فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Tafsirin riwaya

 

Dukkanin abin da muka ambata daga tafsirin aya mai daraja mun ambace shi ne tare da kiyaye takaitawa da rashin tsawaitawa, amma abin da aka ambata cikin tawilin ayar da dabbakata da bayanin cikin cikakaken masadik cikin abubuwan da take gasgatuwa, zamu tsinkaye shi karkashin bijiro da jumlar riwayoyi masu daraja, da sannu zamu kai ga hakika mai huda, ba komai bace sai cewa lallai wannan aya cikin badininta  tana nuni ya zuwa kebanta zuwa ga ma'asumai goma has hudu amincin Allah ya kara tabbata gare su: sune haskaye da suke kewaye da al'arshin ubangiji, sune Fadima da mahaifinta annabi da mijinta wasiyyi da `ya`yanta A'imma goma sha daya[1]

 

1 ـ في تفسير القمّي بإسناده عن طلحة بن زيد، عن الإمام جعفر بن محمّد،

عن أبيه الباقر  8 في هذه الآية (اللهُ نورُ السَّمَاوَاتِ وَالأرْضِ ) قال : بدء بنور نفسه (مَثَلُ نُورِهِ ) مثل هداه في قلب المؤمن (كَمِشْكَاةٍ فِيهَا مِصْبَاحٌ ) والمصباح جوف المؤمن والقنديل في قلبه ، والمصباح النور الذي جعله في قلبه . (يُوقَدُ مِنْ شَجَرَةٍ مُبَارَكَةٍ ) قال : الشجرة المؤمن (زَيْتُونَةٍ لا شَرْقِيَّةٍ وَلا غَرْبِيَّةٍ ) قال : على سواد الجبل لا غربيّة أي لا شرق لها، ولا شرقيّة أي لا غرب لها إذا طلعت الشمس طلعت عليها، وإذا غربت غربت عليها (يَكَادُ زَيْتُهَا يُضِيءُ) يكاد النور الذي في قلبه يضيء وإن لم يتكلّم (نُورٌ عَلَى نُورٍ) فريضة على فريضة ، وسنّة على سنّة (يَهْدِي اللهُ لِنُورِهِ مَنْ يَشَاءُ) يهدي الله لفرائضه وسننه من يشاء (وَيَضْرِبُ اللهُ الأمْثَالَ لِلنَّاسِ )، فهذا مثل ضربه الله للمؤمن . ثمّ قال : فالمؤمن يتقلّب في خمسة من النور: مدخله نور، ومخرجه نور، وعلمه نور، وكلامه نور، ومسيره يوم القيامة إلى الجنّة نور، قلت لجعفر  7: إنّهم يقولون : مثل نور الربّ ، قال : سبحان الله ليس لله مثل قال الله: (فَلا تَضْرِبُوا للهِ الأمْثَالَ )  .

1-daga tafsirin Aliyu bn Ibrahim bn Hashim alkummi da isnadinsa daga dalhatu bn Zaidu daga imam Jafar bn Muhammad daga babansa imam Bakir (as) cikin wannan ayar (Allah hasken sammai da kasa) sai ya ce: Allah ya fara da hasken zatinsa (misalin haskensa) shiriyarsa cikin zuciyar mumini (kamar misalin taga ce da cikin ta akwai fitila) cikin muminai fitila sannan cikin zuciyarsa kuma akwai fitilar aci balbal. Sannan ita misbahu haske ne da Allah ya ajiye cikin zuciyar mumini (ana kunna shi daga bishiya mai albarka) ya ce: mumini shi ne bishiyar (zaituna ba bagabashiya b ace ba kuma bayammaciya bace) ya ce: kan bakantar dutse ba bayammaciya ai ba ta da gabas, ba bagabashiya bace ai ba ta da yamma, idan rana ta huda sai ta huda kanta inda zat fadi sai ta fadi kanta (manta yaku haskaka) ai hasken da ake cikin zuciyar mumini ya kusa haskaka ko da kuwa bai magana ba (haske kan haske) farilla kan farilla sunna kan sunna (Allah yana shiryar da wanda ya so zuwa ga haskensa) ai yana shiryar da wanda ya so zuwa ga farillansa da sunnoninsa (Allah yana buga misalai ga mutane) ai wannan misali yana buga ga mumini, sannan imam ya ce: mumini yana jujjuyawa cikin haskaye biyar: mashigarsa haske, mafitarsa haske, lliminsa hasake, maganarsa haske, hanyarsa ranar kiyama wacce zai shiga aljanna haske, sai na cewa Jafar (as) lallai su suna cewa misalin hasken ubangiji, Allah matsarkaki ya ce: babu wani misali ga Allah (kada ku bugawa Allah misalai)

