ludufi na farko daga mishkat

 

lallai larabawa saboda kada baki wutar fitila ya kashe ko kuma fitilar kwai, lallai su kan sanya lawajin fitikar cikin kwalaba don ya kareshi daga mutuwa daga iska sannan su sanya ta cikin ramin jcikin bango domin ya haskakae geffa ko kuma gefuna biyu na dakin wanka da dakin sauya kamar yadda mukai bayani a baya, haske a wani lokacin akan kirashi da fitilar kwai a wani lokacin kuma a kira shi da fitila, na farko yafi haske daga na biyu, wanda ya kasance cikin sa akwai haske mai hudowa ta yanda yake korar duhu, a sanya shi a wurin aje fitila daga tasirin haske, lallai shi ana kiransa da fitila, annabi shi ne fitila kamar yadda imam Husaini (as) ya kasance fitila

 
 (حسين منّي وأنا من حسين )

Husaini daga gare ni yake nima daga husaini nake.

Lallai yadda al'amarin yake an rubuta kan al'arshi da koren launi

(إنّ الحسين مصباح الهدى وسفينة النجاة )

Lallai husaini fitilar shiriya ne kuma jirgin tsira ne.

Ya zo cikin ziyara jami'atul kubra an kira da A'imma tsarkaka da sunan fitilun cikin duhu lallaiAllah yahalicce su haskaye ya sanya su a al'arshinsa suna kewaye da ita, babu dare babu duhu cikinsu, bari dai samuwarsu da rayuwarsu na korar dukkanin duhu da baki

 

عن الإمام الصادق  7: والله إنّ أمرنا هذا ـأي الإمامة والولاية ـ أوضح من نور الشمس .

 

An karbo daga imam Sadik (as): wallahi lallai al'amarinmu ma'ana imamanci da wilaya-yafi bayyana daga hasken rana.

Wadannan sune imamai: kadai dai su hasken tsarkaka ne kuma fitilun Allah, duk wanda bai gansu ba to lallai kadai idanunsa nada dundumi, lallai shi makauniyar zuciya ke gare shi kamar misalin wanda bai gana hasken rana sakamakon makantar da ke cikin sa.

Sannan sarkin muminai Ali (as) shi ne kwalabar wannan fitila ta annabta, lallai ita kwalaba daga cikin abin da ta kebantu da su hsine cewa ita tana bada hasken da yake cikin ta tana kuma kare lawajin da yake kunne cikin fitilar daga guguwar iska daga cikin abin da ke janyo bushewar wutar hasken.

Imamanci da halifanci na gaskiya wanda suka misaltu cikin ali da `ya`yansa suna kare mana hanya da addini da muke kai da layin da muke kai na annabta daga karkata da halaka da mutuwar haske da bushewar haskakarsa, tana kuma yada shi cikin duniya kasantuwa duniyar halitta da duniyar shari'a, sannan kwalaba ta biyu da ta cikin fadinsa madaukaki ishara ce zuwa ga imam Hassan mujtaba (as) sannan tauraro haske ishara ce zuwa imam Husaini shugaban shahidai (as) shi kuma mai tsananin haske ishara ce zuwa ga imam Sajjad Aliyu bn Husaini (as) haka dai har zuwa kan fadinsa madaukaki: (Allah yana shiryarwa zuwa haskensa) ma'ana imam Mahadi ka'im daga iyalan Muhammad (wanda ya so) daga bayinsa sannan Allah yana buga misalai ga mutane tsammaninsu sayi tunani sa hankalta.

Lallai shi girmansa ya girmama yana buga misali zuwa ga haskensa kamar mishkat wacce cikin ta akwai fitila, sannan wani karon ya bada labari da cewa wannan mishkat da abin da yake cikin ta daga hasken tsarkaka kadai dai ita tana cikin su wasu gidaje da Allahb ya bada izini a daga sunansa sha'aninta mukaminsu ya daukaka a ambaci sunansa cikinsu, sai matsarkaki ya ce:

 (فِي بُيُوتٍ أذِنَ اللهُ أنْ تُرْفَعَ وَيُذْكَرَ فِيهَا آسْمُهُ )

Cikin wasu gidaje da Allah ya bada izinin daga su kuma a ambaci sunansa cikin su.[1]

Ma'ana hasken Allah kamar mishkat ne da cikin ta akwai fitila yana kasancewa cikin wannan gidaje wadanda Allah ya yi umarni da a daga darajarsu a girmama mazaunansu. Lallai su gidajen annabawa da wasiyyai da malamai nagargaru, lallai daga cikin mafi darajasu gidan muahammad da iyalan Muhammad (as).[1] Nuru:36