فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ KALMAR TARBIYYA CIKIN HARSHEN LARABCI DA YANDA AKA YI 4
■ FASALI NA ( 2 ) 24
■ AUREN DABI'A 24
■ FASALI NA 3
■ FASALI NA 4 73
■ FASALI NA 5 131
■ FASALI NA 6 176
HAQQOQIN DA MA'AURATA SU KAYI TARAYYA CIKI 177
1 – HAQURI 178
2 – KAMEWA DAGA ZALUNCI DA CUATARWA 179
HAQQOQIN MATA 180
CIYARWA DA YALWATAWA 185
TAUSAYAWA DA KAMEWA DAGA ZALUNCI 187
KAMEWA DAGA BARIN DUKA MAI CUTARWA 187
UMARNI DA KYAKKYAWA DA HANI DA MUMMUNA 193
GARKUWA 196
8 – KYAUTATAWA : 196
9 - KYAWUNTA ZAMANTAKEWA 197
3 – TAUSAYAWA MIJI : 208
4 – HIMMATUWA DA KULA DA CIKIN GIDA DA KAYYAKINSA : 209
5 - HIMMATUWA CIKIN SAUKE HAQQOQI 209
6 – JIMA'I 210
7 - ADO 213
8 – KAMEWA CIKIN MAGANA : 219
SHUGABANTAR IYALI 225
DALILAI DA SUKE SANYA DAWWAMAR AURE 227
1 – SON JUNA 228
2 – YAWAITA AIKATA ALHERI: 228
4 – SANYA FARIN CIKI: 229
5 – BIYAYYA DA NEMAN YARDAR MIJI: 230
6 – KIYAYE MUTUNCI DA DUKIYA : 230
7 – TAIMAKO DA TALLAFAWA 230
8 – TARBAR MIJI DA KYAWUNTA BANKWANA DA SALLAMA : 231
9 – KALAMIN AQIDOJI MAI KYAWU DA QARFAFAFFEN FURUCI. 232
10 – KARBAR UZURI DA YIWA JUNA UZURI : 232
11 – BINSU SANNU SANNU CIKIN KOWANNE HALI : 233
12 – KYAWUNTA LAFAZI CIKN KOWANNE YANAYI : 233
13 – RASHIN SAURARON KYAUTATA AIKI DARI BISA DARI 233
14 – RASHIN IKON DAUKAR NAUYI A RAYUWANCE : 234
15 – RASHIN GORI KAN MIJI : 234
16 – RASHIN QAURACEWA AL'AMARIN SHIMFIDA: 235
17 - YIN SHAWARA DA MATA BANDA BIYE MUSU: 235
18 – TAKA TSAN TSAN DA KUMA FARKAWA : 238
19 – HANKALTA 239
20 - MIJI SHI NE MUTUNCIN MATARSA 240
21 – KISHI 240
22 – TAIMAKEKENIYYA 242
23 – DADADAWA IYALI 243
27 – WATSI DA BOAKANCI DA TSAFE TSAFE : 244
28 - HIDIMA MADAWWAMIYA 245
29 – GODIYA 246
29 – QAUNAR JUNA 247
TSINTUWA GUDA BIYU GIDAN ALI DA FATIMA (AS) 248
■ FASALI NA 8 252

ASALAN LADUBBA 341

                             ASALAN  LADUBBA               

Ya zama dole  akiyaye wadannan asalai wajen neman ladabi da tabbatar da shi:

Na farko:  kamewa daga miyagun siffofi da munanan dabi'u ko da kuawa hakan ya zamanto ta hanyar wa'azantuwar da waninka, haqiqa.

فإنّ أمير المؤمنين علي  7 يقول : (إذا رأيت في غيرک خلقآ ذميمآ فتجنّب من نفسک أمثاله

 sarkin muminai ali (as) ya na cewa : idan ka ga mummunar dabi'a daga waninka ka qaurace ma irinta daga cikin kanki kanka.

Wannan muhimmin asali daga ladabi.

لا تنهَ عن خُلُقٍ وتأتي مثله         عارٌ عليکَ إذا فعلتَ عظيمُ

Ka da kayi hani daga wata dabi'a amma kai kuma ka zakke ma irinta  abin kunya yak e kanka idan ka aikata wannan aiki mai girma.

