فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN QAI
■ FASALI NA FARKO : MALHAMOMI NA FARI GAME DA
■ FASALI NA BIYU
■ FASALI NA UKU
■ DAGA FALSAFAR HAJJI CIKIN ALQUR'ANI
■ DAGA CIKIN SIRRIN AYAR HAJJI
■ KUFAIFAYIN HAJJI DA UMARA CIKIN DUNIYA DA LAHIRA KAMAR YADDA YA ZO CIKIN HADISAI
■ JIKKANTUWAR HAJJI GA ASALAN ADDINI
■ HAJJIN JAZZURU(RAQUMI) DA HAJJIN USFURI(TSATSTSEWALA
■ FASALI NA HUDU
■ DAGA SIRRIKAN HARAMIN MAKKA
■ Daga cikin sirrikan miqatai
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MAKKA MAI KARAMACI DA MASALLACIN HARAMI
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN DAKIN KA'ABA MAI DARAJA
■ DAGA SIRRIKAN DUTSEN HAJARUL ASWAD
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MUQAMU IBRAHIM
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN HADIMU DA WANDA AKE LAZIMTA
■ DAGA CIKIN SIRRKAN HAIMA (DAKIN) ISMA'IL(AS)
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MUSTAJAR DA RUKUNUL YAMANI
■ DALILIN SHAFAR RUKUNUL YAMANI
■ FALALAR MUSTAJAR DA LADUBBANSA
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN RIJIYAR ZAMZAM
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN DUTSEN SAFA DA DUTSEN MARWA
■ SIRRIKAN HAJJI WAJEN IMAMU SADIQ(AS)
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MIQATI
■ FASALI NA BIYAR
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN HAJJI
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN TALBIYYYA(FAXIN LABBAIKA
■ DAGA SIRRIKAN BARIN ABUBUWAN DA AKA HARAMTA
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN XAWAFI
■ DAGA CIKIN FALSAFAR XAWAFI
■ Daga cikin falsafar xawafin nisa'i
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN SALLAR XAWAFI
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN SA'AYI
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN SIRRIKAN SAISAYE DA ASKI
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN TARWIYYA
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN ARAFAT
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MAHS'ARUL HARAM
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN MINA
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN JIFAN JAMARAT
■ DAGA CIKIN SIRKAN HADAYA
■ DAGA CIKIN SIRRIKAN IBADUN CIKIN HAJJI
■ FASALI NA SHIDA
■ ku cika hajji da umara
■ XAWAFIN BANKWANA DA LADUBBANSA
■ KARBUWAR HAJJI DA HASKENSA
■ ADADIN HAJJIN DA ANNABI YA YI DA UMARARSA
■ HAJJIN ANNABAWA
■ TSUGUNARWAR DA IBRAHIM (AS) YA YIWA XANSA DA MATARSA A GARIN MAKKA
■ XAGA HARSASHIN GININ XAKIN KA'ABA DA HANNUN IBRAHIM DA ISMA'IL(AS)
■ QISSAR YANKAN IBRAHIM GA XANSA ISMA'IL{AS}
■ KHATMA
■ CIKIN ZIYARAR ANNABI MAFI GIRMA MUHAMMADU DA IYALANSA TSARKAKA.
■ DAGA CIKIN LADUBBAN BIRNIN MADINA HASKAKKA.
■ DAGA CIKIN FALALOLIN ZIYARA DA SIRRIKANTA
■ DANGANTAKAR MANZON ALLAH(S.A.W) DA AL'UMMA

FALSAFAR HUKUNCE-HUKUNCE DA SIRRIKANTA

 Da sunan Allah mai rahama mai jin qai

Allah matsarkaki ya umarcinsa badaxinsa masoyinsa Ibrahim da yay i yekuwar hajji cikin mutane bayan Ibrahim da xansa isma'il sun kammala xaga harsashin ginin xakin ka'aba

 (وَأَذِّن فِي آلنَّاسِ بِالْحَجِّ يَأْتُوکَ رِجَالاً وَعَلَى كُلِّ ضَامِرٍ يَأْتِينَ مِن كُلِّ فَجٍّ عَمِيقٍ )[1]

Ka yi yekuwa  cikin mutane da ibadar hajji za su zo maka da qafafuwansu za su kan dukkaninin xankwararren doki za su daga rango mai nisa.

Cikin kowacce shekara miliyoyin musulmi ke amsa kiran Allah saboda shauqi da soyayya sai su nufi xakin Allah mai alfarma domin girmama wuraren ibadun Allah, zukata na begen garin makka da ka'aba mai daraja

 (فَاجْعَلْ أَفْئِدَةً مِنَ آلنَّاسِ تَهْوِي إِلَيْهِمْ ) [2]

Ka sanya zukata suna bege zuwa garesu.

Daga kowanne yankunan duniya mutane na zuwa hajji da qafafuwan wsu kuma haye kan ababen sufuri da launani daban-daban da harsuna daban-daban da jinsuna mabanbanta da mazhabobi da dai sauransu….

Sautin kowanne xayansu sauti ne guada xaya rak na tauhidi da wahada

(لبّيک اللّهُمّ لبّيک لبّيک لا شريک لک لبّيک ).

Mun amsa kiranka ya Allah mun amsa kiranka babu abokin tarayya gareka mun amsa kira.

Me yafi kyawu daga waxancan wuraren ibada tsarkaka da wancan taron muslunci na duk duniya wanda ake yinsa dukkanin shekara cikin qididdigaggun kwanaki sanannu, me ya fishi alfanu addini da duniya da dukkanin sasanninta na wayewa da zamantakewa da kasuwanci da siyasa da dai sauransu waxanda musulmi ke halarta dukkanin waxannan na daga albarkar hajji, da albarkar xakin ka'aba mai alfarma. Daga qarqashin ayoyi masu alfarma zamu iya nuni da ishara a taqaice zuwa ga jula daga falsafar hajji cikin wasu nukxoxi kamar haka:

 

(إِنَّ أَوَّلَ بَيْتٍ وُضِعَ لِلنَّاسِ لَلَّذِي بِبَكَّةَ مُبَارَكاً وَهُدىً لِلْعَالَمِينَ )[3]

Xaki na farko da aka sanya domin mutane shi ne wannan wanda ya ke a bibakka mai albarka da shiriya ga mutane.

Bakkatu it ace makka mai karamci, ko kuma dukkanin wani waje da mutane ke turmutsitsi cikinsa, kamar yadda ya ke qasqantar da masu girman kai, ko kuma saboda kukan da ake yi kewaye da ita da cikinta, sai Allah ya sanya `yantaccen xaki wanda ya yantar shi daga ruwana xufana wanda ya yi sandaiyyar halakar mutanen annabi nuhu(as), ko kuma kasantuwarsa mafi tsufan xaki da aka sanya domin mutane wanda ya kasance shiriya garesu kuma mahallin saukar albarka da bayyanannan luxufi da boyayye game gari da kebantacce.

Ita albarka it ace alheri tabbatacce madawwami wanda bai yankewa makka ba ta kebantu da mazauna cikinta ta kowa da kowa ce ita shiriya ce ga dukkanin mutane tun daga adamu har zuwa tashin qiyama ga dukkanin wanda ya nufe ta da tsarkin niyya.

2- makoma da aminci ga mutane

  (وَإِذْ جَعَلْنَا آلْبَيْتَ مَثَابَةً لِلنَّاسِ وَأَمْناً( [4]

Ya yin da muka sanya xakin makoma ga mutane da aminci.

Lalle Allah matsarkaki ya umarci badaxinsa Ibrahim ya riqi alkawali gareshi tare da xansa isma'il

 

(أَن طَهِّرَا بَيْتِيَ لِلطَّائِفِينَ وَآلْعَاكِفِينَ وَآلرُّكَّعِ آلسُّجُودِ)[5]

Da su tsarkake xakin ga masu xawafi da mazauna da masu ruku'I da sujjada.

Lalle `ya`yayen Ibrahim da addinansu guda uku: yahudu, nasara, muslunci, sun kasance suna ziyartar xakin Allah mai alfarma xakin tsarki da ibada, lalle suna fakewa da komawa ga wannan xakin aminci don guje ma cutuwa da zaba mai tsanani.

3- tsayuwa da tsari ga mutane:

 (جَعَلَ آللهُ آلْكَعْبَةَ آلْبَيْتَ آلْحَرَامَ قِيَاماً لِلنَّاسِ )

             Allah ya sanya ka'aba xaki mai alfarma tsarare ma'aunin addini ga mutane.

Dag cikin haduffa da falsafar aiko da annabawa da manzanni shi ne tsayara da adalci tsakankanin mutane

 (وَأَنزَلْنَا مَعَهُمُ آلْكِتَابَ وَآلْمِيزَانَ لِيَقُومَ آلنَّاسُ بِالْقِسْطِ)

Mu ka saukar musu da littafi da ma'auni don mutane su tsyu kan adalci.

Daga cikin mafi bayyanar dalilan da suke taimakawa mutane don tsayuwa da kawo sauyi cikin fagen tunaninsu da suluki it ace xakin ka'aba mai daraja

قال الامام الصادق  7: «لا يزال الدين قائماً ما قامت الكعبة » .[6]

Imam sadiq(as) ya ce: addini ba zai gushe ba a tsaye matuqar ka'aba na tsaye.

Dukkanin mutnae bai xaya suke babu banbanci cikin ziyartar xakin ka'aba mai alfarma.

 (إِنَّ آلَّذِينَ كَفَرُوا وَيَصُدُّونَ عَن سَبِيلِ آللهَ وَآلْمَسْجِدِ آلْحَرَامِ آلَّذِي جَعَلْنَاهُ لِلنَّاسِ سَوَاءً آلْعَاكِفُ فِيهِ وَآلْبَادِ .( [7]

Lalle waxanda suka kafirta suna katange mutane daga tafarkin Allah da masallaci mai alfarma wanda muka sanya shi daidaito ga mutane cikinsa babu banbanci daga mazauni da baqauye.

Dukkaninsu Allah ya kirasu zuwa ga hijira daga sabo zuwa ga xa'a daga nesata zuwa ga kusanta daga duniya zuwa ga lahira, daga yuqurawa da motsawa da sauyi na duk duniya daga hajji daga xakin Allah mai alfarma daga ka'aba maxaukakiya.

 


 

 

DAGA CIKIN SIRRIN AYAR HAJJI

 Allah maxaukaki cikin littafinsa mai hikima ya na cewa

(وَللهِ عَلَى آلنَّاسِ حِجُّ آلْبَيْتِ مَنِ آسْتَطَاعَ إِلَيْهِ سَبِيلاً وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ الله غَنِيٌّ عَنِ الْعَالَمِينَ.([8]

Kuma akwai ziyartar xakin Allah kan mutane ga wanda ya samu da zuwa gareshi, wanda ya kafirta lalle shi Allah mawadaci ga barin talikai.

A wani wajen kuma matsarkaki ya ce:

 

: (وَأَتِمُّوا آلْحَجَّ وَآلْعُمْرَةَ للهِ)[9]

Ku cika hajji da umara domin Allah.

