Muhadarar daren lailatul kadari na biyu

 

Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai tsira da aminci su kara tabbata ga muhammadu ga mafi daukakar halittun Allah Muhammad da iyalansa tsarkaka, ya Allah ka kimsa mini tsoranka ka bude bakina da shiriya, kai mini taufiki da daren lailatul kadari da mafi falalar hali da yanayi da kake so daya daga cikin waliyanka ya kasance ciki, ina mai godiya da yabawa da salati da da'a da neman gafara da kuka da tsoro da neman taimako daga gare ka. mai bautawa maka kai kadai.

Muna maka godiya ya Allah yayin da ka datar damu da raya wannan dare na lailatul kadari, muna rokonka ka sanya shi mafi alheri daga watanni dubu, ka azurtamu da lafiya, lafiyar addini da lahira.

Menene yafi girmama wajen Allah da manzonsa da wasiyyansa da waliyyansa daga lailatul kadari, lallai shi dare ne na saukar kur'ani mai girma, wancan littafi da babu kokwanto cikin sa shiriya ga masu takawa.

Dukkanin wanda yake misalta cikin sa ayoyin kur'ani kuma suke sauka kan samuwarsa, to ya jikkantu da kur'ani cikin akidarsa da sulukinsa da ayyukansa da dabi'unsa, sai ya zama yana dabi'antuwa yana jikkantuwa da kur'ani lallai hakan yana daga daga abubuwan da suke gasgata daren lailatul kadari, ya riski albarkarsa da rahamarsa da falalarsa da mukaminsa madaukaki duk wanda ya dabbaka kur'ani mai girma ya yi aikida shi cikin rayuwarsa da dabi'unsa to zai kasance cikin lailatul da yininsa, sannan duk wanda ya juya masa baya (wa'ayabillahi) babu banbanci cikin wanda juyawa baya shin kur'ani mara magana ne ko kuma kur'ani mai magana wanda shi ke bayani kur'ani da ya sauko daga sama ma'ana imam ma'asumi cikin kowanne zamani, lallai lailatul kadarinsa zata kasance daga lailatul kabari gare shi daren kabari, wannan mutumi ya kasance mai matacciya zuciya ko da kuwa a zahiri ga shi yana rayuwa rayuwar dabba da tsirrai yana ci yana sha yana biyewa sha'awe-sha'awe, lallai wannan mutumi yam utu cikin mutumtakarsa da cikin ta ruhu da malakutiyya ke misalta.[1]

(وَنَفَخْتُ فِيهِ مِنْ رُوحِي ).

Na huri cikin sa daga ruhina.

Mutane cikin misalin wadannan darare masu alabarka ko dai su kasance daga lailatul kadari ko kuma cikin lailatul kabari, duk wanda ya kasance yana dauke da ma'arifofi ilimin sanin Allah na gaskiya da ilimummukan Allah, da Akhlak din muhammadiya, siffofin alawiyya, da karamomin fadimiyya, da falalolin hasaniyya, da kyawawan dabi'un husainiyya, zai shiga da'irar saklaini:littafin Allah da itira tsarkaka Ahlil-baiti, lallai shi yana daga lailatul kadari, amma duk wanda ya karkacewa siradi mikakke da labari mai girma, ya kuma ki kafircewa jibtu da dagutu, ya riki son ransa abin bautarsa, tsiyatarsa tayi galaba kansa, lallai shi zai kasance daga lailatul kabari.

Sannan kamar yadda ya zo daga riwaya daga bangarori biyu shi'a da sunna daga manzon Allah (s.a.w) ya ce: 

عليّ مع القرآن والقرآن مع عليّ لن يفترقا حتّى يردا عليَّ الحوض .

Ali yana tare da kur'ani hakama kur'ani yana tare da Ali ba zasu taba rabuwa da juna har sai sun gangaro tafkina.

Hakama ya ce:

«عليّ مع الحقّ والحقّ مع عليّ أينما دار يدور».

Ali yana tare da gaskiya haka kuma gaskiya tana tare da shi duk inda ya juya tana juyawa.

Duk wanda ya kasance tare da kur'ani tare da Ali cikin ya kasance  daren lailatul ya kuma riski falalarsa da alherinsa da darajarsa da albarkatunsa, za kuma a rubuta shi cikin illiyun madaukaka.

Idan ya kasance cikin hadisan Ahlil-baiti (as) ya zo cewa Fadima ita ce lailatul kadari, saboda haka duk wanda ya santa tabbas ya riski lailatul kadari, lallai yadda al'amarin yake shi ne bisa la'akari da cewa Fatima ita ce mafi cikar abin da ke gasgata lailatul kadari, sannan kirjinta masaukin tabbatattun ilimummukan kur'ani ne kuma iatce ruhin annabi da yake tsakankanin geffansa biyu kamar yadda nan gaba za muyi bayanin wannan ma'anar insha'Allah cikin lailatul kadari dare na uku.

