MARUFINSA ALMISKI

 

 

 Madalla da abin dazan rufe littafina in hattama shi da abin damasanin Allah Arifi muhakkik Ayatollah mirza Jawad Maliki ya kawo cikin littafins amai kima mai suna (Almurakabat fi a'amal wa murakabat shahrul jimada sani) inda yake cewa: cikin rana ta uku shugabar matan duniya amincin Allah ya kara tabbata gare ta ta yi wafati, bari ingantacciya magana shi ne a wannan rana ne tayi shahada lallai ita amincin Allah ya kara tabbata gare ta ta bar duniya tana abar zalunta wacce aka kwace mata hakkinta, saboda haka ya kamata `yan shi'arta daga masu cika alkawari sun girmama wannan rana da take daga ranaku bakin ciki da musibu, lallai ranarta ta kasance dayan biyun ga ranar manzon Allah (s.a.w)  Ahlinta basu ga wata rana mafi tsanani ga sarkin muminai Ali (as) bayan wafatin manzon Allah (s.a.w) mafi tsananin musiba da bala'i da bakin ciki ba daga ranar da ta yi shahada, ta yadda cikin wannan rana ta uku ga jimada sani wani babban al'amari ya faru daga kunan zuciya da bakin ciki da sanya  sarkin muminai Ali (as) yana waken bakin ciki da kuka da kokawa kan rabuwa da ita yana mai fadin:

 

نفسي على زفراتها محبوسةٌ         يا ليتها خرجت مع الزَّفراتِ

لا خير بعدک في الحياة وإنّما         أبكي مخافة أن تطول حياتي

Na kunshe da tsare raina da zuciyata daga shashshkar kukan bakin cikin rashinta* inama dai raiana ya fita tare da shashshakar kukan bakin cikin.

Babu alheri bayan rashinki cikin rayuwa* kadai dai ina kuka don tsoro da gudun kada rayuwata ta tsawaita bayan rashinki.

 

Hakama an rawaito daga gare shi cewa shi ya raira wasu baitukan wakn jaje da bakin ciki rashinta daga jumlar wake akwai wannan baituka da zasu a kasa:  

وإنّ افتقادي فاطمآ بعد أحمدٍ         دليلٌ على أن لا يدوم خليلُ

وكيف هنأک العيش من بعد فقدهم         لعمرک شيء ما إليه سبيلُ

يريد الفتى أن لا يموت خليله         وليس إلى ما يبتغيه سبيلُ

Lallai rashin da nayi na Fadima bayan na rasa Ahmad* dalili kan cewa masoyi bai dawwama* ta kaka rayuwar zatai dadi baya rashinsuna rantse da mai rayaka wannan wani abu ne da babu tafarki zuwa gare shi* saurayi na son kada ace abokinsa masoyinsa ya mutu* sai dai cewa babu tafarki zuw aga abin dayake nema.

 

Na ranste da wanda rayuwata ke hannunsa lallai wannan wakoki da tare da abin damuka tattaro ambatonsa daga wakensa da zubensa cikin wancan al'amari mai girma daga sarkin muminai Ali (as) yana buga hankali da gigita shi da yaye girman mukaminta da falalarta wajen Allah lallai rakinsa da bakin cikin sa cikin wannan rashi tare da kasantuwarsa cikin hakuri da juriya kamar misalin dogon dutse yake da guguwa ba ta iya motsa shi, hare-hare basu gusar da shi, daga shin ruwa ke gangara, babu wani mai tashi da zai iya kaiwa gare shi, wannan na daga mafi ban mamakn mamaki, ta kaka hakan zai kasantu kuwa bada ban darajar ta kai wani matsayi da daukaka ba da gigita ke kyawuntacikin sha'anin rashinta lallai da sarkin muminai Ali (as) bai kasance yana bayyana wanna gigita da firgita ba mai girma. Ko yaya ma dai ya kasance to wajibi kan shi'arta su kwaikwayi sarkin muminai Ali (as) cikin bayyana bakin ciki da damuwa, da raya bukukuwan zaman makokin shahadarta da karanta musibun da suka sameta, lallai ita dayan babanta ce masoyiyarsa wacce ya kasance yana yi mata mu'amalar da bai yin irinta ga kowa daga mutane.

