فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

sharuddan annabi

 

Cikinsa isma tana wajabta tilas ya kasance ma'asumi, wacce ita isma ludufi ne daga Allah da ya sanya shi cikin annabawansa, domin nafsin annabi da yadda take, ita nafsi ce ta mutum, tana hukunta kwatankwaci daga abin da ke gangarowa daga sabo da zunubai, sai dai cewa tana da shinge domin toshe waccan kofa mai hukunta dukkanin halayen misalan sa daga mutane da abin da ke biye da ita, wancan shinge hijabi shi ne karfi nafsin sa da hakalin sa daga fuskanin kamalar ilimin sa da kewayar sa da tushen kura-kurai da laifuka da zunabai da kufaifayin su, baya gafala gwargwadon kiftawar ido daga hallarar Allah tsarki ya tabbatar masa, sai ya hanu ya kame daga zakkewa aikata laifi da sabo da zunubi bisa zabin sa bawai ta fuskanin tilasta shi a tankwara shi kan hakan ba, sai annabi ya zama ya katangu da hijabantu daga baki dayan zunubai daga dukkanin abin da zai gurbata shi.

Kadai dai isma tana wajabtuwa cikin annabi domin a samu amintuwa da kalaman sa, sai manufa ta tabbata daga annabta daga mika kan mutane zuwa gare shi da misalta umarnin sa.

Idan ma'asumi ya aikata munkari wajibi ai inkarin hakan kan sa domin hani daga barin munkari gamamme wanda ya hado ya gamo har da annabi, sannan abin da hakan ya ke lazimtawa shi ne cutar da annabi wanda haka an hana shi daga barin sa.

A wannan lokaci ya zama dole mu yi imani da ismar annabawa daga dukkanin zunubai baki dayan su kananan su da manyan su haka daga rafkana da mantuwa da gafala da dukkanin abin da yake tauye mukamin annabtar sa. Kammaluwa da cikar hankali na shardantuwa cikin annabi da kaifin basira da karfin ra'ayi da tsarkakuwa daga dukkanin abin da dabi'a ke gudarma daga kazantuwar iyaye da fasikanta da fajirci cikin iyaye mata da makamancin wannan, don gudun kada a dinga kyamarsa daga munana domin kare hadafin annabta.

Ya zama dole ya kasance ma'asumi tun daga farkon rayuwar sa har zuwa karshenta mai daraja, saboda rashin mikuwa zuciya zuwa ga da'ar wanda aka san cudanyar sa da sabo da manyan laifuka da kananan su da abin da zukata ke kyamata a cikin tarihin rayuwar sa.

Kamar yadda yake wajaba dole ne ya kasance shi ne mafi falala a zamanin sa, saboda munana fifita wanda aka darajanta kan mai daraja a hankalce da nakalce, lallai wanda aka falalantar yana bukatuwa ya zuwa kammaluwa ta kaka zai fifita kan mai falala kammalalle, wannan abu ne mai muni daga mai hikima masani labarin halittun sa, duk wanda ya kasance daga dan aji daya a ilimin mandik ta kaka zai gabata kan Arasdodalis wanda shi ne ya rubuta mandik ya dawwana shi? Hakama cikin ragowar ilimai da fannoni, hakika madaukaki cikin bayanannen littafin sa da yankakken zancen sa ya ce:    

(أفَمَنْ يَهْدِي إلَى الحَقِّ أحَقُّ أنْ يُتَّبَعَ أمَّنْ لا يَهِدِّي إلاَّ أنْ يُهْدَى فَمَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ ).

Shin wanda yake shiryarwa zuwa gaskiya shi ne mafi cancanta da abi ko kuma wanda bai shiryarwa sai dai shima a shiryar da shi me ya same ku kaka kuke hukunci ne.[1]

Wannan kenan sannan hanyar sanin annabi shi ne bayyanar mu'ujiza a hannun sa tare da da'awar annabta, da zai tabbatu daga gare shi abin da ba a saba gani ba ko kuma ya kore abin da aka al'adantu kan sa aka saba da shi daga keta al'ada –wannan shi ne abin da ake kira da mu'ujiza-lallai hakan yana shiryarwa zuwa ga annabtar sa, idan ya ce: ni annabin Allah ne mu'ujizata mayar da sanda macijiya ko kuma raya matattu, ko kuma tsaga wata, sannan wadannan abubuwa suka faru, za a san lallai cewa shi mai gaskiya ne abin gasgatawa cikin da'awar sa, a wannan lokaci da tasrihin hukuncin hankali dole a gasgata shi ai masa da'a. da ace shi makaryaci ne sannan mu'ujiza ta bayyana a hannun sa da hakan ya lazimta cewa Allah ya cuna mutane zuwa ga karya da makaryaci, wannan abu ne mai muni daga mai iko masani, Allah ya tsarkaka daga dukkanin munanan abubuwa, saboda shi mawadaci ne wajibul wujud wanda samuwar sa take wajibi ga zatin sa.

Wajibi aiko da annabawa cikin kowanne lokaci domin hujja ta kasance mai isarwa ga Allah madaukaki, dole ne hujja ta kasance cikin kasa koma wane ya kasance hujjar, ba da ban hujja ba da kaasa ta hadiye mutanen dake kanta, lallai shi yana kira zuwa ga Allah matsarkaki yana kuma yada shari'ar da ta zo daga sama saukakakkiya, yana kuma shiryar da mutane zuwa ga tafarki madaidaici hanya mikakka, yana koyar da su littafi da hikima, yana tsayar da adalci tsakankanin su.

Sannan ita ma'arifa kamar yadda ya zo cikin hadisanmu masu daraja lallai Allah madaukakiya ya aiko annabawa da manzanni dubu dari da ashirin da hudu 124000 na farkon su Adamu (as) na karshensu kuma shi ne cikamakin annabawa mafi daukakar halittun Allah Muhammad bn Abdullah (s.a.w) biyar daga cikin annabawan ulul azmi ne ma'ana ma'abota shari'a ne zuwa ga mutane an basu litattafai su ne: Nuhu Ibrahim Musa Isa da Muhammad (s.a.w) halalin Muhammad halali ne har zuwa tashin kiyama haramun din Muhammad haramun ne har tashin kiyama. Dukkanin wanda ya nemi wani addinini koma bayan muslunci ba za a taba karba daga gare shi ba, lallai addini wurin Allah shi ne muslunci.     


 [1] Yunus:35