فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

SADAUKARWA

 

Amincin Allah ya tabbata gareka ya kaka na ya manzon Allah da rahamar Allah da albarkun sa.

Amincin Allah ya tabbata gareka ya masoyin zukatanmu likitan ruhinmu mai ceton zunaban mu.

Amincin Allah ya tabbata gareka ya masoyin Allah zababbensa amintaccen sa mafi daukakar halittarsa.

Ina yi maka hadayar wannan dan kankanin kokarin nawa da yake cikin takardun akidu na ina mai saran ka karba da kuma samun ceton ka.

Ya manzon Allah kai mini shaida wurin Allah da cewa lallai ni ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, bashi da abokin tarayya, na shaida lallai kai manzon sa ne lallai kai ne Muhammad bn Abdullah, na shaida lallai kai ka sauke sakon ubangijinka ka isar da shi, kayi nasiha ga al'ummarka, kayi jihadi cikin tafarkin Allah da hikima da wa'azi mai kyawu, ka sauke abin da yake wuyaka daga gaskiya, tabbas kai ka tausasawa muminai ka kausasa kan kafirai, ka bautawa Allah da tsarkake niyya har sai da yakini ya zo maka, sai Allah ya isar da kai zuwa mafi daukakar mahallin masu daraja, godiya ta tabbata ga Allah wanda ya tseratar damu ta hanyarka daga shirka da bata.

Ya Allah kayi salati ga Muhammad da iyalansa, ka sanya salatinka da salatin mala'ikunka dana annabawanka da manzanninka da bayinka nagargaru ga Muhammad bawanka manzonka annabinka amininka masoyinka tacaccenka zababbenka kebantaccenka tsarkakakkenka mafi alherin cikin halittarka, ka bashi falala da daraja da wasila da daraja madaukakiya, ka aiko masa da wani mukami abin yabawa wanda mutanen farko da na karashe za suke burin samunsa.

Allah ya saka maka ya manzon Allah da mafi falalar abin da ya sakawa wani annabi daga al'ummarsa, Allah kayi salati ga Muhammad da iyalansa mafi falalar salatin da ka yi ga Ibrahim da iyalansa, lallai kai godadde ne mai girma mai jine mai kuma amsa addu'a ne.

 

 

Bawanka mai zunubi Adil-Alawi