Siradi mikakke:

 

Lallai shi mumini da musulmi yana cikin kowacce sallah da yake yi darensa da yininsa, cikin karatun fatiharsa da kur'aninsa, yana rokon Allah matsarkaki yana kuma nema daga gre shi da ya shiryar da shi zuwa siradi mikakke, wancan siradi da Allah ya yi ni'ima da shi da ni'imarsa ta jin kai kebantatta kan mutanensa  wadanda bai fushi dasu ba kamar yahudawa, kuma bai batar dasu ba kamar nasarawa           

 (اهْدِنَا الصِّرَاطَ المُسْتَقِيمَ * صِرَاطَ الَّذِينَ أنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ المَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلا الضَّالِّينَ ).

Ka shiryar damu siradi mikakke, siradin wadanda kai ni'ima kansu ba wanda kai fushi kansu ba*ba kuma batattu ba.[1]

 

Hakika Allah matsarkaki yam ambaci su wanene wadanda ya ni'ince su da ni'imarsa a kebe cikin fadinsa madaukaki:

 

 (وَلَهَدَيْنَاهُمْ صِرَاطآ مُسْتَقِيمآ * وَمَنْ يُطِعِ اللهَ وَالرَّسُولَ فَاُوْلَئِکَ مَعَ الَّذِينَ أنْعَمَ اللهُ عَلَيْهِمْ مِنَ النَّبِيِّينَ وَالصِّدِّيقِينَ وَالشُّهَدَاءِ وَالصَّالِحِينَ وَحَسُنَ اُوْلَئِکَ رَفِيقآ * ذَلِکَ الفَضْلُ مِنَ اللهِ وَكَفَى بِاللهِ عَلِيمآ) 

Lallai zamu shirayar da su siradi mikakke* duk wanda ya bi Allah da manzon Allah wadancananka suna tare da wadanda Allah ya ni'imta su daga annabawa da siddikai da shahidai da salihai, wadannan sun kyautata abokan tafiya* wancan falala ce daga Allah ya isar Allah kasantuwa masani.[2]

 

Sannan shi wannan siradi kadai yana misaltuwa yana jikkantuwa da al'amuran da zasu zo kamar haka:

Na farko: bautawa Allah azza wa jalla hakikanin bauta, wannan bauta wacce take daga falsafar rayuwa da sirrin halitta

 

 (وَأنِ آعْبُدُونِي هَذَا صِرَاطٌ مُسْتَقِيمٌ ) .

Ku bauta mini wannan hanya tace mikakke[3]

Na biyu: addninn muslunci wanda ke kan shiriya kamar yadda ya zo cikin fadinsa madaukaki:

 (إنَّنِي هَدَانِي رَبِّي إلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ دِينآ قِيَمآ مِلَّةَ إبْرَاهِيمَ حَنِيفآ).

Lallai ni ubangijina ya shiryar dani zuwa siradi mikakke addini kimantawa akidar Ibrahim mai karkata zuwa ga shiriya.[4]

(وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الإسْلامِ دِينآ فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ ) .

Duk wanda ya nemi addini koma bayan muslunci ba za a taba karba daga shi ne ba.[5]

Na uku:biyayye ga annabi(as) kamar yadda ya zo cikin fadinsa madaukaki:

 (وَأنَّ هَذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيمآ فَاتَّبِعُوهُ ).

Lallai wannan shi ne tafarjina mikakke ku bishi.[6]

 

Na hudu: riko da Allah:

(وَمَنْ يَعْتَصِمْ بِاللهِ فَقَدْ هُدِيَ إلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ ) .

Duk wanda ya nemi kariya da Allah hakika ya shiriya zuwa hanya mikakka.[7]

 

Na biyar: hukunci da adalci da dukkananin abin da ke bayyanar da adalci:

(هَلْ يَسْتَوِي هُوَ وَمَنْ يَأمُرُ بِالعَدْلِ وَهُوَ عَلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ ) .

