Watan Ramadan mai albarka jagoran watanni:

 

(شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي اُنزِلَ فِيهِ القُرْآنُ هُدىً لِلنَّاسِ ) .

watan Ramadan wanda aka saukar da kur'ani cikin sa shiriya ga mutane[1]

Kadai dai lailatul kadari ta kasance tun farko, saboda Allah cikin al'arshinsa ta mulki da tafiyarwa yana tafiyar da al'amuran halittunsa yana hukunci da kaddarawa, lallai shi yana saukar da komai bisa kaddara shi da hukuntawa da tafiyarwa, yana bijiro da wannan kaddarawa kan hujjarsa cikin halittunsa, lallai shi mutum ne kammalalle kuma mafi girman hujjojin Allah, lallai shi halifan Allah ne kuma jakadansa a doran kasa, ba da ban shi ba da kasa ta hadiye mutane dake kanta, da sama ta halakar da wanda ke cikin ta, sakamakon danganta halitta sashensu ga sashe, shi mai yawaita ne cikin dayantarsa kuma dayantacce ne cikin yawaitarsa, akwai wata dangantaka ta halitta da shari'a cikin lailatul kadari tsakanin hujjar Allah da wacce take bayyana yau cikin sahibuz zaman (af) al'amuran da ake hukuntawa cikin wannan dare mai albarka ake kuma rarraba dukkanin al'amari mai hikima, Mala'iku na sauka da ruhi amintacce wanda shi mala'ika ne mafi girma daga Jibrilu da Mika'ilu (as) dukkanin Mala'iku mataimakansa ne rundunarsa ne.

ya isar maka cikin girman wannan dare cewa cikin sa ne aka saukar da kur'ani, wancan littafi da yake mai bada kariya ga dukkanin littafai, wannan littafi da babu kokwanto cikin sa shiriya da masu takawa, mai rarrabewa ga mutane, wannan littafi da bata bai zuwa ta kowacce fuska bai zuwar masa ta gaba ko ta baya, littafin da aka tattara dukkanin alheri dake duniya da lahira, aka tattaro ilimummukan mutanen farko da mutanen karshe.

lallai lailatul kadari shi ne mafi girman darare kuma mafi daukakarsu a wurin Allah, hakika saboda girman wannan dare Allah ya boye shi tsakankanin dararen cikin shekara, musammam ma tsakankanin wadannan darare guda uku daga watan Ramadan ma'ana daren sha tara 19 da daren ishirin da daya 21 da daren ishirin da uku 23, risker wadannan darare da raya su da addu'a da ibada da fuskantar Allah matsarkaki da kuka da kamun kafa da waliyyai da zababbun bayinsa da bayinsa tsarkakakku, me yafi yawa daga ayoyi da riwayoyi masu daraja da sukai bayanin falalar wannan dare, me yafi yawa daga addu'o'i gameda risakarsa, cikin kowacce rana mai azumi yana addu'a yana kiran ubangijinsa da ya azurta shi da risker wannan are da mafi falalar yanayi da Allah yafi so da waliyansa.

Zan baku shaida kan addu'ar da ake karantawa cikin kowacce rana daga watan Ramadan mai albarka daga ciki za a san me mutum yake so cikin wannan dare mai albarka:       

«اللهمّ صلِّ على محمّد وآل محمّد واجعل دعائي فيه إليک واصلا ورحمتک وخيرک إليَّ فيه نازلا، وعملي فيه مقبولا، وسعيي فيه مشكورآ، وذنبي فيه مغفورآ، حتّى يكون نصيبي فيه الأكثر الأكبر، وحظّي فيه الأوفر.

Ya Allah ka yi salati ga Muhammad da iyalan Muhammad ka sanya addu'ata cikin sa gare ka mai sadarwa rahamarka da alherinka cikin sa su zamanto masu sauka zuwa gare ni, aiki na ya kasance karbabben aiki, sa'ayina ya zama abin yabawa, zunubina ya kasance an gafarta shi, har nasibina ya kasance cikin sa mafi yawa, rabona ya kasance mafi cika.

اللهمّ صلّ على محمّد وآل محمّد، ووفّقني فيه لليلة القدر على أفضل حال تحبّ أن يكون عليها أحدٌ من أوليائک وأرضاها لک ، ثمّ اجعلها لي خيرآ من ألف شهر، وارزقني فيها أفضل ما رزقت أحدآ ممّن بلّغته إيّاها وأكرمته بها، واجعلني فيها من عتقائک من جهنّم وطلقائک من النار وسعداء خلقک بمغفرتک ورضوانک يا أرحم الراحمين ».

Ya Allah ka yi salati ga Muhammad da iyalan muhammd, ka datar dani cikin lailatul kadari da mafi falalar hali da yanayi da kake so wani ya kasance kai daga waliyyanka mafi yarduwarsa wurinka, sannan ka sanya shi mafia fi alheri daga watanni dubu, cikin sa ka azurtani da mafi falalar abin da ka azurta wani daga wand aka riskar da shi da wannan dare ka karrama shi da shi, ka sanya ni cikin sa daga wadanda kake `yantarwa daga jahannama da `yantattunka daga wuta da azurtattun halittunka da gafararka da yardarka ya mafi jin kan masu jin kai.

 

A wani wuri kuma:

«اللهمّ لک الأسماء الحسنى والأمثال العليا والكبرياء والآلاء، أسألک باسمک بسم الله الرحمن الرحيم إن كنت قضيت في هذه الليلة تنزّل الملائكة والروح فيها أن تصلّي على محمّد وآل محمّد وأن تجعل اسمي في السعداء وروحي مع الشهداء وإحساني في علّيّين وإساءتي مغفورة ، وأن تهب لي يقينآ تباشر به قلبي ، وإيمانآ لا يشوبه شکّ ، ورضىً بما قسمت لي ، وآتني في الدنيا حسنة وفي الآخرة حسنة ، وقِني عذاب النار، وإن لم تكن قضيت في هذه الليلة تنزل الملائكة والروح فيها فأخّرني إلى ذلک ، وارزقني فيها ذكرک ، وشكرک وطاعتک وحُسن عبادتک ، وصلِّ على محمّد وآل محمّد بأفضل صلواتک يا أرحم الراحمين ».

