فهرست کتاب‌‌ لیست کتاب‌ها
■ SADAUKARWA
■ Kalmar mu'assasa
■ ASALAN ADDINI (USULUD DINI)
■ ASALI NA FARKO
■ dalilai kan tabbatar da samuwar mahalicci
■ Mukami na biyu
■ Asali na biyu
■ Adalci
■ Annabta
■ Asali na uku daga Asalan addini
■ Mukami na farko annabta game gari
■ sharuddan annabi
■ mukami na biyu
■ Annabta kebantacciya
■ Asali na biyu
■ Imamanci
■ Mukami na farko
■ Imamanci gamamme
■ Mukami na biyu
■ Imamanci kebantacce
■ Asali na biyar
■ Ma'ad
■ Asalan addini cikin ma'auni da sikelin kur'ani
■ Tauhidi
■ Tauhidi cikin hadisai
■ Siffofin rububiya cikin kur'ani mai daraja
■ babin jawami'ul tauhid
■ Adalci
■ Adalcin Allah daga cikin madaukakan hadisai
■ Annabta
■ Annabta gamammiya daga cikin kur'ani mai girma
■ Annabta kebantatta daga cikin kur'ani
■ Annabta gamammiya a kebantatta daga cikin hadisai masu daraja
■ Imamanci
■ Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja
■ Ma'ad
■ Kiyama
■ Ma'ad daga cikin riwayoyi masu daraja
■ Tauhidi
■ Adalci
■ Annabta
■ Imamanci
■ Ma'ad
■ Munajatin Arifai
■ FURU'UD DINI
■ RESHE NA FARKO
■ SALLAH
■ Cikin falalar mai sallah
■ iyakokin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai kushu'i
■ Daga cikin ladubba akwai tsantseni daga haramun
■ Daga cikin laubba akwai halarto da zuciya cikin sallah
■ Daga cikin ladubba akwai tadabburi cikin sallahDaga cikin ladubba akwai rashin jin kasala cikin sallah
■ Daga cikin ladubba kiyayewa sallah kan lokaci
■ Na kwadaitar da ku zuwa ga abubuwan da suka taro ladubban sallah
■ Reshe na biyu
■ Azumi
■ Amma dalilin sanya azumi da hikimarsa wajabta shiYa zo cikin falalar mai azumi
■ Cikin ladubban azumi
■ Amma gadon azumi da kufaifayinsa da yake haifarwa
■ 
■ Reshe na uku
■ Zakka
■ Cikin hikimar zakka da illar wajabcinta
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na hudu
■ Kumusi
■ Reshe na biyar
■ Jihadi
■ Reshe na shida
■ Hajji
■ RASSA GUDA BIYU NA RESHE NA BAKWAI DA NA TAKWAS
■ Umarni da kyakkyawa da hani da mummuna
■ Rassa biyu reshe na tara da na goma
■ Wilaya da bara'a
■ HATTAMAWA

Imamanci gamamme da kebantacce daga kur'aniImamanci gamamme da kebantacce daga hadisai masu daraja

 

ــ عن العبد الصالح الإمام موسى بن جعفر  7، قال  :

«إنّ الحجّة لا تقوم لله على خلقه إلّا بإمام يعرف ».

Daga bawan Allah nagari imam Musa bn Jafar (as) ya ce: lallai hujja ba ta tsayu ba kan halittun sa face da imam da za a san shi.[1]

ــ وعن إسحاق بن عمّار، قال : سمعته ـأي الإمام الصادق  7ـ يقول  :

«إنّ الأرض لا تخلو إلّا وفيها إمام كيما إن زاد المؤمنون شيئآ ردّهم ، وإن نقصوا شيئآ أتمّه لهم

Daga Is'hak bn Ammar ya ce: na ji Imam Sadik (as) yana cewa: lallai kasa ba zata taba wofinta ba face cikinta akwai imami idan muminai son kara wani abu sai ya mayar musu, idan sun tauye wani abu sai ya cika shi gare su.

ــ وعن أبي عبد الله  7، قال  :

«إنّ الله أجلّ وأعظم من أن يترک الأرض بغير إمامٍ عادل ».

Daga Abu Abdullah (as) ya ce: lallai Allah ya girma ya girmama daga ya bar kasa ba tare da sanya imami adali.