Hakika wanda muka dace dashi da wanda muka saba duk sun rawaito fadinsa (s.a.w)  

«فاطمة بضعةٌ منّي من آذاها فقد آذاني »

Fadima tsoka ce daga gare ni duk wanda ya cutar da ita tabbas ya cutar dani.

Da wannan ta kafa hujja lokacin wafatinta kan na farko da na biyu bayan ta karbi ikirari daga gare su su biyun kan cewa su sunji wannan hadisi daga manzon Allah (s.a.w) sai tace alhalin tana mai daga hannunta zuwa sama:

    «اللهمّ اشهد أنّهما آذياني »

Ya Allah ka yi shaida lallai su sun cutar dani.

Sannan tayi wasiyya ga mijinta Ali (as) da cewa ya boye binneta da kabarinta daga gare su.

 

Na rantse da mai rayani lallai wannan wasiyya wacce take daga gare ta amincin Allah ya kara tabbata gare ta mujahada ce da taimakon addnin Allah addnin gaskiya it ace mafi amfanarwa cikin tabbatar mazhabar shi'a da rusa mazhabar mutane gama gari, daga dukkanin aya da hujja ta kaka za ace kabarinta ya buya an kuma boye binneta wannan al'amari da tambaya ba zasu taba buya ba tsawon zamani har abada, duk sa'ilin da ka tambayi dalili kan haka, sannan ya bayyana kan lallai cewa hakan ya faru ne sakamakon wasiyyarta, gaskiya zata bayyana karara lallai ita ta bar duniya tana fushi da shehunai biyu kamar misalin bayyanar  rana lokacin take tsakiyayini, ta hadu da babanta da shugabanta tana mai kai kararsu wajensa, hakan na lazimta musu munana da babu wani munana samanta, musammam ma da la'akari da abin da Allah ya saukar cikin littafinsa mai girma:

 

(قُلْ لا أسْألُكُمْ عَلَيْهِ أجْرآ إلاَّ المَوَدَّةَ فِي القُرْبَى ) .

Kace bana tambayarku wani lada face soyayya cikin makusanta.[1]

 

 Karfafawa ga wannan shi ne hukunci da fadinsa:

 (قُلْ مَا سَألْـتُكُمْ مِنْ أجْرٍ فَهُوَ لَكُمْ ) .

Kace abin dana tambayeku daga lada shi gare ku yake.[2]

 Manzon Allah (s.a.w) ya bar duniya babu wani mutum a ban kasa mafi kusanci da shi daga Fadima amincin Allah ya kara tabbata gare ta.

Ta kaka mutum mai hankali zai shakku cikin cewa lallai wanda ya ha'inci manzon Allah (s.a.w) cikin ladan sakon da ya kawo lallai bai dace da ya kasance amintacce ba cikin halifancinsa, lallai wanda bai kiyaye alfarmarsa ba cikin makusantansa ta kaka zai kiyaye cikin wanda suke nesa da shi, duk wanda ya zalunceshi cikin`yarsa ta kaka zai masa adalci cikin al'ummarsa? Wannan al'amari jahili da malami ya san shi, kebantacceda gama gari kowa ya sani musammam ma Fadima amincin Allah ya kara tgabbata gare ta cikin sha'aninta ayar tadhir ta sauka da ijma'in bangarori biyu sunna da shi'a, da gasgatawar jama'a daga manya-manyan malaman tafsiri Ahlus-sunna da sauran malamansu.

Ba zai yiwu ga wanda ya zalunce ta ya kwace mata hakkinta ya ce zai bada uzuri kan yin hakan da wata fuska ta shari'a bayan gasgatawar kur'ani ya yi kan tsarkakarta da wajabcin sonta da kaunarta.

