فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Imamanci

 

Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'ani:

Fadin Allah madaukaki:

 (يَا أيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا آتَّـقُوا اللهَ وَكُونُوا مَعَ الصَّادِقِينَ ).

Yaku wadanda suka yi imani kuji tsoran Allah sannan ku kasance tare da masu gaskiya.

(يَا أيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا أطِيعُوا اللهَ وَأطِيعُوا الرَّسُولَ وَاُوْلِي الأمْرِ مِنْكُمْ فَإنْ تَـنَازَعْتُمْ فِي شَيْءٍ فَرُدُّوهُ إلَى اللهِ وَالرَّسُولِ ).

Yaku wadanda suka yi imani kiyi da'a ga Alah kuyi da'a ga manzon Allah da ma'abota al'amari daga cikinku idan kun samu sabani da juna cikin wani abu to ku dawo da shi zuwa ga Allah da manzon Allah.[1]

(وَإذا جَاءَهُمْ أمْرٌ مِنَ الأمْنِ أوْ الخَوْفِ أذَاعُوا بِهِ وَلَوْ رَدُّوهُ إلَى الرَّسُولِ وَإلَى اُوْلِي الأمْرِ مِنْهُمْ لَعَلِمَهُ الَّذِينَ يَسْتَنْبِطُونَهُ مِنْهُمْ وَلَوْلا فَضْلُ اللهِ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَتُهُ لاتَّبَعْتُمُ الشَّيْطَانَ إلاَّ قَلِيلا).

Idan wani al'amari ya zo musu daga aminci ko tsora sai su yada shi da ace sun dawo da shi zuwa ga manzon Allah zuwa ga ma'abota al'amari daga cikin su da wadanda za su tsamo shi daga cikin su tabbas sun san shi ba da ban falalar Allah kanku da rahamarsa da tabbas kun bi shaidan face yan tsiraru.[2]

(وَمِمَّنْ خَلَقْنَا اُمَّةٌ يَهْدُونَ بِالحَقِّ وَبِهِ يَعْدِلُونَ ).

Daga cikin wadanda muka halitta akwai wata al'umma da suke shiryarwa da gaskiya da ita kuma suke adalci.[3]

(إنَّمَا أنْتَ مُنذِرٌ وَلِكُلِّ قَوْمٍ هَادٍ) .

Kadai dai kai mai gargadi ne ga kowacce al'umma tana da mai shiryar da ita.[4]

(إنَّ اللهَ اصْطَفَى آدَمَ وَنُوحآ وَآلَ إبْرَاهِيمَ وَآلَ عِمْرَانَ عَلَى العَالَمِينَ ذُرِّيَّةً بَعْضُهَا مِنْ بَعْضٍ وَاللهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ ).

Lallai Allah ya zabi Adamu da Nuhu da Alu Ibrahim da Alu Imrana kan talikai zuriya ce sashen su ga sashe Allah mai ji ne masani.[5]

(وَإذِ ابْتَلَى إبْرَاهِيمَ رَبُّهُ بِكَلِمَاتٍ فَأتَمَّهُنَّ قَالَ إنِّي جَاعِلُکَ لِلنَّاسِ إمَامآ قَالَ وَمِنْ ذُرِّيَّتِي قَالَ لا يَنَالُ عَهْدِي الظَّالِمِينَ ).

Yayin da ubagijin Ibrahim ya jarraba shi da wasu kalmomi sai ya cikasu ya ce lallai ni mai sanya imami ga mutane ne ya ce daga zuriyata ma ya ce azzalumi baya samun alkawari na.[6]

(وَكَذَلِکَ جَعَلْنَاكُمْ اُمَّةً وَسَطآ لِتَكُونُوا شُهَدَاءَ عَلَى النَّاسِ وَيَكُونَ الرَّسُولُ عَلَيْكُمْ شَهِيدآ).

Hakama na sanyaku al'umma tsakankani domin ku zamanto masu shaida ga mutane manzon Allah ya zama shaida kanku.[7]

(قُلْ كَفَى بِاللهِ شَهِيدآ بَـيْنِي وَبَـيْنَكُمْ وَمَنْ عِنْدَهُ عِلْمُ الكِتَابِ ) .