  (آلْحَجُّ أَشْهُرٌ مَعْلُومَاتٌ فَمَن فرَضَ فِيهِنَّ آلْحَجِّ فَلاَ رَفَثَ وَلاَ فُسُوقَ وَلاَ جِدَالَ فِي آلْحَجِّ وَمَا تَفْعَلُوا مِنْ خَيْرٍ يَعْلَمْهُ آللهُ وَتَزَوَّدُوا فَإِنَّ خَيْرَ آلزَّادِ آلتَّقْوَى وَآتَّقُونِ يَا أُولِي آلاْلْبَابِ.( [10]

Hajji wasu sanannun watanni ne, duk wanda ya yi niyyar hajji cikin waxannan watanni, to babu jima'I babu fasiqanci babu jayayya cikin hajji, dukkanin abin da kuka aikata daga alheri Allah na sane da shi, kuyi guzuri lalle mafi alherin guzuri shi ne guzurin taqawa, kuji tsorona yak u ma'abota hankula.

tun farko ayoyin masu daraja suna nuni kan wajabcin hajji ga wanda yake da ikon zuwa

 

 (وَللهِ عَلَى آلنَّاسِ).

Allah na da haqqi kan mutane, bayanin (Allah na haqqi) na nuni kan wajabci da iklasi da iayakance ibadarsa.

(على الناس )

Kan mutane: na nuni da cewa shi hajji ya kasance tun zamani da  tun daga adamu har zuwa tashin qiyama

عن الامام الصادق  7: إن الحجّ لعامّة الناس ، فلا يختصّ بزمان ولا مكان ولا أقوام ولا طوائف ولا اُمم ولا شعوب.

An karbo daga iama sadiq(as) lalle shi hajji ya game dukkanin mutane bai kebanta da wani zamani ko wani bigire ko wasu mutane   ko wasu qungiyoyi ko wasu al'ummu ba.

Kalamar hajji a luggance idan akai ma harafin ha'un wasalin fataha to ta samo asaline daga

حجّ يحجّ حجّاً فهو مصدر يدلّ على مجرّد الحدث من دون أن يقترن بأحد الأزمنة الثلاثة ـ الماضي والحاضر والمستقبل ـ وانّه بمعنى القصد المتكرّر.

Ya yi hajji ya na yin hajji, wanda asalinsa masdari ne da ke shiryarwa zuwa ga faruwar wani abu ba tare da ya cuxanya da zamani uku ba madi, mudari'I da amri, lalle shi ya na da ma'anar maimaita nufi.

Amma cikin isxilahin: ya na nufin wsu kebantattun ibadu cikin sanannun kwanaki qididdigaggu.

Amma hijji idan anyiwa ha'un wasalin kasara: ta ya na nuni ga sunan masdari da ya shiryarwa game da abin da ke faruwa a hajji daga kaufaifayin ma'anawiyya da ruhiyya, shi masdari na shiryarwa kan asalin aiki sannan sunan masdari kuma na shiryarwa game da abin da ke faruwa cikin aikin daga sauke nauyin shari'a da kusantar Allah matsarkaki.

Hajjin da ubangiji ya ke son kayi bai taqaitu da gundarin asalin aiki ba, a'a ana buqatar kiyaye janibin ma'anawiya cikin hajji da kufaifayin ruhiyya da muqamai maxaukaka wanda Kalmar taqawa ta tattaro su, kamar yadda wannan banbanci ya guda tsakanin Kalmar

الصوم والصيام

Abin da ka rubuta aka wajabta kan muminai shi ne siyam azumi kamar yadda aka wajabta shi kan waxanda suka gabace su, bawai gundarin azumi zalla ba sakamakon da yawan lokaci za ka samu mai azumi baai da wani rabo cikin azuminsa in banda shan yunwa da ishurwa, abin da aka nufa cikin azumi shi ne samun taqawa, haka cikin hajji.

 (وَتَزَوَّدُوا فَإِنَّ خَيْرَ آلزَّادِ آلتَّقْوَى )[11]

Ku yi guzuri lalle mafi alherin guzuri shi ne guzurin taqawa.

Sai dai cewa ya zo cikin hadisan da muka kawo cewa:

«ما أكثر الضجيج وأقلّ الحجيج »

Me yafi yawa daga masu iface iface me ya fi qaranci daga mahajjata.

 (وَقَلِيلٌ مِنْ عِبَادِيَ آلشَّكُورُ)[12]

 kaxanne daga bayina masu godiya.

Lalle mafi yawancinsu zaka same su kamar dabbobi kai suni dabbobi ma batan hanya.

Sannan abin da ake nufi da xakin Allah, shi ne xakain nan `yantacce wanda Allah ya sanya shi domin mutane tun farkon duniya, ya kasance `yantacce daga ruwan xufana, kamar yadda ya kasance mai adaraja kamar matsayin tsihon kayan gado lalle ambatonsa ya zo cikin qur'ani har wurare goma cif cif.

 (من استطاع إليه سبيلاً)

Ga wanda ya samu iko gareshi.

Wannan iko bai taqaitu da iko cikin dukiya ba da lafiyar jiki ya haxa har da amincin hanya kamar yadda malaman fiqihu suka ambaci haka cikin risalolinsu.

(ومن كفر فان الله غنيّ عن العالمين )

Duk wanda ya kafirce lalle Allah mawadaci ne ga barin talikai.

Duk wanda ya bar zuwa aikin hajji ya qi alhalin yana da halin zuwan to lalole ya kafircewa ni'imar Allah, wannan na daga kafirci na aiki, mala'ika zai zo masa lokacin cire ransa ya ce masa: mutu ka na bayahude ko banasare ko bamajuse, ba zai mutu cikin musluncin muhammadu na asali, ya Allah ka tsare daga irin wannan mutuwa.

Sannan shi wanda ya kafircewa ni'imar Allah babu abin da ya ke cutarwa da ya wuce kansa, lalle shi Allah mawadaci ne daga mahajjaci da hajjinsa bari ma dais hi mawadaci ne daga dukkanin talikai, shi mawadaci ne a zatinsa, lalle shi ne tsantsar kamala da kamala tsantsa cikin zati da siffofin aiki

(أَنتُمُ آلْفُقَرَاءُ إِلَى آللهَ وَآللهُ هُوَ آلْغَنِيُّ آلْحَمِيدُ) [13]

Ku ne matalauta zuwa ga Allah shi Allah mawadaci ne godadde.

Bai cutar da shi wanda ya bata daga barin tafarkinsa ya zakkewa sabonsa ya kafircewa ni'imarsa, shi wanda ya aikata hakan shi ne wanda yay i hasara mabayyaniya.

Sannan daga cikin abin da ke nuni kan wajabcin hajji ga wanda ke da iko sune fuskoki masu zuwa:

1 ـ (لله على الناس )

1-Allah na da haqqi kan mutane.

Wannan aya jumla ce kabariya wanda tafi qarfi daga jumla insha'iyya da ke nuni kan wajabcin hajji da assasar hukunci da zartuwarsa.

2- lalle ita jumlace ismiyya(ta suna) tafi jumla fi'iliya(aikatau) nuni kan wajabcin hajji sakamakon shiryarwarta kan tabbatuwa da dawwama.

3- harafin lamul taklif cikin(lillahi) qarfafa ne da ya cakuxa Kalmar allahu wanda shimfixa ne kan mubtada, wanda shi ne hajji saboda sai ya zamanto ya nuni kan iyakancewa.

4- ambaton alal nasi bayan faxinsa lillahi hakan na fa'idantar da qarfafa da ya ke shiryarwa kan wajabci.

5- ambaton mukallafai har sau biyu(alal nasi… manista xa'a ilaihi) maimakon ya ce Allah na da haqqi kan masu iko, cikin ayar anyi ixlakqin ba'ari kan kowa da kowa, wanda hakan na fa'idantar da qarfafawa da wajabcin hajji.

6- bayyana wanda ya bar zuwa aikin hajji matsayin kafiri, wanda ya na daga kafircin aiki:

عن الامام الصادق  7: «من مات ولم يحجّ حجّة الاسلام لمن يمنعه من ذلک حاجة تجحف به أو مرض لا يطيق فيه الحجّ ، أو سلطان يمنعه ، فليمت يهوديّاً أو نصرانيّاً».

Daga imam sadiq(as) duk wanda ya mutu bai je aikin hajjin wajibi ba,  wanda wata buqata ta hana shi ko kuma wani ciwo da ba zai iya zuwa hajji ba cikinsa, ko kuma wani basarake ya hana shi, sai ya mutu bayahude ko banasare.

Wannan na nuni da wajabcin hajji nan take idan ka samu iko da dam aka da ka jinkirta kai ta sanya lokaci har mutuwa ta riskeka sakamakon baka san lokacin mutuwarka ba.

7- Allah bai damu da wanda ya bar zuwa hajji ba da gangan cikin faxinsa maxaukaki matsarkaki:

(فان الله غنيّ عن العالمين )

Lalle shi Allah mawadaci ne ga barin talikai.

Ba wai kaxai ya wadatu ga wand aba suje hajji kai ga dukkanin taliakai.

Sannan cikin hajji akwai sirrika da hikimomi wanda kammalallen imani ya tattara su da mafara da makoma ga Allah da ranar lahira, da abin da ke tsakankaninsu daga imani da manzanni da littafan da aka saukar musu, da iamanci bayan manzanci.

Na naqashceka ka duba wannan hadisi ma daraja:

عن الامام الصادق  7 في سرّ من أسرار الحجّ وهو التذكّر بيوم القيامة ، وفي خبر آخر من أسراره الاختبار والامتحان .

Daga imam sadiq(as) cikin sirrin hajji shi ne tunatawa da ranar qiyama, a wani hadisin kuma shi hajji jarrabawa ce da gwaji.

قال  7: «وإعلم بأنّ الله تعالى لم يفترض الحجّ ولم يخصّه من جميع الطاعات بالاضافة إلى نفسه بقوله عزّوجلّ : ولله على الناس حجّ البيت من إستطاع إليه سبيلاً، ولا شرع نبيّه  6 سُنّة في خلال المناسک على ترتيب ما شرّعه للاستعداد والاشارة إلى الموت والقبور والبعث والقيامة بمشاهدة مناسک الحجّ من أوّلها إلى آخرها لاُولى الألباب واُولى النهى[14]

 

Ya ce: ka sani cewa Allah maxaukaki bai farlanta hajji ba ba kuma bai kebantar da shi ba daga dukkanin biyayya ba da jingina ya zuwa kansa, Allah mai girma da xaukaka na cewa: Allah ya farlanta hajji ga waxanda suke da iko zuwa gareshi, annabinsa bai sunnanta wata sunna ba cikin ibadun hajji a tsare misalin yadda ya shar'anta shi don tanadi da ishara zuwa ga mutuwa da kabari da tashin daga kabari da tashin kiyama da halartar tun daga farko har zuwa qarshe ga ma'abota hankula.

Babban malami quxubul rawandi cikin littafin lubbul albabi, ya rawaito cewa: yanayi da halayen yay i kama da na mutuwa, kamar yadda mutummke rubuta wasuiyyarsa ya yin da zai bar duniya haka ma ya ke rubutawa lokacin tafiyar hajji, kamar yadda mai hajji ke hawan taguwarsa don zuwa hajji haka ma mamaci ke hawa makara don ya qarasa kabari, kowanne mutum da sannu zai shiga makararsa ya na xauke hanun makusanta da maqiya ya na so ko bai so.