Ya Allah gare ka kyawawan sunaye suke da madaukakan misalsalai da girma da ni'imomi, ina rokonka da sunanka bismillahi rahamanir Rahim idan ka kasance ka hukunta wannan dare kana saukar da Mala'iku da ruhu cikin sa ka yi salati ga Muhammad da iyalan muahammad ka sanya suna na daga wadanda ka azurta ka sanya ruhina tare da shahidai ihsanina cikin madaukaka munanawata ka gafarta, ka bani yakini da zuciya zata damfaru da shi, ka bani imanin da shakka bata cudanya da shi, ka yardarm dani cikin abin da ka sanya kasona, ka bani kyakkyawa cikin duniya da lahira, ka azurtani cikin ta da ambatonka, da godiyarka da biyayyarkada kyawun ibadarka, ka yi salati ga Muhammad da iyalan Muhammad da mafi falalar salatyinka ya mafi jan kan masu jin kai.

Sannan dararen lailatul kadari guda uku suna dangantaka da zaluncin shugaban wadanda aka zalunta sarkin muminai jagoran masu hasken goshi imam Ali bn Abi dalib (as) ta yadda daren farko na lailatul kadari a cikin sa ne tsinannen Allah bamajuse Abdur-rahman bn muljam ya sare shi a kansa, sannan dare na biyu daren ishirin da daya 21 shi ne daren shahadarsa daren na uku daren ishirin da uku 23 kuma daren imam ne.

yayin da lailatul kadari ta kasance daren addu'a daren amsa kiran Allah, sarcikin muminai Ali (as) ya kasance mutum mai yawan addu'a da sannu magana gameda wannan zai kasance cikin maudu'ai biyu: na farko sarkin muminai wanda zai kasance bahasi na akida, maudu'I na biyu shi ne addu'a wanda zai kasance bahasi kan Akhlak kyawawan dabi'u

amma na farko bai saukake mana mu san sarkin muminai hakikanin sani domin babu wanda ya san shi sai Allah da manzonsa kamar yadda ya zo cikin riwaya, kadai zamu san shi karkashin abin da bayani ya zo kan mukaminsa madaukaki da hakkinsa cikin kura'ni mai girma ta yadda daya bisa ukun kur'ani ya sauka kansa ne da kuma karkashin nassoshin annabta da madaukakan hadisai, sannan dukkanin abin da muka sani dangane da sarkin muminai to kasha daya daga cikin kashi dari kamar yadda ya zo cikin madaukakin hadisi 

  «نزّلونا عن الربوبيّة وقولوا فينا ما شئتم ، ولن تبلغوا، وما تقولونه إنّما هو معشار عشر».

Ku nesanta mu daga ubangijintaka ku fadi abin da kuka so cikin mu* ba zaku kai ba, abin da kuke fadi kadai daya cikin dari ne.

Ita ma'arifa wani sa'ilin ta kan kasancewa jalaliya wani karo kuma daga jamaliyya a wani lokacin kuma ta kasance daga kamaliyya, ta farko game gari ce ga kowa da kowa ta biyu kuma kebantatta ta uku kuma kebantacciyar kebantatta.

Ta farko ana iya sanin abu da ita sakamakon girmamar abu da girmansa a zahiri, ta biyu kyawun abu da badininsa, ta uku hakikarsa da zurfinsa da iyakarsa

A wannan dare kadai dai muna neman hanyoyi kofa daga kofofin  kyawuntar sarkin muminai cikin kasantuwarsa ya tattaro siffofin annabawa da kamalarsu.

Cikin mukaddima da share fage muna cewa: lallai Allah yanada sunaye hakika ya zo cikin hadisi mai daraja cewa Allah yanada sunaye dubu hudu, guda dubu ya kebanci kansa da su suna daga cikin sunaye da ya fifita da su babu wanda ya sansu sai shi kadai, sannan ya keabnci masoyinsa annabinsa cika makin annabawa da manzanni Muhammad (s.a.w) da guda dubu, sannan kuma ya kebanci sauran annabawa da guda dubu, sannan guda dubu sai ya koyawa sauran mutane su kamar yadda ya zo cikin addu'ar jaushul kabir.

Wadannan asma'ul husna guda 99 wadanda ambatonsu ya zo cikin kur'ani mai girma da siffarsa madaukakiya suna sauran sunayensa, sunada mabayyanu cikin halittun Allah, lallai Allah masani mai iko rayayye iliminsa da kudurirarsa da rayuwarsa na tajalli cikin halittunsa, haka zalika wasu sunayen da siffofin daban, mafi darajar halittu shi ne mutum, mafi darajar mutane annabawa, sune halifofin Allah da jakadunsa cikin kasa, sai kuma wasiyyai sannan waliyyai sannan malamai wadanda sune magada annabawa, wadannan suke dauke da sunayen Allah da siffofinsa, saboda haka tajallin ilimin na kasancewa na kasantuwa cikin

«من وقّر عالمآ فقد وقّر ربّه ».

Duk wanda ya girmama malami hakika ya girmama ubangijinsa.