Ya ku mutane cikin duniya ku yi kuka kan wannan yankewa mai radadi mai tsananin muni dangane manzon Allah mai karamci mafi karamci annabi ai tausayi da jin kai cikin zaluncin da akai kan tsokar jikinsa tsarakakka, `yarsa mai tsarki wacce suka kwace mata hakkinta, suka kwace dukiyarta suka hanata gadon babanta, suka mari fuskarta, suka kashe jaririnta da take dauke da shi a cikin ta daidai lokacin da likkafanin manzon Allah (s.a.w) bai gushe ba yana cikin sabuntarsa, suka ce akawo musu wuta domin su kona kofar gidanta wacce Mala'iku makusanta suka tsaya bakinta domin neman izini shiga.

Koma ya ta kasance to wajibi kan shi'a su yi mu'amala tare da ita amincin Allah ya kara tabbata gare ta cikin wannan arana daga karin salati har sai manzon Allah (s.a.w) ya gamsu ubangijin Fadima batula amincin Allah ya kara tabbata gare ta ya yarda, hakkin shi'anci ya lazimcesu.

Ranar ashirin daga wannan watan ne ranar haihuwarta amincin Allah ya kara tabbata gare ta-bisa dogaro da riwayar shaik Mufid Allah ya kara yarda da shi ya ce:

Ranar ashirin ga watan jima sani dfaga cikin sa aka haifi sayyada Fadima Zahara amincin Allah ya kara tabbata gare ta shekaru biyu bayan aiko annabi (s.a.w) rana ce mai daraja farin cikin muminai yana sabunta, sannan mustahabbi ne yin azumi a wannan rana da kuma yin tadawwu'I da alheri da sadaka.

Ina cewa: ana kaddara girmama wannan rana gwargwadon girman darajarta wajen Allah girmansa ya girmama, da wajen Mala'iku tsarkaka, da waliyyan Allah, lallai ya zo cikin ingantattun hadisai cewa lallai shugabar matayen duniya na kowanne zamani itace Fadima, sannan Maryam amincin Allah ya kara tabbata gare ta ita shugabar matan duniya ce a zamaninta, da wannan shugabancin Fadima siddika da gasgatawar kur'ani mai girma ya tabbata kan Maryam (as) , bari ma dai ya yanke da cewa lallai itace mafi darajar daga sauran annabawa da manzanni, na rantse da mai rayani lallai wannan ne falala mabayyaniya.    Daga jumlar abin daya zo garemu ta yankakkiyar hanya ingantacciya daga falalarta wacce ta kebanta da ita kan dukkanin matayen duniya shi ne cewa lallai tana da wani littafi mai girma da jibrilu ya zo mata da shi bayan wafatin annabi (s.a.w) sarkin muminai Ali (as) ya rubuta shi littafin yana hannun `ya`yanta ma'asumai, cikin sa akwai ilimin abin daya kasance da wanda zai kasance nan gaba da abin dake kasancewa kamar yadda cikin riwayar sikatul isla kulaini daga Sadik (as).

A jumlace dai mai sabani da mai dacewa cikin ra'ayinmu sun rawaito hadisai masu tarin yawa kan falalarta  wadanda zasu iya cika manya-manyan mujalladan litattafai, wannan dan takaitaccen littafi ba zai iya tattaro su, sai dai cewa cikin abin da muka ambata akwai isarwa              

 (لِمَنْ كَانَ لَهُ قَلْبٌ أوْ ألْقَى السَّمْعَ وَهُوَ شَهِيدٌ)

Ga wanda gare shi akwai zuciya ya gaza kunne alhalin yana shaida.[3]

Da bai kasance daga falalolinta ba face abin daya zo daga cetonta ga masoyanta da masoyan zuriyarta da shi kadai ya isar ga shi'a hujja cikin tabbatar girmamata da girmama ranar haihuwarta gwargwadon karfi da iko, bayan hakan da ikirarin takaitawa cikin girmamata, lallai asu ba'arin hakkokin ba a iya saukesu duk inda mautum yakai ga kokainsa, daga muhimman ayyuka cikin wannan rana ta haihuwarta amincin Allah ya tabbata gare ta shi ne la'antar wadanda suka zalunceta , ana hattama wannan rana da misalin abin da ake hattamawa cikin misalsalanta


[1] Shura:23

[2] Saba'i:47

Kaf:37