فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Ma'ad

 

Daga cikin asalan addini da rukunai da asasan sa da tushen sa: shi ne imani da makoma ranar kiyama, mutum musulmi yana imani da cewa lallai dukkanin wanda ya siffantu da rayuwa lallai za a dawowa da shi bayan mutuwa dawowa ta ruhi da gangar jiki, hakan ya tabbatu da dalilan hankali da nakali.

Hakika baki dayan musulmai sun yi ittifaki kan haka, ba da ban ma'ad ba da taklifi ya munana, lallai shi taklifi wahala ce dole ne ya kasance yana da wani mayi da sakamako, ta yiwu wannan mayi da sakamako ya zama bai kasantu cikin gidan duniya ba, kamar yadda muke shaida hakan, saboda haka dole ne a samu wani gida da wani wuri daban wanda shi ne ranar kiyama wacce cikin sa sakamako zai bayyanu.

Sannan raya jikkuna abu ne mai yiwuwa, Allah mai iko ne kan abubuwa masu yiwa baki dayan su, hakika mai gaskiya annabi (s.a.w) abin gasgatawa ya bamu labarin haka, sannan gabanin manzanni da annabawa ma haka, da wannan ne raya jikkuna zai kasance gaskiya, kamar yadda ayoyi da riwayoyi masu daraja suka shiryar zuwa ga hakan, suka yi inkari kan wanda yake jayayya da shi da gafala daga barin sa.

Lallai dawo da wanda yake da mayi ko kuma wanda kansa akwai mayi kamar misalin mutum wajibi ne, hakika ma'asumi (as) ya bamu labarin haka saboda haka dawo da matacce gaskiya ne babu kokwanto ciki.

Saboda haka ma'ad da tashin mutane bayan sun mutu da tara su ciki sabuwar halitta cikin wannan rana da akaiwa bayi alkawari hakika ce tabbatacciya, Allah zai sakawa masu da'a da biyayya zai kuma azabtar da masu sabo da azzalumai, sannan zai karbarwa wanda aka zalinta hakkin sa daga wanda ya zalunce shi, dukkanin wanda ya yi imani da mafara wajibi ne ya yi imani da ma'ad makoma, dukkanin wanda ya yi imani da annabta da imamanci ya zama tilas ya yi imani da makoma, shakka cikin ma'ad na lazimta shakka cikin ragowar asalan addini.

Kadai dai mun yi imani da makoma ta gangar jiki sakamakon bayanin da ya zo karara daga kur'ani mai girma:   

 (وَإنْ تَعْجَبْ فَعَجَبٌ قَوْلُهُمْ أإذَا كُنَّا تُرَابآ أئِـنَّا لَفِي خَلْقٍ جَدِيدٍ).

Idan za kai mamaki to mamakin kam shi ne fadin su shin yanzu idan mun kasance turbaya shin kuma lallai mu zamu kasance cikin sabuwar halitta.[1]

Da kuma da yawa daga ayoyi da hadisai masu daraja da suke shiyarwa zuwa ga haka, ba wani abu bane face dawo da mutum cikin ranar kiyama da gangar jikin sa da komo da shi zuwa hakikar sa ta farko bayan da ya wayi gari rududduge.

Jahili mai mamaki kan tashin mutum da komo da shi yana fadin:

 (مَنْ يُحْيِي العِظَامَ وَهِيَ رَمِيمٌ ) .

Wane ne zai raya kasusuwa alhalin suna rududduge.[2]

Kai kace shi ya manta yadda aka halicce shi da farko, hakika da babu shi, kuma yankunan jikin sa sun kasance gari, sai ya harhadu daga kasa har ya zamanto cikakken mutum madaidaici, sai ya manta da halittar sa:

 (أوَ لَمْ يَرَ الإنسَانُ أنَّا خَلَقْنَاهُ مِنْ نُطْفَةٍ فَإذَا هُوَ خَصِيمٌ مُبِين وَضَرَبَ لَـنَا مَثَلا وَنَسِيَ خَلْقَهُ ).

Ashe mutum bai gani ba lallai cewa mu mun halicce daga ruwan maniyyi ba sai gashi ya zama mai jayayya mai bayyanarwa* ya buga mana misali ya manta halittar sa.[3]

Me yafi kyawu da kayatarwa daga amsa da mahaliccin duniya ya bayar, wa yafi Allah gaskiyar magana:

 (يُحْيِيهَا الَّذِي أنشَأهَا أوَّلَ مَرَّةٍ وَهُوَ بِكُلِّ خَلْقٍ عَلِيمٌ ).

Yana raya su wanda ya kage su da farko shi ga kowacce halitta masani ne.[4]

Ya kai mutum rudadde, ya zama dole da mika wuya ka sallama ga wannan hakika wacce mai tadabburi da lura da kasantattu ya ba da labarinta, masani mai iko tsarki ya tabbatar masa madaukaki.