Ita Fatima Zahara shugabar matayen duniya ita tattaro tsakanin, ita `yar cikamakin annabawa ce kuma ita ce matar shugaban wasiyyai, lallai ita mabayyana babbar ismar Allah ce, dukkanin ma'asumi shi lailatul kadari ne, bari dai abun ya shallake nan kai dukkanin dan shi'a mai imani da wilayar, mai aiki da kur'ani kuma kur'ani yana misaltuwa cikin sa, sannan cikin rayuwarsa akwai haskayen saklaini-littafin Allah da tsatso tsarkakka Ahlil-baiti shima lailatul kadari ne, da gwargwadon abin da yake dauke da shi daga ilimi da ma'arifofin kur'ani da annabta da wilaya lallai shi ya riski lailatul kadari, amma wanda ya kasance ya tattaro munanan siffofi da munanan dabi'u, ya kuma bi shaidan da rudunarsa da mataimakansa, ya shiga wilayar jibtu da dagutu, lallai shi zuciyarsa zata mutu, yakuma kasance lailatul kabari. Duk wanda yake son fita daga kabarinsa da darensa, ya shiga cikin lailatul kadari da darajarsa da falalarsa, to wajibinsa ya siffantu da ayoyin kur'ani mai girma, ya kuma dabi'antu da dabi'un Allah da manzon Allah (s.a.w).

 

wasiyyai da tsatso tsarkakakke:

idan cikamakin annabawa shugaban manzanni Muhammad (s.a.w) rahama ne ga talikai, lallai kadai shi wani yanki ne daga rahamar Allah mudlaka ba tared karshe ba, lallai Allah yana kare mutumcin bawansa gaban halittu idan ya kasance daga ma'abota raya daren lailatul kadari, amma wanda ya aikata zakkewa zunubi da sabo, ya munana littafin reokdin din ayyukansa, lallai ya yi kokari ya tuba cikin wannan dare kamar yadda ya tuba a daren farkon lailatul kadari, sannan ya yi ado da da'ar ubangijinsa ya kuma nemi gafararsa, lallai Allah zai gafarta masa zai kuma karbi tubansa zai masa sassaukan hisabi, ba zai tona asirinsa ba gaban mutane bari dai zai suturta shi ya rufa msa asiri ya bayyana kyawawansa, lallai shi wannan dare dare ne na tsafatace kai da ado da kyawawan dabi'u, lallai Allah zai masa gafara zai sanya kasa ta manta daga zunubansa, kamar yadda yake mantar da gabbansa, bari dai rahama Allah mai yalwa zata mamaye shi har ta kai ga Allah ya mantar da shi zunuban da ya aikata sai ya zama bai jin kunyarsa kansa, lallai wanda ya tuba daga zunubi kamar misalin wanda bai taba aikata zunibi bane, sannan Allah zai sanya shi cikin aljanna zai shiga, ba zai dinga tunawa da zunubinsa ba domin shi tunawa da zuna na kona da sanya bakin ciki, ita kuma aljanna cikin ba babu kunan rai babu bakin ciki babu damuwa, zai kasance kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi tsarkake tsarkakakke kiyayayye daga zunubi.

Kan kowanne mutum wajibi ya zama mabayyanar lailatul kadari lokacin da yake kasancewa cikin halarto da kur'ani mai girma da tsatso tsarkaka a sulukinsa da ayyukansa da tunaninsa da akida da jihadi.

Daga nan muke kara yakini da sabati cikin akidarmu, lallai dararen cikin su zalunci da akaiwa sarkin muminai shugaban masu tauhidi imamin masu tsoran Allah zakin Allah mai galaba Ali bn Abu dalib (as) ina son in dan yi ishara zuwa ga wani haske daga haskayensa (as) karkashin ma'arifa jamaliyya mai haskaka, domin mu kasance cikin fadar sahibuz-zaman imaminmu wanda muke sauraro hujjar Allah ta goma sha biyu amincin Allah ya kara tabbata shi ne Abadan abidin, Allah ya gaggauwata bayyanarsa, ya sanya mu daga zababbun shi'arsa da mataimakansa masu tallafa masa ya sanya mu masu shahada a gabansa, ubangijin talika ya amsa.

Ku taho muje mu sha bishiyar hashimawa karkashin inuwar sarkin muminai Ali (as) mu gurfanar da gwiwowinmu gaban girma da tsarkakarsa, mu nemi tallafi da taimako daga gare shi domin ya ceto wajen Allah matsarkaki (ya mai alfarma wajen Allah kasa ma mana ceto wajen Allah)

Bahasimu da maganarmu za ta kasance kan hakika siradi mikakke lallai yadda ala'amarin yake shi ne wilayar sarkin muminai Ali (as)[1] Nayi bayani filla-filla dalla-dalla kan wannan maudu'I cikin littafi mai suna (Fatima zaharafi lailatil kadari) an buga shi sannan yana cikin mausu'ar (risalatyl islamiyya) mujalladi na shida