FADIMA ZAHARA (AS) ABAR KOYI DA KWAIKWAYO

 

 

Daga cikin batutuwa da ake bincike kansu cikin ilimin sanin halayya dan adam na zamani, kamar yadda lallai batun yana da muhimmancin gaske cikin sakafar muslunci da kamus din muslunci shi ne mas'alar (abin koyi da kwaikwayo) lallai mutum tun fara tsirowar farcensa daga halittarsa da dabi'arsa lalla ishi yana bincike da neman abin koyi da kwaikwayo da zai koyi da shi cikin zantukansa da ayyukansa, ma'ana daga dabi'arsa ta fari daga zatinsa na halittarsa lallai shi mutum yana kamantuwa da wani mutumin daban bayan karkatarsa ta zuciya zuwa gare shi, lallai shi idan ya so shi to zai ta'allaku da shi ya kuma dabi'antu da dabi'arsa, lallai kufaifayin masoyinsa wanda ya rike abin koyi cikin rayuwarsa zasu bayyana cikin sulukinsa da kaikawonsa da rashin motsinsa.

Yaro karami cikin kwanakin yarintarsa sannan cikin shekarun matasantakarsa da samartakarsa yana koyi da kwaikwayon wanda yake ganinsa matsayin abin kwaikway, sai ya dinga tasirantuwa da dabi'unsa da Akhlak dinsa da sulukinsa, lallai daga cikin larurar rayuwa shi ne akwai (abin koyi da kwaikwayo) sai dai cewa wane ne abin koyin da kwaikwayon? da wa za kwaikwayantu? wane ne jagora?

Malaman sanin halayyar dan adam sun tafi kan cewa mutum mace da namiji suna koyi da farko da mahaifiyarsu wanda hakan shi ne gaskiya al'amari, lallain ita uwa tana taka babbar rawa cikin rayuwar mutum ta fuskanin koyi da kwaikwayo, sannan kuma yana koyi da mahaifinsa da `ya'uwansa maza da mata ma'ana dai da wadanda yana koyo da kwaikwayon wadanda suke rayuwa tare da juna cikin da'irar iyali da zawiyyar dangi, sai kuma daga baya daurar abokai ta tsallako, har asan mutum da abokanansa, ya karanta ka yi abota a bukaci tambayar wane ne kai? Idan igiyar da alakar abokantaka da soyayyar juna ta kullu tsakanin mutum biyu, lallai aboki yana bin hanyar da abokinsa yake bi, sannan misdaki a biyu ga koyi da kwaikwayo shi ne malami mai koyarwa da mai tarbiyya, hatta wasu ba'ari wurare dalibi kan tasirantuwa da ustazunsa, sai a san shi karkashin motsinsa lallai shi daga daliban malam wane yake, wannan shi ne abin da ke faruwa cikin hauza ilimiyya cikin mafi yawan lokuta, hakama cikin jami'o'i ilimin zamani, sannan wani misdakin daban kwaikwayon matshi yakan misaltuwa da bayyana cikin wasu masu wasannin motsa jiki kamar dan kwallon kafa, da kuma wanda ke kira mawaka da jaruman fina-finai sinima, wannan ne abin da ke yawan faruwa da `ya`yanmu mata, sai kuma tasirantuwa da `yan siyasa ga wanda ya kasance yana karkata ga harkokin siyasa. Wadannan sune adadin wadanda ake kwaikwayo da koyi da su cikin rayuwarmu ta yau da gobe cikin dukkanin duniya ta fuskanin gamewa, mutum na kaunar jagoransa abin kwaikwayonsa da koyinsa ya kasance ya fifita wasu kebantattun abubuwa da suke banbanta shi da sauaran mutane, wadanda suke bashi stamp din cancanta cikin kasantuwarsa abin koyi, wajibi abin koyinsa ya zama ya kamala daga waninsa hakama ya zama yafi ilimi, haka nan uwa ta kasance mai shaidar digiri na biyu to lallai yaron da ya taso hannunta zai burin samun shedar digiri na uku, hakama mutum yana kaunar ace abin koyin ya kasance cikin zabinsa, duk sanda ya nufe shi zai zama ya na kusa da shi domin neman shawararsa da koyi da shi cikin tsarin tafiyarda rayuwarsa, yana kuma san ya kasance ya tattaro kamala da kyawu, misalin wannan siffofi basu tattaruwa cikin wadanda muka ambata a baya daga misdakan ababen kwaikwayo da koyi face cikin ma'asumai daga annabawa da wasiyyai, sune mafi kamalar cikin mutane sune mafi iliminsu suna mafi tattaro siffofin kyawu da kamala, babu mai kamnceceniya da su daga mutane cikin zamninsu sune hujjojin Allah kan halittunsa, hakika Allah ya umarcemu mu rikesu ababen koyi da kwaikwayo.      