 

annabawa sune mabayyanar sunayen Allah kyawawa da madaukakan siffofinsa, sai dai cewa cika makinsu ya tattaro dukkanin sunayen da siffofi, shi ne kammalallen mutum wanda ya tattaro dukkanin tattara, lallai hakikarsa muhammadiya tana gudana cikin daukacin annabawa da manzanni hakama cikin wasiyyai da waliyyai, sannan ta bayyanu tana kuma misalta wannan tattarowa a wani karon cikin nafsin manzon Allah (s.a.w) wanda yake dauke da dukkanin iliminsa da siffofinsa in ka cire annabta da saukar da wahayi, wannan ba kowa bane da ya wuce sarkin muminai shugaban masu tauhidi imam Ali bn Abu dalib (as) shi Ali sirrin Allah ne sirrin manzon Allah ne sirrin daukacin annabawa ne, ya kasance tare da annabi a bayyane ya kuma kasance da daukacin annabawa a sirrance, ba a karbi annabtar wani annabi face da wilayar Ali (as)     

قال رسول الله  9: لمّا اُسري بي في ليلة المعراج واجتمع عليَّ الأنبياء في السماء، فأوحى الله تعالى إليَّ: سلهم يا محمّد بماذا بُعثتم ؟ فقالوا : بعثنا على شهادة أن لا إله إلّا الله وحده ، وعلى الإقرار بنبوّتک والولاية لعليّ .

Manzon Allah (s.a.w) ya ce lokacin da aka tafi dani isra'I cikin daren mi'iraji aka tara mini annabawa, sai Allah ya yi mini wahayi ya ce: tambaye su ya Muhammad dame aka aiko ku? Sai suka ce Allah ya aiko mu kan shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai, da kuma ikrari da annabtarka da wilayar Ali (as)[2]

 

وعن أبي ذرّ قال : كنت جالسآ عند النبيّ  9 ذات يوم في منزل اُمّ سلمة ورسول الله  9 يحدّثني وأنا أسمع إذ دخل عليّ بن أبي طالب  7 فأشرق وجهه نورآ فرحآ بأخيه وابن عمّه ، ثمّ ضمّه إليه وقبّل بين عينيه ، ثمّ التفت إليَّ فقال : يا أبا ذرّ، أتعرف هذا الداخل علينا حقّ معرفته ؟ قال أبو ذرّ: فقلت  : يا رسول الله، هذا أخوک وابن عمّک وزوج فاطمة البتول وأبو الحسن والحسين سيّدي شباب أهل الجنّة . فقال رسول الله  9: يا أبا ذرّ، هذا الإمام الأزهر، ورمح الله الأطول ، وباب الله الأكبر، فمن أراد الله فليدخل من هذا الباب . يا أبا ذرّ، هذا القائم بقسط الله والذابّ عن حريم الله، والناصر لدين الله، وحجّة الله على خلقه ، إنّ الله تعالى لم يزل يحتجّ به على خلقه في الاُمم كلّ اُمّةٍ يبعث فيها نبيّآ 

An karbo daga Abu Zar ya ce: na kasance zaune wajen annabi cikin wata rana a gidan ummul salma manzon Allah (s.a.w) yana zantar dani ni kuma ina sauraro kwatsam sai ga Ali bn Abu dalib (as) sai fuskarsa tayi walka haske saboda farin ciki da ganin dan'uwansa dan baffansa, sannan ya rungume shi ya sumbaci tsakanin idanunsa, sai ya waiwayo gare ni ya ce: ya Abu zar, shin kasan wannan da shigo wajenmu hakikanin saninsa? Sai Abu zar ya ce: sai na ce: ya manzon Allah wannan dan'uwanka ne kuma dan baffanka mijin Fatima batula baban Hassan da Husaini shugabannin samarin gidan aljanna. Sai manzon Allah (s.a.w) ya ce ya Abu Zar wannan ne imami mafi haskaka, mashin Allah mafi tsayi, kofar Allah mafi girma, dukkanin mai nufin Allah to ya shigo ta wannan kofa, ya Abu Zar wannan mai tsayar da adalci mai kare alfarmar Allah hujjar Allah kan halittunsa, lallai Allah madaukaki bai gushe ba yana kafa dalili da shi kan halittunsa cikin daukacin al'ummu da ya aiko annabi cikin su[3]

 

عن أبي الحسن  7 قال : ولاية عليّ مكتوبة في جميع صحف الأنبياء، ولن يبعث الله نبيّآ إلّا بنبوّة محمّد  9 وولاية وصيّه عليّ  7.

Daga Abu hassan (as) ya ce: wilayar Ali rubutacciya ce ckin dukkanin litattafan annabawa, Allah bai taba aiko wani annabi face da annabta Muhammad (s.a.w) da wilayar wasiyinsa Ali (as)

عن محمّد بن مسلم ، قال : سمعت أبا جعفر  7 يقول : إنّ الله تبارک وتعالى أخذ ميثاق النبيّين على ولاية عليّ وأخذ عهد النبيّين بولاية عليّ.

An karbo daga Muhammad bn muslim, ya ce: naji baban Jafar (as) yana cewa: lallai Allah madaukaki matsarkaki ya riki alkawari daga annabawa kan wilayar Ali ya kuma karbi alkawarin annabawa da wilayar Ali.

عن أبي بصير، عن أبي عبد الله  7، أنّه قال : ما نبّئ نبيّ، ولا من رسول اُرسل ، إلّا بولايتنا وبفضلنا على من سوانا.

An karbo daga Abu basir daga Abu Abdullah (as) cewa shi ya ce: ba a annabtar da wani annabi ba babu kuma wani mmanzo da aka aiko face da wilayarmu da falalarmu kan waninmu.