Allama dabadaba'I ya ce: wannan hadisi na karfafa abin daya gabata daga cikin tafsirin ayar, hakika ya isar ya wadatar cikin tafsirin ba'arin wasu fakarorin ayar ta hanyar aambato wasu ba'arin misdakai kamar misalin wanda ya ambata cikin karshen ayar (manta ya kusa haskawa) da fadinsa madaukaki (haske kan haske)

2-Ya zo cikin kitabul tauhid na shaik Saduk da isnadinsa: na rawaito daga imam Sadik (as)

أنّه سئل عن قوله الله عزّ وجلّ : (اللهُ نورُ السَّمَاوَاتِ وَالأرْضِ مَثَلُ نُورِهِ كَمِشْكَاةٍ فِيهَا مِصْبَاحٌ )، فقال : هو مثل ضربه الله لنا، فالنبيّ والأئمة صلوات الله عليهم من دلالات الله وآياته التي يهتدي بها إلى التوحيد ومصالح الدين وشرائع الإسلام والسنن والفرائض ، ولا قوّة إلّا بالله العليّ العظيم

Lallai an tambayi imam sadik (as) dangane da fadin Allah Azza wa Jalla: (Allah hasken sammai da kasa misalin haskensa kamar taga cikin akwai fitila) sai imam ya ce: misali ne da Allah ya buga shi garemu, annabi da A'imma amincin Allah ya kara tabbata gare su suna daga alamomin Allah da ayoyinsa wadanda aake shiriya da su zuwa ga tauhidi da maslahohin addini da shari'ao'in muslunci da sunnoni da farillai, babu tsimi babu dabara face da Allah madaukaki mai girma.

Allama dabadaba'i yana cewa: wannan riwaya tana daga fusaknin ishara zuwa ga ba'arihn misdakai wanda sune annabi (s.a.w) da tsarkaka daga mutanen gidansa, idan bahaka ba to fa lallai zahirin ayar na tattaro wanda ba daga cikin su suke ba daga annabawa da wasiyyai da waliyyan Allah.

Na'am ayar ba ta gamo dukkanin muminai ba da har za a riketa cikin siffanta su, lallai ba ta tattaro dukkaninsu sakamakon fadinsa matsarkaki:      

 (رِجَالٌ لا تُلْهِيهِمْ تِجَارَةٌ وَلا بَيْعٌ عَنْ ذِكْرِ اللهِ)

Mazaje ne da kasuwanci da saye da sayarwa basa shagaltar da su daga barin ambaton Allah)[2]

Har zuwa karshen ayar.

Lallai wasu adadin hadisai sun zo daga hanyar shi'a cikin dabbakuwa mufradat din ayar kan annabi (s.a.w) da Ahlin gidansa (as): su riwayoyin cikin dabbakawa ba tafsiri ba, daga cikin dalili kan hakan sassabawarsu ta fuskanin dabbakawa kamar riwayar cikin raudatul kafi.

 

3 ـ الكافي بإسناده عن جابر عن أبي جعفر  7 وفيها: أنّ المشكاة قلب محمّد  9 والمصباح النور الذي فيه العلم ، والزجاجة علي أو قلبه ، والشجرة المباركة الزيتونة التي لا شرقيّة ولا غربيّة إبراهيم  7 ما كان يهوديّآ ولا نصرانيّآ، وقوله (يَكَادُ زَيْتُهَا يُضِيءُ) إلخ : يكاد أولادهم أن يتكلّموا بالنبوّة ، وإن لم ينزل عليهم ملک .