(اُولئک الذين هدى الله فبهداهم اقتده )

Sune wadancan ne Allah ya shiryar dasu ka koyi da shiriyarsu[1]

(لقد كان لكم فيهم اُسوة حسنة لمن كان يرجو الله) .

Hakika abin kwaikwayo mai kyau ya kasance gare ku cikin manzon Allah ga wanda yake fatan lahira.[2]

Mu musulmi abin kwaikwayonmu shi ne manzon Allah (s.a.w) kamar yadda Allah ya umarcemu da hakan.

(لقد كان لكم في رسول الله اُسوة حسنة )

Hakika abin kwaikwayo mai kyau ya kasance gare ku cikin manzon Allah.[3]

Sannan bayana manzon Allah mafi girma (s.a.w) ababen kwaikwayonmu da koyinmu sue wadanda ya halifantar da su kanmu, ina nufin littafin Allah da tsatson manzon Allah (s.a.w) saklaini nauyaya biyu, kamar yadda ya zo cikin hadisin saklaini mutawatiri wurin bangarori biyu–sunna da shi'a lallai manzon Allah manzon rahama da muslunci (s.a.w) bai bar mutane kara zube ba a bayansa, bari dai sai da ya halifantar musu da nauyaya biyu cikin su littafin Allah da tsatso manzon Allah (s.a.w) wadanda matukar mukai riko dasu baza mu taba bata bayansa ba, lallai su biyun ba zasu taba rabuwa da juna ba har sai sun gangaro tafkina.

Sannan munyi imani da rayuwar kur'ani mai girma:

 (يا أيّها الذين آمنوا استجيبوا لله وللرسول إذا دعاكم لما يحييكم ) .

Yaku wadanda sukai imani ku amsawa Allah da manzon Allah idan suka kira ku zuwa ga abin da yake rayaku.[4]

Kamar yadda mukai imani da rayuwar A'imma da mahaifiyarsu Fadima Zahara, lallai su rayayyu ne suna azurtuwa wajen ubangijinsu, suna masu shaida kan halittu haka kan wannan al'umma suna ganin ayyukan mutane.

Sannan kamar yadda manzon Allah (s.a.w) da sarkin muminai (as) suke iyayen wannnan al'umma kamar yadda manzon Allah (s.a.w) ya fada

 (أنا وعليّ أبوا هذه الاُمّة )،

ni da Ali mune iyayen wannan al'ummar.

Lallai Fadima Zahara ma haka ita ma mahaifiyarsu ce, kamar yadda uwa ga mahaifinta ita bar koyi ce da kwaikwayo kamar babanta da mijinta, dukkaninsu haske ne kwaya daya cikin hanyar shiriya cikin mukamin koyi da kwaikwayo.

Lallai Fadima shugabar matan duniya amincin Allah ya kara tabbata gare ta har abada itace uwa ga muminai maza da muminai mata bisa tsawon tarihin bil adama, itace mahaifiyar A'imma zababbu kamar yadda take uwa ga shi'arsu maur karamci, uwa gare su abar koyi cikin duniyar ma'ana da samuwa da turbaya.

Lallai Fadima Zahara (as) abar koyi ce da kwaikwayo sai dai cewa me son koyi da ita kan tsinkayar wani abu lokacin da yake karanta tarihinta da mudala'ar rayuwarta, sai mutum ya kamantu ko mace ta kamantu da ita, sai dai cewa ta yiwu a wannan zamanin da muke ciki ya zama ya wahalantu kamar yadda hakan yake faruwa sakamakon dabbakuwar fasahar kimiyya da kere kere da abin da ke cikin sa na cigaban teknolaji kan zamanint, sai mutum ya rayu cikin halin kishiyanta ko kadaita ko dayantuwa, wani lokacin kuma yana koyi da ita cikin hadisanta masu daraja da madaukakan kalamanta, sai dai cewa wani ishkalin da ya gabata na kara zuwa, daga ckin maganganunta mafi alherin matayen duniya

 

 «خير النساء أن لا ترى الرجال ولا يراها الرجال »،

Mafi alherin mata kada ta ga maza sannan kada maza su ganta.