Amma magana kan cewa shi ya tattara siffofin annabawa to ga wasu yanki daga hadisai masu daraja a wannan fage:

عن رسول الله  9 أنّه قال : من أراد أن ينظر إلى آدم في علمه ، وإلى نوح في فهمه ، وإلى إبراهيم في حلمه ، وإلى يحيى في زهده ، وإلى موسى في بطشه ، فلينظر إلى عليّ بن أبي طالب[4]

Daga manzon Allah (s.a.w) cewa lallai shi ya ce: duk wanda yake son ganin Adamu cikin iliminsa, yake son ganin Nuhu cikin fahimtarsa, yake son ganin Ibrahim cikin hakurinsa, yake son ganin Yahaya cikin zuhudinsa, yake son ganin Musa cikin[5] damkarsa to ya kalli Ali bn Abu dalib (as)

وعن الثمالي ، عن عليّ بن الحسين ، عن أبيه ، قال : نظر رسول الله  9 ذات يوم إلى عليّ  7 قد أقبل وحوله جماعة من أصحابه ، فقال : من أحبّ أن ينظر إلى يوسف في جماله ، وإلى إبراهيم في سخائه ، وإلى سليمان في بهجته ، وإلى داود في حكمته ، فلينظر إلى هذا.

An karbo daga sumali daga Aiyu bn Husaini daga babansa ya ce: manzon Allah (s.a.w) wata rana ya kalli Ali (as) ya fuskanto kewaye da shi kuma jana'a daga sahabbansa, sai yac: duk wanda ke kaunar ganin Yusuf cikin kyawunsa, Ibrahim cikin kyautarsa, Sulaiman cikin kyawuntarsa, dauda hikimarsa to ya kalli wannan ya yi nuni zuwa ga Ali.[6]

عن الحارث الأعور صاحب راية عليّ  7 قال : بلغنا أنّ النبيّ  9 كان في جمع من أصحابه فقال : اُريكم آدم في علمه ، ونوحآ في فهمه ، وإبراهيم في حكمته ، فلم يكن بأسرع من أن طلع عليّ  7 فقال أبو بكر: يا رسول الله، أقست رجلا بثلاثة من الرسل ؟ بخٍ بخٍ لهذا الرجل ، من هو يا رسول الله؟ قال النبيّ  9 : ألا تعرفه يا أبا بكر؟ قال : الله ورسوله أعلم . قال : أبو الحسن عليّ بن أبي طالب . قال أبو بكر: بخٍ بخٍ لک يا أبا الحسن ، وأين مثلک يا أبا الحسن ؟.

Daga Harisul A'awar ma'abocin tutar Ali (as) ya ce: mun sami labari cewa lallai annabi (s.a.w) ya kasance cikin taron sahabbansa sai ya ce: yanzu zan nuna muku Adamu cikin iliminsa, Nuhu cikin fahimtarsa, Ibrahim cikin hikimarsa, baui rufe bakinsa ba sai ga Ali (as) ya hudo ya fuskanto sai Abubakar ya ce: ya manzon Allah (s.a.w) ka kiyasta mutumin da manzanni uku, lale-lale da wannan mutumin, sai ya ce: ya manzon Allah wanene wannan mutumin? Annabi (s.a.w) ya ce: shin baka san shi ya Abubakar sai ya ce Allah da manzonsa sune mafi sani, ya ce: to shi ne baban Hassan Aliyu bn Abu dalib, Abubakar ya ce: farin ciki farin ciki gare ka ya baban Hassan, ina za a samu misalinka ya baban Hassan?.[7] 

عن أبي ذرّ الغفاري قال : بينما ذات يوم من الأيام بين يدي رسول الله  9 إذ قام وركع وسجد شكرآ لله تعالى ثمّ قال : يا جندب ، من أراد أن ينظر إلى آدم في علمه ، وإلى نوح في فهمه ، وإلى إبراهيم في خلّته ، وإلى موسى في مناجاته ، وإلى عيسى في سياحته ، وإلى أيّوب في صبره وبلائه ، فلينظر إلى هذا الرجل المقبل الذي هو كالشمس والقمر الساري والكوكب الدرّي ، أشجع الناس قلبآ وأسخى الناس كفّآ، فعلى مبغضه لعنة الله والملائكة والناس أجمعين ، قال  : فالتفت الناس ينظرون من هذا المقبل فإذا هو عليّ بن أبي طالب عليه الصلاة والسلام .

Daga Abu zar giffari ya ce: daidai lokacin da wata rana daga ranaku muna wajen manzon Allah (s.a.w) kwatsam sai ya tashi ya yi ruku'I ya yi sujjada domin godiya ga Allah madaukaki sannan ya ce: ya jundub, duk mai son ya kalli Adamu cikin iliminsa, Nuhu cikin fahimtarsa, Ibrahim cikin badadintakarsa, Musa cikin munajatinsa, Isa cikin ibadarsa, Ayyuba cikin hakurinsa da musibar da ya shiga, to ya kalli wannan mutumin da yake fuskantowa shi kamar rana ne da wata mai tafiya da tauraro mai haskaka, shi ne mafi karfin zuciya cikin mutane, shi ne mafi kyautar hannu, tsinuwar mutane da Mala'iku ta tabbata kan makiyinsa, ya ce: sai mutane suka waiwaya suka wanene wannan mutumin mai fuskantowa kawai sai ga Aliyu bn Abu dalib amincin Allah ya kara tabbata shi ne.[8]

Rayuwar sarkin muminai da tsarin yadda annabi ya rayu mai albarka dukkaninsu suna shaida kan wadancan madaukakan siffofi na Allah da annabi kamar yadda tarihi ke bamu labarin hakan filla-filla

Amma maudu'i na biyu: lallai ita addu'a tana ma'anar yankewa zuwa matsarkakim da fuskanta zuwa shi ne, da tsananta alaka da dangantaka da shi, lallai hakan shi ne bargon adddu'a da ruhinta, sannan babu wani da yake halaka matukar ya rungumi addu'a, sannan ita ibada ita ce hadafin halittu halittu da ma'anar horar da hanya zuwa Allah matsarkaki yana misaltuwa cikin yankewa da komawa zuwa ga Allah da nema daga gare shi cikin kowanne abu kai hatta gishirin cikin guzuri, da gyara taguwar takalmi, duk sanda bawa ya larurantu ya na ce cikin addu'a Allah zai kusanta da amsa masa  

 (أمَّنْ يُجِيبُ المُضطَرَّ إذَا دَعَاهُ وَيَكْشِفُ السُّوءَ).

