فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

DAGA WAHAYIN ZIYARAR FADIMIYYA

 

 

 

 Hakika ya tabbata da hujjoji masu huda da dalilai na yankan shakku karkashin hujjojin hankali da nakali daga ayoyi masu daraja da madaukakan hadisai da cewa lallai zababbun halittu da tacewar duniyar imkani da sirrin samuwa da digon dambar faraway cikin duniyoyin al'amari da halitta sune ma'asumai goma sha hudu: su dukkaninsu samuwa ce ta halitta da samuwa baki daya ta imkani, sune Fadima Zahara da babanta da mijinta da `ya`yanta A'imma goma sha daya daga amincin Allah ya kara tabbata gare su Abadan abidin, hakika Allah ya karrama su da daukaka da girma da mukamai wadanda hakula basu iya riskarsu, sub a a kiyasta su da wani mutum daga cikin mutane, ya isar musu girmama da kamala da daukaka da cewa lallai Allah da su ya fara halitta da su kuma zai hattama kamar yadda ya zo cikin ziyarar jami'a kubra wacce ake kirgata asasin shi'anci cikin sanin imami (as)

 (بكم بدأ الله وبكم يختم )ـ

Daku Allah ya fara da kuma ku zai hattama.

Sai ubagijinsu makaginsu ya basu karamomi da falaloli wadanda basu kidaituwa basu kirguwa, ya fifita su da wasu kebantattun darajoji wadanda bai bawa wani koma bayansu ba daga makusanta cikin duniyar kasantuwa da kuma duniyar shari'a duniya da lahira, duk sanya mukai nutso cikin zurfafar matsayinsu tsarkakka lallai mu ba zamu cimma daya cikin dari ba kamar yadda ya zo cikin hadisi mai daraja:  

: «نزّلونا عن الربوبيّة وقولوا فينا ما شئتم ولن تبلغوا وما تقولونه معشار العشر»،

Ku nesanta mu daga ubangijintaka sannan ku fadi abin da kuka ga  damu dangane damu lallai da duk abin da kuke fadi ba zaku kai daya cikin dari ba.

Lallai su madubin madaukakan siffofin Allah ne da mabayyanan kyawawan sunayensa.  

  «لا فرق بينک وبينهم إلّا أنّه عبادک فتقها ورتقها بيدک » 

Babu banbanci tsakaninka da su face cewa dai su bayinka ne tsagosu da hade su na hannunka.[1]

Daga cikin madaukakin matsayinsu shi ne cewa lallai baki dayan halittu na cikin liyafarsu, lallai yadda al'amarin yake albarkacinsu ake azurta mutane, da samuwarsu ne kasa da sama suka samu tabbatuwa. 

«بهم يمسک السماء أن تقع على الأرض »،

Da sune aka rik sama daga fadowa kasa.

 «ولولا الحجّة لساخت الأرض بأهلها».

Ba da ban samuwar hujja ba da kasa ta halakar da mutanen cikin ta.

Sannan Allah ya kebanci shi'arsu da masoyansu da liyafa data kebantu da waliyansu hakika ya zo daga gare su cikin fadin kakansu manzon Allah (s.a.w)

«لا تعادوا الأياّم فتعاديكم »،

Kada ku dinga nuna kiyayya da kwanaki sai su kiku.

Lallai kowacce rana cikin sati cikin duniya kasantarwa tana kebanta da daya daga cikin su ko da wasu ba'arinsu tunda Allah ya halicci sammai da kasa, ana ziyarta ma'asumi (as) cikin wannan rana mai ziyara masoyi ma'abicn wilayarsu sai ya kasance cikin liyafarsa cikin shingensa da kariyarsa.

Misali ranar Asabar ran ace ta kakansu manzon Allah (s.a.w) mai ziyara mumini namiji ko mace bayan Ambato siffofi annabi sai ya ce: 

«يا رسول الله، صلوات الله عليک وعلى آل بيتک الطاهرين ، هذا يوم السبت وهو يومک وأنا فيه ضيفک وجارک فأضفني وأجرني فإنّک كريم تحبّ الضيافة ومأمور بالإجارة فأضفني وأحسن ضيافتي وأجرنا وأحسن إجارتنا بمنزلة الله عندک وعند آل بيتک  : وبمنزلتهم عنده وبما استودعكم من علمه فإنّه أكرم الأكرمين ».

Ya manzon Allah amincin Allah ya kara tabbata da iyalan gidanka tsarkaka, yau ranar asabar ce ita ranarka ce ni cikin ta bakonka ne makocinka ne ka karbi bakuntata da makotaka ta, lallai mai karamci ne kuma an umaraceka da liyafa da makotaka ka liyafanceni ka kyawunta liyafata ka makotakancemu ka kyawunta makotakarmu don matsayin Allah wajenka da iyalan gidanka, don matsayinsu wajensa da abin da ya ajiye gare ku daga iliminsa lallai shi ne mafi karamcin masu karamaci.[2]

 

Ranar Lahadi rana ce da sunan sarkin muminai Aliyul murtaza da Fadima Zahara (as) mai ziyara bayan sallama da salati da ambaton siffofi daga siffofin imam sai ya ce: 

 «يا مولاي ، يا أمير المؤمنين ، هذا يوم الأحد وهو يومک وباسمک وأنا ضيفک فيه وجارک
فأضفني يا مولاي وأجرني فإنّک كريم تحبّ الضيافة ومأمور بالإجارة فافعل

ما رغبت إليک فيه ورجوته منک بمنزلتک وآل بيتک عند الله ومنزلته عندكم وبحقّ ابن عمّک رسول الله صلّى عليه وآله أجمعين ».

Ya shugana ya sarkin muminai wannan rana ranar lahadi ce da sunanka sannan ni cikin ta bakonka ne makocinkane, kai mini liyafa ya shugabana ka bani mafaka lallai kai mai karamci ne kana kaunar liyafa an kuma umarceka da bada mafaka kai mini abin da na ke kwadayi cikin sa zuwa gareka nayi fatansa daga gare ka don matsayinka da matsayin iyalan gidanka wajen Allah da matsayinsa wajenku don matsayin dan baffanka manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata gare shi.[3]

Ranar Litinin da sunan jikoki imamai Hassan Almujtaba da Husaini shugaban shahidai, bayan sallama mai ziyara zai ce:   

«يا مولاي يا أبا محمّد، ويا مولاي يا أبا عبد الله، هذا يوم الاثنين وهو يومكما وباسمكما وأنا ضيفكما فأضيفاني وأحسنا ضيافتي فنعم من استضيف به أنتما وأنا فيه من جواركما فأجيراني فإنّكما مأموران بالضيافة والإجارة فصلّى الله عليكما وآلكما الطيّبين ».

Ya shugabana ya baban Muhammad ya shugabana ya baban Abdullah wannan rana ranar litinin ce ita ranarku ce da sunanku ni bakonku ne ku mini liyafa ku karbi bakuntata ku kyawuntata, madallah da wanda ku kaiwa liyafa lallai ni cikin ta ina daga makotanku ko karbi makotaka ta lallai ku an umarceku da liyafa da makotaka amincin Allah ya kara tabbata gare ku da iyalanku tsarkakakku.[4]

Ranar talata da sunan imamai tsarkaka imam Sajjad da imam Bakir da imam Sadik: mai ziyara bayan ziyartarsu sai ya ce:

«يا مواليّ هذا يومكم وهو يوم الثلاثاء وأنا فيه ضيف لكم ومستجير بكم فأضيفوني وأجيروني بمنزلة الله عندكم وآل بيتكم الطيّبين الطاهرين ».

