Fadima Zahara ruhin annabi

 

Lallai annabi mafi girmama (s.a.w) ya kira fadima Zahara da cewa lallai ita

 (روحي التي بين جَنبَيَّ)

Ruhina wanda yake tsakankanin geffana biyu.

Lallai anyiwa wannan hadisi mai daraja wasu adadin ma'anoni:

Daga ciki shi ne lallai yayin da Allah matsarkaki ya halicci ruhin annabi, lallai shi yadda al'amarin yake bayan haifarta ta fifitu da ilimi da aiki, ma'ana da ilimin ladunni daga Allah matsarkaki da ibada sai ruhin annabi ya hade da ilimi da aiki.

Ita Zahara (as) kadai dai ita ruhin annabi ce wanda yake hade da ilimi da aiki.

Daga ciki: annabi ya kasance yanada geffa biyu: gefan sako da gefan wilayar halitta d ata shari'a, lallai shi yana zartar da haddodin Allah da wilayarsa, zahirinsa annabta badininsa kuma wilaya –kamar yadda ya zo cikin hadisi annabi mai daraja-ita kuma Fadima Zahara (as) itace ruhin annabi wacce ta tattaro sakon sama saukakka da kuma wilayar Allah madaukakiya. Kamar yadda ya zo cikin hadisi mai daraja: lallai ita Fadima an farlanta biyayyarta kan ba dayan halittun Allah daga aljannu da mutane da Mala'iku kai hatta dabbobin daji, a cikin duniyar haske da sinadarai idan Fadima (as) ta bada umarni to wajibi kan dukkanin halittu bin umarninta, lallai yardar Allah na cikin yardarta kamar yadda yardarta na cikin yardar Allah, lallai Allah yana fushi da fushin Fadima yana kuma yarda da yardarta, wannan duk daga wilaya kulliya ta halitta.

Daga ciki: lallai annabi yana fifita da da bangaren malkutiyya da nasutiyya, lallai shi mutum ne sai dai cewa ana yi masa wahayi:       

 (قُلْ إنَّمَا أنَا بَشَرٌ مِثْلُكُمْ يُوحَى إلَيَّ) ،

Kace kadai dai ni mutum ne irinku da ake wahayi zuwa gare ni.[1]

Lallai shi ne tsanin faila tsakanin mahalicci da halittunsa, kunnensa kunne ne mai jin wahayi harshensa harshe ne mai magana zuwa ga mutane, yana tattara duniya malakutiyya da da duniyar nasutiyya, ita kuma Fadima Zahara (as) itace ruhin annabta wanda ya ake tsakanin geffan malakutiyya da nasutiyya.

Itace mishkat ai mai tattarowa wacce ta kasance cikin annabi mafi karamci (s.a.w) in banda annabta.[1] Kahf:110