Ko wanene yake amsawa wanda yake cikin larura idan ya kiraye shi ya kuma yaye masa mummuna[9]

(وَقَالَ رَبُّكُمُ آدْعُونِي أسْتَجِبْ لَكُمْ إنَّ الَّذِينَ يَسْتَكْبِرُونَ عَنْ عِبَادَتِي سَيَدْخُلُونَ جَهَنَّمَ دَاخِرِينَ ).

Kuma ubangijinku ya ce ku kirayeni zan amsa muku lallai wadanda suke girman kai daga bautata da sannu zasu shiga jahanna suna kaskantattu[10]

(قُلْ مَا يَعْبَأُ بِكُمْ رَبِّي لَوْلا دُعَاوُكُمْ )

Kace ubangijinku bai damu daku b aba don addu'o'inku ba.[11]

Lallai Allah yana kaunar addu'ar bawansa mumini yana jinkirta amsa masa domin yaji sautinsa: 

«عن العالم  7: إنّ الله عزّ وجلّ ليؤخّر إجابة المؤمن شوقآ إلى دعائه ويقول : صوتٌ اُحبّ أن أسمعه ، ويعجّل دعاء المنافق ويقول : صوت أكرهه ».

An karbo daga malami (as): lallai Allah yana jinkirta amsawa bawansa mumini saboda shaukin addu'arsa yana cewa: murya ce dana ke son jinta, sannan Allah yana gaggauta addu'ar munafuki, yana cewa: murya ce da bana sonta.[12]

 

عن أمير المؤمنين  7: أحبّ الأعمال إلى الله عزّ وجلّ في الأرض الدعاء.

An karbo daga sarkin muminai (as) mafi soyuwar ayyuka zuwa ga Allah mai girma da daukaka a doran kasa ita ce addu'a.

Ita addu'a cikin kowanne hali kewaye take da taufiki da amsawa ko cikin jinkiri ko kuma cikin gaggawa kamar yadda ya zo daga madaukakin hadisi ita addu'a tana da ladubba da sharudda kamar misalin kyauata zato da Allah da yakini da amsawarsa da larurantuwa zuwa gare shi da tsarkake niyyada shiga ta kofar da Allah madaukaki ya yi umarni da ita, da fuskantar da zuciya zuwa ga Allah, da kaskantar da kai da sirantar da zuciya da daga hannuwa zuwa sama, da farawa da bismillah da girmama Allah da istigfari, da salati ga Muhammad da iyalansa gabanin fara addu'a da bayan idar da ita, da cika alkawari, da cudanya addu'ar da aiki domin ita addu'a tana daga cikin sunnonin Allah, da taruwa wuri daya don yin addu'a da kuma neman mumiani suce amin da sakankancewa cikin addu'a da nema da naci da magiya cikin nema da kiran Allah da sunayensa kyawawa tare da naci

«إنّ الله يحبّ الملحّين في الدعاء».

Lallai shi yana son masu naci cikin addu'a

«إنّ الله يحبّ السائل اللحوح ، ومتى تكثر قرع الباب يفتح لک ».

Allah yana son mai roko da mai naci*duk sanda aka yawaita kwankwasa kofa za a bude kofar

عن الصادق  7: الدعاء يردّ القضاء بعدما اُبرم إبرامآ، فأكثر من الدعاء فإنّه مفتاح كلّ رحمة ونجاح كلّ حاجة ، ولا ينال ما عند الله عزّ وجلّ إلّا بالدعاء وإنّه ليس باب يكثر قرعه إلّا أوشک أن يفتح لصاحبه.

An karbo daga imam sadik (as) addu'a na komar da abin da aka rigaya aka hukunta bayanda an tabbatar da shi tabbatarwa, ka yawaita yin addu;a lallai ita addu'a mabudin dukkanin rahama ce, ita ce kuma nasarar dukkanin bukata, ba a samun abin da ke wajen Allah mai girma da daukaka face da addu'a lallai babu wata kofa da za yaiwata kwankwasa ta face ya yi kusa a buda ga mai kwankwasa.[13]

وعن الباقر  7: إنّ الله كره إلحاح الناس بعضهم على بعض في المسألة ، وأحبّ ذلک لنفسه.

An karbo daga imam bakir (as) lallai Allah yana kyamar nacin mutane sashensu ga sashe cikin wata bukata, yafi son hakan zuwa gare shi

عـن أمير المؤمنين  7: فالحح عليه في المسألة يفتح لک أبواب الرحمة .

An karbo daga sarkin muminai (as) naci zuwa ga Allah cikin wata bukata na bude maka kofofin rahama.

Daga cikin sharudda da ladubban addu'a shi ne yin addu'a ga wasu mutane da kuma yin addu'a tare da wasu, da yin addu'a lokacin da ruwan sama ke sauka, da yin addu'a tsakiyar dare, ita addu'a it ace kur'ani mai hawa cikin kausul su'udi, shi kuma kur'ani mai girma shi ne kur'ani mai sauka cikin kausul nuzuli, shi kur'ani mai sauka kira ne na gaskiya da ubangijin talikai zuwa ga tauhidi da ibada da inkarin dawagitai, da'awa daga gaskiya Allah zuwa halitta, ita kuma addu'a amsa wannan da'awa ce, lallai ita daga halittu zuwa gaskiya zuwa ga Allah.

Akwai wasu kayoyi da tubatubai da suke hanawa suke tsare addu'a daga amsuwa daga hawa zuwa ga Allah matsarkaki, daga cikin mafi muhimmancinsu shi ne aikata zunubai da sabo da laifuka da alfasha wacce take bayyane da ta boye.