Ya shugabanni na wannan rana ranarku ce itace ranar talata ni bakonku ne mai neman tsira da ku, ku karbi bakuntata ku tseratar dani don matsayin Allah wajenku da wajen iyalanku zababbu tsarkakakku.[5]

Ranar laraba da sunan A'imma rabautattu imam Kazim da imam Jawad da imam Rida da imam Hadi: bayan ziyartarsu sai kace:

 «أنا مولى لكم مؤمن بسرّكم وجهركم متضيّف بكم في يومكم هذا وهو يوم الأربعاء ومستجير بكم فأضيفوني وأجيروني بآل بيتكم الطيّبين الطاهرين ».

Ni masoyinku ne mai imani da sirrinku da bayyanarwarku mai neman liyafarku cikin wannan rana taku ranar laraba mai nema tserata daku ku tseratar dani ku karbi liyafa don iyalan ghidanku zababbu tsarkaka.[6]

Ranar Alhamis da sunan imam Hassan Askari (as) bayan karanta ziyara zaka ce:

«أنا مولى لک ولآل بيتک وهذا يومک وهو يوم الخميس وأنا ضيفک فيه ومستجير بک فيه فأحسن ضيافتي وإجارتي بحقّ آل بيتک الطيّبين الطاهرين ».

Ni masoyinka ne da iyalan gidanka wannan ranarka ce ranar Alhamis ni bakonka ne mai neman makotaka dakai cikin ta ka kyawunta liyafata da makotaka ta don matsayin iyalan gidanka zababbu tsarkaka.[7]

Ranar Juma'a da sunan shugabana imamin zamanina sahibul Asri waz-zaman hujjatul muntazar imami na goma sha biyu (as) Allah ya gaggauta bayyanarsa mai daraja bayan sallama da salati gare shi sai mu ce:
«يا مولاي ، يا صاحب الزمان ، صلوات الله عليک وعلى آل بيتک ، هذا يوم الجمعة وهو يومک المتوقّع فيه ظهورک والفرج فيه للمؤمنين على يديک وقتل الكافرين بسيفک ، وأنا يا مولاي فيه ضيفک وجارک وأنت يا مولاي كريم من أولاد الكرام ومأمور بالضيافة والإجارة فأضفني وأجرني صلوات الله عليک وعلى أهل بيتک الطاهرين ».

Ya shugabana ya sahibuz-zaman, amincin Allah gareka da iyalan gidanka, yau ranar juma'a ce ranarka da ake tsammani da saran bayyanarka da yayewa ga muminai cikin ta a hannunka da kashe kafirai da takobinka, ni ya shugabana cikin ta bakonka ne makocinka ne kai kuma ya shugabana mai karamci daga `ya`yan masu karamci ka fito, an umarceka da liyafa da makotaka kai mini liyafa ka makotace ni amincin Allah ya kara tabbata gareka da iyalan gidanka tsarkaka.[8]

Sannan ga dukkanin bako ana tanadar masa gara da karamci, to su Ahlil-baiti (as) suna ma'adanar dukkanin alheri da ihsani sune ma'abota kyauta da karamci bau korar mai rokonsu basa tozarta wanda ya nufosu Allah ya basu umarni da su bada mafaka ga wanda ya nemi fakewa dasu su kuma karbi bakon da ya je wajensu su shirya masa gara hakika ya zo cikin hadisi:

 (أكرم الضيف ولو كان كافرآ)

Ka girmama bako ko da kuwa ya kasance kafiri.

Sai suka kasance suna girmama bako ko da kuwa ya kasance daga kafirai to kaka idan kuma ya kasance daga masoya mai wilya gare su daga cikin`yan shi'arsu masu bin umarninsu masu biyayya gare su, lallai su babu shakka da kokwanto zasu yi masa liyafa da mafi kyawu da kamalar liyafa, za kuma su bashi mafaka da mafi kyawun mafaka, sai dai cewa liyafar ma'asumai na nufin samun taufiki da samun dacewa cikin rayuwa da dacewa da ziyartarsu cikin duniya da mutum cikin wilayarsu da addininsu, da samun tausayinsu da addu'arsu, da samun cetonsu a ranar lahira, da kuma tashi cikin gayyarsu cikin mafakarsu, kamar yadda manzon Allah (s.a.w) ya ce:

«يا عليّ أنت وشيعتک جيراني في الجنّة »

Ya Ali kai da shi'arka makotana ne cikin aljanna.[9]

Liyafar manzon Allah (s.a.w) da iyalansa tsarkaka: kadai dai tana nufin tatacce daga iliminsa da saninsa, su abincinsu ilimi ne da ma'arifa kamar yadda hakan ya zo cikin hadisi mai daraja karkashin fadinsa madaukaki:

(فَـلْيَـنْظُرِ الإنسَانُ إلَى طَعَامِهِ ) ، قال الإمام الباقر  7: «فلينظر إلى علمه

ممّن يأخذ» فالطعام في عالم المعنى هو العلم ،

Mutum ya yi duba zuwa ga abincinsa,[10] imam Bakir (as) ya ce: ya yi duba zuwa ga iliminsa daga wanne mutum zai karbo.

Abinci a duniyar ma'ana shi ne ilimi.

Garar A'imma ga bakinsu shi ne shayar da su daga ilimansu na ubangiji su kuma ciyar da su daga teburin darbar Allah daga littafinsa mai daraja da kyawawan sunayensa da madaukakan siffofinsa, su tabbatar da su kan wilayarsu, babu mai samun haka sai ma'abocin babban rabo.

Sannan abin da muka nufa cikin wannan dan takaitaccen bayanin shi ne bayanin abin daya zo cikin ziyarar shugabarmu Fadima Zahara hujjar hujjoji farin cikin zuciyar annabi Musdafa sanyin idaniyar manzon Allah (s.a.w) dahira batula shugabar matayen duniya Fadima Zahara (as) hakika hatimin malaman hadisi babban malaminmu shaik Abbas Alkummi (rd) cikin littafinsa mafatihul-jinan ya kawo ziyara guda biyu kamar yadda zai zo:

Ziyara ta farko:  

«السلام عليکِ يا ممتحنة ، امتحنکِ الذي خلقکِ فوجدکِ لما امتحنکِ صابرةً ، أنا لکِ مصدّق صابر على ما أتى به أبوک ووصيّه صلوات الله عليهما وأنا أسألکِ إن كنتُ صدّقتکِ إلّا ألحقتني بتصديقي لهما لتسرّ نفسي فاشهدي أنّي ظاهر بولايتک وولاية آل بيتکِ صلوات الله عليهم أجمعين ».

Amincin Allah ya tabbata gareki ya wacce aka jarrabata, Allah ya jarrabaki sai ya sameki mai hakuri kan abin daya jarrabceki, tabbas ni mai gasgataki ne mai hakuri ne kan abin damahaifinki ya zo da shi da wasiyyinsa amincin Allah ya kara tabbata a gare su ni ina rokonki idan na kasance na gasgataki ki riskara dani da gasgatawata dasu domin raina ya yi farin ciki ki shaida lallai ni mai bayyana wilayarkine da wilayar iyalan gidanki amincin Allah ya kara tabbata gare su.[11]

Ziyara ta biyu:  

«السلام عليکِ يا ممتحنة ، امتحنکِ الذي خلقکِ قبل أن يخلقکِ وكنتِ لما امتحنکِ به صابرة ونحن لک أولياء مصدّقون ولكلّ ما أتى به أبوکِ صلّى الله عليه وآله وسلّم وأتى به وصيّه عليه السلام مسلّمون ونحن نسألک اللهمّ إذ كنّا مصدّقين لهم أن تلحقنا بتصديقنا بالدرجة العالية لنبشّر أنفسنا بأنّا قد طهّرنا بولايتهم عليهم السلام ».