Alkafi da isnadinsa daga jabir daga Abu Jafar (as) cikin ta: lallai mishkatu zuciyar Muhammad (s.a.w) sannan kuma ita misbahu hasken da cikin sa akwai ilimi, zujajatu shi ne Ali ko dai zuciyarsa, shajara bishiya mai albarka wacce ba bagabashiya ba ba kuma bayammaciya ba shi ne Ibrahim (as) bai kasance bayahude bai kuma kasance banasare ba, fadinsa (manta ya kusa haskuwa) zuwa karshen ayar na nufin `ya`yan Ibrahim sun kusa su yimagana da annabta duk da cewa mala'ika bai sauka gare su ba.

4 ـ تفسير نور الثقلين بإسناده إلى يعقوب بن سالم عن رجل عن أبي جعفر  7 حديث طويل وفيه أنّ الله تعالى بعث أهل البيت  : بعد وفاة النبيّ من يعزّيهم فسمعوا صوته ولم يروا شخصه ، فكان في تعزيته : جعلكم أهل بيت نبيّه ، واستودعكم علمه ، وأورثكم كتابه ، وجعلكم تابوت علمه وعصى غرّه ، وضرب لكم مثلا من نوره .

4-daga tafsirin nurul saklaini da isandinsa zuwa ga Yakub bn Salim daga wani mutum daga Jafar (as) hadisi mai tsayin gaske wanda cikin sa ya zo cewa: Allah ya aikowa Ahlil baiti bayan wafatin annabi (s.a.w) wanda zai musu ta'aziyya sai sukaji sautinsa basu ganshi ba, ya kasance cikin ta'aziyyarsa yana fadin:, ya Allah ya sanya ku Ahlin gidan annabinsa, ya ajiye ilimsa cikin ku, ya gadar muku da littafinsa, ya sanya ku akwatin

 

5 ـ عن الفضيل بن يسار قال : قلت لأبي عبد الله  7: (اللهُ نُورُ السَّمَوَاتِ وَالأرْضِ ) قال : كذلک الله عزّ وجلّ ، قال : قلت : (مَثَلُ نُورِهِ ) قال  : محمّد  9. قلت : (كَمِشْكَاةٍ ) قال : صدر محمّد  9. قلت : (فِيهَا مِصْبَاحٌ ) قال : نور العلم يعني النبوّة ، قلت : (المِصْبَاحُ فِي زُجَاجَةٍ )، قال : علم رسول الله  9 إلى قلب عليّ  7. قلت : (كَأنَّهَا كَوْكَبٌ دُرِّيٌّ) قال : لأي شيء تقرأ كأنّها؟ قلت : فكيف جعلت فداک ؟ قال : (كأنّه ) قلت : (يُوقَدُ مِنْ شَجَرَةٍ مُبَارَكَةٍ زَيْتُونَةٍ لا شَرْقِيَّةٍ وَلا غَرْبِيَّةٍ ) قال : ذاک أمير المؤمنين عليّ بن أبي طالب  7 لا يهودي ولا نصراني . قلت : (يَكَادُ زَيْتُهَا يُضِيءُ وَلَوْ لَمْ تَمْسَسْهُ نَارٌ) قال : يكاد العلم يخرج من فم العالم من آل محمّد من قبل أن ينطق به ، قلت  : (نُورٌ عَلَى نُورٍ) قال : الإمام في أثر الإمام .

An karbo daga Fuzailu bn yasar ya ce: na cewa Abu Abdullah (as) : (Allah hasken sammai da kasa) sai ya ce: haka nan Allah mai girma da daukaka yake, sai na ce (misalin haskensa) sai ya ce: Muhammad (s.a.w), sai na ce: (fitila cikin kwalaba) sai ya ce: ilimin manzon Allah (s.a.w) zuwa ga zuciyar Ali (as) sai na ce (kai kace tauraro mai tsananin haske) sai ya ce: yaya kake karanta kai kace? Sai na ce: raina fansarka ya ya ake karantawa yake? Ya ce: kai kace shi, sai na ce (ana kunna shi daga bishiya mai albarka zaituna ba bagabashiya bace ba kuma bayammaciya bace) wannan ai sarkin muminai Ali bn Abu dalib (as) ba yahude bane ba kuma banasare bane, sai na ce: (manta ya kusa haskuwa koma wuta bata taba shi ba) ya ce: ilimi ya kusa fita daga bakin malami daga gidan iyalan Muhammad gabanin furta shi, sai na ce: (hasken kan haske)[3] ya ce imami kan sawun imami.    

