فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

HAQIQANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI ( AS ) 329

HAQIQANIN LADABI KAN HASKEN MAZHABAR IYALN GIDAN ANNABI ( AS )

Haqiqadan adam ya daukaka da hankalinsa mai riska  cikin hikimar aubangiji kan dukkanin sauran  halittu, lalle hankali kyautar ubangiji ne ya sanya shi cikin mutum, don ya yi yawo cikin smaniyar falaloli da sasannin ilimai  ya daga ya kai ga qaba qausani ya kai qolloluwar kamala da girma ya kasance mazaharin sunayen Allah kyawawa da madaukakan siffofinsa, lalle shi duk sa'ilin da ya qara kamala da kyawuntaka lalle shi zai kasance mazharin ga sunan ubangiji har ya kai ga zuwa narkewa cikin Allah da zama mazharin jalaliya dukkanin sunayen ubangiji su yi tajalli cikinsa.

وَما رَمَيْتَ إذْ رَمَيْتَ وَلـكِنَّ اللهَ رَمى[1]

(( ba kayi jifa sa'ilin da kayi jifa sai dai cewa Allah ya yi jifan )

وَما يَنْطِقُ عَنِ الهَوى إنْ هُوَ إلّا وَحْيٌ يُوحى[2]

(( bai furruci da so zuciya dukkanin abin da ke furtawa wahayi ne da ake masa  ))

إنَّ الَّذينَ يُبايِعونَکَ إنَّما يُبايِعونَ الله[3]

(( lalle wadanda ke yi maka muba'a kadai dai suna yiwa Allah mubaya'a ne )

مَنْ يُطِعِ الرَّسولَ فَقَدْ أطاعَ الله[4]

 (( duk wanda ya yiwa manzo da'a haqiqa ya yiwa Allah da'a ))

Manzon mafi girama (saw) ya kai ga daukaka ta hanyar kamalarsa yay aye duhu da kyawunsa ya kasance mazhari mafi cika ga ubangiji wanda giramans ay girmama , jifan annabi jifan Allah ne kalaminsa kalamin Allah ne mubaya'a ga annabi mubaya'a ga Allah da'a gareshi da'a ga Allah, haka ba komai bane face ludufi daga Allah da kuma kamalar hankalinsa.

Girman mutum da daukakarsa da fifikonsa kan ragowar halittu da azurtar gida biyu kadai dai sakamakon hankalinsa ne, hankali shi e abin nan da aka bautawa ubangiji mai rahama da shi aka samu aljanna da shi ya na dakarunsa, daga cikinsu akwai kyawuntar ladabi  kamar yadda shi ma jahilci na da dakaru, daga cikindakarunsa munana ladabi, ma'abocin hankali na kasancewa mai ladabi mai ladabtarwa mai koyar da ladubba cikin sulukinsa da zantukansa da da dukkanin motsinsa da shirunsa.

ويقول أمير المؤمنين علي  7: الأدب كمال الرجل

Sarkin muminai ali (as) na cewa: ladabi shi ne kammalar da namiji.

وقال : الأدب أحسن السجيّة ، أفضل الشرف الأدب

 ladabi shi ne mafi kyawun hali, mafi daukakar daraja  ladabi.

وقال  7: خير ما ورّث الآباء الأبناء الأدب ، حسن الأدب خير مؤازرٍ وأفضل قرين

Ali (as) : mafi alherin abinda iyaye suka barwa `ya`yansu ladabi shi ne mafi alherin mai taimako mafi falalar abokin zama.

Wannan na nufin mafi alherin wanda zai taimake ka da qarfafarka da abokantaka cikin tsanani rayuwa da matsalolinta mafi alherin guzuri cikin rayuwar duniya shi ne ladabi.

