فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Kalmar mu'assasa

[1]

Dukkanin godiya tabbata ga Allah mai rainon talikai, tsira da aminci su kara tabbata ga Muhammad da iyalansa tsarkaka.

Bayan haka:

tun lokacin da wutar juyin-juya halin muslunci mai albarka daga Iran ta fara ruruwa wacce take kona karagun dawagitai da azzalumai da `yan amshin shatan karnukan turawan yamma `yan mulikin mallaka, wannan juyin juya hali ke haskaka hanyar `yantattu da masu son kawo sauyi cikin duniya, tun fara yunkurin al'ummar musulmi muslunci keta habbaka kowacce rana bayan rana yake ta yin tasiri take da kara karuwa-sakamakon hakan ne ya zama an wayi gari cikin matsananciyar bukata ga wadanda za su dauki nauyin yada hukunce-hukuncen muslunci da kuma wandanda za su baza da yada hasken shiriyarsa da koyar da mutane fahimtocin muslunci wadanda suka kifu kan hanyar matafiyar dan Adam har zuwa bakin gabar farin ciki da arziki da aminci, saboda haka ne malamai wayayyu da mujahidai suka yunkura suka tashi don daukar wancan nauyi mai nauyin gaske suka yi sa'ayi da fafutika don toshe wancan bukata da ake tsananin bukatuwa da ita koda da abin da ya samu ne ya saukaka, suka sadaukar da dukiyarsu da lokacinsu da rayuwarsu saboda samun tabbatuwar hakan.

Sakamakon haka ne kake ganin wallafe-wallafe masu kima wadanda suke bayanin muslunci da girmamarsa da hukunce-hukuncen sa, hakama zaka ga cibiyoyin sakafa na addini da kungiyoyi yada alheri suna habbaka da samun cigaba, bazai yiwu wani yayi da'awar hakan ya isar ba cikin toshe bukata mai girma da fadin gaske ba, saboda haka ne ma aka samu wasu adadi daga dalibai muminai wayayyu ma'abota faffadan tunani suka yi gaggawa cikin assasa cibiyoyi da mu'assoshin muslunci na kowa da kowa domin aikin tablig da shiryarwa karkashin kulawar Ayatollah samahatus Sayyid Adil-Alawi Allah ya dawwamar da albarkarsa suna masu fata da saran hakan ya kasance ya toshe wani yanki koda kankani ne daga matsananciyar bukatar da duniyar musulmi ke da ita a wannan zamani da muke da ma wanda zai zo nan gaba.        

Amma hadafofin wannan cibiya sun tattaru cikin abin da ya gabata cikin abubuwa masu zuwa nan gaba kamar haka:

 

1-Amsa tambayoyin addinin da na tunani da sakafa, wadanda suke gangarowa da zuwa wannan cibiya daga mabanbanta nahiyoyin duniya, ana bada amsoshin ne daga mafi muhimmancin masadir din litattafai ababen dogaro wajen musulmi.

2- buga litattafai wadanda za su amfanar da wannan fage na tabligin muslunci daga ciki akwai samar da mujallolin muslunci da muke sa rai a nan gaba bada jimawa ba da za su cigaba da bin wannan hanya da tsari da kuma himmatuwa da al'amuran musulmi, haka za a dinga aika litattafai muslunci kyauta ga masu aiko da wasiku zuwa ga wannan cibiya.

3- gina dalibai wayayyu muminai wadanda za su iya tablig cikin gida da waje, hakan zai kasance ne karkashin shirya zama da muhadarorin musluncin a kowanne sati wadanda wannan cibiya mai albarka zata dinga samar da su da binsu.

Wasu ayyukan sakafa na addini na daban.

 wannan kenan sannan muna fata da sa rai daga mahaliccinmu mai girma da daukaka da ya datar da masu wannan aiki domin yada muslunci muhammadi na asali.

Daga wannan tushe ne da fahimta ta muslunci muke kaddamarwa masu karatu masu daraja wannan littafi mai kima mai suna (akidun muminai) wannan yana daga cikin na uku daga litattafan da wannan cibiya ta yada, muna rokon Allah taufiki da dacewa domin yada ma'arifofin muslunci mai karkata zuwa ga gaskiya shari'ar sama saukakakkiya.

Wannan kenan daga karshe muna muku fatan dawwama cikin alheri da habbaka, maganarmu ta karshe dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai.

 

Shugaban cibiya

Sayyid Kazim musawi

 
[1] Cikin godiyar Allah wannan cibiya cikin shekara goma ta samar abubuwa kamar haka:mujallar kausarcikin rabin shekara an buga goma sha hudu, 2 mujallar ushshaku Ahlil-baiti da harshen urdu indiya fakistan adadi 10, 3 jaridar sautul kazimaini duk wata-wata adadi105, 5 an buga fasotcin tablig, 6 an aika dubban litattafai ga masu aiko da wasiku kyauta daga kasashe 45, sannan hanyar yanzu fa farawawa ne mukai ba muyi komai ba cikin abin da muke son cimma, muna neman taufiki daga Allah da dacewa. Daga mai yadawa na wanna cibiya