فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani

 

Kur'ani mai girma da tsatso manzo mafi karamci (s.a.w)    

Muna imani da cewa lallai mafi alherin mai shiryarwa zuwa ga Allah mai girma da daukaka shi ne cika makin annabawa shugaban manzanni muahammad (s.a.w) da kuma cewa lallai farin cikin mutum cikin rayuwar sa da mutuwar sa suna cikin addinin muslunci, wannan addini mai kima, duk wanda ya nemi wani addini koma bayan sa ba za a karba daga gare shi ba, masdarin shari'ar muslunci cikin dukkanin zawiyoyin sa: shi ne kur'ani mai girma da sunna da ke misaltuwa cikin maganar ma'asumai, da aikinsu da abin da suka zartar, kur'ani da ma'asumai nauyaya biyu ne wadanda manzon (s.a.w) Allah ya barwa al’ummar sa.

 a wurare da dama yana mai fadin sa

«إنّي تارکٌ فيكم الثقلين : كتاب الله عزّ وجلّ ، وعترتي ، كتاب الله حبل ممدود بين السماء والأرض ، وعترتي أهل بيتي ، وإنّ اللطيف الخبير أخبرني أنّهما لن يفترقا حتّى يردا عليَّ الحوض ، فانظروا بماذا تخلفوني ».

Lallai ni cikin ku mai barin nauyaya guda biyu: su ne littafin Allah da tsatsona, littafin Allah mikakkiyar igiya ce tsakanin sama da kasa, da kuma tsatsona Ahlin gidana, lallai mai ludufi masani ya bani labari lallai cewa su biyun ba za su taba rabuwa da juna ba har sai sun gangaro tafkina ku duba kaka zaku halifantar dani cikinsu.[1]

وعن الصادق ، عن آبائه  :، قال  :

«سئل أمير المؤمنين   عن معنى قول رسول الله  9: (إنّي مخلّف فيكم الثقلين : كتاب الله وعترتي ) من العترة ؟ فقال : أنا والحسن والحسين والأئمة التسعة من ولد الحسين تاسعهم مهديّهم وقائمهم ، لا يفارقون كتاب الله ولا يفارقهم ، حتّى يردوا على رسول الله   حوضه ».

An karbo daga imam Sadik daga babannin sa (as) ya ce: an tambayi sarkin muminai Ali (as) dangane da ma'anar fadin manzon Allah (s.a.w) lallai ni ina halifantar da nauyaya biyu cikinku: littafin Allah da tsatsona, sai aka tambaye shi su waye tsatso? Sai ya ce ni da Hassan da Husaini da imamai tara daga `ya`yan Husaini na taransu shi ne mahadinsu mai tsayuwarsu, littafin Allah bai rabuwa da su suma basa rabuwa da shi, har sai sun gangaro tafkin manzon Allah (s.a.w).

Tsira da rabauta cikin farko da karshe kadai yana cikin biyayya ga kur'ani mai girma da Ahlil-baiti, a wannan lokaci ne mutum ke samun kammaluwa ya shiga cikin gayyar masu takawa.

Dukkanin su daga imani da takawa suna da alaka da dangantaka da juna suna karfafar juna, sannan imani ya na gabata da daukaka da girma cikin rutuba kan takawa, sai dai cewa kuma ba a samun kyakkyawan karshe face da takawa, babu shiriya face ga masu takawa.

Shi imani bayani ne kan kudurce rukunai biyar wadanda su ne: Tauhidi Adalci Annabta Imamanci da Ma'ad.

Sannan ita kuma takawa bayani ne kan zartar da abubuwan da Allah ya yi umarni da kuma nesantar abin da ya hana, sannan ita takawa tana da zahiri, shi ne takawar gabbai ta hanyar aikata da'a ta zahiri da kamewa daga ayyukan sabo bayyanannu, sannan tana da badini, shi ne: takawar zukata ta hanyar wofinta daga munanan halaye da cancada ado da kyawawan halaye.

Shi imani ilimi da kudurcewa ne, ita kuma takawa aiki ce da damdagatar.

Kan wannan akida ce zamu yi ishara zuwa ga ba'arin wasu ayoyi masu karamci da riwayoyi madaukaka, domin ita wannan akida cike take da dalilan hankali, zamu Ambato wani yanki daga ciki ta fuskanin takaitawa da kuma ishara cikin asalan addini da rassan sa, ba komai bace face tafkuna haskaye masu haskaka, da taurarin sama masu haske, da Allah muke neman dacewa


[1] Biharul-anwar: m 3 sh 104