فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja

 

ــ قال هشام بن الحكم : سأل الزنديق الذي أتى أبا عبد الله   فقال : من أين أثبت أنبياءً ورسلا؟

قال أبو عبد الله   :

«إنّما لمّا أثبتنا أنّ لنا خالقآ صانعآ متعاليآ عنّا وعن جميع ما خلق ، وكان ذلک الصانع حكيمآ، لم يجز أن يشاهده خلقه ولا يلامسوه ولا يباشرهم ولا يباشروه ، ويحاجّهم ويحاجّوه ، فثبت أنّ له سفراء في خلقه يدلّونهم على مصالحهم ومنافعهم وما به بقاؤهم ، وفي تركه فناؤهم ، فثبت الآمرون والناهون عن الحكيم العليم في خلقه وثبت عند ذلک أنّه له معبّرين وهم الأنبياء وصفوته من خلقه ، حكماء مؤدّبين بالحكمة مبعوثين بها غير مشاركين للناس في أحوالهم على مشاركتهم لهم في الخلق والتركيب ، مؤيّدين من عند الحكيم بالحكمة والدلائل والبراهين والشواهد، من إحياء الموتى وإبراء الأكمه والأبرص ، فلا تخلو أرض الله من حجّة ، يكون معه علم يدلّ على صدق مقال الرسول ووجوب عدالته » .

Hisham bn Hakam ya ce: zindiki wanda ya je wajen Abu Abdullah (as) ya tambaye shi sai ya ce: ta yaya zan iya tabbatar da annabawa da manzanni?

Sai Abu Abdullah (as) ya ce: kadai dai mun tabbatar da cewa muna da mahalicci makagi mai daukaka daga garemu daga dukkanin abin da ya halitta, wancan mahalicci ya kasance makagi mai hikima, bai halasta halittun sa su ganshi ba ko su shafe shi ko kuma ya taba su ko su taba shi, ko kuma suyi jayayya da shi shima ya yi jayayya da su, sai ya tabbata lallai shi yanada jakadu cikin halittun sa suna shiryar da su zuwa kan abubuwa da suke gyaran su ne da amfanonin su da abin da wanzuwar su take tare da shi cikin barin sa kuma karewar su take, sai masu umarni da hani suka tabbata daga mai hikima masani cikin halittun sa, ya kuma tabbata wannan lokaci cewa lallai shi yana da masu bayanin sa wadanda su ne annabawa da zababbun sa daga halittun sa, masu hikima masu ladabi da hikima wadanda aka aiko su da ita ba masu tarayya da mutane cikin yanayiyyikan su kan tarayyar su gare su cikin fasalin yadda aka halicce su da harhaduwar su, masu samu goyan baya da hikima da dalilai da hujjoji da shaidodi daga wurin Allah mai hikima. Daga raya matattu da warkar da kuturu da makaho, lallai kasa ba zata taba wofinta daga hujja Allah ba, wanda tare da shi akwai ilimi da ya ke shiryarwa zuwa ga gaskiyar maganar manzon Allah da wajabtin adalcin shi.[1]

   ــ وعن أبي الحسن الرضا  ، قال  :

«إنّما سمّي اُولو العزم لأنّهم كانوا أصحاب العزائم والشرائع ، وذلک أنّ كلّ نبيّ كان بعد نوح   كان على شريعته ومنهاجه وتابعآ لكتابه إلى زمن إبراهيم الخليل ، وكلّ نبيّ كان في أيام إبراهيم وبعده كان على شريعة إبراهيم ومنهاجه وتابعآ لكتابه إلى زمن موسى ، وكلّ نبيّ كان في زمن موسى وبعده كان على شريعة موسى ومنهاجه وتابعآ لكتابه إلى أيام عيسى ، وكلّ نبيّ كان أيام عيسى وبعده كان على منهاج عيسى وشريعته وتابعآ لكتابه إلى زمن نبيّنا محمّد  .

فهؤلاء الخمسة اُولوا العزم وهم أفضل الأنبياء والرسل   :، وشريعة محمّد لا تنسخ إلى يوم القيامة ، ولا نبيّ بعده إلى يوم القيامة ، فمن ادّعى بعده نبوّة أو أتى بعد القرآن بكتاب فدمه مباح لكلّ من سمع ذلک منه » .

Daga Abu Hassan Rida (as) ya ce: kadai an sanyawa annabawa ulul azmi wannan suna sakamakon sun kasance ma'abota azamomi da shari'a, hakan ya kasance, saboda lallai dukkanin annabin da ya zo bayan Nuhu (as) ya kasance kan shari'ar sa da tsarin sa mai bin littafin sa har zuwa zamanin Ibarahim masoyin Allah, dukkanin wani annabi lokacin Ibrahim da bayansa to ya kasance kan shari'arsa da tsarinsa da tafiya  kan littafin sa har zuwa zamanin Musa, haka dukkanin wani annabi a zamanin sa da bayan sa to yana kasancewa ne kan shari'ar sa da tsarinsa da tafiya kan littafin sa har zuwa zamanin Isa, haka shima dukkanin wani annabi a zamanin sa da bayan zamaninsa yana kan shari'arsa da tsarinsa da tafiya kan littafin sa har zuwa zamanin annabinmu Muhammad (s.a.w).