Amincin Allah ya tabbata gare ki ya wacca aka jarraba, wanda ya halicce ki ya jarrabaki gabanin ya halicceki kin kasance ga abin daya jarraba ki da shi mai hakuri mu gare ki masoya ne masu gasgatawa ga dukkanin abin da babanki ya zo da shi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi da abin da wasiyyinsa ya zo da shi amincin Allah ya kara tabbata gare shi lallai mu masu sallamawa ne mu muna rokonki idan mun kasance masu gasgatawa gare su ki riskar damu da gasgatawarmu gare su zuwa ga daraja madaukakiya domin mu yiwa kawukanmu bushara da cewa lallai mu mun samu tsarkakuwa da wilayarmu gare su.[12]

Bai buya ga ma'abota hankali kan cewa wannan ziyara mai girma wacce ake ziyartar shugabar Zahara (as) cikin kowacce ranar lahadi cikin kowanne sati, ana kidayata daga mafi girman ziayarorin fadimiyya da aka sameta daga riwayoyin Ahlil-baitin isma da dahara, lallai ita tsakanin kalmominta tsarkaka tana tattaro haskaye da sirrika da taskoki daga iliman da ma'arifofi da tabbatattun abubuwa wadanda zamu ishara zuwa wani haske daga haskayensu domin mu samu shiriya daga tsonarsu, lallai yadda al'amarin yake shi ne unwani da take shida na fitowa da bayyana daga wannan ziyara wadanda hasken ilima da ma'arifa yake bazu daga gare su, kamshin turaren wilaya da soyayya da kauna ke tashi daga gare su kamar yadda zai zo kamar haka:

 

1-Ibtila'i da hakuri kansa:

«يا ممتحنة ، امتحنکِ الذي خلقکِ قبل أن يخلقکِ وكنتِ لما امتحنکِ به صابرة »، «فوجدکِ لما امتحنکِ صابرة ».

Ya ke wacce aka jarrabta, hakika wanda ya halicce ki ya jarraba ki gabanin halittarki sai kika kasance mai hakuri kan jarrabawar da ya yi miki, ya sameki mai hakuri kan abin daya jarraba ki.

Gwaji da jarrabawa da ibtila'i suna daga sunnonin Allah cikin rayuwa, hakika shi ne wanda ya halicci mutuwa da rayuwa

 (لِـيَـبْلُوَكُمْ أيُّكُمْ أحْسَنُ عَمَلا)

Don ya jarrabaku wane ne cikin yafi kyawunta aiki.[13]

Duk inda zabi ya kasantu to tabbas gwaji da jarraba na wajen, lallai mutum cikin mukamin ibtila'i da jarrabawa yana kasancewa cikin zabi, tabbas Allah ya shiryar da shi hanya biyu, ko dai ya kasance mai godiya ai aikace da kuma a baki, mai bauta mai biyayya ga Allah matsarkaki, ko kuma dai ya yi butulci ya kafircewa ni'momin Allah cikin abin daya umarce shi da wanda ya haneshi.

  (إمَّا شَاكِرآ وَإمَّا كَـفُورآ)

Ko dai mai godewa ko kuma mai kafircewa.[14]

Sannan yana bayyana daga ayoyin kur'ani mai girma da madaukakan hadisai cewa lallai wannan gwaji da jarrabawa ya kasance cikin zabi tun da can cikin duniyoyin al'amari da abubuwa marasa gangar jiki daga haskaye da inuwa da ruhi da cikin duniyar kwayar zarra, ma'ana cikin duniyoyin malakutiyya gabanin duniya nasutiyya, ma'ana duniya mafi kaskanta, lallai bayyanar ga wadancan duniyoyin ya kasance cika hujja, lallai Allah yanada hujja mai isarwa, magana kan wannan yana fadi da kuma cin lokaci matuka…

Sannan Allah ya jarrana shugabarmu Fadima Zahara (as) ya jarrabata ne gabanin halittatta da halittar duniya da muke ciki, ma'ana ya jarrabata da bala'i cikinumarni.

 (ألا لَهُ الخَلْقُ وَالأمْرُ) ،

Ku saurara gare shi halitta da umarni yake.[15]

Ma'ana cikin duniyar malakutiyya daga ruhuna da haskaye, cikin duniya daukar alkawari da kwayar zarra, hakika Allah ya jarrabata da bala'o'i da ibtila'i da abin daya gudana kanta cikin gidan duniya da kan `ya`yanta tsarkaka da zuriyarta rabautattu daga jarrabawar kisa da takobi da shayar da su guba da daure a gidan kaso fursun da korarsu daga garinsu da nesantar da su da azabtar da su da dai musibu wadanda da zasu sauka kan kwanaki da tabbas sai sun koma darare, yadda take fadi (as) bayan wafatin babanta manzon Allah (s.a.w)   

صبّت عَلَيَّ مصائبٌ لو أنّها         صُبّت على الأيّام صرن لياليا

Musibu sun sauka kaina da ace zasu sauka kan kwanaki da sai sun kasance darare.[16]

Sannan duk wanda Allah yake sonsa to zai jarraba shi da bala'i mai kyawu, lallai shi fa mumini dama abin jarrabawa ne, bala'insa ya kasance sakamakon wilayar da yake dauke da ita, mafi yawan bala'insu shi ne mafi yawan wilaya cikin su, duk wanda aka jarraba sannan ya yi hakuri da jarrabawar to tabbas ya rabauta rabauta mai girma, lallai Allah yana cikawa masu hakuri ladansu ba tare da hisabi ba, hakika mun tabbatar da hakan cikin risala mai sunan (isma bi nazara jadida) da cewa lallai rukunan isma sune: ilimi zuhudu hakuri, duk wanda ya sani da ilimin Allah ya yi zuhudu cikin duniyarsa ya yi hakuri kan bala'in da yake ciki to lallai shi Allah zai katange shi daga aikata zunubi da laifuka, ko dai ta hanyar ismar zatiyya ko kuma ta hanyar isma kulliya mudlaka kamar yadda take cikin annabawa da wasiyyai, ko kuma dai da isma Af'aliyya kamar yadda yake cikin waliyyai da salihai da muminai.

Amma ma'asumai goma sha hudu lallaisusun shallake ragowar halittun Allah baki dayansu cikin ilimi da zuhudu da hakuri, ismarasu tana cikin mafi daukakar martabar isma, ismarsu da tsarkakarsu da girmansu sun yi tajalli cikin babarsu Fadima Zahara (as) lallai ita ta tattaro hasken ismar annabta da hasken ismar imamanci, ta kasance mabayyana cikakka ga ismar Allah mafi girma, shi asasin ismarta ya kasance ne bayan jarrabata da zabi da ya kasance kan ibtila'i da hakuri.

 

2-Wilaya da soyayya:

«ونحن لکِ أولياء».

Mu masoyanki ne.

Wila'u yana da ma'anar soyayya da taimako da biyayya da da`a, hakika ya tabbata a mahallinsa cewa lallai addnin muslunci shien wilaya da soyayya ga annabi da iyalansa, shin annabi wani abu ne daban da ya wuce ga mmanzo Allah (s.a.w) da iyalan gidansa Ahlil-baiti tsarkaka da kuma nuna kiyayya ga makiyan manzon Allah (s.a.w) da iyalan gidansa tsarkaka.lallai ladan sakon muhammadiya kadai yana cikin nuna soyayyar makusanta iyalan musdafa, ina nufin Fadima Zahara da A'imma goma sha biyu halifofin manzon Allah (s.a.w) dukkaninsu daga kuraishawa.