ــ وعن أبي جعفر  قال  :

«والله ما ترک أرضآ منذ قبض آدم  7 إلّا وفيها إمام يهتدى به إلى الله، وهو حجّته على عباده ، ولا تبقى الأرض بغير إمام حجّة لله على

عباده ».

Daga Abu Jafar (as) ya ce: Allah bai bar kasa haka ba tun lokacin da ya karbi ran Adamu (as) face sai ya sanya imami cikinta wanda za a shiriya da shi zuwa ga Allah, shi hujjar Allah ne kan bayin sa, kasa bata wanzuwa ba tare da imami hujjar Allah kan bayin sa ba.

ــ وعن أبي حمزة ، قال : قال لي أبو جعفر  : «إنّما يعبد الله من يعرف الله، فأمّا من لا يعرف فإنّما يعبده هكذا ضلالا».

Daga Abu Hamza, ya ce: Abu Jafar (as) ya ce mini: kadai wanda ya san Allah ke bautawa Allah. Amma wanda bai san shi ba kadai yana bauta ne haka a bace.

قلت : جعلت فداک ، فما معرفة الله؟

قال : «تصديق الله عزّ وجلّ ، وتصديق رسوله  ، وموالاة عليّ   والائتمام به وبأئمة الهدى  :، والبراءة إلى الله عزّ وجلّ من عدوّهم ، هكذا يعرف الله عزّ وجلّ ».

Raina fansarka, mene ne sanin Allah?

Sai ya ce: gasgata Allah mabuwayi mai girma, da gasgata zancen manzon sa (s.a.w) da wilaya ga Ali da biyayyya ga imaman shiriya, da bara'a zuwa ga Allah mabuwayi mai girma daga makiyin su, haka ake sanin Allah mai girma mabuwayi.

ــ وروى الفريقان عن الرسول الأكرم  :

«من مات ولم يعرف إمام زمانه مات ميتة الجاهلية ».

Bangarori biyu daga shi'a da sunna sun rawaito daga manzo mafi karamci (s.a.w): duk wanda ya mutu bai san imamin zamanin sa ba ya mutu mutuwar jahiliya.

ــ عن أمير المؤمنين  ، قال  :

«إنّ الله تبارک وتعالى طهّرنا وعصمنا وجعلنا شهداء على خلقه وحجّته في أرضه ، وجعلنا مع القرآن ، وجعل القرآن معنا، لا نفارقه ولا يفارقنا».

An karabo daga sarkin muminai (as) fadin sa: lallai Allah albarku sun tabbatar masa madaukaki ya tsarkake mu ya katangemu ya sanya mu masu bada shaida kan halittunsa hujjojin sa cikin kasa, ya kuma sanya mu tare da kur'ani ya kuma sanya kur'anin tare da mu, bama rabuwa da shi shima baya rabuwa da mu.

ــ يقول أبو عبد الله   :

«نحن ولاة أمر الله، وخزنة علم الله، وعيبة وحي الله».

Abu Abdullah (as) yana cewa: mu ne majibanta al'amari, taskar ilimin Allah, mazubin wahayin sa.

ــ وعن أبي الحسن الرضا   :

«الأئمة خلفاء الله عزّ وجلّ في أرضه ».

Daga Abu Hassan Rida (as) A'imma halifofin Allah ne mabuwayi mai girma cikin kasa.

قال ابو عبد الله:

«الأوصياء هم أبواب الله عزّ وجلّ التي يؤتى منها، ولولاهم ما عرف الله عزّ وجلّ ، وبهم احتجّ الله تبارک وتعالى على خلقه ».

Abu Abdullah (as) ya ce: wasiyyai su ne kofofin Allah mabuwayi mai girma da ake zuwar masa daga gare su, ba da ban su ba da ba a san Allah mabuwayi mai girma, da su Allah albarku sun tabbatar masa madaukaki ya kafa hujja kan halittun sa.

ــ وقال داود الجصّاص : سمعت أبا عبد الله  7 يقول  :

«(وَعَلامَاتٍ وَبِالنَّجْمِ هُمْ يَهْتَدُونَ )[2] ، قال : النجم رسول الله،

والعلامات هم الأئمة  :».