Wankan xaura haramin hajji kamar wankan janaa'iza ne, xaura farin kyalle da mahajjaci key i yay i kama da likkafanin mamaci. Idan ya baro miqati kamar misalin fitowa daga kabari ne, faxin labbaika kamar amsa addu'a ne, z aka gashin yay i buxu buxu gashin kansa wargaje ba tare da tajewa kai kace misalign wanda ya fito daga cikin kabarinsa ne, duk sa'ilin da ya shiga wani hanya da ke kan dutse sai ya tuna da ta lahira, saransa ya tsira daga gareta.[15]

الكافي بسنده عن عيسى بن يونس قال : كان أبي العوجاء من تلامذة الحسن البصري ، فانحرف عن التوحيد، وقدم مكّة متمرّداً وإنكاراً على من يحجّ ، وكان يكره العلماء مجالسته ومساءلته لخبث لسانه وفساد ضميره ، فأتى أبا عبدالله7 فجلس في جماعة من نظرائه فقال : يا أبا عبدالله إن المجالس أمانات ولابدّ لكلّ من به سعال أن يسعل ، أفتأذن في الكلام ؟ فقال : تكلّم ، فقال  : إلى كم تدوسون هذا البيدر (أي شبّه الكعبة والطائفين بالحيوانات التي لا تعقل تدور حول بيدر الطعام ) وتلوذون بهذا الحجر وتعبدون هذا البيت المعمور بالطوب وتهرولون حوله هروة البعير إذا نفر؟ إن من فكّر في هذا وقدّر، علم أن هذا فعل أسّسه غير حكيم ولا ذي نظر، فقل فانّک رأس هذا الأمر وسنامه ، وأبوک اُسّه وتمامه .

فقال أبو عبدالله 7: «إنّ من أضلّه الله وأعمى قلبه استوخم ولم يستعذ به ، وصار الشيطان وليّه وربّه وقرينه يورده مناهل الهلكة ، ثمّ لا يصدره ، وهذا البيت استعبد الله به خلقه ليختبر طاعتهم في إتيانه ، فحثّهم على تعظيمه وزيارته ، وجعله محلّ أنبيائه وقبلةً للمصلّين إليه ، فهو شعبة في رضوانه ، وطريق يؤدّي إلى غفرانه ، منصوب على إستواء الكمال ، ومجمع العظمة والجلال ، خلقه الله قبل دحو الأرض بألفي عام ، فاحق من أُطيع فيما أمر وانْتُهيَ عمّا نهى عنه ، وزجر الله المنشئ للأرواح والصور» .[16]

Alkafi da isnadinsa daga isa ibn yunusa ya ce: ibn abul auja'I ya kasance daga almajiran hasanul basari, sai ya karkace daga tauhidi, ya zo makka alhalin ya na  munkiri mai tsaurin kai kan wanda ke zuwa hajji, malamai sun kasance suna kyamar zama da shi da tambayarsa sakamakon munin kalamansa da gurbatar zuciyarsa, sai ya je majalisin baban Abdullah(as) ya zauna cikin tsarikunsa ya ce: ya baban Abdullah lalle majalisai na da amanoni wajibi ga duk wanda ke son yi tari ya yi tarinsa, shi ko z aka bani izini yin Magana? Sai imam ya ce masa: yi maganarka, sai ya ce: ya zuwa ina zaku karanta wannan masissika, ya kamanta xakin ka'aba da masu kewaya ta don xawafi da dabbobin da basu da hankula da suke kewaya masissikar abinci) kuna fakewa da wannan dutse kuna bautawa wannan xaki da aka gina da tubali kuna sassarfa irin sassarfa raqumi sa'ilin da aka koreshi? Dukkanin wanda ya staya ya yi tunani ya qaddara zai gane cewa wannan aiki ba ma'abocin hikima ba ne da nazari  ya assasashi, ya ce masa ai kai jagoran wannnan al'amari kuma ahalinsa, babanka ya assasshi ya kammala ka bani amsa.

Sai baban Abdullah(as) ya ce: lalle dukkanin wanda Allah y abatar da shi bya makantar da zuciyarsa ba zai taba ganin gaskiya ba dadai ba zai taba sanin daxinta ba, shaixani zai ksance masoyinsa ubangijinsa abokin cuxanyarsa zai kuma kais hi ga halaka ba kuma zai taba fitar da shi da ga gareta ba. shi wannan xaki Allah ya bautar da bayinsa da shi don ya gwada biyayyarsu cikin ziyartarsa, sai ya kwaxaitar da su kan girmama shi da ziyartarsa, ya kuma sanya shi mahallin annabwansa alqibla masallata, shi wani reshe ne daga yardar Allah,  shi wata hanya ce da ke kaiwa ga gafarar ubangiji wanda aka nassaba kan daidaito da kamala, shi matattarar girma ne , Allah ya halicce shi gabanin shimfixa qasa da shekara dubu biyu, shi ne mafi cancanta wanda akaiwa biyayya daga abin da ya yi umarni da shi, aka hanu daga abin da ya yi hani daga gareshi, Allah ya tsawatar maqagin ruhi da surori.

 

 


 

KUFAIFAYIN HAJJI DA UMARA CIKIN DUNIYA DA LAHIRA KAMAR YADDA YA ZO CIKIN HADISAI

 

 

Lalle shi hajji wani alqawali daga ga mutane, cikinsa akwai abu8buwa dake alamunta adddini da muslunci, ya tattaro tsakankanin asalansa da reshensa daga sallah da azumi da jihadi da zakka da kumusi da umarni da kyakkyawa da hani daga mummuna da wilaya da bara'a

قال الامام الصادق  7: «ودّ من في القبور لو أنّ له حجة بالدنيا وما فيها»[17]

Imam sadiq(as) ya ce: wanda ke cikin kabari zai qaunaci ace  yana da hajji guda xaya rak a duniya da abin da ke cikinta.

Lalle mahallin hajji da zamaninsa da abin da ke cikinsa daga ibadu da wuararen ibadu dukkaninsu suna daga abubuwa da ke sanyawa tunawa da Allah

 (إِنَّ آلصَّفَا وَآلْمَرْوَةَ مِن شَعَائِرِ آللهِ)

Lalle safa da marwa na daga wuraren iabadr Allah.

Domin bayanin himmatuwar maqagin shari'a tsarkakakke kan kiayaye wuraren ibadu da ya sanya su daga cikin wurare masu alfarma.

(وَمَن يُعَظِّمْ حُرُمَاتِ آللهَ فَهُوَ خَيْرٌ لَّهُ عِندَ رَبِّهِ )[18]

Duk wanda ya kiyaye alfarmomin Allah lalle hakan alheri ne gareshi wajen ubangijinsa.

                                                                          

  (ذلِکَ وَمَن یعَظِّمْ شَعَائِرَ آللهَ فَإِنَّهَا مِن تَقْوَى آلْقُلُوبِ [19] .(

Wancan ne duk wanda ya girmama wuraren ibadun Allah lalle ita na daga taqawar zukata.

Sannan daga cikin abin da ke nuni da xayantar Allah da qagarsa shi ne ibadun hajji.

 

 (فِيهِ آيَاتٌ بَيِّنَاتٌ مَقَامُ إِبْرَاهِيمَ ) [20]

Cikinsa akwai ayoyi mabayyana muqamu Ibrahim.

  (فَاجْعَلْ أَفْئِدَةً مِنَ آلنَّاسِ تَهْوِي إِلَيْهِم )[21]

Ka sanya zukatan mutane su karkata da bege garesu.

Hajji na daga cikin manya manyan ni'imomin Allah.

(وَإِن تَعُدُّوا نِعْمَةَ آللهَ لاَ تُحْصُوهَا)[22]

Da za ku qidaita ni'imomin Allah ba ku iya iyakance su.

Wane zai iya qirga kufaifayin hajji da sirrikansa da fa'idojinsa da ni'imominsa cikin duniya da lahira? Nesa nesa, kwata kwata babu mai iyawa, kaxai dai zamu mu iya xan kamfata daga tafkin haskensa gwargwadon yalwar tafin hannuwan m, mu na sa ran qosar da ba'arin masu kishirwa ilimi da irfani, ba mu da wata dacewa face daga Allah maxaukaki mai girma.

Ga wsu `yan kaxan xa ckin cokali daga kufaifayin hajji da umara daga abin da ya zo daga riwayoyi masu daraja zamu taqaitu da kawo nassinsu mu barwa mai karatu ta'aliqi da sharhi da kansa daga \|w    basirarsa da iliminsa da wayewarsa da kaifin basirarsa daga abin da yake da shi daga taskokin ilimi da ma'arifa:

1 lamuncin mahajjaci na kan Allah idan ya wanzar da rayuwarsa ya dawo da shi zuwa ga iyalinsa idan kuma ya karbi ransa ya shigar da shi aljanna.

2- ladan hajji aljanna ladan umara kankare dukkanin zunubi.

3- duk kanin wanda ya yi zaton cewa Allah ba zai gafarta masa bayan hajji lalle hakan na daga ckin babban laifi.

4- Allah na rubuta ladan kyawawan aiki goma ga dukkanin taku guda, ya kuma kankare masa zunubi goma.

5- Allah zaikare shi cikin iyalinsa.

6- zai kasance cikin aminci duniya da lahira.

7- zai samu yardar Allah

8- ya na cikin hasken hajji matuqar bai aikata zunubi ba.

9- idan ya roqi  Allah zai bashi, idan ya yi addu'a zai amsa masa, idan ya nemi cetonsa zai ceceshi, idan ya kame bakinsa Allah zai canja masa cikin kowanne dirhami da dirhami dubu, a wani hadisin da dirhami miliyan.

10- mahajjaci na cikin lamuncewar Allah idan kuma yam utu ya ne mia fuskantar hajji Allah zai gafarta masa zunubansa, idan ya mutu alhalin ya riga ya xaura harami Allah zai tashe shi ranar qiayama ya na mai amsa kira ya na faxin labbaika, idan yam utu cikin xayan haramai biyu Allah zai tashe cikin amintattu, idan kuma yam utu ya na mai dawowa daga aikin hajji Allah zai gafarta masa dukkanin zunubansa.

11- shi hajji jahadin raunana ne, imamai(as) sunce mu ne raunana.

12-  idan mutum ya fito aikin hajji ba zai gushe ba cikin xawafi har ya koma gida.

13- dukkanin wanda yam utu kan hanyar zuwa makka ko dawowa daga gareta haqiqa ya aminta daga mafi girma firgicin qiyama da tsoro.

14- hajji da umara kasuwanni ne daga kasuwannin lahira, dukkanin mai aiki cikin yana maqotaka da Allah, idan ya riski abin da ya ke fata Allah zai gafarta masa, idan ajali ya hana shi cimma abin da yake fata ladansa zai tabbata.