Sannan muwadda a isdilahance tana da ma'anar soyayya da biyayya, dukkanin wanda ya so ya yi musu biyayya zai kasance tare da su cikin duniya da lahira, mu masoyan Fadima Zahara (as) ne kuma da izinin Allah mu muna daga `yan shi'arta, lallai wanda ya kasance cikin mazhabarsa da kudurinsa da addninsi akwai soyayyar Fadima ya kuma kasance musulmi mai imani da annabi a akidance ma'abocin wilaya a mazhabance, ma'ana mai biyayya da da'a ga wasiyyi waliyin Allah (as)

Sannan Fadima Zahara (as) sirrin samuwa hakika ta tattaro tsakankanin hasken annabta da wilaya, ita `yar manzon Allah (s.a.w) sannan matar waliyin Allah uwa ga A'imma zababbu, dukkanin wanda ya so ta to hakika ya so Allah da manzonsa da waliyyansa, dukkanin wanda yake kinta tabbas yana kin Allah ne da manzonsa da waliyyansa, ki shaida ya shugabata lallai mu masoyanki ne masu kaunarki masu gaskiya cikin wilayarki da sonki da kaunarki, muna fansar da rayukanmu da dukkanin abin da muka mallaka don fansoku da wilayarku mafi gram da ayarku mafi girmama, me yafi kyawu daga kisa da shahada cikin tafarkinku lallai tafi dadi daga zuma kan harshe, zamu rayu zamu mutu kan wilayarku da soyayyarku, lallai mu muna tare da ku bama tare da makiyinku ba tare da waninku ba, lallai neman shiriya daga waninku yana matsayin inkarinku, daku muke koyi da kwaikwayo, sannan kan wilayarku muke rayuwa muke mutuwa kuma don ita muke fansar muku da rayuwarmu.

 

3-Gasgatawa:  

«أنا لکِ مصدّق »،

Ni mai gasgatawa gareki ne.

 «نحن لکِ أولياء مصدّقون ».

Mu masu gasgatawa gareki ne.

Tasdik daga sidku yake wanda kizbu karya ke kishiyantarsa , ba dukkanin mai da'awar wilaya da soyayya bane yake kasance mai gaskiya cikin abin da yake da'awa, bari dai ya zama dole ya tabbatar da hakan a harshe a zuciya da gabbai da aiki da rukunai, ma'ana ya gasgatar da da'awarsa cikin harshe da aiki cikin mukamin da'a da biyayya da bai'a, sai ya sayar da ransa da dukiyarsa domin neman yardarm Allah, lallai Allah matsarkaki yana yarda da yardarta Fadima Zahara (as) yana kuma fushi da fushinta, yardarm Allah na cikin yardarta hakama yardarta na cikin yardar Allah, sannan yardarta yardar babanta ce yardarm mijinta ce da `ya`yanta, lallai mai wilaya da soyayya dan shi'a tsantsa yana tabbatar da shi'ancinsa da iklasinsa cikin wilaya da kauna da da'a da ibada, da ilimi mai amfani da aiki nagari, lallai mutum yana cikin hasara face dai wadanda sukai imani da Allah sukai da manzonsa da Mala'ikunsa da litattafansa da wasiyyansa anabinsa sukai aiki nagari sukai wasicci da gaskiya, Ali (as) yana tare da gaskiya gaskiya tana tare da Ali duk inda ya juya taa juyawa, saukai wasicci da yin hakuri kan jarrabowowi da musibu da suke sauka kansu daga makiya Allah sakamakon wilayarsu da soyayyarsu ga waliyyan Allah da Fadima Zahara (as) lallai mu

muna gasgata Fadima Zahara (as) cikin simarta da hajjantakarta da matsayinta da kusancinta daga Allah ta'ala da wilayarta da fadak dinta da hudubarta da zaluncin da akai akanta da bainda ya faru kanta bayan wafatin babanta daga zalunci azzalumai da danniyar ja'irai Allah ya la'ance su baik dayansu har aban abidin.

 

  «اللهمّ العن أوّل ظالم ظلم حقّ محمّد وآل محمّد وآخر تابعٍ له على ذلک »،

Ya Allah ka la'anci farkon azzalumi da ya zalunci hakkin Muhammad da iyalan Muhammad da karshen wanda ya bishi kan haka.

Mu masoyanki ne mu masu yakar makiyanki ne, lallai mu a cikin mu akwai wanda ya rigaya ya cika alkawarinsa akwai kuma mai jira, Allah ya azurta mu da shahada cikin tafarkinku tafarkin Allah, ya kuma tashe mu cikin gayyarku ya azurta mu da ziyartarku da tausayinku da addu'arku cikin gidan duniya. A lahira kuma ya azurtamu da samun cetonku da tashi cikin gayyarku da fakewa daku.

 

4-sallamawa da sabati da istikama da dukkanin abin da wahayi ya zo da shi da wilaya –ma'ana annabi da wasiyyi (as)

«ولكلّ ما أتى به أبوکِ  9 وأتى به وصيّه  7 مسلّمون »، «صابر على ما أتى به أبوکِ ووصيّه صلوات الله عليهما».

Ga dukkanin abin da babanki (s.a.w) ya zo da shi da abin da wasiyyinsa (as) ya zo da shi mu masu sallamawa ne, hakuri kan abin da babanki ya zo da shi da wasiyyinsa amincin Allah ya kara tabbata gare su.

Lallai daga cikin mutane akwai wanda aka bashi ajiyar imani (Allah ka tsaremu) akwai kuma wanda ya imani ya tabbatu cikin sa, jigo cikin imani shi ne gasgatwa da sabati kansa, nawa daga wanda ya yi imani daga baya duniya ta rude shi ya juya kan bayansa ya mutu kafiri?!

Shin ashe mutane basu yi ridda ba ta aiki bayan manzon Allah Muhammad (s.a.w) ga barin wilayar sarkin muminai Ali (as) ta juya mata baya tare da ya nasabta shi ranar gadir, sai sukai inkarin gaskiya suka tozarta ta suka saba mata, sannan duniya kaskantacciya ta rudar da su, suka aikata abin da suka aikata daga abin da goshin mutumtaka ke zubar da gumi da zufa daga abubuwan abin kunya da sabo da laifuka da zalunci da danniya, a wannan lokaci ba zai isar kawai muce Allah ne ubangijinmu ba girmansa ya girmama annabinmu Muhammad (s.a.w) ba tare da tashi tsaye ba da gwagwarmaya ba da sabati da tabbatuwa kan haka. ya zama dole mu tsaya kyam kan wannan furuci da imani da suluki da aiki da da'a ga Allah da manzonsa, da bin halifofinsa da wasiyyansa wadannda manzon Allah (s.a.w) ya nassanta su da gaskiya, lallau duk wanda ya mutu bai san imamin zamaninsa bay a mutu mutuwar jahiliyya, ka kafirci da munafunci, saboda haka mu wane ne imamin zamaninmu wanda Allah ya nasabta shi halifan manzon Allah (s.a.w) da nassi daga gare shi

 

 (الَّذِينَ قَالُوا رَبُّـنَا اللهُ ثُمَّ آسْتَقَامُوا تَـتَـنَزَّلُ عَلَيْهِمُ المَلائِكَةُ ) ،

Wadanda suka ce ubangijinmu Allah sannan suka tsaya kyam Mala'iku suna sassauka kansu.[17]

Ya zama dole a sallama tsanstar sallamawa ga ma'asumi (as) hatta idan imami ma'asumi (as) zai ce rabin wannan kayan lemon halal ne daya rabin kuma haramun ne to da take zamu ci barin rabin halaldin mu yi watsi da barin rabin da ya haramta kamar yadda ya zo cikin hadisi mai daraja.

Shin muslunci wani abu ne da ya wuce sallamwa ga Allag da manzonsa da wsiyyansa da gaskiya? Shin addini wani abu da ya wuce sabati da tsayuwa kyam kan gaskiya tare da gaskiya, ku kasance tare da gaskiya har ranar addini ranar kiyama, kadai dai Allah yana cikwa masu hakuri ladansu ba tare da hisabi ba.

 

5-riskar annabta da imamanci, kadai dai yana sadar da igiyar sadarwa da Zahara.

«ونحن نسألک اللّهم إذ كنّا مصدّقين لهم أن تلحقنا بتصديقنا بالدرجة العالية »،

 و«وأنا أسألک إن كنت صدّقتک إلّا ألحقتني بتصديقي لهما».