Ya ishi mutum wa'azi ya wa'azantu da waninsa lalle shi mai hanakali shi ne wanda ya fadaka da wa'azantuwa daga waninsa, idan ya ga wani munkari daga waninsa to sai ya qauracewa shigensa cikin kankin kansa, ya tsiwirwiri ladubban da bai da su daga waninsa.

Lalle wannan ma'ana ta zo cikin kariin maganar farisawa: lalle ni na koyi ladabi daga wurin wanda bai da shi.

قيل لعيسى بن مريم  8: مَن أدّبک ؟ قال : ما أدّبني أحد، رأيت قبح الجهل

[1] فجانبته

An tambayi isa (as) waye ya ladabtar da kai ? sai ya ce: babu mutum guda da yay i mini ladabi, kadai nag a munin jahailci sai na qaurace masa.

وقال أمير المؤمنين علي  7: (كفاک أدبآ بنفسک اجتناب ما تكرهه من غيرک[2]

Sarkin muminai ali (as) ya ishe ka ladabi ga kanaka qauracema abin kake qi  daga waninka.

Na biyu: haquri asasin kyawawan dabi'u cikin dukkanin marhalolinta uku: qauracewa daga siffofi munana, yin ado da kyawawan dabi'u, haquri shi ne tajalli kuma shi sinadari ne na farko cikin ilimin kyawawan dabi'u daga nan kuma ladubba.

يقول أمير المؤمنين علي  7: (ليس شيء أحمد عاقبةً ، ولا ألذّ مغبّةً ، ولا أدفع لسوء الأدب ، ولا أعون على درک المطلب من الصبر).

Sarkin muminai ali (as) na cewa: babu wani mai kyakkyawan qarshe da dadin abin nema da tunkude munana ladubba da mafi taimakawa kan cimma buqata kamar haquri.

Na uku : bincike , lalle duk wamda ya nemi wani abu dole ne ya ne meshi da zage dantse har zuwa samunsa, ladubba na daga cikin ababen nemada himmatuwa da su.

قال الإمام علي  7: (لا يستعان على الدهر إلّا بالعقل ، ولا على الأدب إلّا بالبحث

Sarkin mumainai ali (as) ba a neman taimako kan zamani da komai face da hankali haka kan ladabi face da bincike.

وقال لقمان الحكيم : (مَن عني بالأدب اهتمّ به ، ومن اهتمّ به تكلّف علمه ، ومن تكلّف علمه اشتدّ طلبه ، ومن اشتدّ له طلبه ، أدرک منفعته فاتّخذه عادة ، فإنّک تخلف في سلفک وتنفع به من خلفک[3]

Lukmanu hakim ya ce: ( duk wanda ya damu da ladabi zai himmatu kansa, duk wanda ya himmatu da shi zai kallafawa kansa saninsa, duk wanda ya kallafawa kansa saninsa zai zage dantse kan nemansa,  duk wanda ya zage dantse nemansa zai riski amfaninsa ya riqe shi al'ada, lalle kai z aka bar ma magadanka shi wadanda za su daga baya za su amfana da shi.

Na hudu:ilimi, haqiqa muslunci ya himmatu da batun ililmi matukar himmatuwa.

Ta fu bangaren lokaci ya zama dole mutum ya nemi ilimi tsawon rayuwarsa  tun dag ranar farko har zuwa qarshen rayuwarsa, kamar yadda ya zo a hadisi: ku nemi ilimi tun dag shimfidar haihuwa har zuwa kabari, ta bangaren mahlli kuma to ka neme shi a kowanne bigire ka neme shi daga mafi nisan bigireb wanda shine jazirar larabawa(ku nemi ilimi ko da kuwa zuwa qasar sin ne) lalle shi ili,I wajibi kan dukkanin musulmi da musulma.