15- hajji kashe uku ne:  mafi falalar rabo shi ne hajjin da aka gafartawa ma'abocinsa dukkanin zunubansa da suka gabata da wanda za su zo nan gaba, Allah ya tseratar da shi daga azabar kabari, na biyun kuma shi ne hajji da aka gafartawa ma'abocinsa daga zunubansa da suka gabata, sai ya sake sabon aiki cikin kwanakin da suka rage a rayuwarsa , na ukun kuma shi ne wanda ya fi su qarancin rabo shi ne mutumin da ake kiyaye shi cikin iyalinsa da dukiyarsa. A wata riwayar ma ance ba a karbar hajjinsa.

16-  masaoyin ahlul baiti ana gafarta masa, waninsa kuma ana kiyaye shi cikin iyalinsa da dukiyarsa.

17- mahajjaci da wanda ya yi umara  suna dawowa gida kamar misalign jinjirin da aka Haifa, xayansu zai mutu qanqanin yaron da ba laifi kansa, xayan kuma zai rayu kamar misalign yadda ma'asumi ke rayuwa.

18- mahajjaci ya rabauta, idan aka ce wane ya je hajji ma'ana wane ya rabauta.

19- lalle Allah mai girma dea xaukakana yin gafara da ga mahajjaci da iyalansa, da abokan mu'amalarsa da duk wanda mahajjai ke nemawa gafara da ragowar kwanakin watan hajji da muharrama da safar da rabi'u auwal har zuwa ishirin ga watan rabi'u akar.

20- mhajjaci iadan ya shiga makka Allah zai wakilta masa mala'iku biyu da za su dinga yi msa gadin xawafinsa da sallarsa da sa'ayinsa, idan ya tsaya tsayuwar Arafat sais u bugi kafaxar damansa su ce masa: amma dukkani akinka da ya gabata yanzu baka da matsalarsa, sai ka duba qaqa zaka kasance nan gaba cikin abin da z aka fuskanta.

21- cikin faxainsa maxauakaki(ku gudu zuwa ga Allah) ma'ana ku tafi hajji.

22- hajji da umara suna korar talauci da zunubi kamar yadda zuga zugi ke kora da narkar da tsatsar jikin qarfe.

23- mahajjaci da mai umara suna cikin liyafar Allah, zai musu kyauta da gafara.

24- duk wanda ya nufi zuwa hajji

25- lalle Ibrahim(as)b ya yi yekuwa cikin mutane da zuwa aikin hajji, sai ya ce: yak u mutane lalle ni badaxin Allah ne , lalle Allah ya umarce ku  da ziyartar wannan xaki ku ziyarce shi, sai9 waxanda ke son hajji suka amsa yekuwarsa har zuwa ranar qiyama. Farkon waxanda suka fara amsa yekuwarsa sune mutanen qasar yaman.

26- ku je hajji da umara jikkunanku za su sami lafiya, arziqinku zai yalwata, imaninku ya gyaru, zaku xauki nauyin muatne da nauyin iyalanku.

27- na umarce ku da hajji ku dawwama kan zuwa hajji, lalle cikin dawwamarku akwai tukuxewar sharrin duniya da bala'inta daga barinku, da tsorace tsorace ranar qiyama.

28- duk wanda ya je hajji sau biyu ba zai gushe ba cikin alheri har zuwa mutuwarsa.

29- duk wanda ya je hajji sau uku talauci ba zai taba shafarsa ba.

30- kuje hajji za ku wadatu.

31- ban ga wani abu mai saurin kawo arziqi da Korar talauci fiye da dawwama kan zuwa hajji.

32-  haqqin hajji shi ne kasancewa shi liyafa ne zuwa ga ubangijinka, kuma guduwa ne daga zunubinka, da shi ne za akarbi tubanka da hukunta farillar da aka wajabta kanka.

33- haji da umara na korar talauci, suna kankare zunubai, suna wajabta aljanna.

34- wanda yak i zuwa aiki hajji da gangan ya yi ta sa rana da lokaci ya na xagawa har ajali ya riskeshi Allah zai tasheshi ranar qiyama bayahude ko banasare.

35 – cikin faxinsa maxaukaki:

 (وَمَن كَانَ فِي هذِهِ أَعْمَى فَهُوَ فِي آلاْخِرَةِ أَعْمَى وَأَضَلُّ سَبِيلاً) [23]

Duk wanda ya kasance cikin wannan duniya makaho lalle shi zai tashi qiyama makaho mafi batan hanya.

Shi ne wannan da yake jinkirta zuwa hajji da gangan har ajali ya riskeshi.

36- hajji biyu ne hajji domin Allah da hajji domin mutane, duk wanda ya je hajji domin Allah lalle ladansa na kan Allah wanda shi ne aljanna. Amma wannda ya je hajji domin mutane to sai ya nemi ladansa gurinsu ranar qiyama. A ranar qiyama kowa ke gudun kowa kowa ya shagaltu da tunanin kansa da yaya za ta qarke masa.

  (يَوْمَ لاَ يَنفَعُ مَالٌ وَلاَ بَنُونَ * إِلاَّ مَنْ أَتَى آللهَ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ )

 [24]              
Ranar da dukiya da `ya`y aba sa amfanarwa face wanda ya je ma Allah da zuciya mai tsarki.

 (يَوْمَ يَفِرُّ آلْمَرْءُ مِنْ أَخِيهِ * وَأُمِّهِ وَأَبِيهِ * وَصَاحِبَتِهِ وَبَنِيهِ ) .[25]

Ranar da mutum ke guje ma xan'uwansa da mahaifiyarsa da da mahaifinsa da matarsa da xansa.

37- duk wanda yaje hajji domin nufin Allah da domin riya ba da neman suna, to lalle Allah ya gafarta masa yanke.

38- duk wanda ya nufi wannan xaki mai alfarma domin hajji ko umara yana barranta daga girman kai, zai dawo gida ya kubuta daga zunibinsa kamar ranar da babarsa ta haifeshi.[26]

39-  kaxai dai an umarce su da zuwa hajji ne don suyi tarayyar cikin kiyafar Allah, da neman qari da fita daga cikin dukkanin zunubin da bawa ya aikata daga abin da ya gabata, da kuma sake sabon aiki daga abin da zai fuskanta  a gaba.

40- wani zamani zai zowa mutane da sarakuna za su dinga zuwa hajji don yawon buxe ido da shaqatawa, mawadata kuma za su je don kasuwanci, talakawa kuma za su je domin su yi barace barace.

41- lalle wanda ya je liyafar Allah shi ne mutumin da ya yi hajji da umara ba zai gushe ba cikin liyafar Allah har dawowarsa gida.

ـ عن الامام الصادق  7 قال لرجل لم يحجّ بيت الله الحرام : «انظر إلى أبي قبيس ـ جبل معروف في مكّة المكرّمة ـ فلو أن أبا قبيس لک ذهبة حمراة أنفقته في سبيل الله، ما بلغت به ما يبلغ الحاج.

42- daga imam sadiq(as) ya cewa wani mutumin wanda bai je hajji ba: ka kalli dutsen abu qabisu(wani sanannen dutse a makka) da ace abu qaisu zinare ja da ka ciyar da shi cikin tafarkin Allah da ba z aka taba kaiwa inda mahajjaci ya kai ba.

ـ وعنه  7: «إنّ الحاج إذا أخذ في جهازه لم يرفع شيئاً ولم يضعه إلّا كتب الله له عشر حسنات ، ومُحي عنه عشر سيّئات ، ورفع له عشر درجات ، فاذا ركب بعيره ، لم يرفع خفاً ولم يضعه إلّا كتب الله له مثل ذلک ، فاذا طاف بالبيت خرج من ذنوبه

43-Daga gareshi(as) lalle mahajjaci idan ya xaki kayansa ba zai xaga wani abu ko ya aje shi face Allah ya rubuta masa kyawawa goma ya kuma goge munana goma ya xaukaka shi daraja goma, idan ya hau kan raquminsa ba zai xaga huffi ko ajiye shi face Allah ya rubuta masa lada misalin wancan, idan ya kewaya xakin ka'aba sai ya fita daga dukkanin zunubansa.

Ina cewa: cikin wannan zamani namu zaka hau mota ku jirin ruwa ko jirgin sama ta yiwu xagawa kuffi ya zamanto yana da ma'anar motsin tayoyin mota ko cirawar jirgin sama zuwa sararin samaniya ko tafiyar jirgin ruwa, Allah shi ne mafi sani.

ـ قال رسول الله 6 لأميرالمؤمنين  7: «يا علي تارک الحجّ وهو مستطيع كافر، قال الله تعالى : (وَللهِ عَلَى آلنَّاسِ حِجُّ آلْبَيْتِ مَنِ آسْتَطَاعَ إِلَيْهِ سَبِيلاً وَمَن كَفَرَ فَإِنَّ آللهَ غَنِيٌّ عَنِ آلْعَالَمِينَ ) .
[27]

44- manzon Allah(saw) cikin nahjul balaga ya cewa sarkin muminai Ali(as) ya Ali lalle mai barin hajji alhalin yana da ikon zuwa kafiri ne, Allah maxaukaki ya ce: Allah ya farlanta ibadar hajji kan mutane ga wanda ya samu iko gareshi, duk wanda ya kafirce lalle Allah mawadaci ne ga barin talikai.

ـ قال أميرالمؤمنين  7 في نهج البلاغة في فلسفة الحجّ : «وفرض عليكم حج بيته الحرام الذي جعله قبلة للأنام يردونه ورود الأنعام ، ويألهون إليه ولوه الحمام ، وجعله سبحانه علامة لتواضعهم لعظمته ، وإذعانهم لغرّته ، وإختار من خلقه سُمّاعاً أجابوا إليه دعوته ، وصدّقوا كلمته ، ووقفوا مواقف أنبيائه ، وتشهبّهوا بملائكته المطيفين بعرشه ، يحرزون الارباح في متجر عبادته ، ويتبادرون عنده موعد مغفرته ، جعله سبحانه وتعالى للاسلام علماً، وللعائذين حرماً، فرض حقّه ، وأوجب حجّه ، وكتب عليكم وفادته

Sarkin muminai Ali(as) cikin nahjul balaga cikin falsafar hajji yana cewa: Allah ya farlanta ziyartar xakinsa mai alfarma wanda ya sanya shi alqibla ga talikai suna gangara gareshi irin ganagara da dabbobi da suke cikin qishirwa suke gangara  ga ruwa, suna razana da guduwa gareshi kamar yadda tsuntsun tattabara ke razana ya gudu shekarsa, Allah ya sanya shi alama saboda tawali'unsu da ga girmansa, da miqa wuyansu ga izzarsa, ya zabi masu saurare daga halittunsa suka amsa kiransa zuwa ibadarsa ta hajji, suka gasgata kalmarsa, suka tsaya wuraren da annabawansa suka tsaya, suka kamantu da mala'iku waxanda suke xawafi daura da al'arshinsa, suna kwasar riba cikin kasuwar ibadarsa, suna rigengeniya zuwa ga mahallin alqawalin gafararsa, Allah matsarkaki  maxaukaki ya sanya shi ga muslunci tuta mafaka, harami ga masu neman tsari,ya farlnta haqqinsa, ya wajabta ziyartarsa, ya rubuta muku ziyartarsa.

 ـ وقال  7: «إنّ أفضل ما توسّل به المتوسّلون إلى الله سبحانه وتعالى الإيمان به وبرسوله والجهاد في سبيله ... وحجّ البيت وإعتماره ، فانّهما ينفيان الفقر، ويُرخصان الذنب ، ـ الرخص بمعنى الإسقاط ـ.