Mu muna rokonka ya Allah idan har mun kasance masu gasgata gare su to ka riskar damu da gasgatawarmu da daraja madaukakiya.

Ni ina rokonka idan har na kasance mai gasgatawa ka riskar dani da gasgatawa dasu. 

(قُلْ مَا يَعْبَأُ بِكُمْ رَبِّي لَوْلا دُعَاوُكُمْ ) ،

Kace ubangijinku bai damu daku ba badon addu'o'inku.[18]

 

Lallai addu'ar itace bargon ibada.

 (وَمَا خَلَقْتُ الجِنَّ وَالإنسَ إلاَّ لِـيَعْبُدُونِ

Ban halicci mutane da aljannu ba face sai don su bauta mini.[19]

Lallai mu bayan wilaya da soyayya da kauna ta cikin zuciya da gasgatawa a aikace da sabati da tsayuwa kyam zamu riski gaskiya da Ahlinta ta hanyar lazimtarsu da binsu da yi musu da'a lallai:

 «المتقدّم عليهم مارق ، والمتأخّر عنهم زاهق ، واللازم لهم لاحق »

Mai gabatarsu ya fita daga addini, mai jinkirta musu ya halaka, mai binsu sau da kafa da lazimtarsu mai riskarsu ne.

Sai dai cewa makullin dukkanin gyara da rabauta yana cikin addu'a ya zama dole mu roki Allah mu kirashi da ya datar damu da riskarsu, kamar yadda ya zo cikin ziyara fadimiyya bari ma dai cikin da yawan ziyarori da addu'o'i da aka rawaito daga manzon Allah (s.a.w) da tsatsonta tsarkaka, ya zama dole mu nemi taimako daga gaibu da tallafin Allah domin samun madaukakan mukamai da darajoji masu daukaka, kadai dai hakan na tabbatuwa ta hanyar addu'a da tawassuli da kuka da da'a, nema daga annabi da iyalansa cikin hakikar ala'amari nema daga Allah matsarkaki, kamar bai'a ga annabi da da'a gare shi, duk wanda ya yi bai'a ga annabi (s.a.w) ya yi da'a gare shi kamar ya yi bai'a da da'a ga Allah ne kamar yadda hakan ya zo cikin kur'ani mai girma mu muna rokanka ya Allahu idan mun kasance masu gasgata manzonka da wasiyyansa A'imma tsarkaka a fade da aikace ka riskar damu da gasgatarwarmu da daraja madaukakiya cikin aljannar kyawawan sunayenka, cikin aljanna wacce fadinta kamar fadin sammai da kasa yake, cikin matsugunin gaskiya wurin mai ikonyi mai iya zartarwa.

Kamar yadda muke rokanka ya ubangijin wancan, muna kuma rokon baiwarka ismarka mafi girma Fadima Zahara (as) lallai yaradarka na cikin yardarta fushinka na cikin fushinta, dukkanin abin da ya fusata ta yana fusataka dukkanin abin da ya yardarm da kai yana yardar da ita, muna rokonta da ta riskar damu da imaninmu da gasgatawarmu ga annabi da wasiyinsa da babanta da mijinta da `ya`yanta tsarkaka cikin duniyar imakani.

 

6-Bushara da rabauta da farin ciki da tsarkaka:

«لنبشّر أنفسنا بأنّا قد طهرنا بولايتهم  :»،

Domin muyi kawukanmu bushara da cewa lallai mu tabbas mun

Tsaraka da wilayasru.

Daga cikin bayanannen al'amari lallai sakamako da natijar wilaya ta zuciya da gasgatawa ta aiki da sallamawa ta suliki da sbati da tsayuwa kyam da riskar annabta da imamanci cikin imani da suluki da kuma a aikace cikin kowanne fage daga fagen rayuwa, kadai dai shi rabauta ce da ni'ima a duniya da lahira, da bushara da farin ciki da tsarkakar rai da zukuta, da tashi tare da rabautattu tsarkakakku wurin mai ikon yi cikin matsugunin gaskiya, babu tsoro kansu babu bakin ciki tare da su.

Sannan ibadar gabbai na zahiri dana badini, badininta shi ne jibantar waliyyan Allah, kamar yadda badinin zunubai da laifuka da sabo da alfasha yake jibanta ga makiya Allah, Allah bai halicci mutane da aljanu face don su bauta masa, sannan hakikar ibada na cikin wilaya da addu'a, ita kuma hakikanin addu'a shi ne yankewa zuw aga Allah, daga cikin mutane akwai mai kusantar Allah da ibada don tsora da kwadayi da godiya, sai dai cewa yadda al'amarin yake dole ne ya kasance tare da takawa da iklasi tsarkake niyya yayin da yake addu'a da ibada, lallaia aiki tsarkakke Allah na daukaka shi yana kuma karbarsa.

 

(إنَّمَا يَتَقَبَّلُ اللهُ مِنَ المُتَّقِينَ )  ، (إلَيْهِ يَصْعَدُ الكَلِمُ الطَّـيِّبُ وَالعَمَلُ  الصَّالِـحُ يَرْفَعُهُ )  ،

Kadai dai Allah yana karba daga masu takawa.[20]

Gare shi daddadan kalami ke dagawa kuma aiki nagari Allah yana daukaka shi.[21]

Kadan ne daga bayin Allah suka kasance masu godiya da iklasi.

Lallai mutane baki dayansu sun hallaka face malamai sannan malamai baki dayansu sun halaka sun masu aiki da iliminsu, sannan masu aiki da iliminsu baki dayansu sun halaka face masu tsarkake niyya, sannan su kuma masu tsarkin niyya suna cikin hastari, lallai riya cikin aiki kamar misalin tafiyar bakar tururuwa ce kan kurman dutse cikin dare mai tsananin duhu wanne mutum zai iya jin karar tafiyarta, to haka jiji da kai shima lallai yana gurbata aiki kamar yadda kunu ke bata zuma, shi jiji da kai yanke ni'ima ne daga ma'abocinta da dangantata ga kansa, duk wand ayake jiji da kansa da ibadarsa da aikinsa bai ganin haka daga ni'imar Allah kansa, bari dai yana ruduwa da kansa yana cin mutuncin wasunsa, sai ka sameshi ya jarrabtu da girman kai da ruduwa da jiji da kai da riya har sai ayyukansa da ya yi sun tafi a iska a banza, saboda addu'a da ibada suna cikin mabijirar hatsari. Sai dai cewa ibtila'i da bala'i yana wofinta daga jiji da kai da riya kai ta yiwu ma ya dace da aibobinmu da yanayinmu, ta yiwu ibtila'in ya zama hanyar shiriyar mutum ko al'umma kamar ibtila'i da ya kasantu kan annabi Yusuf (as) da wanda yake kasantuwa kan waliyyan Allah daga annabawa da wasiyyai da malamai da salihai da muminai.

bai buya kan cewa mafi girman bala'i da ya sanya sama da kasa kuka ya gigita Mala'iku da ma'abota hankula shi ne abin da ya afku da manzon Allah (s.a.w) lallai shi ya ce:

 «ما اُوذي نبيّ بمثل ما اُوذيت »،

Babu wani annabi da aka cutar misalin yadda aka cutar dani.

Haka zalika abin da ya faru kan iyalan gidansa tsarkaka da wasiyinsa murtaza da `yarsa Fadima Zahara, da jikokinsa biyu furensa Hassan da Husaini amincin Allah ya kara tabbata gare su da kuma abin da ya faru kan A'imma tsarkaka daga kisa da azabtarwa da kora da dauri da matsa musu da takura musu da haramtawa da kwace halifancinsu da inkarin falalarsu da hakkokinsu, kamar yadda tarihi ke shaida kan haka.