يَرْفَعِ اللهُ الَّذينَ آمَنوا منكُم وَالَّذينَ اُوتوا العِلْمَ دَرَجاتٍ )[4] ، و(هَلْ يَسْتَوي الَّذينَ يَعْلَمونَ وَالَّذينَ لا يَعْلَمونَ[5]

 Allah ya na daukaka wadanda suka yi imani cikinku da wadanda aka baiwa ilimi darajoji, shin yanzu masu ilimi za su daidaita da wadanda ba su da shi.
mutum mai hankali bai qosawa da neman ilimi bai gajiya, masu nema biyu basu qoshi su ne mai neman ilimi da mai neman duniya. Ya zama dole a zage dantse a nemi ilimi dare da rana, lalle ubangiji masani mai yawan sani ya na son ilimi da malamai nagargaru ma su neman ilimi, lalle su mabayyana ne daga mabayyanun iliminsa azali sarmadi.

Lalle ilimi na taimakon mutum kan neman ladabi da kyawawan halaye.

يقول أمير المؤمنين علي  7: (إذا زاد علم الرجل زاد أدبه ، وتضاعفت خشيته لربّه

Sarkin muminai Ali(as) ya ce: idan ilimin mutum ya qaru sai ladabinsa ya qaru. Tsoron Allah ya ninninka.

قال الإمام الصادق  7: (إنّ خير ما ورّث الآباء لأبنائهم الأدب لا المال ، فإنّ المال يذهب والأدب يبقى )، قال مسعدة : يعني بالأدب : العلم

Imam sadiq(as) ya na cewa: mafi alherin abin da iyaye sukar barwa `ya`yayensu shi ne ladabi ba dukiya ba, lalle ita dukiya tana tafiya ta qare, ladabi kuma ya wanzu.

Daga cikin ribar ladabi kaifafa kwakwalwa, mutum ya damarar neman ilimi fiye da komai.

أمير المؤمنين  7: (بالأدب تُشحذ الفِطَن ، فزد في فطانتک وذكائک لتستعين بهما على طلب العلم والعمل به بالأدب

Sarkin muminai Ali(as) ka yi qari cikin basirarka da kaifafarka don ka samu taimako da su wajen samun ilimi da yin aiki da shi.

Na biyar:ganin girman ubangiji, lalle daga cikin ribar ilimi mai amfanihi ne ganin girman ubangiji da tsoronsa. Lalle shi malami ya na rayuwa tsakanin tsoro da fata, ma'ana ya tsorata daga zunubin da ya aikata ya na kuma fatan rahamar ubangiji , duk sa'ilin da ya qaru da ilimi da aiki na nagari sai ya qaru cikin tsoron Allah.

إنَّما يَخْشى اللهَ مِنْ عِبادِهِ العُلَماء[6]ُ

Kadai masu tsoron Allah da ganin girmansa daga bayinsa sune malamai.

Shi ilimi ya na haifar da ganin girman ubangiji da tsoronsa.

وقد قال الله تعالى لعيسى : أدّب قلبک بالخشية

Haqiqa Allah madaukaki ya cewa da isa (as) ka ladabtar da zuciyarka da tsoro

Wannan na nuni da cewa kowacce gaba ta na da kebantattun ladubbanta. Ladabin idaniya shi ne ka da ta kalli abinda Allah ya haramta, ladabin harshe ka da ya yi qarya ka da ya furta alfasha ka ya  yi gulma ka da yay i kalaman kafirci da dai sauransu…

Ladabin hannuwa da qafafuwa shi ne suyi kai kawao cikin da'ar Allah, kamar yadda mutum ya na da kebantattun laduba gwargawadon halinsa. Ladabinsa tare da ubangijinsa  ya banbanta daladabinsa tareda ragowar mutane , wajibi kansa ya kiyaye ladubban iyali da jama'a qarama zuwa babba, kamar misalign ladabinsa cikin muhallin iliminsa kamar makaranta wajen aiki ma'aikata da dai sauransu…

Majalisin game gari na da ladabinsa a kebance, haka kebantacce majalisi na da ladabinsa , kowacce al'umma na da al'adunta da wayewarta, wanda ke son zama da wta qungiya ko wani aboki dole ya kiyaye ladubbansu, kowanne abu gwargwadon yadda ya ke, amma ladabin zuciya wadda ita zuciya it ace sarauniya ganagar jiki, idan ta gyaru ragowar gabobi za su gyaru, idan kuma ta lalace dukanin gabobi sun lalace, iadan malami ya lalce duniya za ta lalace, saboda haka gyaranta da ladabinta shi en jin tsoron Allah matsarkaki, ka ladabtar da zuciyarka da jin tsoron Allah.

