فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Imamanci kebantacce

 

Ka sani lallai hakika shi imamanci bayan manzon Allah (s.a.w) da halifanci da wasiyyanci ba tare da yankewa ba kadai dai tana ga shugabanmu sarkin muminai Ali bn Abu dalib (as) sakamakon dalilai da hujjojin hankali da nakali wadanda Allama Hilli (rd) ya kidaya su sun haura fiye da dubu cikin littafinsa mai daraja mai suna (Alfaini)

Daga cikin mafi muhimmancin dalilan: shi ne cewa daga cikin sharuddan imamanci akwai isma, sannan babu wani mutum ma'asumi bayan annabi face sarkin muminai Ali (as) da ijma'i, shi ne imamin gaskiya ba tare da yankewa ba, kamar yadda Allah ya ambata cikin littafin sa mai girma cikin ayar tadhir da ayar mubahala da ayoyin da'a da zakka da ciyarwa hakama da gomomin ayoyi daga kur'ani mai daraja, kamar yadda riwayoyi mutawatirai suka nassantu kansa kamar misalin hadisin gadir da hadisi da'ir da hadisin mazila da makamantansu, kamar yadda lallai shi ne mafi falala da darajar al'umma cikin dukkanin falaloli na nafsu da na gangar jiki da waje.

Hakika mu'ujizozi da karamomi sun bayyana kan hannun sa, hakika shi da kansa yayi da'awar imamanci, sannan dukkanin wanda ya kasance haka lallai shi imami da gaskiya da gasgatawa, idan ko ba haka ba to al'amarin zai lazimtawa Allah cuna mutane zuwa ga halaka wanda wannan abu ne mummuna shi kuma Allah ya tsarkaka ya daukaka daga aikata munana. Kamar yadda lallai al'ummar musulmai suka yi ijma'i kan halifancin sa koma bayan waninsa, hakika sabani ya afku cikin halifancin sa wasun sa sannan rashin cancantar su ta tabbatu, shi Ali (as) shi ne yafi cancantuwa da dacewa da halifanci, kamar yadda al'umma ta hadu kan halifancin ga Ali (as) imamanci wanin sa ya gurbata da hujjar aya mai daraja

(لا يَنَالُ عَهْدِي الظَّالِمِينَ )  .

Azzalumai basu samun alkawarina.

و(إنَّ الشِّرْکَ لَظُلْمٌ عَظِيمٌ )  .

Lallai shirka hakika zalunci ce mai girma.

Wanda ya kasance mafi yawan yin da'awar halifanci ga wanin Ali cikin shirka shi ne Umar, azzalumai basa samun alkawarin Allah, wanda shi ne imamanci, bisa siyakin aya, sai ya tabbata lallai cewa halifanci ga Ali (as) yake, domin shi Ali bai taba tarayya da Allah gwargwadon kiftawar ido, sannan zargin mai zargi bai taba kama shi ba bai taba damun sa ba, Allah ya karrama fuskar sa daga yiwa wanin sa sujjada.

Dalilai kan haka ba za su kidayu ba saboda yawan su, manyan malamai sun yi rubutu da tasnifi cikin wannan fagen sukuwa rubuce-rubuce masu matukar yawa da bazai yiwu a iyakance su ba, me yafi kyawu daga abin da aka fada cikin hakkin sa:

«ما أقول في رجلٍ كتم أعداؤه فضائله حسدآ، وكتم أحبّاؤه فضائله خوفآ، وظهر في بين هذا وذاک ما ملأ الخافقين ».

To ni me zance cikin mutumin da makiyan sa suka boye falalolin sa saboda hassada* su kuma masoyan sa suka boye su saboda tsoro* sai ya bayyanu cikin tsakanin wannan da wancan abin da ya cika sama da kasa.