Me yafi girman musiba daga musibar da ta samu shugaban shahidai imam Husaini bn Ali (as) hakika musibar da ta faru kansa ta sanya Mala'ikun sama kuka


«لقد عظمت الرزيّة علينا وعلى جميع أهل الأرض وعلى جميع أهل السماوات »،

Hakika musiba ta girmama kanmu hakama kan dukkanin halittun da suke kan doran kasa hakama kan dukkanin wadanda ke sama.

Sannan dukwanda ke kan hanyar shugaban shihaidai yake kuma koyi da tsarinsa yake kwaikwayon jahadinsa da shahadarsa, da abin da ya faru kan mutanen gidansa daga kisa da dauri tabbas zai burin cewa ya kasance tare da su  

  «يا ليتنا كنّا معكم فنفوز فوزآ عظيمآ»

Zai nemi ubangijinsa ya bashi mafi ladan da yake baiwa ma'abocin musiba da musibarsa, lokacin da yake jujjuyawa tare da musibar data samu shugaban shahidai (as) tare da ibtila'insa sai dai cewa sharadin kyautar ubangiji kadai yana tabbatuwa ne idan an jarraba mu da irin bala'insu, lallai hakan yana sanya samun kusancin Allah matsarkaki kamar yadda yake janyo shiriya da kamal, lallai a badinin wannan bala'I shi ne akwai liyafa wurin Allah, kamar yadda wannan ma'ana take tajalli cikin sujjada da ake karshen karatun ziyarar ashura, lallai ita sujjada ce ta neman kusanci zuwa ga Allah da godiya kan musiba, ma'ana ana kirga hakan daga ni'imar Allah kansa, wanda aka ni'imta cikin liyafar mai ni'imtawa.

Sannan abin da ya faru kan `ya`yan manzon Allah (s.a.w) kadai dai yana faruwa ne kan mahaifiyarsu Fadima Zahara(as) lallai ibtila'in da ya same su ibtila'inta ne, bakin cikin su bakin cikin ta ne musbarsu musibarta ce, ita ce uwar musibu mafi girma, hakika Allah ya gwada ta ya jarrabata da wadancan bala'o'i  sai ya same ta mai hakuri da dangana, sai ya sanyata igiyar sadarwa tsakanin annabi da wasiyyi tsakanin halittu muminai cikin duniyar halitta, duk wanda aka riskar da shi da su lallai shi zai rabauta da aljanna    

 (وَآدْخُلِي جَـنَّـتِي )

Ka shigar dani aljannata.[22]

 

Aljannar kyawawan sunaye ya rabauta da yardar Allah mai mafi girma.

Sannan ya tabbata lallai cewa bauta da azurtar duniya da lahira kadai dai yana tacewa cikin wilaya da bara'a, ma'ana cikin soyayya da kiyayya, kamar yadda yake wilaya ta hakika shi ne tauhidi, lallai Kalmar (la'ilaha illallahu) shingen Allah ce, dukkanin wanda ya shiga cikin shingensa ya aminta daga azabarsa, sai dai fa da sharadinta da sharuddanta.

Sannan hakika wilayar A'imma tsarkaka halifofin shiriya na  manzon Allah (s.a.w) muktar sarkin muminai Ali (as) da `ya`yansa goma has daya suna daga cikin sharaddunta kamar yadda ya zo daga shugabanmu imam Rida (as) cikin hadisin nan da ya shahara da sunan silsila zahabiyya da kuma jarrabawarsu da ibtila'io'insu wadanda suna daga cikin mafi girman ibadoji, da jurewa ibtila'I daga gare su wand aya kasance sababin ga kusancin duniyar halitta zuwa ga Allah matsarkaki   

«بنا عُبد الله، وبنا عُرف الله»

ta hanyarmu aka bautawa Allah ta hanyarmu ake sanin Allah.

Daga mafgi girman ibadarmu shi ne fuskantar wadancan ibtila'o'i masu girma, wanda ya jahilce ta kaka zai tunkaresu ta kaka zai mu'amala da su a tunanance da akiadance da suluki da aiki da jihadi, lallai tukarar zuwa ga wadancan ibtila'o'i na daga mafi muhimmancin dalilai da suke wajabta tafiya zuw aga Allah da fana'i cikin sa, sannan abin da waccan tunkarar ke lazimtawa shi ne ilimi da ma'arifa, wanda ya jahilce su ta kaka zai tunkaresu ta kaka zai mu'amala da su ? lallai tsakanin ilimi da jahilic akwai kishiyantar juna kamar yadda tsakanin hankali da jahilci, lallai hankali yana wasu rundunoni kamar yadda ya zo cikin hadisi daga littafin Alkafi lallai su rundunoni da'a ne da ibada, lallai shi hankali shi ne abin da ta hanyarsa aka bautawa Alah ake samun aljannoni, kamar yake cewa su rundunonin manzon Allah (s.a.w) ne lallaui shi hankli shi ne mmanzo na badini a boye wanda shi ne mai taimakon manzon bayyane na zahiri, Allah yanada hujjoji biyu hujjar badini ta boye itace hankali, sai hujjar bayyane ta zahiri itace annabi, sannan shi jahilci shi ne shaidan, shima yanada rundunoninsa da mataimakansa da masu tallafarsa da masoyansa.

Sannan maksudi daga halittar mutum shi ne ya samu kamala da cika ya kuma kasance mabayyana mazhari ga sunayen Allah da madaukakan siffofinsa, sai dai cewa Allah ya shiyar da shi hanyoyi biyu: kodai ya kasance daga madaukaka makusanta Allah ya jibanci al'amarinsa     

 (اللهُ وَلِيُّ الَّذِينَ آمَنُوا)

Allah ne majibancin wadanda sukai imani, sai iblis da rundunarsa su jibance shi.[23]

 (وَإنَّ الشَّيَاطِينَ لَيُوحُونَ إلَى أوْلِيَائِهِمْ ) .

Lallai shiadanu suna wahayi zuwa ga masoyansu.[24]

 

Lallai mutum yanada zabi tsakanin kasancewa daga rundunar hankali ko kuma zabar kasantuwa daga rundunar jahilci, shaidanyana jibantarwanda ya shiga cikin gfagen jahilci da filinsa sai ya sace masa zuciya ya shiga cikin sa ya saka kwai ya kyankyasa ya maida zuciyarsa shekarsa har ya kasance yana kallo da idanun shaidanu yana magana da harshensu, sai ya zama kallon masoyin shaidanu da dubansa kallo ne da duba na shaidanci, ya zamanto furucinsa da kalamansa na iblis ne la'ananne, saboda haka    

 (من أصغى إلى ناطق فقد عبده )

Dukkanin wanda ya kasa kunnuwa ga mai furuci to hakiaka ya bauta masa. Kamar yadda ya zo cikin hadisi mai daraja.

Lallai idan ya yi magana da yaren shaidani ko nafsul ammara ko kuma daga wanda ya rike son ransa ubangijinsa, lallai shi ya bautawa shaidani, idan kuma ya yi magana da yaren Allah to hakika ya bautawa Allah matsarkaki.

Sannan hakikanin jihadi mafi girma yana tare da zuciya mai umarni da mummuna, idan ya amsa ya yi nasara sai yaksance mujahidin cikin tafarkin Allah daga sojojin manzon Allah (s.a.w) nasara bata samuwa cikin jihadul Akbar face da fuskantar ibtila'o'i irin wanda suka samu manzon Alah (s.a.w) da Ahlin gidansa (as) da abin da ya faru da `yarsa Fadima Zahara (as) daga kwace mata gonar Fadak da kona gidanta da shahadar danta muhsin (as) tsakanin bango da kofa, da abin da ya afku da sarkin muminai Ali (as) daga kwace masa halifanci da jawo shi a daure zuwa masallaci da shahadarsa a wajen ibadarsa, sannan fuskantar zuwa ga musibar da ta samu shugaban shahidai wacce itace mafi girman musibu, lallai kuma babu wata rana kamar ranar Abu Abdullah, me yafi girman musiba me yafi girman bakin ciki?!    

