فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Annabta kebantacciya

 

 

Hakika na hattama annabta da manzon Allah mafi girma Muhammad (s.a.w) mai tseratar da duniya dan adam baki dayanta daga duniyar jahilci da tsiyata zuwa kwazazzabon ilimi da farin ciki da azurtuwa da ni'imtuwa

Kadai dai muna imani da kudurce annabtarsa da kuma cewa lallai shi ne cikamakin annabawa, saboda shi ya yi da'awar annabta  daga wurin Allah madaukaki kamar yadda bai buya wajen wani daga talikai ba, lallai yadda al'amarin yake hakan ya tabbata da tawatiri, sannan tawatiri yana daga cikin abubuwan da suke larura a sallama musu, sannan mu'ujizozi sun bayyana a hannun shi mai albarka kan da'awar sa, dukkanin wanda ya kasance haka to ya kasance annabi na hakika daga wurin Allah tsarki ya tabbatar masa madaukaki, wannan kiyasi ne daga shakalin farko kamar yadda yake rubuce a tasnifin wannan mukami.

Sannan madawwamiyar mu'ujizar sa har zuwa tashin ranar kiyama shi ne kur'ani mai tsayayye, wanda yake shiryarwa zuwa ga wacce tafi tsayuwa wargi bai zuwar masa, hakika kur'ani mai girma yayi kalubale da a zo da misalin sa ko da kuwa cikin sura guda daya rak ko kuma aya daya rak, ko da kuwa mutane da aljannu za su hadu sashen su yana karfafar sashe.

Mu'ujizanci kur'ani mai girma bai iyakantu ba ko togacewa iya cikin balaga da fasahar uslubinsa ba, bari dai fasahar da balagar uslubi tare da ma'arifofi cikin duniyar dabi'a (nature) da abin da yake bayan duniyar dabi'a (methapysics), da siffofi Allah da halaye godaddu da hukunce hukucen shari'a da na siyasar birane, da labarukan gaibu, da yanayiyyikan mafara da makoma, da rashin sassabawa da tufka da warwara cikin ayoyin sa, da dai makamantan haka daga cikin abin da yake zahirin littafin Allah mai girma, tare da badinin sa daga asrarai da hikimomi da kebantattun sirrika da abubuwa masu ban mamaki da ilimai wadanda basu yaye ga dan Adam ba, ba su kuma gushe ba  jahiltattu face ga wasu `yan tsiraru, (babu abin da aka baku daga ilimi face dan kankani)

  ولا يمسّه إلّا المطهّرون .

Babu masu shafar sa face masu tsarki.

Kur'ani mai girma mu'ujiza ne ga dukkanin wanda yake da wani fanni da fannonin ma'arifofi da ilimai, lallai shi zai ga kur'ani ya daukaka cikin wannan fanni, babu wani mutum a yau da ma gobe daga cikin mutane da ya iya samun ikon kawo harafi guda daya daga wani abu daga gare shi face sai tsaurin kai da jahilci, hakika kur'ani ya rushe jahilcin jahili da gamsashshiyar amsar sa, wannan gajiyarwa ce daga kowanne irin mutum ta gangaro, ta kaka ba zai zama haka bacin tabbas annabi ummi wanda aka aiko daga ummiyun wanda basu san karatu da rubutu ba? Sakon muslunci muhammadiya na asali wanda annabi mafi karamci (s.a.w) ya tsinkaya kansa zuwa ga baki dayan mutane har zuwa tashin kiyama hakama ya tsinkaya kan duniya baki daya, kadai dai wannan sako ya misaltu cikin kur'ani mai girma.

Hakika shari'ar muslunci mai karkata ga gaskiya ta fifitu da kebantattun abubuwa da mizozi ababen fifita masu tarin yawa, a cikin sakafarta da take dacewa da tsarin halittar dan adam lafiyayya a kimomi da mafhumai daga rayuwa da mutum, da aiki da alakokin zamantakewa, daga mafi kyawun abin da tarihi ya sani ya kuma shaida daga kimomi wayewa da cigaba da shari'o'in zamantakewa:     

 (وَكَذَلِکَ أوْحَيْنَا إلَيْکَ رُوحآ مِنْ أمْرِنَا مَا كُنْتَ تَدْرِي مَا الكِتَابُ وَلا الإيمَانُ وَلَكِنْ جَعَلْنَاهُ نُورآ نَهْدِي بِهِ مَنْ نَشَاءُ مِنْ عِبَادِنَا وَإنَّکَ لَـتَهْدِي إلَى صِرَاطٍ مُسْتَقِيمٍ ) .

Haka kamar wancan mu ka yi wahayin ruhi daga garemu gareka baka kasance kana sanin littafi ba da imani sai dai cewa mun sanya shi haske muna shiryar da wanda muka so da shi daga bayinmu lallai tabbas kana shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici.[1]

(هُوَ الَّذِي بَعَثَ فِي الاُمِّـيِّينَ رَسُولا مِنْهُمْ يَـتْلُو عَلَـيْهِمْ آيَاتِهِ وَيُزَكِّيهِمْ وَيُعَلِّمُهُمُ الكِتَابَ وَالحِكْمَةَ وَإنْ كَانُوا مِنْ قَبْلُ لَفِي ضَلالٍ مُبِينٍ ).

Shi ne wanda ya aiko da manzo cikin wadanda basu iya karatu da rubutu ba daga cikin su yana karanta ayoyin sa kan su yana tsarkake su yana koyar da su littafi da hikima lallai sun kasance gabanin sa tabbas cikin bata mabayyani.[2]

Me yafi girmama daga kur'ani daga mu'ujizar sa madawwamiya lallai yadda al'amarin yake shi ne duk sanda zamani ya samu cigaba ilimummuka da fannoni suka habbaka lallai shi kur'anin yana wanzuwa cikin sabuntar sa da kyawunsa da dadin sa kan daukakar manufofin sa da tunane-tunanen sa da afkar din sa.

Muna kudurcewa da imani da cewa lallai ma'abocin sakon muslunci shi ne cikamakin annabawa da manzanni mafi falalar su saki babu kaidi mudlakan, kamar yadda muke imani da cewa lallai shi ne shugaban mutane baki dayansu lallai shi hakika yana kan dabi'a mai girma.

Wajibi ne a kanmu mu mutunta da girmama addinin sa da kur'anin sa a aikace da fade, babu mai shafar sa face tsarkakakku, farin cikinmu da izzarmu da karamarmu na cikin kur'ani mai girma.

Sai dai cewa azurtuwa da daukaka da karama basa komawa ga wannan al'umma face idan sun komawa kur'ani a ilimance da aikace da dabi'ance da ladabance, kur'ani zai daukaka wannan al'umma zuwa samun falala da ilimi da kyawawan dabi'u, shi zai iyakance musu nasara da daukakar ambaton sa da dagawar darajar su, abin da wannan al'umma ta rasa da arziki da karfi da wayewa da cigaba, cikin kur'ani akwai abin da yake fitar da mutane daga duffai zuwa haske, shi kur'ani shi ne makwankwadar tarbiyya da Akhlak, shi ne mabubbugar shari'a da dokoki karfafa, da ayar adabi da fanni, shi kur'ani littafin Akida ne da jihadi don neman falala, shi jagoran alheri ne da ihsani da adalci, shi jagoran `yanci ne da cin gashin kai da daukaka, shi ne mikakkiyar igiyar Allah zuwa kasa, lallai shi daga mai hikima yake. [1] Shura:52

[2] Juma'a:2