فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Annabta kebantatta daga cikin kur'ani

 

Allah madaukaki yana cewa:

 (وَمَا مُحَمَّدٌ إلاَّ رَسُولٌ قَدْ خَلَتْ مِنْ قَبْلِهِ الرُّسُلُ ).

Muhammadu ba komai bane face manzo hakika manzanni sun gabata gabanin sa.[1]

(يَا أيُّهَا الرَّسُولُ بَلِّغْ مَا اُنزِلَ إلَيْکَ مِنْ رَبِّکَ وَإنْ لَمْ تَفْعَلْ فَمَا بَلَّغْتَ رِسَالَتَهُ وَاللهُ يَعْصِمُکَ مِنَ النَّاسِ إنَّ اللهَ لا يَهْدِي القَوْمَ الكَافِرِينَ ) .

Ya kai manzo ka isar da abin da ya aka saukar gareka daga ubangijinka idan baka aikata hakan ba baka isar da sakon sa ba Allah zai kareka daga mutane lallai Allah ba ya shiryar da mutane kafirai.[2]

(قُلْ يَا أيُّهَا النَّاسُ إنِّي رَسُولُ اللهِ إلَيْكُمْ جَمِيعآ الَّذِي لَهُ مُلْکُ السَّمَاوَاتِ وَالأرْضِ لا إلَهَ إلاَّ هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ فَآمِنُوا بِاللهِ وَرَسُولِهِ النَّبِيِّ الاُمِّيِّ الَّذِي يُؤْمِنُ بِاللهِ وَكَلِمَاتِهِ وَآتَّبِعُوهُ لَعَلَّكُمْ تَهْتَدُونَ ) .

Kace yaku mutane lallai ni manzon Allah ne gareku baki daya wanda gare shi mulkin sammai da kasa yake babu abin bauta da gaskiya yana rayawa yana kashewa kuyi imani da Allah da manzon sa annabi ummiyi wanda yake imani da Allah da kalmomin sa ku bishi tsammaninku kwa shiriya.[3]

(وَمَا أرْسَلْنَاکَ إلاَّ رَحْمَةً لِلْعَالَمِينَ ).

Bamu aiko ka ba face don rahama ga talikai.[4]

(وَمَا أرْسَلْنَاکَ إلاَّ كَافَّةً لِلنَّاسِ بَشِيرآ وَنَذِيرآ) .

Bamu aiko ka ba face ga dukkanin mutane mai bushara da gargadi.[5]

(مَا كَانَ مُحَمَّدٌ أبَا أحَدٍ مِنْ رِجَالِكُمْ وَلَكِنْ رَسُولَ اللهِ وَخَاتَمَ النَّبِيِّينَ ) .

Muhammad bai kasance uba ga kowa ba daga mazajenku sai dai cewa shi manzon Allah ne cikamakin annabawa.[6]

(ألَمْ نَشْرَحْ لَکَ صَدْرَکَ*وَوَضَعْنَا عَنکَ وِزْرَکَ*الَّذِي أنقَضَ ظَهْرَکَ*وَرَفَعْنَا لَکَ ذِكْرَکَ ) .

Ashe bamu buda maka kirjinka ba* muka dauke maka nauyinka* wanda ya nauyaya bayanka* muka daukaka ambatonka.[7]

(وَإذْ قَالَ عِيسَى آبْنُ مَرْيَمَ يَا بَـنِي إسْرَائِيلَ إنِّي رَسُولُ اللهِ إلَـيْكُمْ مُصَدِّقآ لِمَا بَـيْنَ يَدَيَّ مِنَ التَّوْرَاةِ وَمُبَشِّرآ بِرَسُولٍ يَأتِي مِنْ بَعْدِي آسْمُهُ أحْمَدُ فَـلَمَّا جَاءَهُمْ بِالبَـيِّـنَاتِ قَالُوا هَذَا سِحْرٌ مُبِينٌ ) .

Yayin da Isa dan maryama ya cewa banu Isra'ail lallai ni manzon Allah ne zuwa gareku mai gasgata abin da ke gabana daga attaura da injila kuma mai bushara da wani manzo da zai zo daga baya sunansa Ahmad yayin da ya zo musu da hujjoji sai suka ce wannan sihiri ne mabayyani.[8]

 (وَيَقُولُ الَّذِينَ كَفَرُوا لَسْتَ مُرْسَلا قُلْ كَفَى بِاللهِ شَهِيدآ بَـيْنِي وَبَـيْنَكُمْ وَمَنْ عِنْدَهُ عِلْمُ الكِتَابِ ).