Shin shi zai daidaita da wanda yake umarni da adalci alhalin yana kan hanya mikakka.[8]

 

Na shida- imani:

(وَإنَّ اللهَ لَهَادِ الَّذِينَ آمَنُوا إلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ ) .

Lallai Allah yana shiriyar da wadanda sukai imani zuwa hanya mikakka.[9]

 

Na bakwai: daddadan zance:

 (وَهُدُوا إلَى الطَّيِّبِ مِنَ القَوْلِ وَهُدُوا إلَى صِرَاطِ الحَمِيدِ)[10] .

Kuma ana shiryar dasu zuwa daddada daga magana kuma an shiriyar dasu zuwa hanya abar godewa.[11]

 

Sannan shi magana ita ce ake kira da kalami ammafa tare da aiki kamar yadda ya zo cikin fadinsa:

 (قولوا لا إله إلّا الله تفلحوا).

Kuce babu abin bautawa daga sai Allah zaku rabauta.

Na takwas-tafiya da daidaito da tsakatsaki cikin rayuwa:

 (أفَمَنْ يَمْشِي مُكِـبّآ عَلَى وَجْهِهِ أهْدَى أمَّنْ يَمْشِي سَوِيّآ عَلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ )[12] .

Shin yanzu wanda ke tafiya yana kife kan fuskarsa shi yafi shiriya ko kuma wanda yake tafiya kan hanya madaidaiciya.[13]

Abin da ya tattaro dukkanin wadannan mabayyanu da misalsalai da masadik shie imamanci da wilaya wacce ke tabbatuwa bayan cikamakin annabawa manzon Allah Muhammad (s.a.w) cikin sarkin muminai Ali (as) da `ya`yansa ma'asumai imamai tsarkaka… halifofi goma sha biyu ne dukkaninsu kuma daga kuraishawa suke kamar yadda ya zo cikin sahihan littafan Ahlus-sunna- sune Ali da goma sha daya daga `ya`yansa ma'asumai sune suke kan siradi hanya mikakka.

Bai buya ba lallai siradi cikin fahimtar muslunci sune siradi biyu: siradi cikin gidan duniya da siradi a lahira, sannan dayansu na hikaya da bada labarin dayan, tsakaninsu akwai lazimta cikin

 

عن المفضّل بن عمر قال : سألت أبا عبد الله  7 عن الصراط ؟ فقال : هو الطريق إلى معرفة الله عزّ وجلّ ، وهما صراطان : صراط في الدنيا وصراط في الآخرة ، فأمّا الصراط الذي في الدنيا فهو الإمام المفروض الطاعة ، من عرفه في الدنيا واقتدى بهداه مرّ على الصراط الذي هو جسر جهنّم في الآخرة ، ومن لم يعرفه في الدنيا زلّت قدمه عن الصراط في الآخرة ، فتردّ في نار جهنّم.

Daga Mufaddal bn Umar ya ce: na tambayi Abu Abdullah (as) gameda siradi? Sai ya ce: shi hanya ce zuwa ga sanin Allah azza wa jalla, su kuma siradi biyu: siradi cikin duniya da siradi cikin lahira, amma siradin wanda yake cikin duniya shi ne imami wanda da'arsa take farilla kan kowa da kowa, duk wanda ya san shi a duniya ya shiriya da shiriyarsa zai wuce kan siradi wanda shi gada ce da take shimfida kan jahannama a lahira, duk kuma wanda bai san shi ba a duniya to kafarsa zata zame daga kan siradin lahira ya fada jahannama ya halaka.

Amma magana a anan shi ne wane imamin da da'arsa take farilla kan kowa? Wannan wani abu ne da dalilai masu huda da hujjoji daga hankali da nassoshi daga ayoyin kur'ani da madaukakan hadisai zasu yi mana kain bayani kai, kamar yadda yake an ambace filla-filla a mahallinsa cikin ilimin akida da kalam sai ka koma can-.