«اللهمّ اغفر لي الذنوب التي تحبس الدعاء».

Ya Allah ka yafe mini zunubaina wadanda suke tsare addu'a

«فأسألک بعزّتک أن لا يحجب عنک دعائي سوء عملي وفعالي ».

Ina rokonka don buwayarka ka da ka mummuna aikina ya katange addu'a gare ka.

Zunubai cikin rayuwar mutum suna taka rawa guda biyu:

Ta farko: hijabi da katangeka daga Allah mai aikata zunubi bai iya samun damar fuskanta zuwa ga Allah matukar dai bai tuba ba zuwa ga ubangijinsa.

Na biyu: hijabance addu'a daga hawa zuwa ga Allah matsarkaki, lallai addu'a idan takai ta isa zuwa gare shi zai amsa ta cikin kowanne hali. Saboda kamalar ilimi da kyauta cikin wanda ake roka daga gare shi, wanda shi ne Allah matsarkaki.

Sannan mutum yanada gabban zahiri da na ciki wadanda suke boye, zuciyarsa gabace ta boye da take fesa jini cikin karba da bayarwa, haka zuciyarsa gabace da take alakanta mutum da Allah yanada ka karba daga Allah da rabawa gabban waje da gabban ciki sai rahamar Allah ta bayyana ciki sulukin mutum da rayuwarsa da tsarin yadda yake rayuwa.

Sannan zuciyar tsoka gabace da take mutuwa idan jini ya yanke da toshewar jijiyoyi, haka gabban badini suna mutuwa da aikata zunubi da sabo, zuciya badini tana karbar hasken Allah da shiriya tana bada shi tana kuma rarraba shi cikin dukkanimotsin mutum da shirunsa.

Mafi muhimmanci abubuwan da suke jawo toshewar da rufewar zuciya sune abubuwa guda biyu:

Na farko: bijerewa ayoyin Allah da karyatasu:

   
 (وَالَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا صُمٌّ وَبُكْمٌ فِي الظُّلُمَاتِ ).

Wadanda suka karyata ayoyinmu bebaye ne kurame ne cikin duhuna.[14]

(وَإذَا تُـتْلَى عَلَيْهِ آيَاتُنَا وَلَّى مُسْتَكْبِرآ كَأنْ لَمْ يَسْمَعْهَا كَأنَّ فِي اُذُنَيْهِ وَقْرآ).

Idan aka karanta ayoyinmu kansa sai ya juya yana mai girman kai kamar bai ji ayar ba kamar cikin kunnuwansa akwai nauyi.[15]

 

Na biyu sune zunubai:

 (كَـلاَّ بَلْ رَانَ عَلَى قُـلُوبِهِمْ مَا كَانُوا يَكْسِبُونَ ) .

Bari abin da suke aikatawa ya yi tsatsa cikin zukatansu.[16]

قال الصادق  7: كان أبي يقول : ما من شيء أفسد للقلب من خطيئته ، إنّ القلب ليواقع الخطيئة فلا تزال به حتّى تغلب عليه ، فيصير أعلاه أسفله .

Imam Sadik (as) ya ce: babana ya kasance yana cewa: babu wani abu da yafi lalata zuciya fiye da laifinta, lallai zuciya tana afkawa laifi ba zai gushe ba har sai ya yi galaba kanta, sai sama ta zamanto ta juye ta koma kasa.

Ita zuciya tana karbar haske da shiriya da ayoyin kur'ani wanda muke dora shi a kawunanmu lokacin addu'ar daren lailatul kadari da ayyukansa.

(وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوْلا نُزِّلَ عَلَيْهِ القُرْآنُ جُمْلَةً وَاحِدَةً كَذَلِکَ لِنُثَبِّتَ بِهِ فُؤَادَکَ وَرَتَّـلْنَاهُ تَرْتِيلا) 

Wadanda suka kafirce suka ce don me ba za a saukar masa da kur'ani jumla guda kamar wancan domin mu tabbatar da zuciyarka muka jera karatunsa jerawa.[17]

 

 (اللهُ نَزَّلَ أحْسَنَ الحَدِيثِ كِتَابآ مُـتَشَابِهآ مَثَانِيَ تَقْشَعِرُّ مِنْهُ جُلُودُ الَّذِينَ يَخْشَوْنَ رَبَّهُمْ ثُمَّ تَلِينُ جُلُودُهُمْ وَقُلُوبُهُمْ إلَى ذِكْرِ اللهِ)

Allah ya saukar da mafi kyawun zance littafi mai kamanceceniya  da juna wanda ake konkoma a karatunsa fatukan wadanda suke tsoransa suna kwansarewa da shi sannan tayi taushi da zukatansu zuwa ga ambaton Allah.[18]

(يَا أيُّهَا النَّاسُ قَدْ جَاءَكُمْ بُرْهَانٌ مِنْ رَبِّكُمْ وَأنزَلْنَا إلَيْكُمْ نُورآ مُبِينآ).

Yaku mutane hakika hujja daga ubangijinku ta zo muku kuma mun saukar muku da haske mabayyani[19]

(هَذَا بَيَانٌ لِلنَّاسِ وَهُدىً وَمَوْعِظَةٌ لِلْمُتَّقِينَ ).

Wannan bayani ne ga mutane da shiriya da wa'azi ga masu tsoran Allah.[20]

(هَذَا بَصَائِرُ مِنْ رَبِّكُمْ وَهُدىً وَرَحْمَةٌ لِقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ ).

Wannan kur'ani hukunce-hukuncen nutsuwa ne ga mutane da rahama ga mutanen da suke imani[21]

 Zuciyar da haske da shiriya ke kwarara kanta cikin rayuwa tana kasancewa rayayyiya

 (أوَ مَنْ كَانَ مَيْتآ فَأحْيَيْنَاهُ وَجَعَلْنَا لَهُ نُورآ يَمْشِي بِهِ فِي النَّاسِ ) .