Kace Allah ya isa zama shaida tsakanina da tsakaninku da wanda ilimin littafi ke wurin sa.[8]

(إنَّمَا وَلِيُّكُمُ اللهُ وَرَسُولُهُ وَالَّذِينَ آمَنُوا الَّذِينَ يُقِيمُونَ الصَّلاةَ وَيُؤْتُونَ الزَّكَاةَ وَهُمْ رَاكِعُونَ ) .

Kadai dai majibanci al'amarinku shi ne Allah da manzon sa da wadanda suka bada imani suke tsayar da sallah suke bada zakka alhalin suna masu ruku'u.[9]

(فَمَنْ حَاجَّکَ فِيهِ مِنْ بَعْدِ مَا جَاءَکَ مِنَ العِلْمِ فَقُلْ تَعَالَوْا نَدْعُ أبْنَاءَنَا وَأبْنَاءَكُمْ وَنِسَاءَنَا وَنِسَاءَكُمْ وَأنْفُسَنَا وَأنْفُسَكُمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَلْ لَعْنَةَ اللهِ عَلَى الكَاذِبِينَ ) .

Duk wanda yayi maka jayayya cikinsa bayan abin da ya zo maka da ilimi kace ku zo mu kirayi `ya`yayenmu da `ya`yayanku da matayanmu da matayenku da kawukanmu da kawukanku sannan mu kankantar da kai mu sanya tsinuwar Allah kan makaryata.[10]

 (أفَمَنْ يَهْدِي إلَى الحَقِّ أحَقُّ أنْ يُتَّبَعَ أمَّنْ لا يَهِدِّي إلاَّ أنْ يُهْدَى فَمَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ ).

Shin yanzu wanda yake shiryarwa zuwa gaskiya shi yafi cancanta aiwa biyayya ko kuma wanda baya shiryarwa sai shima a shiryar da shi me ya faru da kune kaka kuke hukunci.[11]

(اليَوْمَ يَئِسَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ دِينِكُمْ فَلا تَخْشَوْهُمْ وَآخْشَوْنِي اليَوْمَ أكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ وَأتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الإسْلامَ دِينآ) .

Yau ne wadanda suka kafirce suka debe tsammani daga addiniku kada kuji tsoran su kuji tsorona yau ne na kammala muku addininku na cika muku ni'imata kanku na yardar muku da muslunci addini.[12]

(يَا أيُّهَا الرَّسُولُ بَلِّغْ مَا اُنزِلَ إلَيْکَ مِنْ رَبِّکَ وَإنْ لَمْ تَفْعَلْ فَمَا بَلَّغْتَ رِسَالَتَهُ وَاللهُ يَعْصِمُکَ مِنَ النَّاسِ إنَّ اللهَ لا يَهْدِي القَوْمَ الكَافِرِينَ ).

Ya kai manzon Allah ka isar da sakon da aka sauke gareka daga ubangijinka idan ba kai ba to baka isar da sakon sa ba Allah zai kareka daga mutane lallai Allah baya shiryar da mutane kafirai.[13]

(وَقِفُوهُمْ إنَّهُمْ مَسْؤُولُونَ ) .

Ku dagatar da su lallai su ababen tambaya ne.[14]

(فَلَنَسْألَنَّ الَّذِينَ اُرْسِلَ إلَيْهِمْ وَلَنَسْألَنَّ المُرْسَلِينَ ).

Lallai mu za mu tambayi wadanda aka aiko da manzanni zuwa gare su lallai kuma zamu tambayi wadanda aka aiko din.[15]

(وَمِنْهُمُ الَّذِينَ يُؤْذُونَ النَّبِيَّ وَيَقُولُونَ هُوَ اُذُنٌ قُلْ اُذُنُ خَيْرٍ لَكُمْ يُؤْمِنُ بِاللهِ وَيُؤْمِنُ لِلْمُؤْمِنِينَ ) .