Sannan halifanci bayan sa yana komawa ga babban dansa Hassan mujtaba, sannan dansa na biyu Husaini shugaban shahidai, sai kuma dansa Aliyu bn Husaini zainul Abidin, sai dansa Muhammad bn Ali bakir, sai kuma dansa Jafar bn Muhammad Sadik, sai dansa Musa bn Jafar Kazim, sai dansa Aliyu bn Musa Rida, sannan Muhammad bn Aliyu Jawad, sai Aliyu bn Muhammadul Hadi, sannan Hassan bn Ali Askari sai dansa alhujjatu ka'imi Muntazar Sahibuz-Zaman (as):

Lallai Alhujjatul Muntazar (as) yana raye yana azurtuwa, hakika ya faku daga barinmu cikin gaibar sa sugra da kubra, yana amfanar da duniya kamar yadda ranar ke amfanarwa lokacin da take cikin girgije, ba da ban shi ba da kasa ta nutse da mutanen da ke kanta, albarkacin sa ake azurta mutane, shi ne sababi da yake hade tsakanin sama da kasa, da sannu zai cika kasa da adalci da daidaito bayan ta cika da zalunci da danniya, sannan mafifitan ayyukan lokacin fakuwar sa shi ne tsimayin bayyanarsa domin da shi ne mutum ke tsarkake kan sa ya rike addinin sa kyam, ya Allah ka saukake al'amarin sa ka gaggauta bayyanar sa ka sanya mu daga yan shi'ar sa daga mataimakan sa da masu samun shahada a gabansa.

Dalili kan imamancin wadannan A'imma tsarkaka wadanda dukkanin su haske ne guda daya shi ne nassi daga nakalin tawatiri daga bangarori biyu sunna da shi'a daga annabi mafi karamci (s.a.w) wanda ya zo a dunkule kamar misalin fadin sa:

«الأئمة بعدي اثنا عشر، كلّهم من قريش ».

Jagorori bayana goma sha biyu ne, dukkanin su daga kuraishawa suke.

Hakama nassi ya zo da bayani filla-filla kamar fadin sa ga Husaini (as)

«هذا ابني ، إمام ابن إمام أخو إمام ، أبو الأئمة التسعة ، تاسعهم قائمهم ».

Wannan dan nawa Imami ne dan imami kuma dan'uwan Imami ne sannan kuma uba ga Imamai tara na taransu shi ne mai tsayuwa.

Da dai makamantan haka daga nassosi masu tarin yawa.

Hakika mun shardanta ismanci cikin Imami, ba ta bakin komai sai cikin su da ijma'i, ba da ban su ba da ya lazimta wofintar zamani daga ma'asumi wanda hakan abu ne da bazai yiwu ba, ba da ban hujja ba da kasa ta nutse da mutanen cikinta, sannan kowanne Imami da ya gabata ya nassanta Imamanci Imamin da zai zo, sannan mu'ujizozi sun bayyana masu keta al'ada kan hannun su tare da da'awar Imamanci daga gare su, lallai su ne mafi falala daga wanin su cikin zamanin su, hakika sun tattaro baki dayan siffofin kammaluwa da kamalolin nafsu da gangar jiki, bai halasta ba gabatar da wanda akaiwa falala kan me falala, su ne suka fi kowa cancanta da shugabanci daga koma bayansu.

Wannan kenan sannan ludufi wajibi ne daga Allah cikin Imamanci, shi ne nasabtawarsa da kallafawarsa ga Imamanci, hakika kuma ya aikata hakan, ubangiji bai kasance mai wofinta daga wajibinsa ba, kadai dai wofintar ta kasance daga al'ummar da ake kiwo su ne basu kiyaye hakkokin ubangiji ba, basu kuma zartar da umarnin sa ba, bari dai sun yake shi ne, saboda haka su ne suka jawowa kansu halaka da hannayen su, sannan rashin halartuwar sa da fakuwar sa daga garemu take ba daga Allah ba mai ludufi tsarki ya tabbatar masa madaukaki.

Ya Allah ka sanyamu masu riko da wilayar su, ka tashemu cikin gayyar su, ka karbi rayukanmu kan soyayyar su ka sanya rayuwarmu misalin rayuwar su, mutuwarmu misalin mutuwar su, ladubbanmu da halayenmu misalin ladubbansu da halayensu

 
ka sanya mu daga tsarkakakkun shi'ar su da mafi alherin masoyansu, amin ya mai rainon talikai.