Dauda Jassas ya ce: na ji Abu Abdullah (as) yana cewa: (kuma da alamomi da tauraro su suke shiriya)[3] tauraro shi ne manzon Allah (s.a.w) sannan alamomi su ne A'imma (as)

ــ وعن أبي جعفر  ، قال  :

«لمّا نزلت هذه الآية (يَوْمَ نَدْعُو كُلَّ اُنَاسٍ بِإمَامِهِمْ ) ، قال

المسلمون : يا رسول الله، ألست إمام الناس كلّهم أجمعين ؟ قال : فقال رسول الله : أنا رسول الله إلى الناس أجمعين ، ولكن سيكون من بعدي أئمة على الناس من الله من أهل بيتي يقومون في الناس فيكذّبون ويظلمهم أئمة الكفر والضلال وأشياعهم ، فمن والاهم واتّبعهم وصدّقهم فهو منّي ومعي وسيلقاني ، ألا ومن ظلمهم وكذّبهم فليس منّي ولا معي وأنا منه بريء».

Daga Abu Jafar (as) ya ce: lokacin da wannan aya ta sauka (ranar da zamu kira kowanne mutane da imamin su)[4]

musulmi sun ce: ya manzon Allah, bakai ne imamin dukkanin mutane baki dayan su ba? Sai manzon Allah ya ce: ni manzon Allah ne zuwa ga mutane baki dayansu, sai dai cewa da sannu imamai daga Ahlin gidana bayana za su kasance jagorori daga Allah kan mutane, za su tsaya cikin mutane sai mutane su karyata su jagororin kafirci da bata da mabiyansu su zalunce su, duk wanda ya jibance su ya bisu ya gasgata su lallai shi yana daga gareni yana tare da ni zai kuma hadu dani, ku saurara duk wanda ya zalunce su ya karyata su ba ya tare da ni, ni kuma na barranta daga gare shi.

ــ وقال يعقوب بن شعيب : سألت أبا عبد الله عن قول الله عزّ وجلّ  : (آعْمَلُوا فَسَيَرَى اللهُ عَمَلَكُمْ وَرَسُولُهُ وَالمُؤْمِنُونَ ) ؟ قال : هم الأئمة .

Yakubu bn Shu'aibu ya ce: na tambayi Abu Abdullah (as) dangane da fadin Allah mai girma mabuwayi: (kuyi aiki da sannu Allah da manzon sa da muminai za su ga aikinku)[5] sai ya ce muminai su ne A'imma (as)

ــ وقال أمير المؤمنين   :

«إنّا أهل البيت شجرة النبوّة وموضع الرسالة ومختلف الملائكة وبيت الرحمة ومعدن العلم ».

Sarkin muminai (as) ya ce:lallai mu Ahlil-baiti bisihiya ce ta annabta mahallin sako wurin saukar mala'iku gidan rahama ma'adanin ilimi.

ــ وعن أبي جعفر ، قال  :

«يا معشر الشيعة ، خاصموا بسورة إنّا أنزلناه تفلجوا، فوالله إنّها لحجّة الله تبارک وتعالى على الخلق بعد رسول الله  9، وإنّها سيّدة دينكم ، وإنّها لغاية علمنا».

Daga Abu Jafar (as) ya ce: yaku jama'ar shi'a, ku yi jayayya da abokin bugawarku da suratu inna anzalnahu za ku yi nasara, wallahi na rantse da Allah lallai ita tabbas hujjar Allah ce albarku sun tabbata gare shi madaukaki kan halittun sa bayan manzon Allah, lallai ita shugabar addininku ce, ita ce magaryar tukewar iliminmu.

ــ وعن أبي بصير، قال : سألت أبا عبد الله  7 عن قول الله عزّ وجلّ  : (أطِيعُوا اللهَ وَأطِيعُوا الرَّسُولَ وَاُوْلِي الأمْرِ مِنْكُمْ ) ؟

فقال : «نزلت في عليّ بن أبي طالب والحسن والحسين  :».

فقلت له : إنّ الناس يقولون : فما له لم يسمِّ عليآ وأهل بيته في كتاب الله عزّ وجلّ ؟

قال : فقال : «قولوا لهم : إنّ رسول الله  9 نزلت عليه (الصلاة ) ولم يسمِّ الله لهم ثلاثآ ولا أربعآ، حتّى كان رسول الله   هو الذي فسّر ذلک لهم ».

Daga Abu Basir, ya ce: na tambayi Abu Abdullah (as) dangane da fadin Allah mai girma mabuwayi: (ku yi da'a ga Allah da mazonsa da ma'abota al'amari daga cikinku).[6]

Sai ya ce ta sauka cikin sha’anin Ali bn Abu dalib da Hassan da Husaini ne.