46- ya ce: lalle mafificin abin da masu tawassali suka yi tawassali da shi zuwa ga Allah matsarkaki maxaukaki shi ne imani da shi da imani da manzanninsa da yin jihadi cikin tafarkinsa, da ziyartar xakinsa da umara, lalle hajji da umara suna korar talauci suna rugurguza zunubi.

ـ وقال  7: «ألا ترون ان الله سبحانه اختبر الأولين من لدن آدم صلوات الله عليه والآخرين من هذا العالم باحجار لا تضرّ ولا تنفع ، ولا تبصر ولا تسمع ، فجعلها بيته الحرام الذي جعله للناس قياماً».

47- ya ce: shin bakwa ganin Allah ya jarraba mutanen farko bat un daga adamu(as) da mutanen qarshe daga wannan duniyar ya jarraba su da wasu dutsuna da basa amfanarwa ko cutarwa, basu gani basu ji sai ya sanya xakinsa harami wanda ya sanya shi tsari domin mutane.

ـ وقال  7: «الله الله في بيت ربّكم لا تخلّوه ما بقيتم ، فانّه إن ترک لم تناظروا ـ أي لم تهملوا فيأخذكم بالعذاب ».

48-Ya ce: na tunatar da ku Allah kan kiyaye xakin ubangijinku ka da ko wofintar da shi matuqar kuna raye, lalle idan aka barshi ba za a jinkirta muku ba, sai a damqeku da azaba.

ـ قال الامام الباقر 7: «أتى آدم هذا البيت ألف آتية على قدميه ، منها سبعمأة حجّة وثلثمأة عمرة ».

49- imam baqir(as) ya ce: adamu ya zo wannan xaki sau dubu a kan qafafuwansa, daga cikinsu ya yi hajji xari bakwai ya yi umara xari uku.

قال الامام الصادق  7: «فجعل فيه ـ في الحجّ ـ الإجتماع من الشرق والغرب ليتعارفوا، ولتعرف آثار رسول الله، وتعرف أخباره ويذكر ولا يُنسى.

50- imam sadiq(as) Allah yab tara muatnen da suke gabas da yamma cikin taron hajji domin su san juna da kuma sani kuafaifayin manzon Allah(saw) da sanin zantukansa da dinga tunawa da qauracewa mantuwa.

وقال  7 في جواب من قال إنه من حجّ مرّة ، فالأولى له أن يتصدّق بماله في سبيل الله على الفقراء ولا يذهب إلى الحجّ مرّة اُخرى ، فقال  7: «كذبوا لو فعل هذا الناس لعُطّل هذا البيت إن الله عزّوجلّ جعل هذا البيت قياماً للناس

51- cikin amsar wanda ya ce lalle wanda yay i hajji sau guda to abin da ya fi cancanta da shi ya sadaqantar da dukiya ga talakawa cikin tafarkin Allah ka da ya qara zuwa hajji karo na biyu, sai imam ya ce: qarya suke faxi da za a dinga aikata haka da xakin Allah ya wofunta, lalle Allah ya sanya wannan xaki tsari ga mutane

وقال  7: «جعلها الله ـ الكعبة ـ لدينهم ومعائشهم

52- ya ce: Allah ya sanya xakin ka'aba domin addinisu da rayuwarsu.

وقال  7: «لا يزال الدين قائماً ما قامت الكعبة

53- addini ba zai gushe ba tsaye matuqar ka'aba na tsaye.

Bai buya cewa mahajjaci hajji mai amfaniwanda ya kasance tsayuwar addini cikin kankin kansa da jama'a, sai sulukin mutum da jama'a ya kasance kan hasken koyarwar addini, idan kuma ya zama sabanin haka to dama lalle manzon Allah(saw) ya bada labari kan mahajjatan qarshen zamani da yadda halinsu yake, sai  ya ce: 

«يأتي على الناس زمان يكون فيه حجّ الملوک نزهةً وحجّ الأغنياء تجارةً ، وحجّ المساكين مسألةً ».

54- wani zamani zai zowa mutane wanda hajjin sarakuna zai kasance yawan shaqatawa, hajjin mawadata kasuwanci, hajjin talakawa barace barace.

() 55 ـ قال رسول الله 6 في حجّة الوداع عند غروب يوم عرفة : «إنّ ربّكم لطوّل عليكم في هذا اليوم ، وغفر لمحسنكم ، وشفّع محسنكم في مسيئكم ، فأفيضوا مغفوراً لكم

55- manzon Allah(saw) cikin hajjin bankwana ya yin faxuwar ranarb Arafat ya ce: lalle ubangijnku ya tsawaita muku cikin wannan rana, ya yi gafara ga mai kyautatawa cikinku, ya baiwa mai kyawuntawar cikinku ceton mai mummunan aiki daga cikinku, ku kwarara an yafe muku zunubanku.

 ـ قال الامام الصادق  7 لأحد أصحابه : «يا عيسى إنّي أُحبّ أن يراک الله فيما بين الحجّ إلى الحجّ ، وأنت تتهيّأ للحجّ

56-  imam sadiq(as) ya cewa wani daga sahabbansa da ake kira da isa: ya isa lalle ni ina qaunar ace Allah ya ganka cikin abi da ke tsakanin hajji zuwa wata hajji alhalin kai kana cikin tanadin hajji.

وقال  7: «ليحذر أحدكم أن يعوّق أخاه عن الحجّ ، فتصيبه فتنة في دنياه ، مع ما يدخل له في الآخرة ـ من العذاب

57-Wani wajen kuma ya ce: xayanku yay i taka tsantsan ka da ya zma matsala ga zuwan xan'uwansa hajji, sai fitiaina ta riskeshi cikin duniyarsa tare da abin da zai shigar masa lahira daga azaba.

58-  me yafi yawa daga neman hajji cikin addu'o'I da munajatin watan Ramadan mai albarka har ya kai ga akusa cewa: watan Ramadan mai albarka tare da lyafarsa mai gamewa da abin da ke cikinsa daga addu'o'i waxanda suke ke bayyana cewa shi: Allah ka azurtani ziyartar xakinka mai alfarma cikin wannan shekara da ne ke ciki haka ma cikin kowacce shekara) kaxai dai ita wannan addu'a share fage ne da shimfixa da tanadi domin neman liyafar Allah a kebance cikin kwanakin hajji, me yafi girma daga hajji?

 

في الأحاديث الشريفة : «الساجد بمكّة كالمتشحّط بدمه في سبيل الله» «تسبيحه بمكّة أفضل من خراج العراقين ينفق في سبيل الله» «من ختم القرآن بمكّة لم يمت حتّى يرى رسول الله ويرى منزله من الجنّة » «النظر إلى الكعبة حُبّاً لها يهدم الخطايا هدماً».

59- ya zo cikin hadisai masu daraja cewa: wanda ya yi sujjada garin makka kamar misalin wanda ya ji rauni ya ke jike cikin jininsa a tafarkin Allah, duk wanda ya karanta qur'ani tun daga farko zuwa qarshe cikin garin makka ba zai mutu ba har sai yay i ido biyu da manzo Allah sannan kuma zai yi ido biyu da gidansa na aljanna, kallon xakin ka'aba domin soyayya gareta yana rugurguza kurakurai

ـ وفي عظمة وشرافة أيّام الحجّ قال رسول الله 6: «ما من أيّام العمل الصالح فيها أحبّ إلى الله عزّوجلّ من أيام العشر، يعني عشر ذي الحجّة إلّا رجل خرج بنفسه وماله فلم يرجع بشيء من ذلک » «ما من أيّام أزكى عند الله تعالى ولا أعظم أجراً من خير في عشر الأضحى

60- cikin girma da darajar kwanakin aikin hajji, manzon Allah(saw) ya ce:  babu wasu kwanakin aiki nagari mafi souywa gareni daga kwanaki goma, ma'ana goma ga watan zil hijja face wani mutum da kansa da dukiyarsa bai kuma koma da komai daga ciki ba, babu wasu kwanaki da suka tsarkaka da girma lada wajen Allah daga alherin kwanaki goma daga zil hijja.

bai buya ba  cewa adadin araba'in  cikin zikiri da wurudai da hatimai mafi falalarsu  a wajen arifai shi ne cikin watan zil qa'ada da goman farko daga zil hijja saboda dogaro da faxin Allah maxaukaki:

(وَوَاعَدْنَا مُوسَى ثَلاَثِينَ لَيْلَةً وَأَتْمَمْنَاهَا بِعَشْرٍ فَتَمَّ مِيقَاتُ رَبِّهِ أَرْبَعِينَ لَيْلَةً) [28] .

Muka yiwa wa musa alqawali dare talatin muka cika shi da goma sai miqatin ubangijinsa ya cika dare arba'in.

annabi musa(as)  tsawon kwanaki araba'in  ya kasance cikin azumi da kuma raya dararen ciki, lalle shi ya kasance yana ciyarwa da shayarwa domin soyayyarsa ga Allah mai girma da xaukaka, kebantattun kyaututtuka na ga kebantattun waliyansa zababbunsa, kaxai dai hakan na kasancewa cikin kwanakin hajji, lalle su malamai magada annabawa ne, lalle shi mai hankali ishara ta isar masa saboda haka sai mu lura.

 () 61 ـ عن الصادق  7: «إنّ ضيف الله عزّوجلّ رجل حجّ وإعتمر، فهو ضيف الله حتّى يرجع إلى منزله ».

61- an karbo daga sadiq(as) lalle mai halartar liyafar Allah mai girma da xaukaka shi ne mutumin da yay i hajji da umara, lalle shi baqone na Allah har dawo gida yana cikin liyafarsa.

وأخيراً وليس بآخر إن شاء الله تعالى : قال الامام الصادق  7 لزرارة حين قال له : سيّدي آتيک أربعين سنة وأسأل عن الحجّ ، ولازلت تحدّثني عنه فقال  7: «يا زرارة بيت حُجّ إليه قبل آدم بألفي عام ، تريد أن تُفني مسائله في أربعين عاماً» .[29]

62- daga qarshe da izinin Allah ba zai zama na qarshe ba: imam sadiq(as) ya cewa zurara ya yin da zurara yake ce masa ya shugabana ina ta zuwa wajenka tsawon shekaru araba'in ina tambayarka game dahajji baka gushe ba kana zantar dani game dashi, sai imam ya ce: ya zurara shi xaklin ka'aba xaki ne da aka ziyarce shi akai hajji gabanin adamu da shekaru dubu, shin kana son mas'alolin suka qare cikin shekaru arba'in.

«يا مُنى قُلُوبِ الْمُشْتاقيüنَ وَيا غايَةَ امالِ الُْمحِبّيüنَ، اَسْئَلُکَ حُبَّکَ وَحُبَّ مَنْ يُحِبُّکَ وَحُبَّ كُلِّ عَمَلٍ يُوصِلُنىü اِلى قُرْبِکَ، وَاَنْ تَجْعَلَکَ اَحَبَّ اِلَىَّ مِمّا سِواکَ، وَاَنْ تَجْعَلَ حُبّىü اِيّاکَ قآئِداً اِلى رِضْوانِکَ، وَشَوْقىü اِلَيْکَ ذائِداً عَنْ عِصْيانِکَ، وَامْنُنْ بِالنَّظَرِ اِلَيْکَ عَلَىَّ، وَانْظُرْ بِعَيْنِ الْوُدِّ وَالْعَطْفِ اِلَىَّ، وَلا تَصْرِفْ عَنّىü وَجْهَکَ،وَاجْعَلْنى مِنْ اَهْلِالاْسْعادِ وَالْحِظْوَةِعِنْدَکَ،يامُجيüبُ يااَرْحَمَالرّاحِميüنَ» .