Na shida:zama da malamai., lalle muslunci a wurare da dama ya umarce muda mu zauna da malamai mu matse su- ku masti malamai da gwiwowinku, kamar yadda luykmanu yak e fadawa dansa sa'ilin da yake masa nasiha – lalle zama da malamaina kawo stira da azurta a cikin gida biyu, game da neman ladubba:

يقول أمير المؤمنين علي  7: (جالس العلماء يزدد علمک ويحسن أدبک

Sarkin muminai Ali(as) na cewa: ka zauna da malamai iliminka zai qaru ladabinka zai kyawunta.

Abinda ake nufi da malami wanda kallonsa ibada ne shi ne wanda zancensa ke gasgata aikinsa, aikinsa ya gasgata zancensa. Idan yay i umarni da aiki to shi za a fara samu kan gaba cikin wannan aiki haka idan yay i hna da barin mummuna aiki shi za'a fara samu ya bari, shi ne malamin furucinsa ke qara maka ilimi, aikinsa ya qara maka kwadayin lahira, ganinsa ya tunatar da kai Allah, shui ne wanda aka umarce mu da tsiwirwirar ilimi daga gareshi, iadan bah aka to iadan kuka ga malami ya fiye kwadayin duniyarsa bai aiki da iliminsa ku tuhume shi, ka da ku karbi addininku daga gareshi, lalle shi ya na daga cikin barayin masu tare hanya barawon addini,

فَلْيَنْظُرِ الإنْسانُ إلى طَعامِه[7]

mutum ya yi duba zuwa ga abincinsa.

Imam baqir(as) ya ce: ai yay i duba wajen wa zai dauki ilimi.

Malami mai taqawa mai tsantseni wanda da z aka zauna da shi lalle ba makawa iliminka zai qaru ladabinka ya qaru.

Na bkwai:fahimta, da yawan lokuta fahimta tafi kebanta daga ilimi wani lokacin kuma ta qawance shi ta biyo bayansa, dole mutum ya ahimci rayuwarsa ya riski sirrikanta don ya ya san qimar kansa, ya kuma son mai ake nema daga gare shi don me aka halicci shi, mai manufar halittarsa,mu ne mi taimakon Allah mu roqi Allah kamar yadda imam zainul abidin dan husaini(as) ya yi

اللّهم ... اجعلنا من الذين تمسّكوا بعروة العلم وأدّبوا أنفسهم بالفهم[8]

Allah ina roqonka ka sanya mu daga cikin wadanda suka yi riqo da igiyarka suka ladabtar da kawukansu da fahimta.

Wanna na nufin mutum ba zai wadatu kadai da neman ladabi da ilimi da haquri da kusantar malamai ba tilas sai ya cudanya da addu'a da tawassali da Allah, shi motsi daga mutum ya ke albarka kuma na wurin ubangiji, dole a samu wnai hannu na gaibu da zai dinga tallafawa mutum cikin motsinsa da tafiyarsa zuwa ga Allah matsarkaki da ado da falala da dabi'u masu karamci, muna roqon Allah ya sanya daga cikin wadanda suka yi riqo da igiyar ilimi cikin dukkanin ayyukansu da zantukansu, suka ladabtar da kawukansu da fahimta da risker abubuwa da haqiqani:

اللهمّ أرني الحقائق كما هي  

( Allah ka nuna mini haqiqanin abubuwa kamar yadda suke )

na takwas : daga cikin alamomin mumii ya kasance mai gaskiya cikin maganganunsa da iliminsa tare da kansa da waninsa, lalle ita qarya na daga cikin alamar munafiki, tushenta kuma kafirci, saboda haka ta yiwu mumini ya yi sata da zina sai dai cewa ba ya qarya, Allah mai gaskiya kuma ya na tare da masu gaskiya, an umarce mu da mu kasance tare da masu gaskiya da kyawuntar dabi'u.

