فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها

Daga cikin abubuwa wadanda ayar nuru ta kebantu da su

 

Amma ayatun nuru hakika malaman ilimin sanin haruffa da aufaku da kwararru cikin sha'anin hatimai da Azkaru da wuridai sun ambaci cewa lallai wannan aya ta nuru ta kebanta da wasu sirrika cikin samun biyan bukatada haskakauwar badini da zuciya da kuma tsinnkayar sirrikan halitta, daga kebantattun sirrikan akwai abin da ke datarwa zuwa ga ganin imam zaman (Af) cikin bayyana da mafarki, duk wanda ya yi salati ga Muhammad da iyalansa sau biyar sannan ya karanta ayatun nuru sau goma sha hudu, sannan ya kara yin wani salatin guda biyar, ya mike da hattamawa cikin tsawon kwanaki goma sha hudu, lallai shi zai gana da shugabanmu imamul muntazar hujjatu bn Hassan (as) cikin mafarki ko kuma a bayyane.

Ita wannan ayar mai daraja taa daga abubuwa masu ban mamaki daga kur'ani mai girma.

Daga cikin tawilinta akwai riwayoy masu tarin yawa lallai ita wannan ayar ta kebanta da ma'asumai goma sha hudu: kamar yadda ya zo cikin tafsirin nurul saklaini da tafsirin burhan da tafsirin Aliyu bn Ibrahim bn hashim Alkummi haka daga Biharul-Anwar, hakika mun ambaci wani bangare daga gare ta.