Wadannan annabawa biyar ulul azami su ne mafi falalar cikin annabawa da manzanni (as) sharia'ar Muhammad ba za a shafe ta ba har zuwa tashin kiyama, duk wanda bayansa ya yi da'awar annabta ko kuma bayan alkur'ani ya kawo wani littafi to jinin sa ya halasta daga dukkanin wanda ya ji hakan daga gare shi.[2]   

ــ وعن الحسين بن نعيم الصحّاف : قلت لأبي عبد الله  7: أيكون الرجل مؤمنآ قد ثبت له الإيمان ثمّ ينقله الله بعد الإيمان إلى الكفر؟

قال : «إنّ الله هو العدل ، وإنّما بعث الرسل ليدعوا الناس إلى الإيمان بالله، ولا يدعو أحدآ إلى الكفر».

قلت : فيكون الرجل كافرآ قد ثبت له الكفر عند الله فينقله الله بعد ذلک من الكفر إلى الإيمان ؟

قال : «الله عزّ وجلّ خلق الناس على الفطرة التي فطرهم الله عليها لا يعرفون إيمانآ بشريعة ولا كفرآ بجحود، ثمّ ابتعث الله الرسل إليهم يدعونهم إلى الإيمان بالله حجّة لله عليهم ، فمنهم من هداه الله ومنهم من له يهده ».

Daga Husaini bn Na'im Assahhaf: na cewa Abu Abdullah (as) shin mutum na kasancewa mumini hakika imani ya tabbatu gare shi sannan Allah bayan imanin ya dauke shi zuwa ga kafirci?

Sai ya ce: Allah shi ne adalci, kadai dai ya aiko manzanni domin suyi kira mutane zuwa ga imani da Allah ka da su kira kowa zuwa ga kafirci.

Sai na ce: sai mutum ya kasance kafiri hakika kafirci ya tabbata gare shi wurin Allah sai bayan haka sai Allah ya dauko shi daga kafirci zuwa imani?

Sai ya ce: Allah mabuwayi mai girma ya halicci mutane kan fidira wacce ya kage su kai basu san imani da shari'a ba haka kafirci da jayayya ba, sannan Allah ya aiko da manzanni zuwa gare su suna kiran su zuwa ga imani da Allah wanda hujjar Allah ce kansu, daga cikin su akwai wanda Allah ya shiryar da shi daga cikin su kuma akwai wanda Allah bai shiryar da shi ba.[3]   

ــ وعن الرضا  ، جوابآ لأحدهم  :

«فإن قال : فلِمَ وجب عليهم معرفة الرسل والإقرار بهم والإذعان لهم بالطاعة ؟ قيل : لأنّه لمّا لم يكن في خلقهم وقواهم ما يكملوا لمصالحهم ، وكان الصانع متعاليآ عن أن يرى وكان ضعفهم وعجزهم عن إدراكه ظاهرآ، لم يكن بدّ من رسول بينه وبينهم ، معصوم ، يؤدّي إليهم أمره ونهيه وأدبه ويقفهم على ما يكون به إحراز منافعهم ودفع مضارّهم ، إذا لم يكن في خلقهم ما يعرفون به ما يحتاجون إليه منافعهم ومضارّهم ، فلو لم يجب عليهم معرفته وطاعته لم يكن لهم في مجيء الرسول منفعة ولا سدّ حاجة ، ولكان يكون إتيانه عبثآ لغير منفعة ولا صلاح وليس هذا من صفة الحكيم الذي أتقن كلّ شيء».

Daga Rida (as) cikin amsa ga dayansu:

Ya ce: idan ya ce: to me yasa Allah ya wajabta sanin manzanni da ikirari da su da mika wuya da da'a gare su kansu? Sai ace: saboda yayin da abin da za su kammala maslahohin su bai kasance cikin halittar su da karfin su ba, sannan makagi ya kasance madaukaki daga barin ganin sa kuma raunin su da gazawar su daga riskar zahiri ya kasance, sai ya zama babu wata makawa daga sanya jakada manzo tsakanin sa da tsakanin su, wanda zai kasance ma'asumi da zai sauke umarnin sa gare su da hanin sa da ladabin sa ya kuma tsinkayar da su kan abin da zai tabbatar da amafanin su da tunkude cutuwar su, saboda cikin halittar su abin da za su sani da shi da abin da za su bukatu da shi zuwa ga amfanin su da cutuwar su bai kasance ba, da bai wajabta sanin sa da da'arsa kansu ba da zuwar manzanni bai kasance mai wani amfani gare su ba da toshe bukata, da lallai ya kasance kasantuwar zuwansa wargi ne da wasa kawai da rashin kawo gyara wana hakan ba ya daga cikin siffar mai hikima wanda ya kyawunta komai[4]

ــ وعن أبي بصير، قال : قلت لأبي عبد الله  : لأيّ علّة أعطى الله عزّ وجلّ أنبياءه ورسله وأعطاكم المعجزة ؟

فقال : ليكون دليلا على صدق ما أتى به ، والمعجزة علامة لا يعطيها إلّا أنبياءه ورسله وحججه ليعرف به صدق الصادق من كذب الكاذب.