يقول أمير المؤمنين علي  7: (تحرّى الصدق وتجنّب الكذب ، أجمل شيمة وأفضل أدب

sarkin muminai ali (as) ya na cewa :ka yi bakin qoqari kan bin gaskiya ka qauracea qarya shi ne mafi kyawun hali da falalar ladabi.

ya kamace mu mu ladabtar da kawukanmu da gaskiya shi mumini qarya ba fita daga bakinsa ko da sau daya.

na tara : tsare rai , lalle ita rai na umarni da mummuna kuma iata tana dabi'a irinta wuta duk sand aka bata abin da ta ke kwadayi ka biye ma sha'awarta sai ta nemi qari ta ce:

هل من مزيد[9]

 ( shin akwai qari )

 ya zama tilas mutum ya yiwa zuciyarsa iyaka ya ladabtar da ita da sanya mata linzami yayin kwadayinta, sarkin muminai ali (as) ya ce: iyakance zuciya yayin kwadayi da tsoro na daga cikin mafifitan ladubba.

na goma : kamewa daga aikata haramun, ita zuciya ba ta wadatuwa da halaliya  , lalle shaidani da miyagun abokai da duniya mai rudarwa suna jan mutum zuwa halaka da aikata haramun, mumini ma'abocin hankali ya zama dole ya ladabtar da kansa da kamewa daga haramun.

قال أمير المؤمنين علي  7: (ضبط النفس عند الرغب والرهب من أفضل الأدب

 lalle sarkin muminai ali (as) ya na cewa: mafi kyawun ladabi shi ne wanda ya kameka daga haramun.

وَأمَّا مَنْ خافَ مَقامَ رَبِّهِ وَنَهى النَّفْسَ عَنِ الهَوى فَإنَّ الجَنَّةَ هِيَ المَأوى[10]

(amma wanda ya ji tsoran tsayuwa gaban ubangijinsa ya hani zuciyarsa daga barin biyewa son rai lalle aljanna ce makomarsa )

وَأمَّا الَّذينَ سعدوا فَفي الجَنَّةِ خالدين فيه[11]ا

amma wadanda sukayi arziqi suna aljanna suna masu dawwama ciknta.

Na sha daya : tsayawa bakin iyaka  daga cikin karin magana da ya shahara: kowanne abu idan ya wuce iyakarsa zai juya ya  zama kishiya

Ma'abocin hanakali ka aje abu a muhallinsa ba tare da wuce goda da iri ba ko taqaitawa, kun kasance matsakaiciyar al'umma mafi alheri al'amura matsakaitanta, ya zama tilas kowa ya ladabci kansa ya tsaya iyakarsa ka da ya shallake ta ka da ya qetare iyakokin ubangiji ya zalunci kansa da waninsa , farin ciki ga wanda ya san mtumcinsa bai shallake iyakarsa ba.

المؤمنين علي  7: (أفضل الأدب أن يقف الإنسان عند حدّه ولا يتعدّى قدره ).

 sarkin muminai ali (as) ya na cewa: mafificin ladabi shi ne mutum ya tasaya bakin iyakarsa ka da ya qetare  iyakarsa .

Na sha biyu : watsi da abota da miyagun abokai, mutum cikin gaggawa yak e dabi'antuwa da dabi'un waninsa, idan ya zauna da mutanen kirki lalle zai samu alheri da kyawunta da daukaka halinsa ya gyaru , amma idan ya zauna da mutanen banza lalle zai tasirantu da da su ya zama abin tuhuma, lalle ka qauracewa wuraren tuhuma a na sanin mutum ta hanyar abokinsa, fada mini da wanene ka ke abota ? zan fada maka wanene kai, kan wannan

الإمام الصادق  7: (أدّبني أبي بثلاث . قال لي : يا بني ، من يصحب صاحب السوء لا يسلم ، ومن لا يقيّد ألفاظه يندم ، ومن يدخل مداخل السوء يتّهم[12] )[

 imam sadiq (as) ke cewa : babana ya bani ladabi da abubuwa uku: ya ce mini: ya kai dana duk wanda ke abota da mugun aboki ba zai kubuta ba , duk wanda baiwa bakinsa linzami zai nadama, duk wanda ke kai kansa miyagun wurare za a tuhume shi.