Daga cikin su akwai wadanda suke cutar da annabi suna kuma cewa shi kunne ne mai sauraren labarai kace kunne yafi alheri gareku yana imani da Allah yana imani ga muminai.[16]

(وَإذْ قَالَ رَبُّکَ لِلْمَلائِكَةِ إنِّي جَاعِلٌ فِي الأرْضِ خَلِيفَةً قَالُوا أتَجْعَلُ فِيهَا مَنْ يُفْسِدُ فِيهَا وَيَسْفِکُ الدِّمَاءَ وَنَحْنُ نُسَبِّحُ بِحَمْدِکَ وَنُقَدِّسُ لَکَ قَالَ إنِّي أعْلَمُ مَا لا تَعْلَمُونَ وَعَلَّمَ آدَمَ الأسْمَاءَ كُلَّهَا ثُمَّ عَرَضَهُمْ عَلَى المَلائِكَةِ فَقَالَ أنْبِئُونِي بِأسْمِاءِ هَؤُلاءِ إنْ كُنتُمْ صَادِقِينَ قَالُوا سُبْحَانَکَ لا عِلْمَ لَـنَا إلاَّ مَا عَلَّمْتَنَا إنَّکَ أنْتَ العَلِيمُ الحَكِيمُ قَالَ يَا آدَمُ أنْبِئْهُمْ بِأسْمِائِهِمْ فَلَمَّا أنْبَأهُمْ بِأسْمِائِهِمْ قَالَ ألَمْ أقُلْ لَكُمْ إنِّي أعْلَمُ غَيْبَ السَّمَاوَاتِ وَالأرْضِ وَأعْلَمُ مَا تُبْدُونَ وَمَا كُنتُمْ تَكْتُمُونَ ) .

Yayinda ubangijinka ya cewa mala'iku lallai ni mai sanya halifa ne a ban kasa sai suka ce yanzu zaka sanya wanda zai bar

na cikinta ya zubar da jini alhalin mu muna tasbihi da godiyarka muna tsarkakeka ya ce lallai ni na san abin da baku sani ba ya sanar da Adamu sunaye baki dayan su sannan ya bijiro da su kan mala'iku sai ya ce ku bani labarin sunayen wadannan idan kun kasance masu gaskiya sai suka ce tsarki ya tabbatar maka bamu sani garemu face abin da ka sanar da mu lallai kai masani ne mai hikima ya ce ya Adamu basu labarin sunayen wadannan yayin da ya basu labarin sunayen su sai ya ce ashe ban gaya muku lallai ni na san gaibun sammai da kasa na kuma san abin da kuke bayyanarwa da abin da kuke boyewa.[17]

(إنَّمَا يُرِيدُ اللهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أهْلَ البَـيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرآ) .

Kadai dai Allah yana nufin tafiyar da duk wata datti daga gareku Ahlil-baiti ya tsarkake ku tsarkakewa sosai.[18]

(قُلْ لا أسْألُكُمْ عَلَيْهِ أجْرآ إلاَّ المَوَدَّةَ فِي القُرْبَى وَمَنْ يَـقْتَرِفْ حَسَنَةً نَزِدْ لَهُ فِيهَا حُسْنآ إنَّ اللهَ غَفُورٌ شَكُورٌ).

Kace bana tambayar wani lada face soyayya cikin makusanta duk wanda ya aikata kyakkyawa zamu kara masa kyawu cikinta lallai Allah mai yawan gafara da godiya ne.[19]

(وَقُلِ آعْمَلُوا فَسَيَرَى اللهُ عَمَلَكُمْ وَرَسُولُهُ وَالمُؤْمِنُونَ وَسَتُرَدُّونَ إلَى عَالِمِ الغَيْبِ وَالشَّهَادَةِ فَيُنَبِّـئُكُمْ بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ ) .

Kace kuyi aiki da sannu Allah da manzo za su ga aikinku da muminai sannan da sannu zaku gangaro zuwa ga masanin gaibu da bayyane sai ya baku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.[20]

Wannan kenan da kuma daruruwan ayoyi masu daraja da suke shiryarwa kan larura da wajabcin imamanci da halifanci da bayanin siffofin A'imma masu shiryarwa halifofi ma'asumai bayan manzon mafi karamci (s.a.w) ya kamaceku ku komawa tafsirai da litattafan hadisai da kalam daga bangarori biyu sunna da shi'a.[1] Tauba:119

[2] Nisa'i:83

[3] A'araf:181

[4] Ra'adu:7

[5] Alu imra:33-34

[6] Bakara:124

[7] Bakara:143

[8] Ra'adu:43

[9] Ma'ida:55

[10] Alu Imran:61

[11] Yunus:35

[12] Ma'ida:3

[13] Ma'ida:67

[14] Saffat:24

[15] A'araf:6

[16] Tauba:61

[17] Bakara:30-33

[18] Ahzab:33

[19] Shura;23

[20] Tauba: 105