6 ـ وبإسناده إلى عيسى بن راشد عن محمّد بن علي بن الحسين  : في قوله عزّ وجلّ : (كَمِشْكَاةٍ فِيهَا مِصْبَاحٌ ) قال : المشكاة نور العلم في صدر النبيّ  9 (المِصْبَاحُ فِي زُجَاجَةٍ ) الزجاجة صدر عليّ  7 صار علم النبيّ إلى صدر عليّ، علّم النبيّ عليّآ  7 (الزُّجَاجَةُ كَأنَّهَا كَوْكَبٌ دُرِّيٌّ يُوقَدُ مِنْ شَجَرَةٍ مُبَارَكَةٍ ) قال : نور العلم (لا شَرْقِيَّةٍ وَلا غَرْبِيَّةٍ ) قال : لا يهوديّة ولا نصرانيّة (يَكَادُ زَيْتُهَا يُضِيءُ وَلَوْ لَمْ تَمْسَسْهُ نَارٌ) قال : يكاد العالم من آل محمّد يتكلّم بالعلم قبل أن يسأل (نُورٌ عَلَى نُورٍ) يعني إمامآ مؤيّدآ بنور العلم والحكمة في أثر الإمام من آل محمّد، وذلک من لدن آدم إلى أن تقوم الساعة فهؤلاء الأوصياء الذين جعلهم الله عزّ وجلّ خلفاء في أرضه وحججه على خلقه ، لا تخلو الأرض في كلّ عصر من واحد منهم .

6-da isnadinsa zuwa Isa bn Rashid daga Muhammad bn Aliyu bn Husaini: cikin fadinsa wanda ya buwaya daukaka: (kamar taga ckin akwai fitila)[4] ya ce: mishkatu hasken ilimi ne cikin kirjin annabi, wanda annabi ya koyar da Ali (as) shi (kwalaba kai kace ita tauraro ne mai tsananin haske ana kunna shi daga bishiya mai albarka)[5] ya ce: hasken ilimi (ba bagabashiya bace ba kuma ba yammaciya bace) ba  bayahudiya ba, ba kuma banasariya ba, (manta ya kusa haskawa koma wuta ba ta shafe shi ba)[6] ya ce: malami daga iyalan Muhammad ya kusa magana gabanin tambayarsa, (haske kan haske)[7] ya ce: imami wanda ake karfafa da haske da hikima cikin sawun imami daga iyalan Muhammad, tun daga lokacin Adamu har zuwa tashin kiyama, wadannan wasiyyai ne da Allah ya sanya su halifofi hujjojnsa kan halittu, kasa a kowanne zamani bata wofinta da daya daga cikin su.  

7 ـ وبإسناده إلى جابر بن يزيد عن أبي جعفر  7 في قول الله عزّ وجلّ  : (اللهُ نورُ السَّمَاوَاتِ وَالأرْضِ مَثَلُ نُورِهِ كَمِشْكَاةٍ ) فالمشكاة صدر النبيّ  9 (فِيهَا مِصْبَاحٌ ) والمصباح هو العلم (فِي زُجَاجَةٍ ) والزجاجة أمير المؤمنين  7 وعلم نبيّ الله عنده .

Da isnadinsa zuwa ga Jabir bn Yazid daga Abu Jafar (as) cikin fadinsa mabuwayi mai girma (Allah hasken sammai da kasa misalin haskensa kamar taga)[8] mishkat kirjin annabi (s.a.w) (cikin ta akwai fitila)[9] misbahu shi ne ilimi (cikin kwalaba)[10] kwalaba sarkin muminai (as) ilimin annabi na wajensa.