Ya wanda yake shi ne burin zukatan masu shauqi, ya tuqewar fatan masoya, ina roqonka soyayyarka da son wandayake sonka  da son dukkanin aikin da zai kaini ga kusantarka, ka sanya kanka ya zamanto shi ne mafi soyuwa gareni daga waninka, ka sanya soyayyata gareka ta zama jagora ya zuwa yardarka da shauqina ya zuwa gareka ya zama garkuwa ga barin sabamaka, ka yi tautayi gareni ya zuwa kallonka, ka kallene da idaniyar qauna da tausayi, ka da ka karkatar da fuskarka daga barina, ka sanya ni daga cikin ma'abota arziqi da rabo gareka, ya mai amsa addu'a ya mafi jin qan masu jin qai.


 قال أميرالمؤمنين  7: «الله الله في بيت ربّكم فلا يخلو منكم ما بقيتم ، فانّه ان تُرک لم تناظروا».

63- sarkin muminai Ali(as) : ina haxa da Allah iana haxa ku da Allah game daxakin ubangijinku ka da ku wofintar da shi matuqar rayuwarku, lalle shi idan aka yi watsi da shi ba za ai muku jinkirin azaba ba.

قال الصادق  7: «إنّ الله ليدفع بمن يحجّ من شيعتنا عمّن لا يحجّ ، ولو أجمعوا على ترک الحجّ لهلكوا، وهو قول الله عزّوجلّ : (وَلَوْلاَ دَفْعُ آللهِ آلنَّاسَ بَعْضَهُم بِبَعْضٍ لَفَسَدَتِ آلاْرْضُ وَلكِنَّ آللهَ ذُو فَضْلٍ عَلَى آلْعَالَمِينَ)[30]

64- imam sadiq(as) ya ce: lalle Allah ya ingije masu zuwa hajji daga shi'ar da waxanda basa zuwa, da ace dukkaninsu zasu taru su yi watsi da zuwa hajji da sun halaka, shi ne ma'anar faxin Allah mai girma da xaukaka,(ba da ban ingijewar Allah mutane ba'arinsu da ba'ari da qasa ta gurbace sai cewa shi Allah ma'abocin falala ne kan talikai.

ـ لو أنّ الناس تركوا الحجّ لكان على الوالي ـ في يومنا هذا الحكومة الإسلاميّة ـ أن يجبرهم على ذلک وعلى المقام عنده ، فان لم يكن لهم أموال أنفق عليهم من بيت مال المسلمين

 65-da cae mutane zasu yi wasti da zuwa hajji da wajibi kan jagoran musulmi a wannan zamani damu ke ciki ya tilasta su kan zuwa, idan kuma ba su da kuxin zuwa sai ya basu daga baitul mali.

() 66 ـ عن سماعة عن أبي عبدالله 7 قال : قال لي : «مالک لا تحجّ في العام ؟» فقلت : معاملة كانت بيني وبين قوم ، وإشغال وعسى أن يكون ذلک خيرة ، فقال  7: «لا والله ما جعل الله لک في ذلک من خيرةٍ » ثمّ قال : «ما حبس عبد عن هذا البيت إلّا بذنب ، وما يعفو أكثر».

66- daga samma'a daga baban Abdullah(as) ya ce: imam ya tambayeni me ya hanaka zuwa hajji a wannan shekara? Sai n ace masa: wata mu'amala ce ta kasance tsakanina da wasu mutane da kuma wasu shagulgula ina saran haka ya fiye mini alheri, sai imam ya ce: wallahi sam ba haka bane Allah bai sanya maka alheri cikin haka ba, sannan ya qara cewa: ba a katange wani bawa daga ziyartar wannan xaki ba face sakamakon wani zunubi da ya aikata. Abin da yake afuwa ya fi yawa.

 عن عذافر: قال أبو عبدالله 7: «ما يمنعک من الحجّ في كلّ سنة ؟» قلت : جعلت فداک العيال ، قال : فقال  7: «اذا متّ فمن لعيالک ؟ أطعم عيالک الخلّ والزّيت ، وحجّ بهم كلّ سنة.

An karbo daga azafir: baban Abdullah(as) ya ce: me zai hanaka zuwa hajji cikin kowacce shekara? Sai nace raina fansaraka iyali ne za su hana, sai imam ya ce: idan ka mutu hannun wa iyalinka suke ? ka ciyar da iyalinka kunu da mai ka tafi hajji kowacce shekara.

قال رسول الله 6: «من أنسأت له في أجله ، ووسعت عليه رزقه ، وصحّحت له جسمه ، ولم يزرني في كلّ خمسة أعوام فهو محروم

68- manzon Allah(saw) ya ce: duk wanda……. cikin ajalin , na yalwata shi cikin arziqinsa, na inganta masa lafiyar jikinsa, sannan kuma yaqi ziyarta ta tsawon shekaru biyar lalle shi haramtacce ne.

() 69 ـ عن الامام الرضا 7: «إنّما جعل وقتها عشر ذي الحجّة ولم يقدّم ولم يؤخّر، لأنّه لمّا احبّ الله عزّوجلّ أن يعبد بهذه العبادة ، بهذه العبادة ، وضع البيت والواضع في أيّام التشريق ، وكان أوّل ما حجّت إليه الملائكة وطافت به في هذه الوقت ، فجعله سنة ووقتاً إلى يوم القيامة ، فأمّا النبيّون آدم ونوح وإبراهيم وموسى وعيسى ومحمّد 6 وغيرهم من الأنبياء إنّما حجّوا في هذا الوقت ، فجعلت سنّة في أولادهم إلى يوم الدين »

69- daga imam rida(as) dalilin da ya sanya Allah ya sanya lokacin hajji  goma daga zil hijja ba gabatar kafinta ba bai jinkirta shi ba. saboda ya yin da Allah ya so a bauta masa da wannan ibada,  ma sanyawa ya sanya xakin a kwanakin sha xaya da sha biyu da sha uku ga zil hijja, mala'iku ne waxanda suka fara ziyartar wannan xaki suka kewaya shi suna xawafi a wannan lokaci, sai sanya shi sunna da lokaci har zuwa tashin qiyama, amma annabawa waxanda suka ziyarce shi sune adamu da nuhu da Ibrahim da musa da isa da muhammadu{as} da wasunsu daga annabawa sun je hajji wannan lokaci sai aka sanya shi sunna cikin `ya`yayensu har zuwa tashin qiyama.
 


 

 

JIKKANTUWAR HAJJI GA ASALAN ADDINI

Lalle hajji da dukkanin alamominsa da wuraren ibadun cikinsa rayayyu yana jikkanta da bayyanar mana da asalan addini da reshensa da kyawawan xabi'u.

Bayanin haka:

Asalna addini guda biyar ne a makarnatr ahlul baiti kamar yadda bayanin haka zai zo:(tauhidi, adalci annabta, imamnci, qiyama).

1 tauhidi: hajji yana jikkanta mana da bayyana mana Kalmar tauhidi da xayanta kalmada wurgi da shirka da munafunci da jayayya, lalle tauhidi cikin bakarsa ta sauka shi ne hajji, sannan hajji cikin bakarsa ta hawa shi ne tauhidi.

عن الامام الصادق  7 في دعاء الحجّ : «فإنّما أنا عبدک وبک ولک

An karbo daga imam sadiq (as) cikin addu'arsa ta hajji: kaxai dai ni bawanka ne da kai naka).

Kusantar Allah abin bauta da xebe haso da shi bai kasancewa face da tauhidi tsarkakka, duk wanda ya tsarkake niyya domin Allah tabbas zai xebe haso da Allah.

قال رسول الله 6: «هذه حجّة لا رياء فيها ولا سمعة » «من تجهّز وفي جهازه عَلَم حرام لم يقبل الله منه الحجّ

 Manzon Allah(saw) ya ce: wannan hajji babu riya da neman suna cikinsa, duk wanda ya xaura xamara ya shirya ya xaure kayansa domin zuwa hajji amma kuma cikin kayansa akwai haramun Allah zai taba karbar hajji daga gareshi ba.

Daga cikin mafi qarafafr dalili daga dalilai kan tauhidi shi ne tauhidin tsarin halittar mutum lafiyayya wadda Allah ya qagi mutune a kanta, it ace take nusantarwa zuwa ga xayantar Allah da kasantuwarsa maqagi, wannan na daga tsarin halitta ta addini da tauhidi.

mahajjaci tun ranar farko zai sanya kyalle guda biyu na ihrami da talbiya wanda suna daga cikin alamomin tsantsar tauhidi.

2-annabta da wahayi:  lalle ayyuka da ibadun cikin hajji annabwa sun zo da su ta hanyar wahayi daga Allah matsarkaki tun daga adamu zuwa cika makin annabawa.

(أرنا مناسكنا).

(ka nuna mana wuraren ibadar hajjin mu)

قال الامام الصادق  7: «إنّ الله بعث جبرئيل إلى آدم فقال : ان الله أرسلني إليک لأعلّمک المناسک التي تطهّر بها» [31].

Imam sadiq(as) Allah ya aiko jibra'ilu zuwa adamu sai ya ce masa: lalle Allah ya aiko ni gareka domin in koyar da kai ibadu da zaka tsarkaka da su.

قال الامام الباقر لولده الصادق  8 عن رسول الله 6 قال : «ما أتيت الركن اليماني إلّا وجدت جبرئيل قد سبقني إليه يلتزمه ».

Imam baqir(as) ya cewa xansa sadiq(as) dag amazon Allah(saw) ya ce: ban taba zuwa rukunul yamani ba face na samu jibra'ilu ya gabace ni gareshi ya na lazimtarsa.

Allah ya umarci masoyinsa Ibrahim:

 (وأذن في الناس بالحج يأتوک رجالاً...)

Ka yi yekuwa cikin mutane ibadar hajji za su zo maka da qafafuwansu.

Ba kawai kawo Ibrahim garin makkka kaxai ba, abri dai domin ya tada harsashin ginin ka'aba, ba kawai kawo mutane kaxai shi ne ya isar ba, bari dai domin su koyi darasussukan tauhidi da annabta da tsabatatacciyar rayuwa daga Ibrahim, kuma su kasance daga ma'baota zukata tsarkaka.

 (إِنَّ أَوْلَى آلنَّاسِ بِإِبْرَاهِيمَ لَلَّذِينَ آتَّبَعُوهُ وَهذَا آلنَّبِيُّ وَآلَّذِينَ آمَنُوا( [32]

Wanda suka fi cancanta ga Ibrahim sune waxannan da suka yi biyayya gareshi, wannan annbi ne da waxanda suka yi imani.

