فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Mukami na biyu

 

Siffofin Allah matsarkaki madaukaki jamaliya da kamaliyya

Lokacin da muke imani da Allah matsarkaki a matsayin mahaliccin wannan duniya da dukkanin halittu mai tsara tafiyar su mai tarbiya gare su kan hikima da gudanarwa, ya zama dole tilas mu tsaya kan siffofin sa karkashin halittar sa da kagar sa ga wannan duniyar halitta, lallai hakan na kashafin ilimin sa da hikimar sa, da abin da ke cikin nutson wannan duniya babba daga karfi (energy) da yake gigitar da hankula, yana shiryar damu cikin dukkanin saukaka zuwa ga ikonsa. da abin da ke cikin sa daga rayuwa da idraki riskar hankali, yana jawuwa zuwa ga rayuwa lallai kuma shi ubangiji rayayye ne tsayayye, kamar yadda dayantuwar gini cikin wannan duniyar halittu tana ishara zuwa ga dayantuwar mahalicci da kuma cewa lallai bashi da abokin tarayya.

Tsarki ya tabbatar masa madaukaki yana siffantuwa da siffofin kamala, su ne: siffofin tabbatuwa na zati, su ne ainahin zatin sa su basu kasance kari ba kan zatin sa, idan ba haka ba kuwa zai lazimta adadantuwa da yawaituwar ubangijai wanda haka ya gurbata kamar yadda yake tabbace cikin mahallin sa, su ne kudura iko ilimi rayuwa, ikon sa da rayuwar sa sun sassabawa cikin ma'anar su ba wai cikin hakikanin su ba.

Siffofin tabbatuwa fi'iliya, su ne ainahin zatin sa kamar azurtawa, lallai shi yana azurta abin azurtawa cikin wani lokaci banda wani lokaci yana azurta wani mutumin koma bayan wani, hakan yana kasantuwa duk sanda hikimar sa ta so, sannan yana da kyawawan sunaye, kamar yadda yake siffantuwa da siffofin jalaliya wanda su da siffofin salbiya ma'ana siffofin kore masa duk wata tawaya, lallai shi ubangiji shi ba jiki bane, kuma shi ba murakkabi bane, shi baya cikin wani muhalli, lallai shi bai hadewa da wanin sa, lallai shi ba mahallin fararru bane, radadi da dadada basu inganta kansa, ba zai taba yiwuwa a ganshi gani na kwayar ido ba, bashi da abokin tarayya, cikin sa babu ma'anonin sassauyawa, lallai shi ya girmama daga dukkanin haka, dukkanin wadannan siffofi suna komawa zuwa ga siffa kwaya daya, shi ne cire imkani(yiwuwa) daga gare shi, saboda shi samuwar sa wajibi ce ga zatinsa (wajibul wujud lizatihi) sai hakan ya lazimta kore dukkanin siffofin da aka ambata na tawaya.

Shi tsarki ya tabbatar masa madaukaki mai iko, da ma'anar idan ya so ya ga dama sai ya aikata idan ya so ya bari tare da nufi da irada, duniyar kasantuwa sakamkon caccanjawarta cikin motsinta da rashin motsinta da jikkunanta da bijirorinta fararru, to mai tasiri cikinta ya zama dole ya kasance mai iko mai zabi, idan ba haka zai lazimta ya kasance mai wajabtawa da kufensa bai kwabu daga gare shi ba, sai ya lazimta gabatuwar duniya, ko kuma faruwar sa matsarkaki madaukaki, dukkanin kaddarawar biyu gurbatattu ne.

Lallai shi tsarki ya tabbatar masa mai zabi ne mai iko ne.

Shi masani ne saboda shi mai zabi ne, sannan dukkanin mai zabi masani ne, domin aikin sa ya biyo nufar sa ne, nufi bashi kasancewa ba tare da ilimi ba, kamar yadda lallai aikin ayyuka kamar yadda dukkanin mai tadabburi cikin halittun sa ke gani da shaidawa da hankaltar ayoyin sa na sasanni da na cikin kawuka, dukkanin mai aikata haka masani ne, Allah matsarkaki masani ne, ilimin sa ya rataya da dukkanin ma'alumat din kulliya da juzu'iya, sakamakon daidaita danganewa dukkanin ma'alumat zuwa gare shi, tabbas shi ya san sirri da dukkann abin da ya buya daga sirri, wancan sirri wanda mutum ya boye sannan daga baya ya manta shi, babu daga wani abu danye ko busashshe babu daga wani abu karami ko babba babu wani ganye da yake fadowa face ilimin su yana wurin Allah mukamin sa ya buwaya.