Yanzu ya za ai wannan ya dabbaku a wannan zamanin namu da muke ciki yanzu?!

Na'am koyi da kwaikwayonta (as) zai wanzu ta fuskanin alaka da dangantakar ruhi da samuwa da ma'anawi, lallai ita raina fansarta uwata ce cikin samuwata ta badini ta ma'anawi da ruhi, uwa da ma'anar farko da ta biyu kadai dai tana daga (uwa mai tasiri) ai mu muna zuwa gare ta mu diba daga tsarin yadda ta rayu da maganganunta, saidai cewa da ma'ana ta uku daga (uwa mai tasirantarwa ga waninta) to itace take kiyaye mu da akremu da kankin kanta da hallararta da rayuwarta, sai ta dinga bamu kariya da madadinta na gaibu da yake daga Allah matsarkaki da numfashinta tsarkakka, idan mun bamu jin haka bama riskarsa cikin rayuwarmu da muke ciki yanzu, to lallai sababin hakan shi ne cewa lallai mun zame hannuwanmu daga hannunta, sai muka bata bat muka rude muka kidume muka karkace muka fadi a mazamar kafa, kamar yadda yaro karami yake bacewa yake rudewa yake zamewa da faduwa lokacin da yake rabuwa da mahaifiyarsa, ko kuma lokacin da yke son cin gashin kai daga gare ta, idan hannuna ya kasance kan hannuna babata tana dagoni tana kula dani da karenito lallai ni ba zan taba bacewa ba cikin rayuwata ta zamani, sannan sanda kafafuna suka harde da juna na nemi hantsilawa da faduwa kasa to lallai babata zata kamo hannuna ta dagoni ta kareni daga hantsilawa da fadawa, jigo shi ne mu karfafa igiya da dangantaka da alakoki samuwa tsakaninmu da mahaifiyarmu Zahara (as) mu kasance fadimawa cikin akidarmu da sulukinmu da badini da samuwa da ruhi.

Sannan dangane nasaba zuwa ga Fadima Zahara (as) duk da kasantuwar abu mafi shahara wajen malaman fikihunmu tana kasance daga bangare uba sai dai cewa hakan bisa la'akari da hukunce-hukuncen fikihu daga kumusi da kuma haramci karbar zakka, idan ba haka ba amma ta fuskanin daukaka da uwantaka da haramci babu banbanci tsakanin zuriyar Zahara (as) maza da

Mata dukkaninsu ta bangare uba ko uwa suna danganewa da ita, in kara kan haka nasabar sababi ta bangaren surukutaka ko shayarwa a wannnan bisa la'akari da (lissafin tsammani) sananne cikin ilimin lissafi da ilimin mandik cikin bibiyar daidaiku zamu ga galibin shi'ar Iraki da iran da garuruwan da suke kewaye da su da geffansu daga cikin wadanda suka da dangantaka da danganewa zuwa ga `yar manzon Allah (s.a.w) Fadima Zahara (as) ko dai ta hanyar sababi auratayya da jininta ko kuma ta hanyar nasaba daga kakanninsu da suka gabata.

Idan Fadima Zahara (as) ta kasance gabanin karni goma sha hudu sannan ya kasane kowannne karni ana kaddara shi da shekaru talatin sai ya zama tsakaninta damu kusan karni araba'in da shida kenan, sannan idan ya kasance wadanda aka haifesu daga gare ta rabi maza rabi mata kamar yadda ya kasance da samuwar Hassanawa da Husainawa da zainawa, to lallai yadda al'amarin yake cikin tsatso na biyar yana lazimta kasantuwa sayyid babana mutum biyu ragowar kuma mutane talatin daga bangaren uwa, cikin lissafi da hisabin tsammani yana lazimta ya kasance cikin wannan zamani da lamba d ata ke kasantu daga tara 9 ma'ana da gwargwadon mazauna kasa a wannan lokaci, sai alura.

Fadima Zahara (as) zata cigaba da wanzuwa bar koyi da kwaikwayo ga dukkani bil adama musammam ma ga shi'arta masu karamci da dukkanin ma'anar koyi da kwaikwayo daga ma'anoni da misdakai, lallai ita uwa ce a ma'anance da samuwance da turbayance, lallai ita malama ce kuma mai bada tarbiya ce, itace siddika sadika musaddaka, lallai ita tauraruwar kasantuwa ce mai tsananin haske itace sirrin samuwa mabayyani.   

 


 

 [1] An'am:90

[2] Ahzab:21

[3] Ahzab:21

[4] Anfal:24