فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Imamanci gamamme

 

Imamanci: sunna ce ta halitta, lallai ita shugabanci ne gamamme ga wani mutum daga cikin mutane cikin addini da duniya, da yake na'ibantakar annabi (s.a.w) da nassi daga manzon Allah (s.a.w) da wannan bayani ne limamin bata da halaka ke fita wanda yake kira zuwa ga wuta.

Imamanci ludufi ne daga Allah domin da shi ne mutum yake samun kusanta zuwa ga da'ar Allah da nesantar sabon sa, da shi ne ake cimma hadafi manufa ke tabbatuwa daga shari'ar da ta zo daga sama, wajibi kan Allah ya nasabta imami domin shiriyar da mutane bayan annabi da dalilai na hankali da nakali: 

 (وَجَعَلْنَاهُمْ أئِمَّةً يَهْدُونَ بِأمْرِنَا).

Muka sanya jagorori suna shiryarwa da umarninmu.[1]

Yana umartar su da kyakkyawa da adalci da ihsani, yana kuma hana su sabo da munkarai, ya wurga musu ma'arifofin Allah da ilimummuka da hukunce-hukunce, yana shiryar da su ya zuwa maslahohin duniya, littafin Allah bai isar musu face tare da wanda ilimin littafin ke gare shi, kamar yadda manzon Allah (s.a.w) ya bayyana hakan cikin hadisin saklaini, saboda haka samuwar imami ludufi ne daga Allah tasarrufin sa ma haka ludufi ne daga Allah, rashin sa kuma cutuwa ne.

Ya zama dole imami ya kasance ma'asumi daga dukkanin abin da ya ke tauye mukamin imamanci, isma ludufi ne daga Allah madaukaki ga bawan sa ta yanda zata katange shi daga afkawa sabo da barin da'a da biyayya tare da cewa yana da iko kan su, sai dai cewa yayin da ma'asumi wata daraja da falala ta kasance gare shi kadai dai isma tana wajaba cikin imami tun ranar haihuwa tun lokacin da aka haife shi har zuwa karshen rayuwar sa mai daraja kamar yadda ta kasance ga annabi (s.a.w), saboda yadda al'amarin yake ba da ban hakan ba da imam ya bukatu zuwa ga wani imamin da zai dinga saita shi da yi masa gyara wanda hakan zai lazimta tasalsuli, da zai halasta gare shi ya aikata sabo lallai inkari ya wajaba kan sa lallai kimar sa za ta fadi daga zukata babu wanda zai yi masa biyayya sai hadafi ya rushe daga imamancin sa, idan kuma inkari kan sa bai wajaba ba to hani daga aikata munkari zai fadi, wanda kuma hakan ya gurbata.

ta kaka ba zai kasance ma'asumi ba alhalin shi ne wanda alhakin kare shari'a ke wuyan sa, kari da dadi ba zasu amintu daga gare shi ba da ban isma ba, ba da ban isma ba da ya lazimta wulakantar addini, babu wanda ya san isma sai ubangijin iyayen giji tsarki ya tabbatar masa madaukaki, wajibi kan Allah da manzon sa da su nassanta imami ma'asumi, kamar yadda tsarin yadda annabi ya rayu ta shiryar kan haka, lallai shi ya kasance mafi tausayin mutane daga tausayin da uba ke yiwa dansa, ya nusantar da su hatta zuwa ga abubuwan da ma basu da wata dangantaka da halifanci da wasiyya a bayansa, kamar yadda shi yayi tafi daga madina ya halifantar da wanda cikinta zai tsayu kan al'amuran musulmi kamar yadda tarihi ya bamu labarin hakan-to ta kaka zai bar mutane kara zube a bayansa? Ta kaka al'amarin imamanci zai sallama shi hannun al'umma, alhalin kowanne mutum kan sa ya fi so kullum kan sa yake jawowa amfani, wajibi imami ya kasance bayan annabi shi ne mafi fifita da falala daga wanin sa, domin yana da muni fifita wanda akaiwa falala akan ma'abocin falala da hujjar hankali da nakali      

 (أفَمَنْ يَهْدِي إلَى الحَقِّ أحَقُّ أنْ يُتَّبَعَ أمَّنْ لا يَهِدِّي إلاَّ أنْ يُهْدَى ).

Shin wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya shi yafi cancanta a yiwa biyayya ko kuma wanda bai shiryarwa sai dai shima a shiryar da shi.[2]

 


 [1] Anbiya'u:73

[2] Yunus:35