Ga wani dan karamin jadawali mai albarka gareka ya kai mai mudala'a da ya tattaro sunayen ma'asumai tsarkaka su goma sha hudu, da sunayen iyayen su da ranakun haihuwar su da wafatin su da wuraren da kaburburan su suke, hakika na ciro su daga litattafai masu kima su ne: Kitabul Irshad, Tauzihuh Almakasid, Ahsanun Takwimi, Tashaful Gida, Kashaful gumma, Durus, da makamantan su daga ingantattun litattafai. 

 

mahaifiya

mahaifi

alkunya

Lakabi

suna

Aminatu

Abdullah

Abu kasim

musadafa

Muhammad (s.a.w)

Fadima bintu Asad

Abu dailb

Abu Hassan

Amirul muminun

Ali (as)

Muhammad nabiyul Akram

Khadijatu bintu kuwailid

Ummal A'imma

Zahara

Fadima (as)

Fadima Zahara

Ali amirul muminun

Abu muhammad

Mujtaba

Hassan (as)

Fadimda Zahara

Ali amirul muminun

Abu Abdullah

Sayyidul shuhada

Husaini (as)

Yazdajardu

Ali zainul Abidin

Abu muhammad

Zainul Abidin

Ali (as)

Fadima bintu Hassan

Muhammad bakir

Abu Jafar

Bakir

Muhammad (as)

 

Ummu farwatu

 

 

Muhammad bakir

 

Abu Abdullah

 

Sadik

Jafar (as)

Hamida barbariyat

 

Jafar Sadik

Abu Ibrahim

Kazim

Musa (as)

Najmatu

Musal Kazim

Abu jafar

Rida

Ali (as)

 

Sabikatu

Aliyul Rida

Abu Jafar

takiyyu

Muhammadas

Samanatu

Muhammad jawad

 Abu jafar

Naki

Ali (as)

Hadis

Aliyun Hadi

Abu muhammad

Askari

Hassan (as)

Narjis

Hassan Askari

Abu kasim

Sahibuz-zaman

Muhammad

 

 

 

inda aka binne shi

Shekarar wafati

wafati

 imamanci

Shekarar haihuwa

haihuwa

suna

 

Madina dayyiba

11 bayan hijira

28 safar

Annabta 23

Shekarar giwa

17 rabi'u awwal

Manzon Allah

 

Najaf Ashraf

40 bayan hijira

21 ramadan

30

30

13 rajab

Sarkin muminai

 

Madina dayyaba

11 bayan hijira

3 jimada sani

 

Kwana 5 bayan annbata

20 jimada sani

Fadima

 

Madina dayyaba

50 bayan hijira

7 ko 27 ga safar

10

3 bayan hijira

15 ramadan

Hassan

 

karbala

61 bayan hijira

10 ga muharram

11

4 bayan hijira

3 sha'aban

Husaini

 

karbala

95 bayan hijira

12 ko 25 ga muharram

34

36 bayan hijira

15 jimada ula

Zainul Abidin

 

baki'a

114 bayan hijira

7 ga zul hijja

19

57 bayan hijira

3 safar

Bakir

 

Baki'a

148 bayan hijira

25 ga shawwal

34

83 bayan hijira

17 rabi'u awwal

Sadik

 

kazimaini

183 bayan hijira

25 ga rajab

35

128 bayan hijira

7 safar

Kazim

 

Mashad mai tsarki

203 bayan hijira

Karhen safar

20

148 bayan hijira

11 zul ka'ada

Rida

 

kazimaini

220 bayan hijira

Karshen zul ka'ada

17

195 bayan hijira

10

rajab

Jawad

 

samarra

254 bayan hijira

3 ga watan rajab

34

212 bayan hijira

15 zul hijja

Hadi

 

samarra

260 bayan hijira

8 ga watan rabi'u Awwal

6

222 bayan hijira

10 rabi'ul sani

Asakari

 

Allah ne masani

Sanin hakan na wajen Allah

Har karshen zamani

255 bayan hijira

15 sha'aban

Mahadi