وقد قال الأمير  7: طالب الأدب أحزم من طالب الذهب ، ومن لم يكن أفضل خلاله أدبه كان أهون أحواله عطبه ، وإنّک مقوّم بأدبک فزيّنه بالحلم ، يا مؤمن إنّ هذا العلم والأدب ثمن نفسک فاجتهد في تعلّمها، فما يزيد من علمک وأدبک يزيد في ثمنک وقدرک

Haqiqa sarkin muminai ali (as) ya ce: mai neman ladabi ya fi tsanantawa daga mai neman zinariya, duk wanda bai kasance mafi falala cikinsa shi ne ladabinsa to halakarsa za ta zama mafi sauqaqa lalle kai mai daidaita ne da ladabinka ka kyawunta shi da yin haquri, ya kai mumini shi wannan ilimi da ladabi shi ne jarin zuciyarka ka yi qoqari cikin koyonta , duk abin da ya qaru cikin iliminka da ladabinka darajarka da qimarka za su qaru.

Na'am qimar kowanne mutum shi ne abin da ya ke aikatawa, ladabinsa shi ne jarinsa.

sarkin muminai ali (as) ya ce: ladabi shi ne kamalar da namiji, a wani wajen y ace : hankalinmutum tsarinsa, ladabinsa daidaitonsa, haqiqa buqatuwar mutane zuwa ga mutum salihi ma'abocin ladabi ta fi buqatuwarsu zuwa zinariya da azurfa, abubuwa uku babu qari kansu kansu: kyawuntar ladabi, qauracewa kokwanto, da kamewa daga haramun.

Yayin da annabi ya aika mu'azu dan jabal qasar yaman ya ce masa: ya mu'azu ka koyar da su littafin Allah ka kyawunta ladubbansu kan nagartattun halaye.

Ta yiwu mutum ya kasance mai daraja cikin matsayinsa  amma saboda munanar ladabinsa sai ya fadi daga daga idanuwan mutane, sau da yawa zaka qasqantacce cikin danginsa  sai dai cewa ya na daukaka ya shuagabanci mutane sakamakon kyawuntar ladabinsa.

ويقول أمير المؤمنين علي  7: الأدب أحد الحسبين ، وأشرف حسب حسن أدب ، وأكرم حسب حسن أدب ، وحسن الأدب أفضل نسب وأشرف سبب ، وطلب الأدب جمال الحسب ، وعليكم بالأدب فإنّه زين الحسب ، وقليل الأدب خير من كثير النسب ، وحسن الأدب ينوب عن الحسب ، ولا حسب أنفع من الأدب ، وكلّ الحسب متناهٍ إلّا العقل والأدب ، وحسن الأدب يستر قبيح النسب ، وفسد حسب من ليس له أدب

Sarkin muminai ali (as) ya na cewa: ladabi daya daga cikin matsayi biyu ne, ma fi girman darajar matsayi kyawuntar ladabi , mafi karamcin matsayi kyawun ladabi, kyawuntar ladabi shi ne mafi falala nasaba da daukakar sababi, neman ladabi shi ne kyawuntar matsayi, na hore ku da ladabi lalle shi adon matsayi ne , mai qaranci ladabi ya fi alheri kan mai yawan dangi , kyawuntar ladabi na maye gurbin matsayi , babu wani matsayi da ya fi amfani daga kadabi, duk wani matsayi mai qarewa ne face hankali da ladabi, kyawun ladabina suturce munanar nasaba , matsayi idan babu ladabi ya na gurbata. ladabi kan saruta ne da ke gadar da girma da shugabanci.

 

sarkin muminai ali (as) :  babu wani ado da ya wuce ladabi, babu kaya cancada ado kamar ladaubba, ladabi kayan ado ne sababbi, ilimi gado ne na karamci, ladabi kayan ado ne masu sabunta .   

daga cikin bayyanannen al'amari shine cewa mutum na asarar girmansa da matsayinsa sakamakon munanar labinsa

sarkin muminai ali (as) babu girma tare da munanar ladabi , duk wanda ladabinsa ya qaranta miyagun ayyukansa zasu yawaita, duk wanda munanar ladabinsa ta qasqantar da shi girmansa da matsayinsa ba u iya daukaka shi , Allah wadarn nasaba tare da munanar ladabi, babu ladabi ga mai mummunan kalami.