«لقد عظمت الرزيّة وجلّت وعظمت المصيبة بک علينا وعلى جميع أهل الإسلام ، وجلّت وعظمت مصيبتک في السماوات على جميع أهل السماوات ، فلعن الله اُمّةً أسّست أساس الظلم والجور عليكم أهل البيت ، ولعن الله اُمّة دفعتكم عن مقامكم وأزالتكم عن مراتبكم التي رتّبكم الله فيها، ولعن الله اُمّةً قتلتكم ، ولعن الله الممهّدين لهم بالتمكين من قتالكم ...» 

Hakika bala'I ya girma musibar ta girmama dakai kanmu hakaa kan dukkanin musulmai, musibar da ta sameka ta girmama ta girma cikin sammai kan dukkanin Ahlin sama, Allah ya rsinewa mutanen da suka assasa tushen zalunci da danniya kanku Alil-baiti Allah ya tsinewa mutanen da suka tunkudeku daga mukaminku suka zamar daku daga martabobinku wanda Allah ya sanyaku cikin su, Allah ya tsinewa mutanen da suka kasheku ya kuma.[25]

 

Sannan shugaban shahidai (as) a waki'ar daffu mai tsananin radadi cikin ranar ashuraya tona asirin rundunar jahailci da kafirci da munafunci da abin da ya kasance ranar sakifa da abin da ya Yazidu tsinanne da shi'arsa har zuwa ranar tashin kiyama. Dukkanin wanda zai zo bayansa kodai ya kasance kan hanyarsa da addininsa wanda shi ne addinin annabawa da wasiyyai, addinin Allah mafi girma, ko kuma dai ya kasance cikin rundunar Yazidu wanda ya jikkantu da jahilci da kafirci da munafunci da bata, ko dai ya kasance tare da gaskiya ko kuma ya kasance tare da karya, lallai shi yana tsakanin wilayoyi biyu, wilyar Allah da wilayar shaidan, kodai mai godiya ko kuma mai butulcewa da kafircewa dukkanin wannan abu yana tajalli ne cikin ranar ashura cikin ziyarar ashura, sannan kowacce rana ashura ce kuma kowacce kasa karbala, idan shirka da kafirci da baki dayan smauwarsu sukai fito na fito da imani da muslunci baki dayansa cikin ranar yakin kandak da yakin Ahzab  cikin mubarazar Amru bn zul wuddi sai kuma sarkin muminai Ali (as) lallai wannan rana dukkanin munafunci a ranar ashura ya fito yakar imani baki dayansa cikin filin karbala. Lallai munafunci bayan tafiyar annabi (s.a.w) ya bazu ya yadu tsakankann musulmi har al'amarin yakai ga girgizuwar muslunci kai hatta cikin zahirinsa takai ga komawarwasu zuwa ga abin da suka bari da raya gabar jahiliya yayin da cikin rashin lafiyar annabi (s.a.w) lokacin da ya ce musu:

 

         «ائتوني بدواة وقرطاس أكتب لكم فلن تضلّوا بعدي أبدآ»: إنّ الرجل ليهجر، وحسبنا كتاب الله،

Ku kawo mini tawada da takarda in rubuta muku ba zaku taba bat aba bayana har abada, amma sai wani cikin su ya ce: wannan mutumin ya zautu.

Sannan bayan shekaru hamsi da wafatin manzon Allah sai suka ce:

لعبت هاشم بالملک فلا         خبرٌ جاء ولا وحيٌ نزل

Hashimawa sun wasa da mulki ba tare da wani labari da ya zo ba tare da wani wahayi da ya sauka

 Ma'ana sun nemi keta zahirin muslunci da inkarin wahayi da inkatin kur'ani mai girma.

Sannan maksudin fadin (wannan mutumin ya zautu) ma'ana annabi yake nufi hakama fadin Yazidu (babu wahayi da ya sauka babu wani labari da yazo) duk daya ne da e wancan magana sai dai cewa na farko yana yanayinsa kebantatta wanda munafunci na kunshe cikin sa (littafin Allah ya isar mana) wannan ya faru sakamakon bazuwar munafuci da bayyana kafirci sai ya ce: (ba tare da labari da yazo ba tare da wahayi da ya sauka ba) dukkanin maganganun biyu suna nuni zuwa ga boyayyen kafirci, saboda sai a lura.

Sannan iblis ya tattara rundunarsa daga aljannu da mutane ya kuma karfafesu kamar yadda ya zoa tarihi da dukkanin abin da ke bayyaa kafirci da munafunci, tun lokacin da Adamu zababben Allah ya sauko doran kasa har zuw aranar ashura, sai suka fito baki dayansu don yakar cikamakin annabawa shugaban manzanni Muhammad (s.a.w) da tsatsona A'imma tsarkaka, ya kasance daga malakut din ashura da tawilinta halartar dukkanin gaskiya da gaskiya baki dayanta, da yaki tsakanin gaskiya da dukkanin samuwarta da karya da dukkanin samuwarta, sai aka kashe shugaban shahidai da iyalan gidansa tsarkaka, domin jini ya yi nasara kan takobi, sai dukkanin duniyoyi sukai masa kuka sakamakon girman musiba da ibtila'i da bala'in da ya sameshi, babu abin da ya rage ga krae muslunci da dawwamuwar rayuwarsa face fansar Allah dan fansar Allah imam husaini bn Ali (as) lallai shi daya tal kwaya daya da aka taskace, ajiyar Allah  da annabi Musdafa (s.a.w) domin kare muslunci da wanzuwarsa da tsayuwarsa       

 «إن كان دين محمّدٍ لم يستقم إلّا بقتلي فيا سيوف خذيني ».

Idan addinin Muhammad ba zai tsayu ba face da kisa na to yaku takubbuna ku far mini.

Sai yaki da fito na fito sai ya kasance cikin ashurar Husaini (as) tsakanin sinfi biyu da rundunoni biyu: sinfin da rundunar Allah wacce take tajalli cikin dan `yar manzon Allah furensa jikansa shugaban shahidai imam Husaini (as) sai sinfi da rundunar shaidanu wacce take misalta cikin yazidu da banu umayya da munafukai a wancan zamani. Na farko daga acikin allah  matsarkaki take, ta biyu acikin shaidan, lallai rundunar farko ta cancan wilaya da aminci, kamar yadda sinfi da runduna ta biyu ta biyu ta cancanci la'ana da bara'a, baki dayan tarihin bil adama un daga lokacin Adamu har zuwa tashin kiyama, ko dai ya kasance cikin rundunar gaskiya saiya cancanci aminci da soyayya, ko kuma dai ya kasance cikin rundunar bata da karya sai ya cancanci la'ana da fushi da barranta.

Lallai ita la'ana take ce na bara'a da barranta kamar yadda muslunci yake taken wilaya kuma shifida da share fagen dukkanin karba da watsarwa kamar yadda yake cikin kalmar tauhidi       

   (لا إله إلّا الله)

Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.

Ya zama dole da fari ayi watsi da duk wani bain bauta sannan ayi imani da Allah matsarkaki, hakama cikin annabta da imamanci, tilas ne ayi watsi da dukkanin mai da'awar annabta da karya kamar misalin musailamatu kazzabu, hakama ayi watsi da halifofin zalunci da farko, da tsine musu da barranta da su, sannan wilaya ga waliyyan Allah da A'immar shiriya:- sabanin wannan cikin rutuba ba cikin zamani ne ba- ranar ashura igiyar sadarwa ce tsakanin ilimin annabta da na wilaya tun daga Adamu har zuwa kan cikamakin annabawa tsakanin al'ummu musulmai har zuw atashin kiyama, na'am yaki ne tsakanin karya da gaskiya tsakanin bata da shiriya, wannan yaki na akida da kason manzanci bazai taba karewa ba har tashin kiyama    

 «يا أبا عبد الله إنّي سلمٌ لمن سالمكم وحربٌ لمن حاربكم إلى يوم القيامة ».

