده خيرٌ له من أن يتصدّق بنصف صاع كلّ يوم

5 – annabi (saw) ya ce:  dayanku ya yiwa dansa tarbiyya shi ya fi alheri daga ya ciyar da rabin kwano cikin kowacce rana.

وعنه (عليه السلام)  : أكرموا أولادكم وأحسنوا أدبهم يغفر لكم

6 – daga gareshi (saw) : ku karrrama yaranku ku kyautata tarbiyyarsu Allah zai muku gafara.

عن الرضا (عليه السلام) ، قال  : قال النبيّ (صلى الله عليه وآله)  : اغسلوا صبيانكم من الغَمَر ـ  زنخ اللحم وما يتعلّق باليد من دسومة  ـ فإنّ الشيطان يشمّ الغمر فيفزع الصبي في رقاده ـ  أي يؤذيه في نومه  ـ ويتأذّى به الكاتبان ـ  الملكان عن اليمين والشمال 

7 – ankarbo daga rida (as) ya ce: manzon Allah (saw) ya ce: ku wanke hannayen yaranku daga qarnin nama, lalle shaidani na sansana ya dinga firgita yara yayin da suke barci. Sannanh mala'iku bbiyu masu rubuta sharrda Alherinsu na takuruwa.

 

Daga hadisai wadanda suka tattaro komai gameda tarbiyya har zuwa cika shekaru arba'in:

عن أمير المؤمنين عليّ (عليه السلام) ، قال  : يرخى الصبي سبعاً ـ  أي دعه يلعب واحمله وإنّه سيّد نفسه  ـ ويؤدّب سبعاً ـ  كما يؤدّب العبد  ـ ويستخدم سبعاً كوزير يستشار ويحمل قسماً من ثقل الاُسرة في المعاش وغيره ـ  وينتهي طوله في ثلاث وعشرين وعقله في خمس وثلاثين  ـ أي إلى هذا السن يستوعب العقل المعلومات الواردة ـ  وما كان بعد ذلك فبالتجارب  ـ والتجربة أكبر برهان وفوق العلم

8 – an karbo daga sarkin muminai alim (as) ya ce: a kyale yaro zuwashekaru bakwai ma'anaa barshi yay i wasa da nishadinsa, sannan a ladabtar da shi shekaru bakwai, sannan a sanya shi hidimakamar waziri shekaru bakwai ya zamanto ana shawartarsa a na dan dora masa nauyi daga buqatun iyali har shekarunsa sukai ishirin da uku, sannan hankalinsa zai kammala cikin shekaru talatin da hudu. sannan kadai dai zai dinga tarbiyyar dansa kan ayyukan kirki da da imanii da tauhidi tun farkon fitar faratansa.

عن أبي عبد الله أو أبي جعفر (عليهما السلام) ، قال  : سمعته يقول  : إذا بلغ الغلام ثلاث سنين فقل له سبع مرّات  : لا إله إلاّ الله  ، ثمّ يترك حتّى يبلغ ثلاث سنين وسبعة أشهر وعشرين يوماً ، ثمّ يقال له  : قل « محمّد رسول الله » ، سبع مرّات ، ويترك حتّى يتمّ له أربع سنين ثمّ يقال له سبع مرّات قل  : صلّى الله على محمّد وآل  محمّد ـ  أي في أوّل الأمر يعلّم التوحيد ثمّ النبوّة ثمّ الإمامة والولاية المتمثّلة بآل محمّد (عليهم السلام)  ـ ويترك حتّى يتمّ له خمس سنين ، ثمّ يقال له  : أ يّهما يمينك وأ يّهما شمالك ، فإذا عرف ذلك حوّل وجهه إلى القبلة ويقال له  : اسجد ثمّ يترك حتّى يتمّ له ستّ سنين ، فإذا تمّ له ستّ سنين قيل له  : صلّ وعُلّم الركوع والسجود حتّى يتمّ له سبع سنين ، فإذا تمّ له سبع سنين قيل له  : اغسل وجهك وكفّيك ، فإذا غسلهما قيل له  : صلّ ، ثمّ يترك حتّى يتمّ له تسع سنين ، فإذا تمّت له عُلّم الوضوء وضرب عليه ، واُمر بالصلاة وضُرب عليها ـ  فيما إذا أراد أن يتماهل أو يتكاسل فيها  ـ فإذا تعلّم الوضوء والصلاة غفر الله لوالديه إن شاء الله