Wadanda suka kafirce suna cewa kai ba manzo bane kace Allah ya isa shaida tsakanina da ku da wanda wurin ilimin littafi yake.[9]

(وَكَذَلِکَ أوْحَـيْنَا إلَيْکَ قُرْآنآ عَرَبِيّآ لِتُـنْذِرَ اُمَّ القُرَى وَمَنْ حَوْلَهَا وَتُـنْذِرَ يَوْمَ الجَمْعِ لا رَيْبَ فِيهِ فَرِيقٌ فِي الجَنَّةِ وَفَرِيقٌ فِي السَّعِيرِ).

Haka mukai wahayi zuwa gareka kur'ani da harshen larabci domin ka gargadi wadanda ke zauna a uwar alkaryu da wadanda ke kewaye da ita kayi gargadin ranar taro babu kokwanto cikinta wata kungiya cikin aljanna wata kungiyar kuma cikin wutar sa'ir.[10]

(قُلْ لا أسْألُكُمْ عَلَيْهِ أجْرآ إنْ هُوَ إلاَّ ذِكْرَى لِلْعَالَمِينَ ).

Kace ni bana tambayarku wani lada lallai shi ba komai bane face Ambato ga talikai.[11]

(فَإنْ أعْرَضُوا فَمَا أرْسَلْنَاکَ عَلَيْهِمْ حَفِيظآ إنْ عَلَيْکَ إلاَّ البَلاغُ ).

Idan suka bijire bamu aiko ka mai gadi ba kansu ba babu abin da ke kanka face isar da sako.[12]

(فَإنَّکَ لا تُسْمِـعُ المَوْتَى وَلا تُسْمِـعُ الصُّمَّ الدُّعَاءَ إذَا وَلَّوْا مُدْبِرِينَ وَمَا أنْتَ بِهَادِ العُمْيِ عَنْ ضَلالَتِهِمْ إنْ تُسْمِعُ إلاَّ مَنْ يُؤْمِنُ بِآيَاتِنَا فَهُمْ مُسْلِمُونَ ) .

Lallai kai baka jiyar da matattu ba kuma ka jiyar kurame kiranka idan sun juya suna masu juya baya lallai kai bamai shiryar da makafi bane daga batansu babu wanda kake jiyarwa face wadanda suke imani da ayoyinmu alhalin suna musulmi.[13]

(وَأنِ آحْكُمْ بَيْنَهُمْ بِمَا أنزَلَ اللهُ وَلا تَتَّبِعْ أهْوَاءَهُمْ وَآحْذَرْهُمْ أنْ يَفْتِنُوکَ عَنْ بَعْضِ مَا أنزَلَ اللهُ إلَيْکَ ).

Sannan kayi hukunci tsakanin su da Abin da Allah ya saukar kada kabi soye-soye ran su kayi taka tsantsan da su daga kada su fitanar dakai daga barin ba'arin abin da Allah ya suakar zuwa gareka.[14]

(هُوَ الَّذِي بَعَثَ فِي الاُمِّـيِّينَ رَسُولا مِنْهُمْ يَـتْلُو عَلَـيْهِمْ آيَاتِهِ وَيُزَكِّيهِمْ وَيُعَلِّمُهُمُ الكِتَابَ وَالحِكْمَةَ وَإنْ كَانُوا مِنْ قَبْلُ لَفِي ضَلالٍ مُبِينٍ ) .

Shi ne wanda ya aiko da manzo cikin wadanda basu san karatu da rubuta ba daga gare su yana karanta musu ayoyin sa yana tsarkake su yana koyar da su littafi da hikima duk da cewa gabanin sa sun kasance cikin bata mabayyani.[15]

(النَّبِيُّ أوْلَى بِالمُؤْمِنِينَ مِنْ أنْفُسِهِمْ ).

Annabi shi ne mafi cancanta da muminai daga kawukansu.[16]

(فَإنْ تَوَلَّوْا فَإنَّمَا عَلَيْکَ البَلاغُ المُبِينُ ).

Idan suka juya baya kadai dai abin da ke kanka shi ne isar da sako mabayyani.[17]

(هُوَ الَّذِي أرْسَلَ رَسُولَهُ بِالهُدَى وَدِينِ الحَقِّ لِـيُـظْهِرَهُ عَلَى الدِّينِ كُلِّهِ وَكَفَى بِاللهِ شَهِيدآ مُحَمَّدٌ رَسُولُ اللهِ وَالَّذِينَ مَعَهُ أشِدَّاءُ عَلَى الكُفَّارِ رُحَمَاءُ بَـيْنَهُمْ ) .