وما أروع ما قاله الإمام الباقر  7، فإنّ المؤمن ملجم لا يتكلّم إلّا بما يرضي الله سبحانه من الذكر وقول الحقّ والنصيحة والموعظة وإرشاد الناس إلى الخير والصلاح والفلاح ، ومن الطبيعي أنّ مَن يدخل مواضع التهم ومداخل السوء أن يتّهمه الناس ، كما إنّ مَن عاشر أهل السوء والمنكر والفحشاء لا يسلم على نفسه ودينه وأهله وسمعته ، فلا بدّ أن نؤدّب أنفسنا بمثل هذه الآداب الإسلامية ونتجنّب مداخل السوء، ونقيّد ألفاظنا، ونجترّ الكلمات ولا نسرع ، فكثيرآ ما يندم الإنسان

 على كلامه ، ولا يندم على سكوته ، فإنّه إن كان الكلام من فضّة فالسكوت من ذهب ، وقد أفلح التقيّ الصموت . يقول أمير المؤمنين علي  7: (إذا فاتک الأدب فالزم الصمت [13]

Me ya fi kyawunta daga abin da imam baqir (as) ke fadi, lalle shi mumini cikin linzami yak e bai Magana sai cikin abin da Allah ya yarda daga zikiri da fadin gaskiya da nasiha da wa'azi da shiryara da mutane zuwa alheri da gyara da rabauta.

A dabi'ance duk wanda ya kai kansa miyagun wurare lalle muatne za su tuhume shi, haka duk wanda ya zauna da mutanen banza da munkari ma'abota alfasha ba zai kubutar da kansa da addininsa da mutuncinsa ba, ya zama tilas mu ladabtar da kawukan mu da ladubban muslunci mu qauracewa zakkewa miyagun wurare ababen tuhuma, muyi bakunan mu linzami, mu san mu zamu dinga cewa mu daina gaggawa da yawa mutum na nadama kana bin da ke fadi, amma bai nadama bisa yin shiru, lalle idan har zance daga azurfa ya ke to shiru zinariya ne, lalle ma'abocin taqawa mai yawaita shiru ya rabauta.

 sarkin muminai ali (as) ya na cewa: idan ladabi ya fauce maka to lazimci shiru.

Na sha uku: himmatuwa da wajibai, kamar yadda wurgi da aikata haramun na daga cikin ladabi haka sauke wajibai babu banbanci cikin kasantuwarsu na shari'a ko al'adu, ita rayuwar mutum na tsakanin korewa da tabbatarwa cikin Kalmar tauhidi, babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, ita wannan Kalmar ta tattaro watsi da dukkanin abubuwan bautar ta kuma tabbatar da bautar Allah daya rak mabuwayi, daga cikin ladabin mutum kiyayewa da himmatauwa da sauke wajibai ka da ya dinga sakaci da ko in kula da abin da yak e larura ne kansa, kamar yadda

قال أمير المؤمنين علي  7: (ومن أدبه ـأي أدب الإنسان ـ أن لا يترک ما لا بدّ منه[14]

sarkin muminai ali (as) ke fadi: daga cikin ladabin mutum bai ya sakaci da abin da ya zame masa tilas.

Na sha hudu: tsarkake dabi'u, lalle ya na daga cikin ilimi mai amfani abin da ke wajabta tsarkake zukata da dabi'u kamar yadda

قال أمير المؤمنين علي  7: (سبب تزكية الأخلاق حسن الأدب

 sarkin muminai ali (as)  ya fadi : sababin tsarkakar dabi'u kyawuntar ladabi.

Akwai lazimci da alaqa qarfaffa ta yiwu ma ya kai ga kasantuwarsa cikakkiyar  illa da ta ke hukunci tsakanin tsarkake dabi'a da kyawuntar ladabi, wanda bai tsarkake dabi;unsa ta qaqa ladabinsa zai zama ya kyawunta ? kadai dai mutum na samu tsira da fuffuka cikin sasannin karamci da daukaka da fuffuke biyu: fuffuken tsarkake zuciya da fuffuken kyawuntar ladabi.