8 ـ في روضة الكافي بسنده عن جابر عن أبي جعفر  7 قال في حديث طويل : ثمّ إنّ رسول الله  9 وضع العلم الذي كان عنده عند الوصي ، وهو قول الله عزّ وجلّ : (اللهُ نورُ السَّمَاوَاتِ وَالأرْضِ ) يقول : أنا هادي السماوات والأرض مثل العلم الذي أعطيته ، ونوري الذي يهتدى به (مثل المشكاة فيها المصباح ) فالمشكاة قلب محمّد  9، والمصباح النور الذي فيه العلم وقوله : (المِصْبَاحُ فِي زُجَاجَةٍ ) يقول : إنّي اُريد أن أقبضک فأجعل الذي عندک عند الوصيّ كما يجعل المصباح في الزجاجة (كَأنَّهَا كَوْكَبٌ دُرِّيٌّ) فأعلمهم فضل الوصيّ (توقد من شجرة مباركة ) فأصل الشجرة المباركة إبراهيم  9 وهو قول الله عزّ وجلّ (رَحْمَةُ اللهِ وَبَرَكَاتُهُ عَلَيْكُمْ أهْلَ البَيْتِ إنَّهُ حَمِيدٌ مَجِيدٌ)[11] ، وهو قول الله عزّ وجلّ : (إنَّ اللهَ اصْطَفَى آدَمَ وَنُوحآ وَآلَ إبْرَاهِيمَ وَآلَ عِمْرَانَ عَلَى

8-daga raudatul kafi daga Jabir daga Abu Jafar (as) cikin wani hadisi mai tsayi ya ce: sannan manzon Allah (s.a.w) ya ajiye dukkanin iliminsa da ya kasance wajensa cikin wasiyyinsa wanda shi ne fadinsa mai girma da daukaka (Allah hasken sammai da kasa) yake cewa: ni ne mai shiryar da sammai da kasa misalin ilimin da aka aa bani, haskena da shi ake shiriya da shi (misalin taga cikin ta akwai fitila) mishkatu ita ce zuciyar Muhammad (s.a.w) sannan fitila shi ne hasken da cikin sa akwai ilimi, sannan fadinsa madaukaki (fitila cikin kwalaba) yana cewa: ni ina son damkarka sai in sanya ilimin da yake wajen wajen wasiyyi kamar yadda ake sanya fitila cikin kwalaba (kai kace shi taurara no mai tsananin haske) sai in sanar da su falalar wasiyyi (ana kunna shi daga bishiya mai albarka) asali bishiya mai albarka shi ne Ibrahim (as) shi ne fadin Allah mai girma da daukaka (rahamar Allah da albarkarsa kanku Ahlil-baiti lallaishi abin yabawa ne mai girma) shi ne fadinsa mai girma da daukaka(lallai Allah ya zabi Adamu da Nuhu da Alu Ibrahim da Alu imrana kan talikai* zuriya sashensu gas ashen Allah mai jinai masani ne) (ba bagashiya ba ba kuma bayammaciya ba) ma'ana ku ba yahudawa bane da za ku yi sallah gabanin magariba, ba kuma nasarsawa bane da za ku yi sallah gabanin hudar rana, alhalin lallai ku kuna kan akidar Ibrahim (as) hakika Allah mai girma da daukaka yana cewa (Ibrahim bai kasance bayahude ba bai kuma kasance banasare ba sai dai cewa ya kasance ya karkata zuwa gaskiya musulmi bai kuma kasance daga masu shirka ba) da kuma fadinsa (manta ya kusa haskuwa koma da wuta ba ta shafe shi) misalin `ya`yanku daga ake haifarsu daga mai da aka matsoshi daga zaitun (manta ya kusa haskaka koma da wuta ba ta shafe shi ba haske kan haske Allah yana shiryar da wanda ya so zuwa ga haskensa) sun kusa magana da annabta duk da cewa mala'ika bai saukar gare su ba.         