Daga Abu Basir, ya ce: na cewa Abu Abdullah (as) da wanne dalili Allah mabuwayi mai girma ya baiwa annabawansa da manzanninsa da ku mu'ujiza?

Sai ya ce: domin ya kasance dalili kan gaskiyar abin da ya zo da shi, ita mu'ujiza alama ce da bai bayar da ita face ga annabawan sa da manzannin sa da hujjojin sa domin a san gaskiyar mai gaskiya daga karyar makaryaci[5]

ــ وقال عليّ بن محمّد بن الجهم لمولانا الرضا : يا بن رسول الله، أتقول بعصمة الأنبياء؟ قال:  بلى.

Aliyu bn Jaham ya cewa shugabanmu Rida (as) ya dan manzon Allah, shin kai ma ka yi imani da ma'sumancin annabawa?

Sai ya ce: na'am.[6]

ــ وقال أمير المؤمنين  7 في ضمن خطبة له  :

«فبعث محمّدآ  9 بالحقّ ليخرج عباده من عبادة الأوثان إلى عبادته ، ومن طاعة الشيطان إلى طاعته ، بقرآن قد بيّنه وأحكمه ليعلم العباد ربّهم إذ جهلوه ، وليقرّوا به إذ جحدوه ، وليثبتوه بعد إذ أنكروه ، فتجلّى سبحانه لهم في كتابه من غير أن يكونوا رأوه بما أراهم من قدرته ...» .

Sarkin muminai (as) cikin wata hudubar sa ya ce: sai Allah ya aiko da Muhammad (s.a.w) da gaskiya domin ya fitar da bayin sa daga bautar gumaka zuwa ga bautar Allah, daga da'a ga shaidan zuwa da'ar ga Allah, da kur'ani hakika ya bayyana hukunce-hukuncen sa domin bayi su san waye ubangijinsu idan suka jahilce shi, domin suyi ikirari da shi idan sun yi jayayya da samuwar sa, domin su tabbatar da shi bayan da sun yi inkarinsa, sai tsarki ya tabbatar masa yayi tajalli gare su cikin littafin sa ba tare da sun ganshi da ido da abin da ya nuna musu daga ikonsa.[7]

ــ وقال   :

«ثمّ إنّ الله بعث محمّدآ   بالحقّ حين دنا من الدنيا الانقطاع ، وأقبل من الآخرة الاطلاع ، وأظلمت بهجتها بعد إشراق ، وقامت بأهلها على ساق ، وخشن منها مهاد... ـإلى أن يقول :ـ ثمّ أنزل عليه الكتاب نورآ لا تطفأ مصابيحه ، وسراجآ لا يخبو توقّده ، وبحرآ لا يدرک قعره ، ومنهاجآ لا يضلّ نهجه ، وشعاعآ لا يظلم ضوءه ، وفرقانآ لا يخمد برهانه ، وتبيانآ لا تهدم أركانه ، وشفاء لا تخشى أسقامه ، وعزّآ لا تهزم أنصاره ، وحقّآ لا تخذل أعوانه ، فهو معدن الإيمان وبحبوحته ، وينابيع العلم وبحوره ، ورياض العدل وغدرانه ، وأثافي الإسلام وبنيانه ...».

Amincin Allah ya kara tabbata gare shi ya ce: sannan ya aiko da Muhammad (s.a.w) da gaskiya lokacin da yankewa daga duniya ta kusanto tsinkaya zuwa ga lahira ta fuskanto, duniya ta duhuntar da haskenta bayan haskawar sa, ta mikar da wanda ke cikinta tsaye kan kwauri, makwanci ya yi kaushi…har zuwa inda yake cewa-sannan ya saukar masa da littafi haske da fitilun sa basa mutuwa.

 Fitila wacce kunnuwar ta bai bushewa, tafki da ba a cimma kasan sa hanyar da ba ta batar da wanda ya bi ta, kyalkyali da hasken sa baya yin duhu, mai banbancewa wanda ba a rusa hujjojin sa, bayani filla-filla ba a iya rusa rukunansa, waraka da ba a tsoran cututtukan sa, buwayar da ba cin nasara kan mataimakanta, gaskiya da ba ta tozarta mataimakanta, shi ne ma'adanin imani da farfajiyar sa, mabubbugan ilimin tafkunansa, dausayin adalci da tsirran sa, turakun muslunci da ginin sa[8]


[1] Biharul-anwar: m 11 sh 29

[2] Biharul-anwar: m 11 sh 34

[3] Biharul-anwar: m 11 sh 40

[4] Biharul-anwar:  m 11 sh 40 daga liattafin ialalul shara'I da littafin uyunu akbarul rida

[5] Biharrul-anwar: m 11 sh 71

[6] Biharul-anwar: m 11 sh 71

[7] Nahjul balaga:317

[8] Nahjul balaga:317