Shin wanda ya kasance mace sai muka rayara da shi muka sanya masa haske yana tafiya da shi cikin mutane.[22]

(يَا أيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا آتَّـقُوا اللهَ وَآمِنُوا بِرَسُولِهِ يُؤْتِكُمْ كِفْلَيْنِ مِنْ رَحْمَـتِهِ وَيَجْعَلْ لَكُمْ نُورآ تَمْشُونَ بِهِ وَيَغْفِرْ لَكُمْ وَاللهُ غَفُورٌ رَحِيمٌ )

Yaku wadanda sukai imani kuji tsoran Allah ku yi imani da manzonsa zai baku rabo biyu daga rahamarsa ya kuma sanya muku haske da zaku dinga tafiya da shi ya kuma gafarta muku Allah mai yawan gafara ne da jin kai.[23]

(وَمَنْ لَمْ يَجْعَلْ اللهُ لَهُ نُورآ فَمَا لَهُ مِنْ نُورٍ).

Duk wanda Allah bai sanya masa haske ta bashi da haske.[24]

Ita zuciya ita ce tsanin da yake tsakanin bawa da Allah tana karbo haske da shiriya sannan da rarraba shi zuwa gabban waje da na ciki boyayyu.


قال أمير المؤمنين
 7: «كتاب الله تبصرون به ، وتنطقون به ، وتسمعون به ».

Sarkin muminai Ali (as) ya ce: littafin Allah kuna gani da shi* kuna magana da shi* kuna saurare da shi.

Idan mutum ya rasa kur'ani mai saukowa, to zai iya rasa samun daga kur'ani mai hawa, ma'ana addu'a sai zuicyarsa ta kulle

 (صُمٌّ بُكْمٌ عُمْىٌ فَهُمْ لا يَرْجِعُونَ ).

Kurmaye baibaye makafi su basa komowa.[25]

Basu ganin gaskiya, basa jin magana, basa kuma iyayin maganar Allah da ita.

 (ثُمَّ قَسَتْ قُلُوبُكُمْ مِنْ بَعْدِ ذَلِکَ فَهِيَ كَالحِجَارَةِ أوْ أشَدُّ قَسْوَةً ).

Sannan zuciyarsu ta kekashe bayan haka ta zama kamar dutse bari ma tafi dutse kekashewa.[26]

(إنَّکَ لا تُسْمِعُ المَوْتَى وَلا تُسْمِعُ الصُّمَّ الدُّعَاءَ) .

Lallai kai baka jiyar da matattu baka kuma iya jiyar da kurame kiranka.[27]

 

Da zunubi mutum ke rasa zakin zikiri, mafi kankantar abin da Allah zaiwa masu aikata zunubi da kuma wadanda basa aiki da iliminsa shi ne ya rabasu da dadi da zakin munajati.

وجاء رجل إلى أمير المؤمنين  7 فقال : يا أمير المؤمنين ، إنّي قد حرمت الصلاة بالليل ، فقال  7: أنت رجل قد قيّدتک ذنوبک ، والمعصية تمنع الإجابة .

wani mutum ya zo wajen sarkin muminai (as) sai ya ce: ya sarkin muminai, lallai ni na haramtu daga sallar dare, sai (as) ya ce: lallai kai mutum ne da zunubai sukai maka dabaibayi, shi sabo na hana amsa addu'a

وعن الإمام زين العابدين  7: والذنوب التي تردّ الدعاء وتظلم الهواء عقوق الوالدين . وفي رواية اُخرى : والذنوب التي تردّ الدعاء: سوء النيّة ، وخبث السريرة ، والنفاق ، وترک التصديق بالإجابة ، وتأخير الصلوات المفروضات حتّى تذهب أوقاتها، وترک التقرّب إلى الله عزّ وجلّ بالبرّ والصدقة ، واستعمال البذاء والفحش في القول .

An karbo daga imam zainul Abidin (as): zunubai wadanda ke wurgi da addu'a suke duhunta iska sune sabawa iyaye. Ya zo cikin wata riwaya daban: zunuban da suke mayar da sune; munana niyya, munanar badini, maunafunci, barin gasgata amsawa, jinkirta sallolin farilla har sai lokacinsu ya fita, watsi da neman kusancin Allah da kyautatawa da kuma yin sadaka, amfani da zagi da kalmomin alfasha cikin magana.

 وعن الإمام أبي جعفر  7: إنّ العبد يسأل الله الحاجة فيكون من شأنه قضاؤها إلى أجل قريب فيذنب العبد ذنبآ فيقول الله تبارک وتعالى للملک : لا تقضِ حاجته واحرمه إيّاها، فإنّه تعرّض لسخطي ، واستوجب الحرمان منّي .

Ana karbo daga imam Abu Jafar (as) lallai bawa yana rokon Allah bukata sai ya zama cikin sha'aninsa amsa wannan bukata zuwa lokaci kusa-kusa, sai bawan nan ya aikata zunubi sai Allah matsarkaki madaukaki ya cewa mala'ika: kada ka biya bukatarsa ka haramta masa ita, lallai shi ya zakkewa fushina, ya cancanci haramtawa.

Daga cikin ludufinsa da rahamarsa ga bayinsa shi ne sanya musu tsani wasila cikin amsa addu'a da kusanta zuwa shi ne, Allah madaukaki ya ce:

(اُوْلَئِکَ الَّذِينَ يَدْعُونَ يَـبْتَغُونَ إلَى رَبِّهِمُ الوَسِيلَةَ ) .