9 ـ في أمالي الصدوق ؛ بإسناده إلى الصادق  7 حديث طويل يقول فيه : أنا فرع من فروع الزيتونة ، وقنديل من قناديل بيت النبوّة ، وأديب السفرة وربيب الكرام البررة ، ومصباح من مصابيح المشكاة التي فيها نور النور، وصفو الكلمة الباقية في عقب المصطفين إلى يوم ا

9-daga littafin Amali Saduk, da isnadinsa zuwa Sadik (as) hadisi ne mai tsayi yana cewa: ni reshe ne daga rassan zaituna kuma fitila daga fitilun gidan annabta wanda ya samu adabi hannu jakadun Allah wanda ya samu tarbiya hannun masu daraja da biyayya ga Allah, ni fitila ne daga fitilun mishkatu wacce cikin ta akwai hasken haske, da tacewar kalma cikin tsatson zababbu zuwa ranar kiyama.

10 ـ قال عليّ بن إبراهيم ؛ في قول الله عزّ وجلّ : (اللهُ نورُ السَّمَاوَاتِ وَالأرْضِ ) إلى قوله تعالى : (وَاللهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ ) فإنّه حدّثني أبي عن عبد الله بن جندب قال : كتبت إلى أبي الحسن الرضا صلوات الله عليه أسأله عن تفسير هذه الآية ؟ فكتب إليّ الجواب : أمّا بعد فإنّ محمّدآ  9 كان أمين الله في خلقه ، فلمّا قبض النبيّ كنّا أهل البيت ورثته ، فنحن اُمناء الله في أرضه ،

10-Aliyu bn Ibrahim cikin fadin Allah mai girma da daukaka: (Allah hasken sammai da kasa) zuwa fadinsa (Allah masanin komai ne) ya ce: lallai yadda al'amarin yake shi ne cewa babana ya zantar da ni daga Abdullah bn jundub ya ce: na rubuta wasika zuwa ga Abu Hassan Rida amincin Allah ya kara tabbata gare shi ina tambayarsa gameda tafsiri wannan aya, sai ya rubuto mini amsa: bayan haka lallai Muhammad ya kasance amintaccen Allah kan halittarsa, lokacin da Allah ya karbi ransa sai mu Ahlil-baiti mu ka kasance magadansa, mu ne amintattun Allah cikin kasarsa,   

عندنا علم المنايا والبلايا وأنساب العرب ومولد الإسلام ، وما من فئة تضلّ مائة وتهدي مائة إلّا ونحن نعرف سائقها وقائدها وناعقها، وإنّا لنعرف الرجل إذا رأيناه بحقيقة الإيمان وحقيقة النفاق ، وإنّ شيعتنا لمكتوبون بأسمائهم وأسماء آبائهم ، أخذ الله عزّ وجلّ علينا وعليهم الميثاق ، يردون موردنا ويدخلون مدخلنا، ليس على ملّة الإسلام غيرنا وغيرهم إلى يوم القيامة ،

A wajenmu akwai ilimin mutuwa da bala'o'i da nasabobin larabawa da haihuwar muslunci, babu wata kungiya da zata batar da dari ta shiryar da dari face mu mun san mai korata da jagoranta da mai magana da sunanta, lallai mu tabbas muna sanin mutum idan mun ganshi da hakikar imani da hakikar nifaka, lallai shi'armu tabbas an rubuta su da sunayensu da iyayensu, Allah mai girma da daukaka ya karbi alkawari kanmu da kansu, zasu gangaro magangararmu zasu shiga mashigarmu, babu wanda yake kan akidar muslunci face mu da su har zuwa ranar kiyama,

 نحن الآخذون بحجزة نبيّنا ونبيّنا الآخذ بحجزة ربّنا، والحجزة النور وشيعتنا آخذون بحجزتنا، من فارقنا هلک ومن تبعنا نجى ، والمفارق لنا والجاحد لولايتنا كافر، ومتّبعنا وتابع أوليائنا مؤمن لا يحبّنا كافر ولا يبغضنا مؤمن ، فمن مات وهو يحبّنا كان حقّآ على الله أن يبعثه معنا،

Mu muna rike da taguwar ubangijnmu muna rike da taguwar annabinmu da haske, sannan shi'armu suna rike kunkurunmu, duk wanda ya baramu ya halaka duk wanda ya bimu ya tsira, mai barium da mai jayayyar da wilayarmu kafiri ne, mai binmu mai bin masoyanmu mumini ne, kafiri baya son mu, mumini bai kin mu, duk wanda ya mutu alhalin yana son mu ya kasance hakki kan Allah ya tashe shi tare da mu.   