Imam Aliyu zainul Abidin bn Husani (as) ya yi bayanin wane ne ke gasgata cikakken misdakin siradi mikakke cikin fadinsa (as):

«ليس بين الله وحجّته ستر، نحن أبواب الله ونحن الصراط المستقيم ، ونحن عيبة علمه ، ونحن تراجمة وحيه ، وأركان توحيده ، وموضع سرّه »[14] .

Babbu wani labule tsakanin Allah da hujjarsa, mune kofofin Allah mune siradi mikakke, mune tsakar iliminsa, mune tarjamomin wahayinsa, mune rukunan tauhidinsa, mune wurin sirrinsa.

وعن أبي حمزة الثمالي عن أبي عبد الله  7 قال : سألت عن قول الله عزّ وجلّ : (قَالَ هَذَا صِرَاطٌ عَلَيَّ مُسْتَقِيمٌ )[15] ، قال : والله عليّ  7 هو والله

الميزان والصراط المستقيم[16] .

An karbo daga Abu hamzatu sumali daga Abu Abdullah (as) ya ce: na tambaye shi gameda fadin Allah (wannan hanya tace mikakka) sai ya ce: wallahi Ali ne shi ne mizani da hanya mikakka.

قال الطبرسي في تفسيره : قرأ القرّاء السبعة (صراط ) منوّنآ مرفوعآ، وعليّ

 

بفتح اللام ، وقرأ يعقوب وأبو رجاء وابن سيرين وقتادة ومجاهد وابن ميمون (عليّ) بكسر اللام وصفآ للصراط  .

Dabarisi cikin tafsirinsa ya ce: ma'abota kira'o'i bakwai sun karanta ayar (siradun) da tanwinin wasalin rufu'a. sannan kalmar (alayya) kuma da yiwa harafin lamun fataha, sannan Yakubu da Abu raja da ibn Sirina da Katada da Mujahid da ibn Maimun kuma sun karanta (aliyyi) da wasalin kasara don siffanta siradi

Allama majalisi ya ce: zahiri lallai (aliyyi) da wasali kasa da izafa zuwa kalma siradi al'amarin yake, sannan abin da Katada ya rawaito daga Hasanul basari yana karfafa hakan ya ce: ya kasance yana karanta harafin dab wasalin kasara   

 

 (هذا صراط عليٍّ مستقيم ).

وعن أبي عبد الله الإمام الصادق  7 في حديث ، قال : قال أمير المؤمنين  7: إنّ الله تبارک وتعالى لو شاء لعرّف العباد نفسه ، ولكن جعلنا أبوابه وصراطه وسبيله والوجه الذي يؤتى منه ، فمن عدل عن ولايتنا، أو فضّل علينا غيرنا، فإنّهم عن الصراط لناكبون.

An karbp daga Abu Abdullah imam Sadik (as) cikin hadisi, sarkin muminai (as) ya ce: lallai Allah matsarakaki madaukaki da ya so da ya bayyanawa bayi kansa, sai dai cewa ya sanya mu matsayin kofofinsa tafarkinsa fuskar da ake zuwar masa daga gare ta, duk wanda ya kauce daga wilayarmu, ka kuma ya fifita waninmu, to (lallai su sun kauce daga tafarki)[17]

 

ishara zuwa ga fadin Allah madaukaki: 

 (وَإنَّکَ لَـتَدْعُوهُمْ إلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ * وَإنَّ الَّذِينَ لا يُؤْمِنُونَ بِالآخِرَةِ عَنِ الصِّرَاطِ لَـنَاكِبُونَ ).

Lallai kai kana kira zuwa ga tafarki madaidaici*wadanda basa yin imani da lahira sun kauce daga tafarki.[18]

 

Sannan duk wanda ya kauce daga tafarki lallai shi yana cikin jahannama tir makoma ta munana.