Sai na ce: lallai mutane suna cewa to me ya sanya Allah mai girma mabuwayi bai ambaci sunan da Ahlil-baiti cikin kur'ani ba.

Ya ce: sai ya ce: ku ce musu: lallai manzon Allah sallah ta sauka gare shi amma bai gaya musu cewa raka'a uku ko hudu ba, har sai da manzon Allah (s.a.w) ya kasance shi ne wanda ya fassara musu hakan.

ــ وعن أبي عبد الله  :

«من ادّعى الإمامة وليس من أهلها فهو كافر».

Daga Abu Abdullah (as) duk wanda ya yi da'awar imamanci alhalin shi ba ahlinta bane to lallai shi kafiri ne.

ــ عن أبي الحسن  7، في قول الله عزّ وجلّ : (وَمَنْ أضَلُّ مِمَّنِ آتَّبَعَ هَوَاهُ بِغَيْرِ هُدىً مِنَ اللهِ) ، قال 

«يعني من اتّخذ دينه رأيه بغير إمام من أئمة الهدى ».

Daga Abu Hassan (as) cikin fadinsa mai girma mabuwayi: (wane ne yafi batuwa daga wanda yabi son ransaba tare da ilimi daga Allah).[7]

Ya ce: ma'ana wanda ya riki addininsa ra'ayin sa ba tare da imaman shiriya ba.

ــ وعن أبي يعفور، قال : سألت أبا عبد الله   عن قول رسول الله : «من مات وليس له إمام فميتته ميتة جاهلية »؟ قال : قلت : ميتة كفر؟

فقال : «ميتة ضلال ».

قلت : فمن مات اليوم وليس له إمام فميتته ميتة جاهلية ؟

قال : «نعم ».

An karbo daga Ya'afuru, ya ce: na tambayi Abu Abdullah (as) dangane da fadin manzon Allah (s.a.w) cewa: (duk wanda ya mutu bai da imami ya mutu mutuwar jahiliya) ? ya ce: sai na ce shin mutuwar kafirci ake nufi kenan?

Sai ya ce: (mutuwar bata)

Sai na ce: a wannan zamani idan mutum ya mutu alhalin bai da imami ya mutu mutuwar jahiliya kenan?

Sai ya ce: na'am  

ــ قال جعفر بن محمّد  7 ـوعنده اُناس من أهل الكوفة ـ :

«عجبآ للناس إنّهم أخذوا علمهم كلّه عن رسول الله  9 فعملوا به واهتدوا، ويرون أنّ أهل بيته لم يأخذوا علمه ، ونحن أهل بيته وذرّيته ، في منازلنا نزل الوحي ، ومن عندنا خرج العلم إليهم ، أفيرون أنّهم علموا واهتدوا وجهلنا نحن وضللنا، إنّ هذا لمحال ».

 Jafar bn Muhammad (as) lokacin da wasu mutane garin kufa ke tare da shi ya ce: (mamaki ga mutane lallai su sun karbi ilminsu baki dayansa daga manzon Allah (s.a.w) suka yi aiki da shi suka shiriya, sannan suna ganin ahlin gidansa basu karbi iliminsa ba, mu ne Ahlin gidansa zuriyarsa, cikin gidajenmu aka saukar da wahayi, daga garemu ilimi ya fito zuwa gare su, shin yanzu suna ganin cewa lallai su sun sani sun kuma shiriya mu kuma mun jahilta mun bace, lallai wannan ba zai taba yiwuwa ba har abada

ــ وقال أبو جعفر  7 لسلمة بن كهيل والحكم بن عتيبة  :

«شرّقا وغرّبآ فلا تجدان علمآ صحيحآ إلّا شيئآ خرج من عندنا أهل البيت ».

Abu Jafar (as) ya cewa: Salmatu bn Kuhailu da Hakamu bn Atibatu:

Ku yi Gabas ku yi yamma ba zaku sami ilimi ingantacce ba face wani abu da ya fito daga garemu Ahlil-baiti.

Hakika mawaki ya kyautata sa'ilin da rera waken yabon imaman gaskiya Ahlil-baitin manzon Allah (s.a.w):

من جاء بالقول البليغ فآخذ         عنهم وإلّا فهو منهم سارقُ

ساووا كتاب الله إلّا أنّه         هو صامتٌ وهو الكتاب الناطقُ

Duk wanda ya zo da zance mai cike da fasaha* to daga gare su ya karbo idan kuma ba haka to lallai shi barawo ne*

Sun daidaitu da littafin Allah sai dai cewa yadda al'amarin yake shi littafin Allah baya magana shi kuma sarkin muminai littafi ne mai magana.