3- qiyama, makoma ta jikkuna da ruhi: lalle hajji da ibadun cikinsa da ihrami tun daga ranar fari yana tunatar da mutane ranar qiyama, lalle kyallen ihrami ya na ishara ga tufafin likkafani da tashi mutane daga maqabartu da qabarurruka suan qasqantar da kawukansu da sunkuyawa ga ubangijin talikai, lalle mutane tare da sabaninsu cikin launin fata da harsuka da qabila da qungiyoyi da sauransu dukkaninsu bai xaya suke babu banbanci hakan na bayyana da tajalli sa'ilin taruwar mahajjata cikin miqatinsu da wuraren wurarren da ibadun hajji:

(يَوْمَ يَجْمَعُكُمْ لِيَوْمِ آلْجَمْعِ )[33]

Ranar da zai tattara ga ranar taro.

 (إِنَّ آلاَوَّلِينَ وَآلآخِرِينَ * لَمجْمُوعُونَ إِلَى مِيقَاتِ يَوْمٍ مَعْلُومٍ )[34]

Lalle na mutanen farko da na qarshe ababen tattarawa ne ga ranar miqati sananne.

  (وَكُلُّهُمْ آتِيهِ يَوْمَ آلْقِيَامَةِ فَرْداً)[35]

Dukkaninsu za su masa ranar qiyama xai xai.

  (فَفِرُّوْا إِلَى آللهَ)[36]

Ku gudu zuwa ga Allah.

عن الامام الصادق  7: «حجّوا إلى الله عزّوجلّ »

An karbo daga imam sadiq(as) ma'anar hakan shi ne ku je hajji zuwa ga Allah.

Alamomi nawa dake ishara ga lahira suke tajalli cikin hajji, lalle ranar qiyama mutane zasu tashi tsirara babu komai jikinsu daga alatun duniya, haka al'amarin yake lokacin hajji bayan xaura harami da nesantar mutane daga xinkakken tufafi daga kayan ado, sannan cikin hajji mutane suna iqirarin zunubansu kamar yadda hakan ke kasancewa ranar qiyama, lalle babu zalunci da aminci ga mutane wannan rana  kai hatta ga dabbobi, kamar yadda ya kasance cikin sa'ayi n hajji akwai qasqanta ga jabberai masu jin girma kai da xagawa haka la'amarin yake ranar qiyama, sakamakon misalign haka hajji ya kasance daga mayan rukunan muslunci.

4- adalcin abin bauta: lalle hajji na jikkanta da nuna adalcin abin bautawa da gaskiya cikin sanya ihramin mutane da sa'ayinsu da xawafinsu da tsyuwarsu a Arafat da mash'aril haram babu banbanci ciki tsakanin mazauni da baqauye da mawadaci da talaka da malami da jahili mace da namiji, da halartar alfanu da tsari ga mutane, da gamammiyar albarka da shiriya da gafara, kkamar yadda ya kasance wanda zai zo qarshen zamani ya cika qasa da adalci da daidaito ma'ana almahadiyu daga iyalan muhammadu(saw) zai fito daga garin makka mai karamci cikin xakin Allah ka'aba mai daraja, lalle idan ya fito zai shiga masallacin mai alfarma ya fuskanci xakin ka'aba ya sanya bayansa zuwa ga muqam sannan yay i sallah raka'a biyu sannan ya ce:

: «أيُّها الناس أنا أولى الناس بآدم ، يا أيُّها الناس أنا أولى الناس بإبراهيم » . [37]

Ya ku mutane ni ne na fi cancanta ga adamu ni ne nafi cancanta ga Ibrahim, yak u mutane lalle mafi cancanta ga Ibrahim.

5- imamanci da halifanci: lalle wilya mafi girma na daga cikin ruhin tauhidi da annabta wadda take dacewa da imamanci da halifanci manzon Allah(saw) ta gaskiya baa i kira ga wani abu ba kamar misalign yadda akai kira ga wilaya, lalle ita ruhin muslunci ce da gundarinsa hatta hajji na kasa da muqamin wilaya,nufar xakin ka'aba na qasa da wilaya, halartar tsayuwar Arafat na qasa da wilaya, hadaya ma  ba tare da  narkewa da miquwa ga imami na qasa da wilaya, jifan shaixan da korarsa na qasa da wilaya, sa'ayi ba tare da sa'ayi cikin sanin haqqin imami  da sanin imamai shabiyu ba na qasa da wilaya, lalle al'amrin yadda yake shi hajjin mahajjaci ba zai amfanar da shi bah aka azumin mai aumi ba zai amfanar da shi matuqar gabbansa basu azumta ba, bai da wani rabo cikin azumi face yunwa da qishirwa, kamar yadda imam zainul abiding(as) ya yi8 bayanin kansa a masallacin umayyawa bayan waki'ar karbala mai raxaxi, yana mai cewa:

«أنا إبن مكّة ومنى ، أنا إبن زمزم والصفّا...» . [38]

Nine xan makka da mina, nine xan zamzam da safa…..

Wannan na nuni da cewa dangantaka tsakanin ka'aba da imamanci kamar dangantakar xa da uba ce sakamkon kasantuwar imami uba ga matattara da shelkwatar bauta da tsuhenta, ta wata fuskar kuma shi imam xa gareta shi kuma shi ne ke da haqqin gadon babansa da kiyaye dukiyarsa, imami shi ne wanda ke kiyaye makka da mina da zamzam da safa, shi xa ga waxannan wurare na ibada tsarkaka, saboda duk wanda ya raba xa da uba lalle bai da wani rabo cikin hajjinsa face wahala da gajiya da batawa kansa lokaci da iface iface mara ma'ana, maimakon  ya isa ga ruhin hajji sai ya buge da iface iface.

 

قال أبو بصير للامام الصادق  7 في حجّ : ما أكثر الحجيج في هذا العام ؟ فقال  7: «ما أكثر الضجيج وأقلّ الحجيج » ثمّ أراه في عالم الشهود والمكاشفة من كان في الطواف فرأى أكثرهم كالأنعام .

Abu  basir game dahajji ya cewa imam sadiq(as) kai wannan shekara mahajjata sun zo da yawa? sai imam ya ce: me yafi qaranci daga mahajjata me yafi yawa daga masu iface- iface. Sai imam ya nunawa  abu basir waxanda ke xawafi cikin duniyar shuhudi da mukashefa sai abu basir ya ga mafi yawancinsu cikin surar dabbobi.

قال الامام الباقر 7 لأحد أصحابه في الحجّ : «أترى هؤلاء الذين يلبّون الله لأصواتهم أبغض إلى الله من أصوات الحمير» ثمّ قال  7: «هكذا كانوا يطوفون في الجاهليّة ، إنّما اُمروا أن يطوفوا، ثمّ ينفروا إلينا فيعلّمونا ولايتهم ، ويعرضون علينا نصرهم »، ثمّ قرء قوله تعالى : (فَاجْعَلْ أَفْئِدَةً مِنَ آلنَّاسِ تَهْوِي إِلَيْهِمْ )[39][40]

Imam baqir (as)  game dahajji ya cewa xaya daga cikin sahabbansa: kaga waxannan muatne da ke faxin labbaika, lalle sautinsu yafi sauti jaki kasantuwa abin qi wajen Allah. Sannan ya ce: haka suka kasance suna xawafi a zamanin jahiliya, kaxai dai an umarce su da su yi xawafi, sannan su komo garemu su sanar damu wilayar su, su bijiro da taimakonsu garemu, sai imam ya karanta faxinsa maxaukaki: ( ka sanya zukatatan mutane su karkta da bege garesu).

Kxai dai dalilin da ya sanya sautinsu ya kasance misalign sautin jaki kasantuwar jahiltar imamin zamaninsu, haqiqa hadisai sun yawaita daga shi'a da sunna cewa manzon Allah(saw) ya ce:

«من مات ولم يعرف إمام زمانه مات ميتة الجاهليّة »

Duk wanda yam utu alhalin bai san imamin zamaninsa bay a mutu mutuwar jahiliya.

Saboda haka su kamar dabbobi ne bari ma sun fi dabbobin batan hanya.

Ba boye yake ba cewa mutuwar kowanne mutum misalin rayuwarsa ce (kamar yadda kuka rayu haka za ku mutu, kamar yadda kuka mutu haka za ku tashe ku, kamar yadda aka tashe ku haka za a tara ku) duk wanda bai san imamin zamaninsa bay a kasance daga dabbobi a ban qasa misalign jaki da tumaki, zai mutu kan kafirci da bta da jahiliya, haka za a tashe ciki da ainahin suarrsa ta dabbobi, haka hajjinsa ke kasancewa misalin jahiliya ke kasancewa, bai da wani rabo daga hajjin annabin ibrahim da annabi muhammadu face wahala, wannan na daga sunnar Allah ba za ka taba samun canji ko sauyi ciki ba.

 Lalle imam shi ne ruhin xakin ka'aba, sannan kuma shi ruhin bai tsayu da gangar jikinsa ba, bari dais hi ruhinsa na rataye da ilimsa da shaidarsa, ita ka'aba a zahiri ta stayu da duwatsun gininta amma kuma a baxini ta tsayu da imamin zamani.

Lalle Allah ya kame hannun abrahata da rundunarsa ya hanasu rusa xakin ka'aba da tsuntsayen wuta, amma abin mamakin bai hana hajjaju ibn yusuf assaqafi(l.a) rusa xakin ka'aba da majaujawwa ba lokacin mulkin abdullahi ibn zubairu, kaxai dai imam zainul abidin(as) bai hana hajjaju ibn yusuf assaqafi rusa ka'aba ba sakamakon shi abdullahi ibn zubairu maqiyin imam zainul abidin ib husaini(as) ne  

(وَمَن يُرِدْ فِيهِ بِإِلْحَادٍ بِظُلْمٍ نُذِقْهُ مِنْ عَذَابٍ أَلِيمٍ )[41]

Duk wanda ya yi nufin karkacewa cikinsa da zalunci za mu xanxana masa azaba mai raxaxi.

Banbanci nawa tsakanin masu rusa ka'aba su abrahata da rusawar hajjaju?

 Saboda haka wajibi ne ga bangarori biyu suyi xawafi daura ga xakin ka'aba da gangar jikinsu, sannan suyi da ruhinsu da daura da imamanci, suna sauke kawukansu da nasara da shahada.

«حضور الحاضر وقيام الحجّة بوجود الناصر.[42]

Halartar mai halarta da tsayuwar hujja tare da samuwar mai taimakawa.

Alfarmar garin makka ta samu ta hanyar alfarmar xaki ka'aba, sannan xaki ka'aba ya samu alfarma da alfarmar annabta da manzanci da wilaya, sannan alfarma da girma dukkaninsu ya samu da alfarma Allah girmansa ya girmama. Da wannan dalili ne aka danganta xakin ka'aba zuwa gareshi

 (أن طهّرا بيتي )

Ku tsarkake xakina.

Alfarma ta zati naga Allah matsarkaki, sannan alfarma ga waninsa na kasance ta hanya bijirowa ba zati bah aka abin da ke kasancewa hawa hawa na farko na kasancewa asali ga mai biye masa na biyu haka na biyu ke kasancewa ga na uku da zai biyo shi, haka abin zai ta kasantuwa……

Shi hajji ciakkaiyar alama ce ga asalan addini haka ga rassansa da akhlaq kai hatta hukumarsa da daula ta bangaren siyasa, hajji kyawawan xabi'u da falaloli.