عن أبي بصير، عن أبي عبد الله  7، قال : الصراط الذي قال إبليس (لأقْعُدَنَّ لَهُمْ صِرَاطَکَ المُسْتَقِيمَ ) ، فهو عليّ  7

Daga Abu basir an karbo daga Abu Abdullah (as) ya ce: shi ne tafarki da iblis yake cewa kansa (lallai zan zaune musu tafarkinka madaidaici) wannan tafarki shi ne Ali (as)[19]

Iblsi ya ranste da buwayar Allah sai ya karkatar da mutane ya kuma halakar dasu baki dayansu face `yan tsiraru daga bayin Allah masu godiya. Wadannan da suka tsarkake niyya don Allah cikin sirrinsu da bayyanarsu.
wannan kenan hakika shaidan ya yi galaba kan mutane sai mutane sukai ridda bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) suka juyawa wilayar Ali (as) da halifancinsa da gaskiya ba face wasu `yan tsiraru daga cikin wadanda suka cika alkawari don kiyaye gaskiya da ma'abotanta, ranar kiyama da sannu annabi (s.a.w) zai magana da su a tafkinsa kamar yadda ya cikin littafin sahihul bukhari yana fadin: (sahabbaina ne sahabbaina ne) sai magana ta zo daga tushen girma (Allah) da cewa: nesa-nesa ma'ana zuwa jahannama, kai baka san wacce bidi'a suka kaga ba a bayanka ya manzon Allah (s.a.w), sannan wacce bidi'a ce da ta fi girma daga kwace halifancin gaskiya?! babu abin da ya rage daga cikin su face kamar dan guntun abincin da ya rage a gefan bakin rakumi ko saniya ma'ana dai sai `yan tsiraru.

 

وقد قال رسول الله  9 في ولاية عليّ  7 وفي حقّه : «فوعزّة ربّي وجلاله إنّه لباب الله الذي لا يؤتى إلّا منه ، وإنّه الصراط المستقيم ، وإنّه الذي يسأل عن ولايته يوم القيامة » .

Hakika manzon Allah (s.a.w) cikin wilayar Ali (as) da hakkinsa ya ce: na ranste da buwayar ubangijina da girmamarsa lallai shi kofar Allah ne da ba a zuwa wurin Allah sai an shigo daga gare ta, lallai shi tafarki ne madaidaici, lallai shi ne wanda Allah zai tambaya gameda wilayarsa ranar kiyama. 

وقال  9: أتاني جبرئيل  7 فقال : اُبشّرک يا محمّد بما تجوز على الصراط ؟ قال : قلت : بلى . قال : تجوز بنور الله، ويجوز عليّ بنورک ، ونورک من نور الله، وتجوز اُمّتک بنور عليّ، ونور عليّ من نورک (وَمَنْ لَمْ يَجْعَلْ اللهُ لَهُ نُورآ فَمَا لَهُ مِنْ نُورٍ)[20] .

Tsira da amincin Allah ya tabbata gare shi da iyalansa ya ce: Jibrilu ya zo mini sai ya ce: shi inyi maka bushara ya Muhammad da abin da zaka ketare siradi da shi? Sai ya ce: eh, ya ce zaka ketare da hasken Allah, Ali kuma zai ketare da haskenka, sannan shi haskenka daga hasken Allah yake, sannan al'ummarka zata ketare da hasken Ali, sannan shi hasken Ali daga haskenka yake (dukkanin wanda Allah bai sanya masa haske ba to bai da haske)
وقال  9: إذا كان يوم القيامة ونصب الصراط على جهنّم لم يجز عليه إلّا

من كان معه جواز فيه ولاية عليّ بن أبي طالب  7، وذلک قوله تعالى  : (وَقِفُوهُمْ إنَّهُمْ مَسْؤُولُونَ )[21] ، يعني عن ولاية عليّ بن أبي طالب  7[22] .

Ya ce (as) idan kiyama ta tsaya aka kafa siradi kan jahannama  babu mai ketarewa face wanda yake takardar izinin ketarewa wacce cikin ta akwai wilayar Ali bn Abu dalib (as) wancan fadin Allah madaukaki: (ku tsayar da su lallai su ababen tambaya ne) ma'ana kan wilayar Ali bn Abu dalib (as)

 

وقال  9: إذا جمع الله الأوّلين والآخرين يوم القيامة ونصب الصراط على جسر جهنّم ، لم يجز بها أحد إلّا من كانت معه براءة بولاية عليّ بن أبي طالب  7[23] .

