Muslunci addinin ilimi da aiki

 

Kadai dai muslunci shi addinin illimi da kyawawan ayyuka, da habbaka da cigaba da wayewa da bunkasa, me yafi yawa daga nassoshi masu huda da hujjoji masu yankan shakku daga ayoyi da hadisai masu daraja da suke nassanta wannan al'amura, lallai muslunci mai girma yana kiran masu gamsuwa da shi zuwa ga fahimta da ilimi kamar yadda yake kwadaitar dasu zuwa ga su yiado da siffatunwa da kyawawa dabi'u da halaye nagargaru da siffofi ababan yabawa da dabi'uu masu kyau, bayan sun tsarkake kawukansu, su kuma nesanta samuwarsu daga munanan halaye da miyagun dabi'u.