Shi ne wanda ya aiko da manzon sa da shiriya da addinin gaskiya domin ya bayyanar da shi kan adinin baki addini baki dayan sa Allah ya isar ya zama shaida Muhammadu manzon Allah kuma wadanda suke tare da shi masu tsanantawa ne kan kafirai masu jin kai tsakankanin junansu.[18]

(سُبْحَانَ الَّذِي أسْرَى بِعَبْدِهِ لَيْلا مِنَ المَسْجِدِ الحَرَامِ إلَى المَسْجِدِ الأقْصَى الَّذِي بَارَكْنَا حَوْلَهُ لِنُرِيَهُ مِنْ آيَاتِنَا إنَّه هُوَ السَّمِيعُ البَصِيرُ) .

Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyar dare da bawan sa ne daga masallacin harami zuwa masallacin Aksa wanda muka albarkanci daura da shi domin mu nuna masa daga ayoyinmu lallai shi mai ji ne mai gani ne.[19]

(يَا أيُّهَا المُزَّمِّلُ قُمِ اللَّيْلَ إلاَّ قَلِيلا نِصْفَهُ أوِ آنْقُصْ مِنْهُ قَلِيلا أوْ زِدْ عَلَيْهِ وَرَتِّلِ القُرْآنَ تَرْتِيلا إنَّا سَنُـلْقِي عَلَيْکَ قَوْلا ثَقِيلا).

Ya kai mai lullubi ka tashi dare face kadan rabinsa ko kuma ka dan tauyeshi kadan ko kuma ka kara ka jera karatun kur'ani jerawa lallai mu da sannu zamu wurga magani mai nauyi kanka.[20]

(وَمَا كَانَ لِرَسُولٍ أنْ يَأتِيَ بِآيَةٍ إلاَّ بِإذْنِ اللهِ فَإذَا جَاءَ أمْرُ اللهِ قُضِيَ بِالحَقِّ وَخَسِرَ هُـنَالِکَ المُـبْطِلُونَ)

Bai kasance ga manzon Allah ba ya zo da wata aya face da izinin Allah idan al'amarin Allah ya zo za a hukunta al'amarin Allah da gaskiya a can ne masu lalatawa za suyi hasara.[21]  

(وَمَنْ يُطِعِ اللهَ وَرَسُولَهُ يُدْخِلْهُ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِنْ تَحْتِهَا الأنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا وَذَلِکَ الفَوْزُ العَظِيمُ وَمَنْ يَعْصِ اللهَ وَرَسُولَهُ وَيَتَعَدَّ حُدُودَهُ يُدْخِلْهُ نَارآ خَالِدآ فِيهَا وَلَهُ عَذَابٌ مُهِينٌ ).

Duk wanda ya yi biyayya ga Allah ya yi biyayya ga manzon Allah zai shigar da shi aljannoni wacce a karkashinsu korama tana gudana madawwama cikinta wancan shi ne rabauta mai girma duk wanda ya sabawa Allah da manzon sa ya ketare iyakokin sa zai shigar da shi wuta yana mai dawwama cikinta gare shi akwai azaba wulakantatta.[22]

(آدْعُ إلَى سَبِيلِ رَبِّکَ بِالحِكْمَةِ وَالمَوْعِظَةِ الحَسَنَةِ وَجَادِلْهُمْ بِالَّتِي هِيَ

أحْسَنُ ).

Kayi kira zuwa ga tafarkin ubangijinka da hikima da wa'azi mai kyawu kayi ja dasu da wacce ita ce mafi kyawu.[23]

(إنَّ اللهَ وَمَلائِكَـتَهُ يُصَلُّونَ عَلَى النَّبِيِّ يَا أيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا صَلُّوا عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا تَسْلِيمآ) .

Hakika Allah da mala'ikun sa suna salati ga annabi yaku wadanda kukai imani kuyi salati gare shi ku salamma sallamawa sosai.[24]

Allah kayi salati kan shugaban manzanni cikamakin annabawa hujjar ubaginijin talikai da iyalan sa zababbu tsarkaka.

 [1] Alu Imran:144

[2] Ma'aida:67

[3] A'araf:158

[4] Anbiya'u:107

[5] Saba'i:28

[6] Ahzab:40

[7] Inshirah:1-4

[8] Saffi:6

[9] Ra'adu:43

[10] Shura:7

[11] An'am:90

[12] Shura:48

[13] Rum:52-53

[14] Ma'ida:49

[15] Juma'a:2

[16] Ahzab:6

[17] Nahlu:82

[18] Fatahu:28-29

[19] Isra'i:1

[20] Muzammil:1-5

[21] Mumin:78

[22] Nisa'i:13-14

[23] Nahlu:125

[24] Ahzab:56