ya zamo dole a zage dantse wajen neman ladabi lalle ya zo cikin hadisi daga iyalan annabi (as) cewa an halicci rai kan munana ladabi, bawa kuma an umarce shi da lazaimtar kyawuntar ladabi, iata rain a sukuwa fagen sabo, shi kuma bawa na dagewa ya gay a dawo da ita daga barin sabo duk sanda bawa ya sakar mata ragama to shi ma ya yi tarayya cikin barnarta, duk wanda ya taimakawa son arnasa haqiqa ya yi tarayya cikin halaka kansa.

hankali duk da kasntuwarrsa kyauta daga Allah matsarkaka sai dai cewa ba'a wadatuwa da shi kadai a rayuwance dole nea cudanya shi da ladabi.

haqiqa sarkin muminai ali (as) na cewa: madalla da ladabi abokin cudanyar hankali, gyaruwar hankali ladabi , kowanne abu na buqatuwa da hankali amma shi hankali ya na buqatuwa da ladabi , hankali ba zai amfanar ba idan babuu hankali , ladabi shi ne ciyar da kwakwale shi ne ribar hankula, lalleshi ladabi shi ne surar hankali lalle shi cikin mutum kamar bishiya ne hankali tushenta, kyawuntar hankali ado, babu ladabi ga wanda bai da hankali, lalle ladabi da addini ribar hankali ne, mafi falalar hankali ladabi , ladaubban malamai na yawaitar hankalinsu, lalle ma'abota hankula na da buqata zuwa ladabi kamar yadda shuka ke buqatar ruwan sama, duk wanda ladabinsa ya fifici hankalinsa shi kamar makiyayi ne tsakanin dabbobi masu tarin yawa.

wanan na nufin ladabi tu farkonsa wabatawa ne da kallafawa kai, sai dai bayan haka zai waya gari matsayin dabi'a da dan adam zaii dinga amfana da ita  cikin rayuwa da bayan mutuwarsa, lalle shi ladabi shi ne mafi alherin gadon da aka barwa al'ummun da za su zo daga baya.

na hudu: ilimi, haqiqa muslunci ya himmatu da da shi matuqar himmatuwa , ta fuskanin zamani ya zama tilas ka ne mi ilimi tsaahon rayuwa daga ranar farko zuwa qarshne numfashinka (( ku nemi ilimi tun daga zanin haihuwa zuwa kabari )) ta fuskanin wuri ka nemi a kowanne bigire cikin qasa kai hatta mafi nisa daga jazirar larabawa (( ku nemi ilimi ko kuwa a qasar sin (cana ) lalle shi ilimi farilla ne kan dukkanin musulmi da musulma.

( Allah na daukaka darajar wadanda sukayi imani daga cikinku da wadanda aka baiwa ilimi.

( shin wadanada suke da ilimi za su daidaita da wadanda bas u da shi.

shi ma'abocin hankali bai gajiya da qosawa cikin neman ilimi, mahandama biyu basa qoshi mai neman ilimi da mai neman duniya, dole a nemi ilimi dare da rana, lalle shi Allah masani ne mai tarin sani ya na son ilimi da malamai nagargaru masu neman ilimi, lalle su mahari ne daga mazharorin iliminsa na azal madawwami, shi ilimi na taimakon mutum cikin samun ladabi da kyawawan dabi'u.

sarkin muminai ali (as) na cewa: idan ilimin mutum ya qaru ladabinsa zai qaru, tsoran allansa zai ninka.

imam sadiq (as) ya ce : lalle mafi alherin abin da iyaye suka barwa 'ya'yansu shi ne ladabi ba dukiya ba, lalle ita dukiya na qareawa ladabi kuwa ya na wanzuwa.

daga cikin ribar ladabi kaifin basira, mutum sai ya zage dantse ya shirya neman ilimi fiye da waninsa.

sarkin muminai ali (as) ya na cewa: da ladabi a ke wasa basira, ka qara basirarka da kaifin kwakwalwarka don ka samu taimako da ita wajen neman ilimi da aiki da ladabi.