Lallai shi rayayye ne sakamakon shi mai iko ne masani ne, sai ya kasance raye a larurance.

Lallai shi yana da irada yayin da yayi umarni da hani, kamar yadda samar da ayyuka cikin wani lokaci koma bayan wani lokacin daban dalili kan samuwar mai kebantarwa, bai kasancewa face da irada, saboda haka shi mai nufi ne.

Lallai shi mai idraki ne riska, ita riska tafi kebanta daga ilimi kamar yadda nakali ya shiryar kan cewa shi mai riska ne daga ayoyi da riwayoyi masu daraja.

Lallai shi kadimi ne azali ne abadi ne, saboda shi samuwar sa wajibi ce ga zatinsa, sai rashi ya zama mustahili kansa, shi ne farko shi ne karshe shi ne zahiri shi ne badini.

Shi mai magana ne mai gaskiya, lallai shi yana samar da magana cikin jikkuna, kamar yadda kan wannan batu na magana akwai ayoyi da riwayoyi da ijma'i, sannan shi baya yin karya, saboda ita karya abu ne mummuna a larurance, shi tsarkakakke ne daga dukkanin munana, domin za su lazimta masa jahilci da gazawa da gafala da makamantan haka daga tawaya, shi Allah shi ne kamala mudlaka wacce ta tattaro dukkanin siffofin kamala cikin jihhohi, lallai shi ya dayantu cikin zatin sa da siffar sa da ayyukan sa, da ibada da soyayya da iklasi shi daya ne dayantacce da bai da na biyu, babu wani abu misalin sa, shi kadimi ne bai gushe ba kuma zai taba gushewa ba, shi mai ji ne mai gani ne, ba ya siffantuwa da halittu babu wata halitta da ta kasance tankar sa ko tsaran sa.

Me yafi kyawu daga abin da sarkin muminai shugabanmu Ali (as) ya fadi cikin Nahjul Balaga:

«وكمال الإخلاص له نفي الصفات عنه ، بشهادة كلّ صفة أنّها غير الموصوف ، وشهادة كلّ موصوف أنّه غير الصفة ، فمن وصفه سبحانه فقد قرنه ، ومن قرنه ثنّاه ، ومن ثنّاه فقد جزّأه ، ومن جزّأه فقد جهله ».

Kamalar iklasi gare shi shi ne kore masa siffofi, da shaida kan cewa dukkanin siffa lallai ita ba ta kasance abin da aka siffanta ba, da shaida dukkanin abin da aka siffanta ba shi ne siffar ba, dukkanin wanda ya siffanta shi matsarkaki tabbas ya cudanya shi, dukkanin wanda ya cudanya shi hakika ya karkasa shi juzu'i juzu'i, dukkanin wanda ya karkasa shi juzu'ai tabbas ya jahilce shi.

 

Hakika cikin addu'a Sabah ya ce:

«يا من دلع لسان الصباح بنطق تبلّجه ، وسرح قطع الليل المظلم بغياهب تلجلجه ، وأتقن صنع الفلک الدوّار في مقادير تبرّجه ، وشعشع ضياء الشمس بنور تأجّجه ، يا من دلّ على ذاته بذاته ، وتنزّه عن مجانسة مخلوقاته ، وجلّ عن ملائمة كيفيّاته ، يا من قرب من خطرات الظنون ، وبعد من لحظات العيون ، وعلم بما كان قبل أن يكون ».

Ya wanda ya hudar da harshen asubahi da furucin bayyanarsa, ya yanke yankunan dare mai tsananin duhu da hasken kyalkyalarsa, ya kyautata kagar falaki cikin makaddaran yayewarsa, ya haskaka haske rana da hasken ruruwarsa, ya wanda ya shirya zuwa ga zatin sa da zatinsa, ya tsarkaka daga jinsuntuwa da ababen da ya halitta, ya girmama da dacewa da yadda yake, ya wanda ya kusanto daga darsawar zato, ya nesanta daga ganin idanu, ya san abin da ya kasance gabanin kasantuwarsa.