فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Adalci

 

Adalcin Allah daga cikin kur'ani mai girma:

Allah madaukakin sarki ya ce:

 

 (إنَّ اللهَ لا يَظْلِمُ النَّاسَ شَيْئآ وَلَكِنَّ النَّاسَ أنْفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ ).

Lallai Allah ba ya zaluntar mutane sai dai cewa mutane ke zaluntar kawukan su.[1]

(قُلْ يَا أيُّهَا النَّاسُ قَدْ جَاءَكُمُ الحَقُّ مِنْ رَبِّكُمْ فَمَنْ آهْتَدَى فَإنَّمَا يَهْتَدِي لِنَفْسِهِ وَمَنْ ضَلَّ فَإنَّمَا يَضِلُّ عَلَيْهَا).

Kace yaku mutane hakika gaskiya ta zo muku daga ubangijinku dukkanin wanda ya shiriya kadai dai ya shiriya don kansa ne dukkanin wanda ya bata ya bata kanta ne.[2]

 

(إنَّ اللهَ لا يُغَيِّرُ مَا بِقَوْمٍ حَتَّى يُغَيِّرُوا مَا بِأنفُسِهِمْ ).

Lallai Allah ba ya canja abin da ke tare da mutane har sai sun canja da kawukan su.[3]

(مَنِ آهْتَدَى فَإنَّمَا يَهْتَدِي لِنَفْسِهِ وَمَنْ ضَلَّ فَإنَّمَا يَضِلُّ عَلَيْهَا وَلا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ اُخْرَى وَمَا كُنَّا مُعَذِّبِينَ حَتَّى نَبْعَثَ رَسُولا)

Duk wanda ya shiriyu kadai dai yana shiriya ne don kan sa duk wanda ya bata yana bata don kan sa wane rai ba zata dauki laifin wani rai ba bamu kasance masu azaba ba sai bayan mun aiko manzo.[4]

(وَقُلِ الحَقُّ مِنْ رَبِّكُمْ فَمَنْ شَاءَ فَلْيُؤْمِنْ وَمَنْ شَاءَ فَلْيَكْفُرْ).

Kace gaskiya ce daga ubangijinku duk wanda ya so sai yayi imani wanda kuma ya so sai ya kafirce[5]

(وَلا نُكَلِّفُ نَفْسآ إلاَّ وُسْعَهَا وَلَدَيْنَا كِتَابٌ يَنطِقُ بِالحَقِّ وَهُمْ لا يُظْلَمُونَ ) .

Bamu kallafawa wani rai face abin da ya yalwaceta garemu akwai littafin da yake magana da gaskiya su ba a zaluntarsu.[6]

(مَنْ كَانَ يُرِيدُ حَرْثَ الآخِرَةِ نَزِدْ لَهُ فِي حَرْثِهِ وَمَنْ كَانَ يُرِيدُ حَرْثَ الدُّنْيَا نُوتِهِ مِنْهَا وَمَا لَهُ فِي الآخِرَةِ مِنْ نَصِيبٍ ).

Duk wanda ke nufin noman lahira zamu kara masa cikin nomansa duk wanda ya kasance yana nufin noman duniya zamu bashi daga gareta sannan bai da wani rabo a lahira.[7]

(مَنْ عَمِلَ صَالِحآ فَلِنَفْسِهِ وَمَنْ أسَاءَ فَعَلَيْهَا) .

Duk wanda yayi aiki nagari to ga kansa duk wanda yayi mummuna ga kansa.[8]

(أمْ حَسِبَ الَّذِينَ آجْتَرَحُوا السَّيِّـئَاتِ أنْ نَجْعَلَهُمْ كَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ سَوَاءً مَحْيَاهُمْ وَمَمَاتُهُمْ سَاءَ مَا يَحْكُمُونَ ).

Yanzu wadanda suka aikata munanan ayyuka suna tsammanin mu sanya su daidai da wadanda suka yi imani kuma suka yi aiki nagari a rayuwar su da mutuwar su abin da suke hukuntawa ya munana[9]

(وَلِكُلٍّ دَرَجَاتٌ مِمَّا عَمِلُوا وَلِـيُوَفِّيَهُمْ أعْمَالَهُمْ وَهُمْ لا يُـظْـلَمُونَ ).

Ga kowanne akwai darajoji daga abin da suka aikata tabbas zai cika musu ayyukan su alhalin su ba a zaluntar su[10]

(وَنَـفْسٍ وَمَا سَوَّاهَافَألْهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَـقْوَاهَاقَدْ أفْلَحَ مَنْ زَكَّاهَاوَقَدْ خَابَ مَنْ دَسَّاهَا) .

da nafsu da abin da ya daidaita ta sai ya kimsa mata fajircinta da takawarta tabbas ya rabauta wanda ya tsaftaceta wanda uya turbude shi hakika ya tabe[11]

 (لَيْسَ لِلإنْسَانِ إلاَّ مَا سَعَى وَأنَّ سَعْيَهُ سَوْفَ يُرَى ) .

babu wani abu ga mutum face abin da yayi sa'ayi lallai sa'ayin sa da sannu za a ganshi.[12]

(مَنْ عَمِلَ صَالِحآ فَلِنَفْسِهِ وَمَنْ أسَاءَ فَعَلَيْهَا وَمَا رَبُّکَ بِظَـلاَّمٍ لِلْعَبِيدِ) .

Duk wanda ya aikata aiki nagari to ga kansa duk wanda ya munana ga kansa ubangijinka ba mai zaluntar bayi bane.[13]

(الَّذِي خَلَقَ المَوْتَ وَالحَيَاةَ لِـيَـبْلُوَكُمْ أيُّكُمْ أحْسَنُ عَمَلا وَهُوَ العَزِيزُ الغَفُورُ).

Wanda ya halicci mutuwa da rayuwa domin ya jarraba ku wane ne cikinku yafi kyawun aiki shi mabuwayi ne mai yawan gafara.[14]

(قُلْ أمَرَ رَبِّي بِالقِسْطِ).

Kace ubangijina yayi umarni da adalci.[15]

(إنَّ اللهَ يُحِبُّ المُقْسِطِينَ ).

Allah yana son masu adalci.[16]

Idan Allah ya kasance yana umarni da yin adalci yana kuma son masu yin adalci ta kaka shi Allah tsarki ya tabbatar masa madaukaki shi ba zai kasance adali ba?[1] Yunus:44

[2] Yunus:108

[3] Ra'adu:11

[4] Isara'i:15

[5][5] kahfu: 29

[6]muminun:62

[7] Muminun:62

[8] Shura:20

[9] Jasiya:21

[10] Ahkafu:19

[11] Shamsu:7-10

[12] Najamu:39-40

[13] Fussilat:46

[14] Muluk:2

[15] A'araf;29

[16] Mumtahanatu:8