Wajibi ikirari da dukkanin abin da annabi (s.a.w) ya zo da shi kamar misalin magana kan siradi da mizani da magana da gabbai da tashin litattafai da afuwa da ceto da yadda mutane za su fito daga kaburburada halayen da za su samu kansu cikin tashin su da lada da ukuba da aljanna da ni'imomin cikinta da wuta da azabarta, sakamakon yiwuwar baki dayan haka, hakika mai gaskiya amintacce ya bada labari, wajibi ne a gasgata a karba ba tare da kowacce shakka da kokwanto ba.

Wannan kenan sannan ya kamata bayan imani da muslunci cikin asalan sa da rassan sa bawa ya tuba zuwa ga Allah ya tsarkake aikin sa, ya kuma kauracewa bin son rai da nafsu mai yawan umarni da mummuna ya nesanci shaidanu daga aljanu da mutane,

Ya nemi taimakon Allah kan haka, ya shagaltu da aikata abin da zai gyara duniyar sa da lahirar sa da kuma cikin abin da zai daukaka darajar sa wurin Allah har ya kasance wurin sarki mai ikon yi, ya kuma dunga zurfafa tunani cikin abin da zai nemi taimako da shi a kan nafsu din sa mai yawan umarni da mummuna, da cikin abin da zai fuskanta bayan mutuwa daga tsoro mai tsinkaya da abubuwan da za su biyo bayan masu tsanani daga fitar rai da tsanance-tsanancen kabari da hisabi da tambayar munkar da nakiri da tsorace-tsoraen duniyar barzahu, da hallara gaban sarki mabuwayi ranar tasowa daga kabari, yaji tsoran ranar da wata nafsu ba zata iya sakawa kanta da komai ba, ba kuma za a karbi wani ceto daga gareta ba, ba za a karbi wata fansa daga gareta ba kuma za a taimake su ba, ya kamata mutum ya siffantu da siffofi madaukaka da siffofin masu takawa, lallai mafi karamcinku wurin Allah shi ne mafi takawarku, kadai dai Allah yana karba daga masu takawa.

Mutane sashen su ya na fifita kan sashe cikin littafin Allah mai girma da abubuwa guda hudu:

Na farko: shi ne muslunci addini mai karkata zuwa ga gaskiya saboda fadin sa madaukaki:

 (وَمَنْ يَبْتَغِ غَيْرَ الإسْلامِ دِينآ فَلَنْ يُقْبَلَ مِنْهُ ).

Duk wanda ya nemi wani addini koma bayan muslunci ba za a karba daga gare shi.[5]

(إنَّ الدِّينَ عِنْدَ اللهِ الإسْلامُ )  .

Lallai addini wurin Allah shi ne muslunci.[6]

Na biyu kuma saboda fadin sa madaukaki:

 (إنَّ أكْرَمَكُمْ عِنْدَ اللهِ أتْقَاكُمْ ).

Lallai mafi karamcinku wurin Allah shi ne mafi takawarku.[7]

Na uku: saboda ilimi sakamakon fadin sa madaukaki:

 

 (يَرْفَعِ اللهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنْكُمْ وَالَّذِينَ اُوتُوا العِلْمَ دَرَجَاتٍ ) .

Allah yana daukaka darajar wadanda suka yi imani daga cikinku hakama da wadanda aka baiwa ilimi.[8]

Na hudu: jihadi, saboda fadin sa madaukaki:

 (وَفَضَّلَ اللهُ المُجَاهِدِينَ عَلَى القَاعِدِينَ أجْرآ عَظِيمآ).

Allah ya fifita masu jihadi kan masu zama da lada mai girma.

Da misalin wadannan kebantattun abubuwa bawa ke samun kusanci zuwa ga ubangijin sa, fifitawa da banbantawa da gabatar da wasu mutane kan wasu bai kasance da kyawun surar su ta zahiri bba, bawai don launin fata ba, bawai don daga kabila ko wata kungiya ba, ba da dukiya da kadarori bada sana'a da fasahar zamani ba, bawai don fin karfi ba da nuna fin karfi da zalunci da danniya ba, bawai don zinare da danyen man fetur da daloli ba, bawai don kwarewa a yaudara da siyasa da damfara da cinikin riba da jakantar da al'umma da mulkin mallaka ba, kadai dai da mau'aunan kur'anin Allah.

Allah ya sanya mu da ku daga cikin mafi alherin bayin sa, musulmai masu takawa, daga malamai mujahidai.


 

 [1] Ra'adu:5

[2]78Yasin:5

[3] Yasin:77-78

[4] Yasin:79

[5] Alu Imran:85

[6] Alu imran:19

[7] Hujrat:13

[8] Mujadala:11