 نحن نور لمن تبعنا وهدى لمن اهتدى بنا، ومن لم يكن منّا فليس من الإسلام في شيء، بنا فتح الله الدين ، وبنا يختمه ، وبنا أطعمكم عشب الأرض ، وبنا أنزل الله قطر السماء، وبنا آمنكم الله عزّ وجلّ من الغرق في بحركم ، ومن الخسف في برّكم ، وبنا نفعكم الله في حياتكم وفي قبوركم وفي محشركم وعند الصراط وعند الميزان وعند دخولكم الجنان ،

Mu haske ne ga wanda ya bimu shiriya ne ga wanda ya nemi shiriya damu, duk wanda bai kasance daga garemu ba to bai kasance bakin komai a muslunci, damu Allah ya bude addini, da mu kuma zai hattama, damu ne ya ciyar daku tsiran kasa, damu Allah saukar da digon sama, damu Allah mai girma da daukak ya amintar daku daga nustewa cikin tafkinku, damu Allah ya amintar daku daga halaka cikin tangaryar kasarsku, damu Allah ya amfanar daku cikin rayuwarku cikin kaburburanku cikin tashinku daga kabari hakama lokacin katara siradinku da lokacin shigarku aljanna.

 مثلنا في كتاب الله عزّ وجلّ (كمثل المشكاة ) المشكاة في القنديل فنحن المشكاة (فِيهَا مِصْبَاحٌ ) المصباح محمّد  9 (المِصْبَاحُ فِي زُجَاجَةٍ ) من عنصره (الزُّجَاجَةُ كَأنَّهَا كَوْكَبٌ دُرِّيٌّ) (توقد من شجرة مباركة زيتونة لا شرقيّة ولا غربيّة ) لا دعيّة ولا منكرة (يَكَادُ زَيْتُهَا يُضِيءُ وَلَوْ لَمْ تَمْسَسْهُ نَارٌ) القرآن (نُورٌ عَلَى نُورٍ) إمام بعد إمام (يَهْدِي اللهُ لِنُورِهِ مَنْ يَشَاءُ وَيَضْرِبُ اللهُ الأمْثَالَ لِلنَّاسِ وَاللهُ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ ) فالنور عليّ صلوات الله عليه، يهدي لولايتنا من أحبّ ، وحقّ على الله أن يبعث وليّنا مشرقآ وجهه ، منيرآ برهانه ، ظاهرة عند الله حجّته .

Misalinmu cikin littafin Allah mai girma da daukaka (kamar misalin taga ce) taga cikin fitilar kwai, mu ne taga (cikin ta akwai fitila) fitila shi ne Muhammad (s.a.w) (fitila cikin kwalaba) daga cikin sinadarinsa (kwalba kai kace tauraro ne mai tsananin haske) (ana kunna shi daga bishiya mai albarka zaituna ba bagabashiya ba bayammaciya ba) ai ba mara asali ba ba kuma munkira ba (manta ya kusa haskuwa koma da wuta bata shafe shi ba) kur'ani (haske kan haske) imami bayan imami (Allah yana shiryar da wanda ya so ga haskensa kuma Allah yana buga misalai ga mutane Allah masanin komai ne) haske shi ne Ali amincin Allah ya kara tabbata gare shi yana shiryar da wanda zuw aga wilayarmu, hakki ne kan Allah ya tashi masoyinmu fuskarsa na haskakawa, dalilinsa na haskakauwa, hujjarsa na bayyana wajen Allah.

Wannan hadisi yanada tsayi mun ciro mahallin bukata daga cikin sa.


[1] Tafsirul nurul saklaini:m 3 sh 603

[2] Nuru:37

[3] Nuru:35

[4] Nuru:35

[5] Nuru:35

[6] Nuru:35

[7] Nuru:35

[8] Nuru:35

[9] Nuru:35

[10] Nuru:35

[11] ()  النور: 40.