فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

ASALI NA FARKO

 

 

 

(أفِي اللهِ شَکٌّ ).

Shin cikin Allah akwai shakku.[1]

Ina samsam cikin Allah matsarkaki madaukaki makagin sammai da kasa babu shakku ko daya babu kuma kokwanto, tabbas hujjojin hankali masu huda sun isar cikin tabbatar da samuwar mahalicci makagi, lallai tafarkoki da hanyoyin tauhidi da dayanta Allah sun kai adadin numfashin halittu:

ففي كلّ شيءٍ له آيةٌ         تدلّ على أنّه الواحدُ

cikin kowanne abu yana da wata aya* da take shiryarwa kan cewa lallai shi daya ne rak.

Babu wani abu misalin sa, masani mai iko, hannun sa mulkin komai yake, gare shi al'amura suke komawa.

Sai dai cewa cikin zamnin da muke ciki mai tsananin duhu, makarantu mulhidai masu inkarin samuwar Allah suna sa'ayi da kai kawo bakin kokarin su ta hanyoyi daban-daban cikin yada tunanunnuka masu gaba da yada muguwar falsafarsu ta wahami, da aidiyoloji (ideology) mara lafiya cikin majami'anmu na ubangiji da kasashenmu na musulmai, domin hadafin su da shirin su na mulkin mallaka kamar jari hujja da mulkin malakar yammacin turai sun togace cikin nesanta matasanmu daga ruhin addini, domin su nesanta kan su daga dukkanin dabaibayi da kaidi da lazimtar riko da addini, wanda hakan zai bawa wadancan miyagu damar sace dukiyar su da hadiye ta cikin sauki, kuma nesantar dasu ya saukaka gare su, sannan suna lamintarwa da kawukan su kazamar holewa da jin dadi.

Daga nan ne muke ganin wata kungiya babba daga malamai da ma'abota budewar tunani kan mikar zamanunnuka da lokuta cikin mabanbanta ilimai da fannoni suna gabatar dalilan su masu warakarwa da hujjojinsu don tabbatar da samuwar mahalicci matsarkaki ta hanyar kwararo da tabbatattun dalilai na ilimi da shaidodin falsafa masu walkawa.

Dan Adam tun lokacin da farcen ya fara tsirowa ya kasance yana imani da kudurce samuwar mahaliccin wannan duniya, sai dai cewa wani lokaci wasu mutane kan karkacewa su fada cikin shubuha cikin bayyana da ayyana abin da suke cigiya suke nema, ba komai ne hakan face amsa kiran lafiyayyar halitta (fidira), lallai ita tana karaji kan fusaken mulhidai masu inkarin samuwar mahalicci da cewa lallai fa wannan duniya tana da wanda ya kage  ta.

 Imanin su da samuwar Allah bai kasance daga jahilci ba ko taklidanci ba bari dai ya kasance daga ilimi da imani da basira mai ketawa.

Lallai dole duniya ta zama tana da wanda ya halicceta ya kageta mai hikima da tafiyarwa, mutum tun farko yana sassarfa bayan wannan kira na badini, shi an halicce shi ne da garizarsa da tsarin halittar sa mai lafiya kan bauta da imani da abin bauta mahalicci masani mai iko rayayye.

Mafi alherin dalili kan tabbatar da samuwar makagi shi ne halittar mutum a kankin kanta, sannan kuma wasu dalilan hankali da na ji nakali suna matsayin makamashi ne don haskaka halitta da yaye mata duhu, ga wasu ba'arin dalilan cikin takaitawa, za kuma mu sanya su cikin mukamin farko daga bahasinmu, sai kuma mukami na biyu ya biyo shi daga baya cikin siffofin Allah matsarkaki madaukaki         


 [1] Ibrahim:10