9 – an karbo daga baban abdullah (as) ya ce: na ji shi yana fadin: idan yaro ya girma ya kai shekaru uku to a karanta masa(la'ilaha-  illAllah ) qafa bakwai har zuwa kaiwarsa shekaru uku da watanni bakwai da kwanaki ishirin, sannan akaranta masa  ( muhammadu rasulillah ) qafa bakwai sai a kyale shi har zuwa kammala shekaru hudu, sannan a karanta masa ( sallallahu a la muhammadu wa'ali muhammadu (as) sannan a sake kyale shi har zuwa kammala shekaru biyar, sai a tambaye shi wanne bangare ne damanka wanne bangare ne hagu, idan ya banbance sai a juya fuskarsa zuwa alqibla a ce masa: yi sujjada, idan ya kai shekaru shida sai ace masa:  sai a koya masa ruku'u da sujjada ace masa yi sAllah har ya zuwa cika shekaru bakwai iadan ya kammal shekaru bakwai sai ace masa: wanke fuskarka da tafin hannuwanka ka yi sallah, sai kyale shi har zuwa cika shekaru tara, bayan cika shekaru tara sai a koya masa alwala da taimama a uarce shi da yin sallah a kuma dake shi iadan ya barta, idan ya zamanto ya iya alwala da sallah ubangiji zai gafarta ma iyayensa da yardarsa.

وما أجمل ما يقوله الإمام السجّاد في رسالة الحقوق في بيان جملة من حقوق الولد ، فقال (عليه السلام)  : وأمّا حقّ ولدك ، فأن تعلم أ نّه منك ومضاف إليك في عاجل الدنيا بخيره وشرّه ، وأ نّه مسؤول عمّـا وليته به من حسن الأدب والدلالة على ربّه عزّ وجلّ والمعونة له على طاعته ، فاعمل في أمره عمل من يعلم أ نّه مثاب على الإحسان إليه ، معاقب على الإساءة إليه

10 – me ya fi kyawu daga abin da imam sajjad (as) ke cewa cikin wasiqarsa ta haqqoqi cikin bayanin jumlar haqqoqin da ya na cewa: amma haqqin danka ka sani cewa shi daga gareka yak e gareka ake jingina shi cikin duniya sharrinsa da alherinsa, sannan abin tambaya ne kan abin da kajibanta masa daga kyawawan ladudda da shiryar da shi zuwa ga ubangijinsa da taimakonsa cikin biyayyarsa, ka yi aiki tuquru cikin al'amarinsa irin aikin wanda zai san cewa shi zai samu lada kan kyautatawar da ya yi zuwa gareshi, da uquba kan munanawa zuwa gareshi.

Lalle idan aka zurfafa gani cikin ayoyin alqur'ani da hadisai masu daraja da suka zo daga annabi da iyalnsa (as) da kuma bincika tarihi da abin yau da gobe suka nuna dukkaninsu sun tabbatar da cewa uwa d uba na babbar gudummawa da tasiri kai tsaye cikin makomar rayuwar yaransu, munga tasirin da iyaye ke da shi kna mokomar rayuwar yaransu cikin marhaloli daban daban tun daga haihuwarsu zuwa yarintarsu zuwa marhalar samartaka, babu banbanci cikin kasantuwar makomarsu ta tsiwirwiri launi arziqi ko na tabewa, yayin da alqur'ani da hadisi ke qarfafa kasantuwar iyaye sun lazimci ginshiqan rayuwar muslunci da kasantuwa sun kula da yaransu da basu tarbiyya da kulawa ta musammam, kadai iyaye ke jagorantar makomar yaransu wadda ke ciki da haske da arziqi, da sama musu ni'imtacciya rayuwa, amma iyayen suka kaucewa ginshiqan addini rayuwar ke gudana cikin ko sakaci da ko in kula da kuma yin kasala wajen tarbiyyantar da yaransu kan koyarwar muslunci, lalle suna tasiri wajen gurbata makomar rayuwa yaransu, suna sanya su karan bara ga dukkanin karkacewa da bata daga hanyar gaskiya.

Hadisi ya zo daga annabi (saw) ya na cewa: mai arziqi shi ne wanda ya azurta tun daga cikin mahaifiyarsa, matsiyaci shi ne wanda ya tsiyata tun daga cikin mahaifiyarsa.

A cikin wata riwayar wata ranamanzon Allah (saw) tare da wani adadi daga sahabbansa ya wuce ta gefen wasu yara suna wasa sai ya kale su y ace: ya ku yaran qarshen zamani su waye iyayensu ? sai aka ce masa: daga cikin iyayensu akwai mushrikai, sai ya ce:  wadanda iyayensu suke muminai wadanda ba su koya musu komai daga farilla ba, idan yaransu  suka tafi koyon ilimi sunfi farin ciki su ga yaran suna neman dukiya duk da cewa abin da suke samu qadan ne bai tka kara ya karya ba, sai ya zamanto  yaran suna tsananin qin wadannan iyaye na su, sai ya ce: ni na barranta daga wadannan iyaye su ma sun barranta daga gareni.