A wata riwayar (as) ya ce: idan Allah ya tattara na farko da wanda suka zo a karshe ranar kiyama aka shimfida siradi kan gadar jahannama babu mai tsallaketa face wanda yake tare da bara'a da wilayar Ali bn Abu dalib (as)

وفي حديث وكيع قال أبو سعيد: يا رسول الله، ما معنى براءة عليّ  7؟ قال : لا إله إلّا الله، محمّد رسول الله، عليّ وليّ الله[24] .

Ya zo cikin hadisin waki'u Abu Sa'id ya ce: ya manzon Allah menene ma'anar bara'ar Ali (as) ya ce: babu abin bauta sai Allah Muhammad manzon Allah ne Ali kuma waliyin Allah

وقال  9 في حديث طويل : وإنّ ربّي عزّ وجلّ أقسم بعزّته أنّه لا يجوز عقبة الصراط إلّا من معه براءة بولايتک وولاية الأئمّة من ولدک .

Cikin wani dogon hadisi amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya ce: lallai ubangijina azza wa jalla ya rantse da buwayarsa lallai cewa babu mai ketare siradi face wanda yake tare da bara'a da wilayarka da wilayar A'imma daga `ya`yanka.

وعنه  9: إذا كان يوم القيامة يقعد عليّ بن أبي طالب على الفردوس ـوهو جبل قد علا على الجنّة فوقه عرش ربّ العالمين ، ومن صفحه تتفجّر أنهار الجنّة وتتفرّق في الجنان ـ وهو جالس على كرسي من نور يجري بين يديه التسنيم ، لا يجوز أحد الصراط إلّا ومعه براءة بولايته وولاية أهل بيته ، يشرف على الجنّة فيدخل محبّيه الجنّة ومبغضيه النار[25] .

Daga shi ne (as): idan kiyama ta tsaya Ali bn Abu dali zai zauna kan Firdausi wanda shi wani dutse da ya daukaka kan aljanna samansa kuma al'arshin ubangijin talikai, daga saman dutsen koramun aljanna ke tsagewa su yaryadu cikin aljannoni-shi Ali yana zaune kan kujera daga haske tasnim na gudana a gabansa, babu wani mutum da zai ketare siradi face tare da shi akwai bara'a da wilayar Ali da wilayar Ahlin gidansa, zai je bakin aljanna zai dinga shigar da masoyansa, ya kuma zuba makiyansa a wuta. 

عن أبي عبد الله  7: «ربّنا آمنّا واتّبعنا مولانا ووليّنا وهادينا وداعينا

وداعي الأنام وصراط المستقيم السويّ، وحجّتک وسبيلک الداعي إليک على بصيرة هو ومن اتّبعه ، سبحان الله عمّا يشركون بولايته ، وبما يلحدون باتّخاذ الولائج دونه ، فاشهد يا إلهي أنّه الإمام الهادي المرشد الرشيد عليّ أمير المؤمنين الذي ذكرته في كتابک وقلت : (وَإنَّهُ فِي اُمِّ الكِتَابِ لَدَيْنَا لَعَلِيٌّ حَكِيمٌ )

لا اُشركه إمامآ، ولا أتّخذ من دونه وليجة ».