Ya Abu Abdullah lallai ni sallamawa ga mai sallama muku yaki

ga dukkanin wanda ya yake ku har tashin kiyama.[26]

Sannan ita la'ana a luggance tana da ma'anar kora daga rahamar Allah, lallai na farko na farko da aka kora ya kasance jefaffe shi ne iblis, hakan ya kasance lokacin da yaki mika wuya da rusunawa ga Adamu bayan da Allah ya umarceshi da ya yiwa Adamu sujjada, amma sai yaki ya yi girman kai ya kasance daga masu butulci, sai Allah ya la'anceshi ya koreshi daga rahamar Allah sannan ita la'ana tana daga masadik din mummunar addu'a, saboda addu'a ce akai kansa, sannan ita addu'a itace bargon ibada, mabudin dukkanin rabautada tsira, kamar yadda take daga falsafar halittar mutum, lallai ita addu'a kodai ta ksance daga don mutum ko kuka akan mutum, ga misalin waliyin Allah addu'a na kasancewa don shi, amma ga makiyin Allah tana kasancewa akanshi.

Lallai shi mumini yana kusantar Allah cikin kowanne yanayi da addu'a, wani lokacin ana addu'a don muminai maza da muminai mata, wani karon kuma ana addu'a kan azzalumai da dagutai, daga cikin la'ana akwai fadimu (Allah ka la'anci shimru) ma'ana ka nesanta sakamakon abin da ya aikata daga zalunci da danniya cikin rayuwarsa.

Sannan la'ana cikin kissar ashura ta Husanini (as) bata kebanta da halartar karbala da yakar shugaban shihidai imam Husaini (as) barti dai dukkanin mutanen da suka assasa asasin zalunci da danniya ga dukkanin wadannan mutane da suka yake shi sukai tarayya cikin yakin suka bi kan kashe shi kai da dukkanin wanda ya yarda da kisan da akai masa a aikace da biyayyarsa ga halifofin zalunci jagororin bata tsawon tarihin muslunci daga bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) har zuwa zamaninmu da ma wanda zai zo nan gaba         

 (يَوْمَ نَدْعُو كُلَّ اُنَاسٍ بِإمَامِهِمْ ) .

Ranar da zamu kira kowanne mutane da jagoransu.

Bai buya ba cewa lallaiabin da ya faru raar ashura cikin filin karbala daga kisa da dauri da musibu da bala'o'i, kadai dai ya faru ne sakamakon shimfida da mukaddima guda biyu- kamar yadda ya zo cikin ziyarar ashura madawwamiya- za muyi istibadin munafunci da gafala da al'umma ta kasance ciki    

(كَالأنْعَامِ بَلْ هُمْ أضَلُّ ).

Kamar dabbobi bari dai sunfi dabbobi bata.[27]

 ta farko:

لعن الله اُمّةً أسّست أساس الظلم والجور عليكم أهل البيت .

Allah ya la'anci al'ummar da ta assasa asasin tsuhen zalunci da danniya kanku Ahlil-baiti.[28]

 

Na biyu:

ولعن الله اُمّةً دفعتكم وأزالتكم عن مراتبكم التي رتّبكم الله فيها.

والنتيجة : ولعن الله اُمّةً قتلتكم (بل ) ولعن الله الممهّدين لهم بالتمكين من قتالكم .

Allah ya la'anci al'ummar da ta turekuda suka kwabeku daga martabobinku wadanda Allah ya sanyaku cikin su, natija shi ne: Allah ya la'anci al'ummar data kasheku bari dai hatta wadanda suka shimfida musu damar kisanku.[29]

Lallai halifofin zalunci da danniya sun saukake hanyar kisan

 imam tun ranar farko kamar sayyada Zainab kubra (as) tayi ishara zuwa ga hakan,saboda haka wajibi kan dukkanin wani mumini wanda ya yi imani da sakon da aka aikowa manzon Allah (s.a.w) dole ya barranata daga wadanda suka assasa zaluntar Ahlil-baiti (as) ya kuma la'ancesu kan mikewar tarihi, lallai la'ana take ne na barranta daga makiya Allah, sannan kuma ya mika wilayarsa ga waliyyan Allah ya yi salati ya sallama musu sallamawa, lallai salati da sallamawa take ne na wilaya ga waliyyan Allah, wannan sabani na rutuba kadai dai yana tajalli da dukkanin bayyana cikin ziyarar ashura, lallai yadda al'amarin yake shi ne an gabatar da bara'a da la'ana a kan wilaya.

Sannan magana ta biyu shi ne ya kasance mumini ya yi kwalliya da kyawawan halaye da kubuta da nesanta alfasha, da kuma nesanta daga munanan dabi'u da miyagun zunubai kamar yadda yake a ilimin Akhlak lallai marhalolin tsaftace zuciya uku ne: wofinta, kwalliya, tajalli.

Lallai ashura husainiyya kulasar tarihin bil adama ce, lallai shi al'amarin ashura na habbaka da sabunta cikin kowanne zamani da kasa da abin da ya dace tare da zamani da wuri daga abubuwan da suke bayyana bakin ciki da radadi da girman musiba da bala'i da ibtila', sai dai cewa karajin kowa da daga sautinsu ya kasance tsawon tarihi, lallai samuwar kowa da kowa da dukkanin samuwa na shela da daga sauti da karaji da fadin:     

 (يا حسين )...

Ya Husain.

Allah ka shaida lallai mu muna tare da shugaban shahidai imam Husaini (as) a akidance da tunani da suluki da jihadi da take da jinmu da wilaya da fansar da kwukanmu. Muna raya bukukuwan makoki muna jimami tare da musibar da sameshi cikin maukibanmu da dukkanin abubuwan da suke bayyana bakin ciki da musiba cikin dukkanin watannin muharram da safar cikin kowacce shekara, na'am tabbas soyayyar imam Husaini (as) ta haukatamu, lallai takenmu tare da waliyinsa da mai neman fansar jininsa imaminmu Muntazar Hujja na goma sha biyu (as)    

(يا لثارات الحسين )

Ya dauki ga masu neman fansar jinin Husaini.

Ya dauki ga masu nema fansar jinin `ya`yan Husaini da sahabban Husaini, ya fansar mahaifiyarsa Fadima Zahara siddika shahida mai hakuri.

Da sannu wadanda suka zalunci iyalan Muhammad zasu san wacce makoma zasu koma kyakkyawar makoma tana ga masu jin tsoran Allah, maganarmu ta karshe dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai


 [1] Na yi bayani filla-filla kan haka cikin littafin fatima zahara sirril wujud da littafin fatima lailatul kadari da littafin isma bi nazra jadida

[2] Mafatihul jinan:116

[3] Mafatihul jinan:117

[4] Mafatihul jinan:118

[5]Mafatihul jinan:118

[6]120 Mafatihul jinan:

[7] Mafatihul jinan:121

[8] Mafatihul jinan:121

[9]

[10] Abasa:24

[11] Mafatihul jinan:117

Jinan: 117[12] mafatihul

[13] Mulk:2

[14] Insan:3

[15] A'araf:54

[16] Mafathul jinan Abbas kummi.

[17] Fussilat:30

[18] Furkan:77

[19] Zariyar:56

[20] Ma'ida:27

[21] Fadir:10

[22] Alfajar:30

[23] Bakara:257

[24] An'am:121

[25] Mafatihul jinan:667

[26] Mafatihul jinan:665

[27] A'araf:179

[28] Mafatihul jinan:665

[29] Mafatihu jinan:666