فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

MEYE LADABI ? 338

ME NENE LADABI ?

A wannan waje mai karatu na da haqqi bayan ya san rawar da ladabi ke taka cikin rayuwar mutumtaka, ya kuma riski muhimmancinsa da kasantuwar babu hankali ga wanda bai da ladabi ba da ban ladabi ba da dan adama ya tsinci kansa a sahun dabbobi  da kamanceceniya da su ko kuma shi ya fi su batan hanya, ya da haqqin tambayar kan cewa meye ladabi, qaqa za mu iya zuwa gare shi , qaqa za mu iya ladabtar da kawukanmu da wanne abu za mu ladabtu ???

Sannan mu ladabtar da wasu musammam 'ya'yan mu wadanda su tsokar zukatanmu ne ?

Za mu rairaye amsar wadannan tambayoyi mu ambace su qarqashin riwayoyi da suka zo daga iyalan annabi (as) lalle sune ma'adanan ilimi da ladabi, kalmansu haske ayyukanku alheri umarninsu shiriya, wasiyyarsu taqawa sune shugannin bayi rukunan qasa su ababaen koyi ne nagari da kwaikwayo.

Ma'anar ladabi:[1] tsari kyakkyawa da halastaccen aiki ya da ce ya afku a kansa cikin addini ko wajen ma'abota hankali cikin al'ummarsu , kamar ladubban addu'a da laduubban ganawa da abokai , idan ka so ka na iya cewa : ladabin kyawuntar aiki .

Idan aiki ya kasance ya kyutata  bayan sauqaqarsa a mahangar sharia tsarkakka ma'ana wahayi da hujjar zahiri ko kuma ta mahangar hankali da boyayyar hujja, lalle shim ma zai kasance daga ladabi, ba zai kasance ba face ta al'amura halastattu wadanda shari'a ba tayi hani kansu ba, baya tabbatuwa face cikin ayyukan da mutum yake da zabi kai wadanda su ke tsare tsare daban daban, har ya zamanto ba'arinta ya yi ado da kwalliya da ladabi koma bayan wani ba'arin, kamar ladabin cin abinci a muslunci daga cikin ladubbansa shi ne a fara ci da yin bismillah  a gama da hamdala sannan idan za'a ka da aci a qoshi maqil ka da adinga kallon wasu a wanke hannuwan kafin fara ci da gamawa da sauransu, kowanne abu na da na sa ladabin a kebance.

Ladabi na nufin kyakkyawan tsari cikin ayyukan da kake da zabi ,

Ladabin kowacce irin al'umma shi ne madubin da ke hakaito wayewarsu da cigabansu da aqidinsu da dabi'unsu.

Sai dai ladabi bay a nufin kyawan dabi'u da zukata siffanta da zurfafa cikinsu  ladabi dais hi ne ayyuka nagari  daga tushen dabi'u  , manufar rayuwa wadda dan adam ke nema iata ke bayyana ladabinsa da ayyukansa ta shata masa layi wanda bai iya shallake shi cikin tafiyarsa a rayuwance  da neman kusantar manufarsa.

Sannan ladabin ubangiji wanda ya ladabtar da annabawa da manzani da walyyai da makusanta cikin bayinsa shine kakyawan tsari cikin ayyuka addini wanda suke hakaito manufar addini da abin da shi yak e san ya ga ya cimma ya kai gare shi , shine bautar Allah bisa dukkanin sabanin addinan sama na gaskiya da sassabawar matabobinsu da kamala.

Muslunci bai gafala daga qramin abu da babba ba bari madai ya karkata zuwa dukkanin fukokin rayuawar dan adam, haqiqa ya yalwata ladabi ya tsarawa kowanne aiki ladabinsa da ke hakaito manufarsa ta rayuwa,  manufar ladabin  muslunci shi ne tauhidi bai da wata manaufa da ta wuce tauhidi a bautawa Allah cikin marhalar aqida da aiki,  mutum ya yi imani da mafara da qarshe lalle tilas ya zama anga  da'a da bauta cikin rayuwarsa da zantukansa da ayyukansa da sauran bangarorin rayuwarsa .

Ladabin ubangiji da annabta da wilaya dukkaninsa  abu guda ne haqiqa ce daya rak wato tsarin tauhidi cikin aiki, sannan kowanne mutum daga cikin mu sai ya fara  ladabtar da kansa kafin waninsa, saboda wanda bai da abu bai iya ba da shi:

أفَمَنْ يَهْدِي إلَى الحَقِّ أحَقُّ أنْ يُتَّبَعَ أمَّنْ لا يَهِدِّي إلاَّ أنْ يُهْدَى فَمَا لَكُمْ كَيْفَ

 [2]تَحْكُمُونَ

( shin wanda ke shiryarwa zuwa gaskiya shi ne ya fi cancanta abi ko kuma wanda bai shiryawa sai dais hi ma a shiryar da shi, me ya faru da ku qaqa kuke hukunci )

 

Ku na da abin kwaikwayo kyakayawa daga annabawa da manzanni da salihai.

Sannan kowanne abu na da asalai da reshe, ya kamata mu fara bayyana muku asalai ku kuma sai ku nemi rassa da dabbaqasu da sanni juzu'ai.[1] Tafsiril almizan m 6 sh 255

[2] Yunus:35