An karbo daga Abu Abdullah (as): (ya ubangijinmu munyi imani mun bi shugabanmu mai shiriyar damu mai kiranmu mai kiran al'umma tafarki madaidaici, hujjarka tafarkinka mai kira zuwa gare ka a kan basira da wadanda suka bi shi, tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke tarayya daga abin da suke karkacewa daga fakewa da wasu mafakoki koma bayansa, ya Allah ka shaida lallai shi imamin shiriya mai shiryarwa Ali bn Abu dalib wand aka ambace shi cikin littafinka (lallai shi uwar littafi madaukaki ne mai hikima) bana masa tarayya da wani, bana kuma rikar wani mafaka koma bayansa.[26]

 

Gaskiyar siradi da hakikarsa da sirrinsa yana kasancewa cikin sarkin muminai Ali da `ya`yansa ma'asumai goma sha daya, bai buya ba lallai cewa wilayar Ahli-baiti (as) na nufin wilayar manzon Allah (s.a.w) wilayar annabi wacce ake kira da sunan hakika muhammadiya ita ce wilayar Allah mafi girmama wacce ta tattaro sunayen Allah da siffofinsa cikin tafiyar da halitta da sha'aninsu.

da wannan wilayar da zuhurinta da tajallint ababen halitta kasantattu suke kaiwa ga kamalolinsu, kamar yadda mutum yake da ita yake cimma farin cikin duniya dana lahira

«سعد من والاكم ، وشقى وهلک من عاداكم ».

Duk wanda ya jibanceku ya azurta, duk wanda ya kiku ya tsiyata ya halaka

قال الإمام الصادق  7: الصراط المستقيم أمير المؤمنين علىّ  7.

Imam sadik (as) ya ce: hanya mikakka shi ne sarkin muminai Ali (as)

وقال أمير المؤمنين  7: أنا الصراط الممدود بين الجنّة والنار، وأنا الميزان .

Sarkin muminai (as) ya ce: ni ne siradi wanda aka mikar tsakanin aljanna da wuta, ni ne mizani.

Amincin Allah da manzonsa da halittu baki dayansu ya tabbata

Kan hanya mikakka da mizani daidaitacce shugabanmu sarkin muminai shugaban wasiyyai zakin Allah mai galaba imam Ali bn Abu dalib (as) da `ya`yansa ma'asumai masu shiryarwa zuwa ga hanyar Allah, dukkanin mai kyamatarsu ya fita daga shiriya, dukkanin mai lazimtarsu zai riski shiriya, mai takaitawa cikin hakkinsu ya gushe, gaskiya tana tare da su daga su take sune ma'adaninta.[27]

Sune tafarki mafi daidaito, duk mai son Allah mai nufinsa da su zai fara dukkanin wanda ya dayanta Allah zai karba daga gare su

Sannnan dole ne a daidaita sahu cikin wannan hanya mikakka ba tare da karkata ba da karkacewa ba tare da takaitawa ba da wuce gona da iri, ma'ana ba tare da gullanci da takaitawa.

Siradin Ali tafarkinsa shi ne tafarkin Allah lallai annabi (as) yana shiryar da mutane zuwa tafarkinsa:

(وَإنَّکَ لَـتَهْدِي إلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ * صِرَاطِ اللهِ الَّذِي لَهُ مَا فِي السَّمَوَاتِ وَمَا فِي الأرْضِ )[28] .

Lallai kai tabbas kana shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici*tafarkin Allah wanda shi ne dukkanin abin da yake sammai da kasa gare shi yake.[29]

Wannan shi ne tafarki wanda Allah ya umarcemu da binsa cikin fadinsa:

 (وَبِعَهْدِ اللهِ أوْفُوا ذَلِكُمْ وَصَّاكُمْ بِهِ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ * وَأنَّ هَذَا صِرَاطِي مُسْتَقِيمآ فَاتَّبِعُوهُ وَلا تَتَّبِعُوا السُّبُلَ فَتَفَرَّقَ بِكُمْ عَنْ سَبِيلِهِ ).

