Sarkin muminai girman fahimta

 

Wata rana daga cikin ranaku anabi (s.a.w) ya nemi Abdullahi bn mas'aud da ya koyar da balaben kauye sabon shiga muslunci kur'ani mai girma, kamar yadda ya koyar da shi suratul zalzal a fadinsa madaukaki: 

 (فَمَنْ يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْرآ يَـرَه ) ،

Dukkanin wanda ya yi aiki gwargwadon kwayar zarra daga alheri zai gani.[1]

Sai balaben kauyen ya ce: wannan ma ya isheni,

Lallai wannan addini yana kira zuwa alheri da kauracewa sharri, sai wannan balaben kauye ya koma wajen mutanensa yaa musulmi nagari, sai annabi (s.a.w) cikin hakkinsa ya ce: ya zo yana bakauye ya koma fakihi.

Sannan fikihu a luggance yanada ma'anar fahimta sannan ita[2] fahimta daidai take da ilimi ko kuma tana lazimtarsa, ana kirnsa kuma da fikihu mafi girma.[3]

Sannan a wajen masana fikihu suna kiran fikihu a isdilahinsu da ciro hukuncin shari'a na rassa daga dalilanta na filla-filla ana kiran wannan da sunan fikihu asgar karamin fikihu, ana kiran na farko da wajibul aini na biyun kuma wajibul kifa'i

Sannan hakika hadisi ya zo daga manzon Allah (s.a.w):

لو كان الفقه رجلا لكان عليّآ  7.

Da ace fikihu fahimtar ilimi ya kasance mutum da ya kasance Ali (as)

Wannan na nufin lallai sarki muminai Ali (as) ya tattaro dukkanin fikihu, lallai farkon fikihu ya kasance daga Adamu (as) sannan ya daga cikin annabawa da wasiyyai da salihai, sai dai cewa an tattara baki dayansa cikin ali (as) kamar yadda hadisin annabi ma daraja ya tabbata da hakan daga sunna da shi'a

من أراد أن ينظر إلى آدم في علمه وإلى نوحه في حلمه ...ـ. فلينظر إلى عليّ بن أبي طالب  7.

Dukkanin mai son ganin Adamu cikin iliminsa da Nuhu cikin hakurinsa .…. to ya kalli Ali bn Abu dalib (as)

Hakika shi ya tattaro baki dayan siffofin annabawa da iliminsu da saninsu ya kuma jikkantu da fikihul Akbar da fikihul Asgar.

Ya zo cikin hadisin annabi mai daraja:

ولولا عليّ لم يكن لفاطمة الزهراء كفؤ،

Ba da ban samuwar Ali ba da Fadima ba ta da tsara daga banu Adam koma bayansa.

Lallai iatce tsaransa wacce take daidaita da shi cikin falala da siffofi nagari.


[1] Zalzal:7

[2] Tafsirul burhan m 1 sh 253

An buga cikin masu'atul risaltul islamiyya cikin mujalldi na bakwai[3] Nayi bayani filla-filla cikin risalar Fatima zahara lailatul kadari