فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Rassan addini goma

 

1-Sallah

2-Azumi

3-Zakka

4-Kumusi

5-Hajji

6-Jihadi

7-Umarni da kyakykyawa

8-Hani da mummuna

9-Wilaya ga Allah da manzan sa da Ahlil-baiti

10-barranta daga makiya Allah da manzon sa da makiya Ahlil-baiti.

Da sannu bayani da bahasi filla-filla dalla-dalla zai zo insha Allah ta'ala.

TaklidI bai halasta ba, zargi da zato bai isarwa cikin sanin Asalan addini (Usulul Dini) bari dai dole ne ya kasance daga zage dantse da ijitihadi da samo dalili da ilimi da yakini, amma rassan addini (Furu'ud Dini) ma'ana wajiban shari'a da hukunce-hukuncen muslunci da suka ratayu da ayyuka, ba wajibi bane cikin yin ijtihadi, bari ya halasta mukallafi ya kasance mujtahidi cikin su ma’ana wanda yake da ikon da kudurar mayar da rassa zuwa ga asalai da yalwatawa cikin tsamo hukunce-hukunce shari'a daga dalilan su na filla-filla daga littafin Allah da sunna da ijm'ai da hankali, hakama ya halasta cikin rassa mukallafi ya kasance muhtadi cikin ayyukan sa cikin abin da yake da yalwar yin ihtiyadi, hakika shari'ar muslunci ta wajabtawa mukallafi yin taklidi da mujtahidin da yake da kwarewa cikin ilimummukan muslunci cikin rassa daga halal da haram, sannan muslunci ya haramta yin takildi cikin asalan addini (Usulud Dini) shari'ar muslunci ba ta yi sausauci ga kowanne mukallafi ba da yin taklidi cikin akidun addini, bari dai sanin akida yana lazimta a shari'ance da hankalce gasgata ubangijin sa da annabinsa da imaminsa da ma'ad din sa makomar sa a lahirar sa.

Baki dayan malamai sun yi ijma'i kan wajabcin sanin asalan addini (usulud dini) da dogaro da dalili bawai da taklidanci ba,

kowanne daga cikin mutane shi ke daukar nauyin sanin akidar sa a wuyansa maimakon yin taklidanci da ra'ayin wasu da dora masu nauyin bincike da sanin asalan addinin sa.

Hakika Allah ya zargi wadannan da suke dora nauyin sanin asalan addinin su kan wuyan iyayen su don gujema nauyin sa, ko kuma sakamakon ta'assubanci ko kasala da jumudi da daskarewar kwakwalwa da hankali, kamar yadda ya zo cikin fadin sa madaukaki: 

(إنَّا وَجَدْنَا آبَاءَنَا عَلَى اُمَّةٍ وَإنَّا عَلَى آثَارِهِمْ مُـقْـتَدُونَ ) .

Lallai mu mun samu iyayenmu kan wata al'ada lallai kuma mu kan kufaifayin su masu shiriya ne.[1]

 

Kadai dai an kallafawa kowanne mutum guda daga cikinmu yin bahasi da bincike da zurfafa tunani cikin addinin sa gwargwadon yadda ya dace da mustawan sa da tanadin sa, lallai Allah bai kallafawa rai face abin da ya yalwaceta.

Hakika Allah matsarkaki ya kwadaitar kan yin bincike da kafa dalili cikin fadin sa madaukaki:

 (آئْـتُونِي بِكِتَابٍ مِنْ قَبْلِ هَذَا أوْ أثَارَةٍ مِنْ عِلْمٍ إنْ كُـنْتُمْ صَادِقِينَ ) .

Ku zo mini da littafi gabanin wannan ko kuma wani gurbi alama daga ilimi idan kun kasance masu gaskiya.[2]

 

Cikin furu'a rassa idan mutum bai kasance daga masu ikon yin ijtihadi ba bai kuma kasance daga masu ihtiyadi ba to wajibi kansa yayi taklidi da malaman fikihu maraji'ai, lallai su ne amintattun manzanni cikin al'umma matukar basu kasance daga masu biyewa duniya ba, lallai malamai su ne magada annabawa, hakika ya zo cikin hadisi mai daraja daga maulana shugabanmu Sahibuz-zaman amincin Allah ya kara tabbata gare shi Allah ya kuma gaggauta bayyanar sa madaukakiya:

«فأمّا من كان من الفقهاء صائنآ لنفسه ، حافظآ لدينه ، مخالفآ لهواه ، مطيعآ لأمر مولاه ، فعلى العوام أن يقلّدوه ».

Amma wanda daga cikin masana fikihu ya kasance mai katange kan sa, mai kiyaye addinin sa, mai sabawa bin son ransa, mai da'a ga umarnin ubangijin sa, to wajibi mutane game gari suyi taklidi da shi.

 

Shi muslunci akida ce da aiki, ya tattaro asalai da rassa.