Ku cika alkawarin Allah wadancananka ya yi muku wasiyya da shi tsammaninku kwa tuna*wannan shi ne tafarkina madaidaici ku bishi kada kubi hanyoyi sai su rarrabaku da hanyarsa[30]

عن بلال بن حمامة قال : خرج علينا رسول الله  9 ذات يوم ضاحكآ مستبشرآ فقام إليه عبد الرحمن بن عوف فقال : ما أضحكک يا رسول الله  9؟ قال : بشارة أتتني من عند ربّي ، إنّ الله لمّا أراد أن يزوّج عليّآ فاطمة أمر ملكآ أن

يهزّ شجرة طوبى فهزّها فنشرت رقاقآ (أي صكاكآ) وأنشأ الله ملائكة التقطوها فإذا كانت القيامة ثارت الملائكة في الخلق فلا يرون محبّآ لنا أهل البيت محضآ إلّا دفعوا إليه منها كتابآ: براءة له من النار من أخي وابن عمّي وابنتي فكاک رقاب رجال ونساء من اُمّتي من النار  .

daga Bilal bn hammamatu ya ce: wata rana manzon Allah (s.a.w) ya fito wajenmu yana dariya yana bushara sai Abdur-rahm bn Auf ya mike tsaye gare shi ya ce: me ya saka dariya ya manzon Allah (s.a.w)? sai ya ce: wata bushara ce ta zo mini daga ubangijina, lallai Allah yayin da ya nufi aurar da Fadima ga Ali ya umarci mala'ika da ya girgiza sai ta zubar da takardu (ma'ana takardar karbar kyauta ku kudi) sai Allah ya aika Mala'iku suka tsince wadannan ganye idan kiyama ta tsaya Mala'iku zasu zaga cikin mutane ba zasu ga wani masoyinmu tsantsa ba face sun bashi takarda daga wadannan takardu bara'a shi ne daga wuta daga dan'uwana da `yata mai `yantar da wuyayen maza da mata daga.

Gamu cikin liyafar Allah cikin watan Ramadan wata mai alabarka ubangijinmu mai karamci abin bautarmu mai rahama da mai girma ya kiramu zuwa ga teburin walimar littafin mai girma da sunayensa kyawawa sa siffofinsa madaukaka, a kan walimar da darbar addu'o'i da Azkaru da ama addu'a da yafe zunubai, bai buya ba lallai cewa tsolloluwar liyafar watan Ramadan da mafi alfarmarta na cikin dararen lailatul kadari mai albarka, lallai Allah ya mikar da shimfidar walimar rahamarsa mai yalwa, yana kaddara dukkanin wani al'amari mai hikima yana tafiyar da al'amuran kasantattu da hisabi da hukuntawa da hikima, yana rubuta shi cikin daren goma sha tara daga watan Ramadan mai albarka, yana yanke shi da tabbatar da shi cikin daren ashirn da daya, sanna ya cika shi da hattama shi cikin lauhul mahfuz cikin daren ashirin da uku, sannan yana tsinkayar da waliyinsa sahibuz zaman imamul muntazar (as) yana sassaukar da Mala'iku da ruhu kansa daga dukkanin wani al'amari, shi daren lailatul kadari aminci ne har lokacin hudowar alfijir

 [1] Fatiha:6-7

[2] Nisa'i: 69-70

[3] Alu imrana:51

[4] An'am:161

[5] Alu imrana:85

[6] An'am:153

[7] Alu imrana:101

[8] Annahlu:76

[9] Hajji:54

[10] ()  البحار :8 66.

[11] Hajji:24

[12] ()  البحار :8 70.

[13] Muluk:22

[14] ()  تفسير البرهان :2 344.

[15] ()  جامع البيان :14 24.

[16] ()  البحار :24 23.

[17] Muminun:74

[18] Muminun:74

[19] Shawahidul tanzil: m 1 sh 61

[20] ()  البحار :8 69.

[21] ()  فرائد السمطين :1 298.

[22] ()  مناقب آل أبي طالب :2 156.

[23] ()  فرائد السمطين :1 292.

[24] ()  الزخرف : 4.

[25] ()  البحار :24 23.

[26] Sai ka nemi littafin (ihkakul hakku wa ta'alikuhu):m 7 sh 114-125   gameda Ali hanyamikakka

 

[28] ()  تاريخ بغداد :4 210.

[29] Shura:53

[30] An'am:152-153