Na sha biyar: kyawunta zamatakewa zamatakeawa na da na ta ladubban kebance, abin da ke tattara cikinta shi ne kyawuntar ladabi sakin fuska da dadada kalami da kyawunta ganawa cikin fagen abokantaka da qauna da makamantansu.

Haqiqani shi ne kowanne daya daga cikinsu na da nasa ladubban a kebance kadai dai mu ambaci muhimmansu da asalnsu na farko da jiga -jigai, amma juz'ansu da masadiq zamu fawwala hukunce hukuncnsu ga mai karatu zai iya fito da su daga abubuwan da muka ambata a baya wadanda suka dace da yanayinsa da inda ya ke rayuwa da al'ummarsa tare da wanda yak e mu'amala da shi, daga cikin muhimman ladubban zamatakewa  shi ne abin da

عن الشعبي قال : تكلّم أمير المؤمنين  7 بتسع كلمات ارتجلهنّ ارتجالا، فقأنَ عيون البلاغة وأيتمن جواهر الحكمة وقطعن جميع الأنام عن اللحاق بواحدة منهنّ ، ثلاث منها في المناجاة ، وثلاث منها في الحكمة ، وثلاث منها في الأدب 

 sarkin muminai ali (as) ya ce:

Daga sha'abi ya ce: sarkin muminai ali (as) ya fadi kalmomo tara take wadanada da su ya gutsure idaniyar balaga gwagwalan hikima sukai marici dukkanin mutane suka gaza risker daya daga cikinsu, uku daga cikin kalmomin munajati da ubangiji, uku daga ciki hikima, uku daga ciki ladabi:

 

(إلهي كفى بي عزّآ أن أكون لک عبدآ، وكفى بي فخرآ أن تكون لي ربّآ، أنت كما اُحبّ فاجعلني كما تحبّ ).

Amma wadanda ke ishara zuwa munajati ya na cewa: ubangijina ya ishene izza ace na kasance bawanka, ya ishe ni alfahari ka kasance ubangiji na , kai kamar yadda na ke so ka sanya ni kamar yadda ka ke so.

(قيمة كل امرئ ما يحسنه ، وما هلک امرؤ عرف قدره ، والمرء مخبوء تحت لسانه ).

 Ammma masu ishara ga hikima:

Qimar kowanne mutum abin da ke aikatawa, babu wani mtum da zai halaka matuqar ya san iyakarsa, mutum na boye qarqashin harshensa.

اُمنن على من شئت تكن أميره ، واحتج إلى من شئت تكن أسيره ، واستغنِ

[15] عمّن شئت تكن نظيره

Amma wadanda ke ishara ga ladabi kayi ni'ima ga wanda ka so zaka kasance sarkinsu, ka kafa hujja kan wanda ka so zaka zama daurarrensa, ka wadatu ga barin wanda ka so zaka zama  misalinsa.

an ce ladabi ya kasu kashi biyu : ladabin ruhi ladabin darasi, ladabin ruhi ya fi dauka kan na darasi kamar daukakar ruhi kan gangar jiki , saboda shi ladabin darasi ya na amfanarwa bai cutarwa , ladabin darasi ba tare da na ruhi ba baya kasancewa daga hankali kadai dai ya na gudana magudanar misalin tarbiyar da kewa dabbobi irinsu biri da giwa.

Jahadin zuciya na daga mafi girman jihadi

وَالَّذِينَ جَاهَدُوا فِينَا لَنَهْدِيَنَّهُمْ سُبُلَـنَ[16]ا

 ( wadanda su kayi qoqari cikin neman yardarmu lalle za mu shiryar da su hanyoyinmu)



[1] Biharul anwar m 14 sh 326

[2] Masdarin da ya gabata m 70 sh 573

[3] Biharul anwar m 13 sh 411

[4] Mujadala:11

[5] Zumar:9

[6] Fadir:28

[7] Abasa:24

[8] Biharul anwar m 94 sh 127

[9] Qaf:30

[10] Annazi'at:40

[11] Hudu:108

[12] Biharul anwar m 78 sh 261

[13] Biharul anwar m 71 sh 293

[14] Biharul anwar m 78 sh 400

[15] Biharul anwar m 77 sh 400

[16] Ankabut:69