ــ وعن زرارة ، قال : سمعت أبا جعفر   يقول  :

«نحن اثنا عشر إمامآ، منهم الحسن والحسين ، ثمّ الأئمة من ولد الحسين  ».

An karbo daga Zurara, ya ce: naji Abu Jafar (as) yana cewa: (mu ne imamai sha biyu daga cikin su Hassan da Husaini, sannan A'imma daga `ya`yan Husaini.

ــ وعن أبي جعفر الثاني  ، أنّ أمير المؤمنين   قال لابن عباس  : «إنّ ليلة القدر في كلّ سنة ، وإنّه ينزل في الليلة أمر السنة ، ولذلک الأمر ولاة بعد رسول الله  ».

فقال ابن عباس : من هم ؟

قال : «أنا وأحد عشر من صلبي ، أئمة محدثون ».

Daga Abu Jafar na biyu (as) lallai sarkin muminai (as) ya cewa da ibn Abbas: (lallai lailatul na cikin kowacce shekara, lallai yadda al'amarin yake shi ne cikin daren lailatul kadari al'amarin shekara yake sauka, cikin wannan al'amari akwai majibanta bayan manzon Allah)

Sai Ibn Abbas ya ce: su wane ne?

Sai ya ce: ni da mutum goma sha daya daga zuriyata, su imamai da ake zance da su daga sama)

ــ وقال رسول الله   لأصحابه  :

«آمنوا بليلة القدر، إنّها تكون لعليّ بن أبي طالب ولولده الأحد عشر من بعدي ».

 Manzon Allah (s.a.w) ya cewa sahabban sa: kuyi imani da lailatul kadari, lallai ita tana kasancewa ga Ali bn Abu dalib da kuma `ya`yan sa goma sha daya a bayana.

Wannan dan yanki daga daruruwan hadisai kai bari dubban hadisai masu daraja cikin sanin A'imma, da hakikanin imami da cewa wane ne zai kasance imamin bayan manzon muktar (s.a.w) ta kaka sanin imamin zamaninka yake zama wajibi?

Hakika bangarori biyu sunna da shi'a sun wallafa dubunnan litattafai masu kima kan haka, saboda babu uzuri, lallai Allah yana da hujja mai isarwa, Allah ya isar ya zama mai hisabi.

na kwadaitar dakai zuwa ga wadannan riwayoyi masu daraja daga littafi mai kima (Alkafi):

 

قال أبو جعفر محمّد بن يعقوب الكليني مصنّف هذا الكتاب ؛ :

حدّثنا :

محمّد بن إسماعيل ، عن الفضل بن شاذان ، عن صفوان بن يحيى ، عن منصور بن حازم ، قال : قلت لأبي عبد الله  : إنّ الله أجلّ وأكرم من أن يعرف بخلقه ، بل الخلق يعرفون بالله.

قال : «صدقت ».

قلت : إنّ من عرف أنّ له ربّآ، فينبغي له أن يعرف لذلک الربّ رضىً وسخطآ، وأنّه لا يعرف رضاه وسخطه إلّا بوحي أو رسول ، فمن لم يأته الوحي فقد ينبغي له أن يطلب الرسل ، فإذا لقيهم عرف أنّهم الحجّة ، وأنّ لهم الطاعة المفترضة . وقلت للناس : تعلمون أنّ رسول الله  9 كان هو الحجّة من خلقه . قالوا: بلى . قلت : فحين مضى رسول الله  9 من كان الحجّة على خلقه ؟ فقالوا : القرآن . فنظرت في القرآن فإذا هو يخاصم به المرجئ والقدري لا يؤمن به حتّى يغلب الرجال بخصومته ، فعرفت أنّ القرآن لا يكون حجّة إلّا بقيّم ، فما قال فيه من شيء كان حقّآ. فقلت لهم : من قيّم القرآن ؟ فقالوا: ابن مسعود، قد كان يعلم وعمر يعلم وحذيفة يعلم . قلت : كلّه ؟ قالوا: لا. فلم أجد أحدآ قال : إنّه يعرف ذلک كلّه إلّا عليّآ  7، وإذا كان الشيء بين القوم فقال هذا: لا أدري ، وقال هذا: لا أدري ، وقال هذا: أنا أدري ، فأشهد أنّ عليآ  7 كان قيّم القرآن وكانت طاعته مفترضة ، وكان الحجّة على الناس بعد رسول الله  9، وأنّ ما قال في القرآن فهو حقّ .

