فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Dare na farko daga dararen lailatul kadari

 

 

dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, tsira da dadin aminci su kara tabbata ga mafi daukakar halittar Allah muhammadu da iyalansa tsarkaka, la'ana madawwamiya kan makiyansu da masu inkarin falalolinsu daga yanzu har zuwa tsayuwar kiyama.

Allah ina rokonka ka kimsa mini tsoranka ka bude bakina da shiriya ka nesantar dani daga bata, ka sanya mana albarka cikin wannan daren namu daren farko daga dararen lailatul kadari, me yafi girma daga daren lailatul kadari wajen Allah da manzanninsa da masoyansa da bayinsa nagargaru, lailatul kadari dare ne da ya fifici watanni dubu wadanda cikin su babu lailatul kadari, lallai ya kasance bai kuma gushe ba tunda Allah ya halicci sammai da kassai, lallai adadin watanni wajen Allah goma sha biyu ne:
(إنَّ عِدَّةَ الشُّهُورِ عِنْدَ اللهِ آثْنَا عَشَرَ شَهْرآ فِي كِتَابِ اللهِ يَوْمَ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأرْضَ )

Lallai adadin watanni wajen Allah goma sha biyu ne cikin littafin Allah ranar da ya halicci sammai da kasa.[1]

 [1] Tauba:36