Asalai su ne akidoji wadanda muslunci ya wajabta imani da su, dukkanin wanda bai yi imani da su ba to shi ba mumini bane, ilimin da ke daukar nauyi bayanin wadannan asalai da karfafarsu da hujjoji da dalilai hankali da dalilan nakali shi ne ilimin(Kalam).

 amma rassa su ne hukunce-hukunce da suka ratayu kan wadanda aka kallafawa yin ibada daga cikin abin da ke gangarowa daga su mukallafan da ya shafi rayuwar su ta yau da gobe wanda ake kira da mu'amalat, sannan ilimi da yake daukar nauyin bayanin wadannan ibadoji da mu'amaloli na hukunce-hukuncen rassa shi ne(ilimin fikihu) samun sanin hukunce-hukuncen shari'a na rassa yana kasancewa ta hanya guda biyu: ijtihadi ga wanda ya nemi ilimin sa da zama fakihi masanin fikihu, taklidi ga wanda bazai iya tsamo hukunci daga dalilan sa na filla-filla ba.

Muslunci yana farlanta aiki da hukunce-hukuncen addini, sannan dukkanin wanda bai aiki da su ba lallai ba ya daga cikin masu da'a da biyayya ga Allah girman sa ya girmama da manzon Allah mafi karamci (s.a.w) da shugabannin Al'umma wadanda Allah da manzon sa suka nasabta su ga al'umma.

 Wannan kenan sannan dalilin dawwana wannan `yar karamar risala wacce na sanya mata suna da (akidun muminai) shi ne cewa lallai ita ta kasance daga babin shimfida zuwa ga littafin fikihu mai suna (Minhajul Muminin) wanda na rubuta cikin mas'alolin fikihu don ya kasance risala ilimiyya da ta dace da fatawowin samahatus ustaz Ayatollah uzma Assayyid Mar'ashi najafi (rd) hakika an buga wannan risala cikin godiyar Allah cikin mujalladai biyu na farko ya kunshi abin da ya shafi ibadoji mujalladi na biyu kuma abubuwan da suka danganci mu'amalat. Allah matsarkaki ya so wannan mukaddima ta fito bayan an buga galibin abin da ke cikinta cikin jaridar larabci mai suna Kihan banagaren sakafa da wannan tsari mai cin gashin kansa, sai nayi bakin kokarina daga abin da na samu dama daga lokaci daga abin da ya shafi Asalan addini da Rassan sa, ina mai kafa dalili da dalilan hankali dana nakali daga littafin Allah da sunna tare da bin tsarin kauracewa tsawaitawa da tare da kuma ishara.

Hakika na gangara bahasosin asalan addini ina mai bayaninsu filla-filla dalla-dalla cikin darasussuka da gidan rediyon jamhuriyar muslunci ta Iran suka nada a watan ramaan shekara ta 1408, hakika ayari daga mutane masu daraja daga cikin wadanda nake kansatuwa cikin hidimasu cikin bada darasussuka a hauza ilimiyya dake cikin birnin Kum mai tsarki sun nakalto cikin kaset kamar yadda cibiyar Majma'ul ilimi ta daliban kasar Bahrain dake kum, bugu da kari harkar hijira da `yan hijira suma sun nakalci darasina da na bayar na littafin Babul Hadi Ashara gabanin `yan shekaru da suka gabata, Allah ya sakawa dukkanin su da alheri, hakama na rubuta sharhin littafi Babul Hadi Ashara cikin juzu'ai da sunan (Bidayatul Fikri fi sharhi Babul Hadi Ashara) shi ne mafi cika da bayani filla-filla.

Hakama an nadi sautin darasina da na yi kan littafin Tajrid cikin juzu'ai na kuma rubuta shi cikin juzu'ai da sunan (Kaulul Hamid fi sharhi Tajrid)

Wannan duka bai kasance komai ba face daga falalar ubangijina mai girma da daukaka, ina rokon ubangijina mai ikon yi matsarkaki madaukaki da ya bani dacewa da katanguwa bani da wani taufiki face daga Allah da shi na dogara gare shi zan koma, Allah na bayan manufa, karshen magarnarmu dukkanin godiya ta tabbata ga Allah mai rainon talikai.

 

«اللهمّ عرّفني نفسک ، فإنّک إن لم تعرّفني نفسک لم أعرف رسولک .

اللهمّ عرّفني رسولک ، فإنّک إن لم تعرّفني رسولک لم أعرف حجّتک .

اللهمّ عرّفني حجّتک ، فإنّک إن لم تعرّفني حجّتک ضللت عن ديني .

اللهمّ لا تمتني ميتة الجاهلية ، ولا تزغ قلبي بعد إذ هديتني ، وهب لي من لدنک رحمة ، إنّک أنت الوهّاب ».

Ya Allah ka sanar da ni kanka* lallai kai idan baka sanar da ni kanka ba ba zan taba sanin manzonka ba.

Ya Allah ka sanar da ni manzonka* lallai kai idan baka sanar da ni manzonka ba bazan taba sanin hujjarka ba.

Ya Allah ka sanar dani hujjarka* lallai kai idan baka sanar da ni hujjarka ba zan bata daga barin addini na.

Ya Allah kada ka kashe ni mutuwar jahiliya, kada ka karkatar da zuciyata bayan ka shiryar da ni, ka bani rahamar daga gareka, tabbas kai ne mai yawan kyauta.

 

«يا الله، يا رحمن يا رحيم ، يا مقلّب القلوب ، ثبّت قلبي على دينک ».

Ya Allahu ya rahmanu ya mai jujjuya zuciya ka tabbatar da zuciya ta kan addininka.

 

Bawan Allah

Adil-Alawi

Birnin kum mai tsarki shekara 1409 bugun farko

Bugu na biyu a shekara ta 1422.

 [1] Zukruf:23

[2] Ahkaf:4