dalilai na fadimiyya wadanda muka kafa hujja da su kan halifacin sarkin muminai Ali

dalilai na fadimiyya wadanda muka kafa hujja da su kan halifacin sarkin muminai Ali (as) ba tare da yankewa ga manzon Allah (s.a.w) hadisin annabi mutawatiri daga bangarori biyu shi'a da sunna

قال رسول الله  9: من مات ولم يعرف إمام زمانه مات ميتةً جاهليّة ، ميتة كفر ونفاق ،

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: duk wanda yam utu bai san imamin zamaninsa bay a mutu mutuwar jahiliya, mutuwar kafirci da munafunci.

Sai muce abkin rigima cikin halifancin manzon Allah (s.a.w) ba tare da yankewa ba, lallai Zahara `yar annabi ta tafi farfajiyar ubangijinta shin itama ta san imamin lokacinta?

Ba nesanta ba kodai abokin rigimarmu ya ce bata san imamin zamaninta ba, wanda wannan shi ne mafi munin maganganun cikin sha'aninta Zahara (as) babu wani musulmi ko musulma da ya taba furta haka kwata-kwata a tsawon tarihi a tsawon zamani.

Ko kuma ya ce: ta san imamin zamaninta, tao dai wannan lokaci shi ya san Abubakr bai kasance imamin zamaninta ba a halin da ta mutu tana fushi da shi-kamar yadda ya zo cikin sahihu bukhari, kamar yadda ta kautar da fuskarta mai daraja lokacin da Abubakar ya ziyarceta, ta kasance tana mummunar adu'a kansa, lallai ita ba ta yarda daga gare shi ba, wannan na nufin kenan ita tayi fushi kan imamin zamaninta wanda wannan na raunana tsarkakarta da ismarta tabbatacciya da ayar tadhir. babu maguda face fadin lallai ita ta san imamin zamaninta shi ne mijinta sarkin muminai Ali (as) saboda haka ne ma ta kareshi ta yi jihadi kan tafarkinsa, ta kasance tana fitowa da `ya`yanta Hassan da Husaini  zuwa gidajen Ansar da muhajirun tananeman taimakonsu cikin yunkurawa kan kishiyantar wadanda suka kwace halifancin babannta ga mijinta.

Lallai ita ta yaki zalunci da kwankwashi dagutai da hudubobinta na saura da kalmominta na hamasa ckin masallacin babanta imamin musulmi wadanda suka juya bayansu.

na'am lokacin da umar ya tara yaransa domin ya kona gidan Fadima Zahara (as) sunce masa lallai cikin gidan akwai Fadima?

Sai ya ce ko da tana cikin gidan, sai ta fito bayan kyaure don kare sarkin muminai domin shi ne kwalabar fitilar annabta wacce take bada haske annabta bayan annabi (s.a.w) sai ta fake bayan kyauren kofa ya karya kofarta ya karya kashin awagarta ya halaka jinjirin da yake cikin ta, sai ta fito masallci domin ta kare imamanci da halifanci domin ai ita mishkat ce mai kare fitila da haskenta, bai daya tana krae annabta da wasiyya daga hatsarin kafirci da shirka da munafunci

 

Daga siffofin Zahara (as):

Manzon Allah (s.a.w) shi ne ranar al'umma Ali (as) watanta

 

وقال رسول الله: إذا غاب القمر فاقتدوا بالزهرة ، فسأل الأصحاب : ومن الزهرة ؟ فقال  9: ابنتي فاطمة الزهراء...

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: idan wata ya faku yabuya to ku shiriya da zuhratu, sai sahabbai sukai tambayi manzon Allah (s.a.w) mene ne zuhratu? Sai ya ce: `yata Fadima Zahara…

Lallai ita bar koyin `yantattu da masu saura muminai al'umma bayan al'umma, domin cewa itace mishkat sannan AIi (as) shi ne mizani ma'aunin karaya da gaskiya, imamanci shi ne ma'aunin gaskiya, sai dai cewa sanin ma'aunin sa mizaninsa ana saninsa da harshensa, shi ne ke furuci da gaskiya yake kare ma'auninnta, sannan Fadima Zahara (as) ce harshen mizani, lallaitace uwa ga babanta, daga cikn ma'anonin uwa shien ita tana kare danta daga bata, to ita Fadima Zahara tana kare sakon babanta ko da kuwa da sadaukar da ranta ne da shahadantar da jaririnta da dukan fuskarta  da jawuntakan idaniyarta  da karya kashin awagarta da kukanta dare da rana.

Na'am tabbas basu san darajartaba da matsayinta da mukaminta mai girma kamar yadda basu riski lailatul kadari ba, basu gushe ba cikin inuwa mai nisa.

Allah ka sanar damu kanka da manzonka da hujjojinka, hujjar hujjoj abar koyin waliyyai, Fadima Zahara (as).