Sune wadanda suke kira suke neman tsani zuwa ga ubangijinsu.[28]

Wannan tsanuka wasilu Allah ya sanya su ga wanda addu'arsa ta gaza hawa zuwa wajen ubangijinsa:

(إلَيْهِ يَصْعَدُ الكَلِمُ الطَّـيِّبُ وَالعَمَلُ الصَّالِـحُ يَرْفَعُهُ ) .

Shi ne daddadan zance ke hawa zuwa gare shi kuma aiki nagari yana daukar ta.[29]

Sannan ya zo a hadisi cikin tafsirin hawan daddadan zance kadai dai daddadan zance shi ne aiki tsarkakakke, yana daga bayyanannen ala'amari cewa iklasi tsarkake aiki yana daga abu mai wahalar gaske, dukkanin mutane halakakku ne face malamai, su malamai dukkaninsu halakakku ne in banda masu aiki daga cikin su, sannan masu aiki dukkaninsu sun halaka in banada masu iklasi, sannan su kuma masu iklasi suna cikin hatsari mai girma.

Shi aiki nagari yana daukaka daddadan zance da shaidar kur'ani mabayyani, sai dai cewa mutum na iya gaza yin aiki nagari sai Allah ya sanya tsani domin hawa:

Daga cikin wadannan wasiloli da tsanuka akwai istigfarin annabi ga al'ummarsa:

(وَلَوْ أنَّهُمْ إذْ ظَلَمُوا أنفُسَهُمْ جَاؤُوکَ فَاسْتَغْفَرُوا اللهَ وَاسْتَغْفَرَ لَهُمُ الرَّسُولُ لَوَجَدُوا اللهَ تَوَّابآ رَحِيمآ) .

Da ace yayin da suka zalunci kawukansu sun zo wajenka sun nemi gafarar Allah kuma manzon Allah ya nema musu gafara tabbas zasu samu Allah mai karbar tuba da jin kai.[30]

Daga cikin akwai tawassuli kamun kafa da manzon Allah da Ahlin gidansa.

عن داود البرقي قال : إنّي كنت أسمع أبا عبد الله  7 أكثر ما يلحّ في الدعاء على الله بحقّ الخمسة ـيعني رسول الله وأمير المؤمنين وفاطمة الزهراء والحسن والحسين  :ـ .

An karbo daga dauda barka'i ya ce: lallai ni na kasance ina jin Abu Abdullah (as) mafi yawan lokaci yana yin naci cikin addu'a kan Allah da alfarmar mutane biyar ma'ana manzon Allah da sarkin muminai da Fatima da Hassan da Husaini[31]

وعن سماعة : قال لي أبو الحسن  7: إذا كان لک يا سماعة إلى الله حاجة فقل : اللهمّ إنّي أسألک بحقّ محمّد وعليّ، فإنّ لهما عندک شأنآ من الشأن وقدرآ من القدر، وبحقّ ذلک القدر أن تصلّي على محمّد وآل محمّد، وأن تفعل بي كذا وكذا ، فتطلب حاجتک .

An karbo daga samma'atu: Abu Hassan (as) ya ce mini ya samma'atu idan wata bukata ta kasance gare ka kace: ya Allah lallai ni ina rokonka don alfarmar Muhammad da Ali kai mini kaza da kaza, sai ka nemi bukatarka.[32]

Hakika Allah ya amsawa Adamu ya kuma karbi tubansa yayin da ya tawassuli da alfarmar mutanen cikin bargo, kamar yadda hadisi ya zo da bayanin haka daga shi'a da sunna.

 

Daga cikin tsani da wasila akwai ikrari da zunubin da ka aikata:

 

«وجعلتُ الإقرار بالذنب وسيلتي »  .

Na sanya ikirari da zunubi tsani zuwa gare ni.

Ya ku muminai, lallai mutum a kankin kansa yana cikin basira koda kuwa ya bada uzurrai, lallai shi mutum yana suturce kansa, kowanne mutum daga cikin mu ya san abin da ya aikata daga zunubai, daren lailatul kadari na farko dare ne na neman gafara dare ne na yin istigfari da tuba da komawa zuwa ga Allah matsarkaki, dare ne na kwabuwa daga laifuka da sabo da dabi'u marasa kyau da suka zama jiki da siffofi munana da halaye munana, muna tawassuli zuwa ga Allah da ma'asumai goma sha hudu: da daga kur'ani a kawukanmu domin kawunkanmu su kasance cikin inuwar kur'ani, cikin da'airar koyarwarsa muna tsiwurwurar daddadar rayuwa da ma'arifofin Allah da ilimummukan sama.

Daga Allah taufiki yake da damdagatar, dukkanin godiya ta tabbata ga ubangijin talikai, tsira da aminci su kara tabbata ga Muhammad da iyalansa tsarkaka. 

 [1] Bakara:185

[2] Gayatul muram sh 608.biharul anwarm 40 sh 55

[3] Manakib  ibn magazilish 212, tarjamar imam Ali daga tarik damashk:m 2 sh 280. Shawahidul tanzil:781.

[4] ()  أمالي الصدوق : 391.

[5] Amali saduk sh 391

[6] Kashful gumma:33.Arrauda:17.fada'il 102

[7] Arrauda3-4

[8] Almilal:62

[9] Annamlu:62

[10] Gafir:60

[11] Furkan:77

[12] Wasa'il: m 4 sh 1086

[14] An'am:39

[15] Lukman:7

[16] Mudaffifin:14

[17] Furkan:32

[18] Zumar:23

[19] Nisa'i:174

[20] Alu Imran:38

[21] A'araf:203

[22] An'am:12

[23] Hadid:28

[24] Nur:40

[25] Bakara:18

[26] Bakara:74

[27] Annamlu:80

[28] Ma'ida:35

[29] Fadir:10

[30] Nisa'i:64

[31] Wasa'il: m 4 sh 1129

[32] Uddatul da'i:38