MUHADARA TA HUDU

 

 Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah makagin sammai da kasa, tsira da amincin su kara tabbata ga mafi daukakar halittunsa Muhammad da iyalansa.

Bayan haka:

Hakika Allah madaukakin sarki cikin littafinsa mai daraja ya ce:

 

(اللهُ نُورُ السَّمَوَاتِ وَالأرْضِ مَثَلُ نُورِهِ كَمِشْكَاةٍ فِيهَا مِصْبَاحٌ المِصْبَاحُ فِي زُجَاجَةٍ الزُّجَاجَةُ كَأنَّهَا كَوْكَبٌ دُرِّيٌّ يُوقَدُ مِنْ شَجَرَةٍ مُبَارَكَةٍ زَيْتُونَةٍ لا شَرْقِيَّةٍ وَلا غَرْبِيَّةٍ يَكَادُ زَيْتُهَا يُضِيءُ وَلَوْ لَمْ تَمْسَسْهُ نَارٌ نُورٌ عَلَى نُورٍ يَهْدِي اللهُ لِنُورِهِ مَنْ يَشَاءُ وَيَضْرِبُ اللهُ الأمْثَالَ لِلنَّاسِ وَاللهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ ).

Allah hasken sammai da kasa misalin haskensa kamar taga ce cikin ta akwai wata fitila fitila cikin wata kwalaba kwalaba kai kace ita tauraro ce mai tsananin haske ana kunna shi daga bishiya mai albarka zaituna ba bagabashiya bace ba kuma bayammaciya bace manta ya kusa haskuwa koma da wuta bata shafe shi ba Allah yana bugawa mutane misali Allah masanin komai ne.[1]

 

عن أبي جعفر الباقر  7: المشكاة فاطمة .

Daga Abu Jafar (as) abin da ake nufi da mishkatu shi ne fadima.

Bai buya ba lallai cwa masdarn shari'ar muslunci da tushen ilimanmu da saninmu da sakafarmu ta shi'a kadai shi ne kur'ani mai daraja da madaukaka hadisai da suka gangaro daga ma'adanan ilimi da wahayi, ma'ana daga manzon Allah (s.a.w) da tsatsonsa tsarkaka Ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata gare su, idan muka sanin mukaman kur'ani mai daraja da matsayin Ahlil-baiti limaman gaskiya, mu tsinkaya kan girmansu da daukakarsu, kadai dai hakan na tabbatuwa lokacin da muka koma zuwa masdara da tushen iliminmu da sakafarmu, ma'ana zuwa ga kur'ani mai girma (littafin Allah)  da sunnar manzon Allah da tsatso tsarkaka.

Lokacin dsa muke bincika ayari cikin ayoyin kur'ani mai girma don ya bamu labari gameda girmamar shugabar matan duniya Fadima Zahara (as) zamu ga Allah matsarkaki yana bayaninta da mafi kyawun jumla da mafi dandakar mafhumi da mafi zurfafar ma'ana, ta yadda yake bayaninta cikin suratun nuru cikin aya da cewa ita mishkat wacce cikin hakikarta ta tattaro haskaye annabta da wilaya.

Sannan mishkat a luggance ma'anarta shi ne wani dan karamin rami d ayake jikn bango bawai taga ba.[2]sannan dukkanin abin da ake ajiyewa cikin sa ko kuma kansa fitila[3] daga cikin sa shi ne akwai wani dan karamin rami da ake sanyata tsakanin ban dakin wanka da dakin da ake sauya kaya ko kwabe su, a tsofaffin gidajen wanka na zamani da ya shude ana sanya fitila da fitilar kwai cikin wannan kwaba domin bandakin wanka ya haskakau daga gefe da gefe guda kuma dakin sauya kaya shima ya haskakau ya yi haske, shi wannan dan karamin ramin shi ne mishkatu shi kuma ba taga bane.


[1] Nuru:35

[2] Na kawo bayani filla-filla cikin littafin imam Husaini fil arshillahi a cikin shafi na dari uku cikin mausu'atu risalatul islamiyya a cikin mujalladi na shida an buga shi

[3]  Munyi bahasi filla-filla kan halittar A'imma ta haske cikin littafi mai suna (anwarul kadasiyya)