Lalle taqawa ita ce asasin kyawawan xabi'u kuma jagoransu kamar yadda hakan ya zo cikin hadisai masu daraja cikin hajji mutum ke risker taqawa.


 (آلْحَجُّ أَشْهُرٌ مَعْلُومَاتٌ... وَتَزَوَّدُوا فَإِنَّ خَيْرَ آلزَّادِ آلتَّقْوَى )[43]

Shi hajji wasu watanni ne sanannu….ku yi guzuri lalle mafi alherin guzuri na taqawa.

Sannan cikin abin yanka a hajji Allah na cewa:

 (لَن يَنَالَ آللهَ لُحُومُهَا وَلاَ دِمَاؤُهَا وَلكِن يَنَالُهُ آلتَّقْوَى( [44]

Har abada namanta da jininta ba zai taba samun Allah ba sai dai cewa taqawa na riskarsa.

Lalle imani da Allah da kafircewa xagutu sune asasi da tushen taqawa, saboda haka asasin hajji shi ne tauhidi da kore tarayya da kafircewa xagutu da barranta daga mushrikai kamar yadda manzon Allah(s.a.w) da sarkin muminai Ali(as)  suka yi lokacin saukar ayar bara'a.

Hajji shi ne tauhidi shi kuma tauhidi shi ne kore shirka da tarayya da imani da xayantar Allah, ma'ana wilaya da bara'a, shin menene addini idan ba soyayya domin Allah da qiyayya domin shi

 (وَأَذَانٌ مِنَ آللهِ وَرَسُولِهِ إِلَى آلنَّاسِ يَوْمَ آلْحَجِّ آلاْكْبَرِ أَنَّ آللهَ بَرِيءٌ مِنَ آلْمُشْرِكِينَ وَرَسُولُهُ ( [45]

Shela daga Allah da manzonsa zuwa ga mutane ranar hajji mafi girmalalle Allah ya barranta da manzonsa sun barranta daga mushrikai.

Wannan yekuwa da shelantawa na annbabta muhammadu cigaba ne kan shelar Ibrahim.

 (وأذّن في الناس بالحجّ )

Yekuwa cikin mutane da ibadar hajji.

Wajibi kan dukkanin musulmi maza da mata su barranta daga mushrikai da xagutai da karnukan farautarsu. Hka wajibi su bada kariya ga xakin Allah mai alfarma da tsreatr da shi daga barayi, hakan share fage ga muqaddimar zuwan ranar tsira

عن الامام الصادق  7: «أما إنّ قائمنا لو قد قام لقد أخذهم فقطع أيديهم وطاف بهم وقال : هؤلاء سُرّاق الله» .[46]

An karbo daga imam sadiq(as) amma lalle mai tsayawarmu idanya tsaya ya bayyana, haqiqa zai kamasu ya yanke hannuwansu ya kewaya da su ya ce waxannan sune barayin xakin Allah.

Wannan dukkaninsa na daga cikin sunnar Ibrahim badaxin Allah da aqidarsa.

 

 (وَمَن يَرْغَبُ عَن مِلَّةِ إِبْرَاهِيمَ إِلاَّ مَن سَفِهَ نَفْسَهُ ) [47]

Duk wanda ya kyamaci aqidar Ibrahim face wanda ya wawaitar da kansa.

Shi wawa koyaushe na kyamar sunnonin annabawa da wasiyai idan al'amarin ka'aba  da haramai biyu masu alfarma ya koma hannunsa, lalle ya kasance daga barayin xakin Allah, wajibi kan mahajjaci da mhajjaciya su barranta daga gareshi, su yiwa imam zaman tanadi da shimfaixa da share fage ga bayyanarsa don ya tsyar da adalci a ban qasa bayn ta cika da zalunci da danniya, wannan na cikin mafi boyuwar siiri cikin karbabben hajji da godadden sa'ayi da yafaffen zunubi, Allah abin neman taimako.  


 

 

 HAJJIN JAZZURU(RAQUMI) DA HAJJIN USFURI(TSATSTSEWALA

Abin da aka fa'idantu da shi daga wasu adadin riwayoyi  da hadisai masu daraja daga makarantar ahlul baiti,  cikin waxannan riwayoyi Kalmar hajji da ta zo ya na nuni da cewa hajji kashe huxu ne:

1- hajji mafi girma: wanda ake nufin ranara idi layya ma'ana rana ta goma ga watan zil hijja cikin ranar juma'a.

2 hajji babba: shi ne asalin hajji da kashe kashensa guda uku: hajjin tamattu'I, hajjin qirani, hajjin ifrad.

3 qaramin hajji: shi ne umara mufrada.

4 hajji mafi qanqanta: shi ne I'itikafi wanda mafi qarancinsa shi ne zama cikin masallatai guda huxu ko kuma dukkanin masallatan juma'a a kowanne gari ne bisa sabanin malaman fiqihu wanda aka kawo hakan cikin littafansu na fiqihu.

Sannan mutane sun kasu kashe ta fuskanin hajji: ko dai wanda zai hajji domin Allah ya na mai tsarkake niyya, ko kuma wanda zai yi domin ganin ido da yardar mutane hatta cikinsu akwai wanda idan ba kira shi da sunan Alhaji b aba zai amsa maka kira ba.

وقد ورد عن أميرالمؤمنين  7: «بالاخلاص يكون الخلاص » (أخلص تنل)

Haqiqa hadisi ya zo daga sarkin muminai Ali(as) cewa: da tsarkake niyya ake samun tsira.
 وفي الحديث : «الناس كلّهم هلكى إلّا العلماء، والعلماء كلّهم هلكى إلّا العاملون ، والعاملون كلّهم هلكى إلّا المخلصون ، والمخلصون على خطر عظيم
».

Ya zo cikin hadisi cewa: dukkanin mutane halakakku ne face malamai, sannan dukkanin malamai halakku ne face masu aiki da iliminsu, sannan dukkanin masu aiki halakakku ne face masu tsarkake niyya, sannan su ma masu tsarakake niyya suna cikin hatsari.

Lalle ita riya kamar yadda ya zo cikin hadisi: tana gudana misalign tafiyar baqar tururuwa cikin dare mai tsananin duhu kuma a kan dutse mai santsi, wanene zai iya jin motsi da qarar tafiyar wannan tururuwa?

Sannan ranar qiyama za ai Magana da mai riya ace masa: ya kai kafiri ya fasiqi ya munafiki, saboda haka wajibi garemu mu yi qoqarin yin iklasi da tsarkake niyya da kore shirka qarama boyayya wato riya

Sannan hajjin da ya kasance domin Allah ya kasu kashi biyu: ko dai ya kasance babba cikakke  ko tauyayye qarami, na farko ma'ana wanda juz'ansa da sharuxxa suka cika suka kammala wanda ya tattaro farillai da da nafila, na biyu shi ne wanda ya xan tawaya daga gareshi cikin martabobin kamala duk da dai hajji ne ingantacce a muqamin sauke nauyi da farilla.

Ya zo cikin hadisi annabi mai daraja cikin falalar salla a farkon lokacinta: ita sallah farkon lokaci tana da girma lada kamar raqumi a qarshen lokacinta kuma tana da  qarancin lada kamar tsuntsu.

An kamanta sallah farkon lokaci da raqumi saboda girma da yawan ladanta, haka an kamanta ta qarshen lokaci da tsuntsun tsetstsewala sakamakon qarancin ladanta kamar yadda shima yake xan qanqani qarami, lalle yainta farkon lokaci na nufin idan sallar ta kasance cikin nutsuwa ta kuma tattaro dukkanin sharuxa da ladubba da sunnoni, lalle irin wannan sallah tana janyo samun yardarm Allah, lalle yardarm Allah shi ne mafi girma daga sallah, daidai lokacin da yin sallah qarshen lokacinta yana da matsayin kusan ace mutum ya aikata sabo sai sallah ta zama gafara gareshi, banabanci nawa ne tsakanin sallolin biyu? A nazarina wannan ma'ana na gudana cikin dukkanin ibadu ma'abota martabobi miqaqqu da masu bijira, daga cikinsu hajji lalle daga cikin mutane akwai wanda hajjinsa kwatankwacin raqumi yake cikin lada, cikinsu kuma akwai wanda hajjinsa misalin tsatstsewala ne cikin qarancin lada, kamar misalign hajji ba'arin mawadata masu dukiya ta yadda suke taqaituwa da ayyukan wajibai cikin hajji da sauke nauyi suyi watsi da zikirori da addu'o'I da nafila da mustahabbai da ladubban hajjin ma'nawiya da sanin sirrika da hikmomin hajji da falsafarsa.

Hajji a lugga da isxilahi:

Hajji a luggance an ciroshi ne daga kalamar hajja yahujju da ma'anar nufi da yake maimaituwa da ma'ana dalili da hujja da wsu ma'anonin daban waxanda ba za mu samu damar bayaninsu ba.

A isxilahi kuma: bayani ne game dasauke nauyin kebantattun ibadu cikin sanannun kwanaki qididdigaggu bisa hasken shari'ar muslunci.

Sannan shi hajji nau'I uku ne: ifradi, qirani, tamattu'i. biyun farko suna ga mazauna makka, na uku kuma ga waxanda ke nesa da garin makka da nisan farsaki sha'uku 13 shi ne mafi falala cikin nau'o'in hajji.[1]Hajji:27

[2] Ibrahim:37

[3] Alu imrana:96

[4]Bakara:126

[5] Bakra:125

[6]

[7] Hajji:25

[8] Alu imrana:97

[9] Bakara:196

[10] Bakara:197

[11] Bakara:197

[12] Saba'i:13

[13] Fadir:15

[14] Misbahul shari'a:47

[15] Mustadrak wasa'il: juz 10 sh 175

[16] Alkafi:juz 4 sh b198

[17] Wasa'ilul shi'a: juz 8 sh 82

[18] Hajji:30

[19] Hajji:32

[20] Hajji:28

[21] Ibrahim:37

[22] Ibrahim:34

[23] Isra'i:72

[24] Shu'ara:88-89

[25] abasa:34-36

[26] Mafi yawan abin da ya zo cikin wannan littafi mun xosano shi ne daga littafin (sabhaye hajji) na malamin mu ustaz Abdullah jawadi amuli(dz)

[27] Alu imrana:97

[28] A'araf:142

[29] Wasa'ilul shi'a:juz 7 sh 8

[30] Bakara:251

[31] Wasa'ilul shi'a: juz 8 sh 160

[32] Alu imrana:68

[33] Tagabun:9

[34] Waki'a:49-50

[35] Maryam:95

[36] Azzariyat:50

[37] Biharul anwar: juz 51 sh 59

[38] Biharul anwar:juz 45 sh 138

[39] Ibrahim:37

[40] Wasa'ilul shi'a: juz 9 sh 57

[41] Hajji:25

[42] Nahjul balaga:kudbatul shakshakiyatu.

[43] Bakara:197

[44] Hajji:37

[45] Tauba:3

[46] Wasa'ilul shi'a: juz 9 sh 355

[47] Bakara:130