na biyar : tsoro , daga cikin ribar ilimi mai amafani shine tsoron Allah matsarkaki , lalle shi malami kowanne hali ya na tsakanin tsoro da fata , ya na tsorata aga zunubansa ya na fatan ubangijinsa , duk sanda ya qaru cikin ilimi mai amfani sai qaga ya qru da tsoro ( kadan masu tsoron Allah daga bayinsa sune malamai ).                                    ilimi na haifar da tsoro.

haqiqa Allah ya cewa isa (as) : ka ladabtar da zuciyarka da tsoro .

wannan na nuni da cewa kowacce gaba jikin mutumna da ke bantattu ladubba, ladubban idanu kame su daga kallon haramun, harshe kama daga yin qarya da alfasha da gulma da kafirci da dai misalinsu, ladabin kunne kamewa daga jin haramun, ladabin hannu da qafafu kayi tattaki da su cikin da'ar Allah, mutum bisa halayyarsa yana da ladubba kebantattu, ladubbansa tare da ubangijinsa  sun saba da ladubbansa da mutane, ya kamace ya kiyaye ladubban iayali da qaramar al'umma zuwa babba, kamar ladabinsa cikin mahalllin iliminsa kamar makaranta da wurin aiki da dai makamantansu , majalisi n agama gari na da ladubbansa kebatattu, haka kebantacce majalisi shi ya na da nasa ladubban da ya kebanta da su, kowacce al'umma na da ladubbanta da sunnoninta da wayewarta kebance, duk wanda ke son ya zauna da wata qungiya to ya zama tilas ya kiyaye ladubbansu, kowanne abu bisa yadda ya ke, amma ladabin zuciya wadda it ace sarauniya kan jiki, idan ta gyaru ragowar gabobi zasu gyaru idan ta lalace za su lalace, idan malami ya lalace duniya sai ta lalace shi ne ma'anar fadin : iadan zuciya ta lalace duniya za ta lalace, gyaranta da ladabinta shi ne tsoron Allah matsrakaki, saboda haka ka ladabtar da zuciyarka da tsoron Allah.

na shida : zma da malamai, lalle muslunci ya umarce mu da mu zauna da malamai hatta mu cadanye su cikin neman ilimi, ka matsi malamai da gwiwowinka fadin lukmanu ga dansa, lalle zama da malamai na kawo tsira da azurta cikin gida biyu, wajen neman ilimi sarkin muminai ali (as) na cewa: ka zauna wajen malamai iliminka zai qaru ladabinka zai kyawunta, abin nufi da malami anan shi ne wanda kallo zuwa gare shi ya kasance ibada shi ne wanda aikinsa ke gasgata fadinsa, idan ya umarce mutane daalheri to za a ganshi kai da farko lalle shi zai far aik da shi kafin umartar mutane, idan yayi hani da barin mummuna za a fara samunsa ya kwabu daga barinsa kafin ya umarci wasu, shi malamin da furucinsa ke qara maka ilimi ya kwadaitar da kai lahira kallonsa ya tunatar da kai Allah, shi ne wanda aka umarce mu da neman ilimi daga gare shi, idan bai da wadannan siffofi to ina.

idan kuka ga malami na neman duniya ku tuhume shi ka da k nemi addinku daga gare shi, lalle shi ya na cikin barayin kan hanya da addini ( mutum ya yi duba ya zuwa abincinsa ) 

imam baqir (as) ya na cewa: ma'ana ilimnsa daga wanda zai karbe shi

na bakwai : fahimta , da yawa ita fahimta ta fi kebanta daga ilimi ya zma tilsa mutum ya fahimci rayuwa ya riski sirrikanta don ya san qimarsa , da abin da ake nema daga gare shi da kan abin da ka halicce shi da manufar halittarsa ? ya zama tilas mu ladabtar da kawukanmu da fahimta

mu nemi taimakon ubangiji kan haka mu roqe shi kamar yaddda iama zainul abiding (as) ka cewa Allah mu na roqonka ka sanya m daga cikin wadanda suka yi riqo da igiyar ilimi suka ladabtar da kawukansu da fahimta.[1] Anfal:17

[2] Annajmu:3

[3] Fathu:10

[4] Nisa'i:80