فقال : «رحمک الله».

1-Abu Jafar Muhammad bn Yakubu Alkulaini mawallafin wannan littafi na Alkafi Allah yayi masa rahama, ya zantar damu daga Muhammad bn Isma'il daga Fadalu bn Shazanu daga Sufwanu bn Yahaya daga Mansur bn Hazim, ya ce: na cewa Abu Abdullah (as) lallah Allah yafi karamci daga ya zama sananne ta hanyar halittun sa, bari halittu za a sani ta hanyar Allah.

Sai ya ce: kayi gaskiya.

Sai na ce: lallai duk wanda ya san cewa lallai yana da ubangiji, to ya kamata gare shi ya san fushi da yardar wannan ubangiji, lallai ba zai taba sanin yardar sa da fushin sa ace ta hanyar wahayi ko manzanni, to dukkanin wanda wahayi bai zo masa ba, to hakika ya kamace shi ya nemi manzanni, idan ya hadu da su sai ya san lallai su hujja ne, lallai gare su da'a take ta farilla da wajibi, na cewa mutane, shin kun san cewa manzon Allah (s.a.w) ya kasance hujja daga halittun Allah, sai suka ce eh, sai na ce: lokacin da manzon Allah (s.a.w) ya tafi to wane ne hujja kan halittun Allah? Sai suka ce: kur'ani, sai na duba cikin kur'ani sai gashi yana rigima da mai akidar murji'anci da kadariya bai imani da shi har sai ya yi galaba da mazaje da husumar sa, sai nasan cewa lallai kur'ani bai kasantuwa hujja face da mai tsayuwa kansa, abin da ka fadi cikinsa daga wani abu ya kasance gaskiya , sai na ce musu: wanene mai tsayuwa da kur'ani: sai suka ce: ibn Mas'ud, hakika ya kasance ya san kur'ani Umar ma ya sani Huzaifa ma ya sani, sai na ce: baki dayan sa?sai suka ce: a'a, ban sami wani mutum guda daya ba da ya ce ya san hakan ba baki dayansa face Ali (as) idan wani abu ya faru tsakankanin mutane sai wannan ya ce ni ban sani wancan ma ya ce ni ban sani ba wannan ma ya ce nima ban sani ba, sai na shaida lallai Ali (as) tsayu da kur'ani kuma da'a gare shi ta kasance farilla, ya kuma kasance hujjar Allah kan mutane bayan manzon Allah (s.a.w) lallai abin da ya ce cikin kur'ani shi ne

ـ عليّ بن إبراهيم ، عن أبيه ، عن الحسن بن إبراهيم ، عن يونس بن يعقوب ، قال : كان عند أبي عبد الله   جماعة من أصحابه ، منهم : حمران بن أعين ، ومحمّد بن النعمان ، وهشام بن سالم ، والطيّار، وجماعة فيهم هشام بن الحكم وهو شاب ، فقال أبو عبد الله  7: «يا هشام ، ألا تخبرني كيف صنعت بعمرو بن عبيد وكيف سألته ؟»

2- daga Aliyu bn Ibrahim daga baban sa daga Hassan bn Ibrahim daga Yunus bn Yakubu, ya ce: wasu jama’a daga sahabban Abu Abdullah sun kasance wurinsa daga cikinsu akwai Himrana bn A'ayunu, da Muhammad bn Nu'umanu, da Hisham bn Salim, da Dayyar, da wasu jama'a wanda cikinsu akwai Hisham bn Hakamwanda shi saurayi ne matashi, sai Abu Abdullah (as) ya ce: ya Hisham, yanzu ba zaka bani labari ba kaka kayi da Amru bn Ubaidu kaka ka tambaye shi?

فقال هشام : يا ابن رسول الله، إنّي اُجلّک وأستحييک ، ولا يعمل لساني بين يديک .

فقال أبو عبد الله: «إذا أمرتكم بشيء فافعلوا».

Sai Hisham ya ce: ya dan manzon Allah, lallai ni ina ganin girmanka ina kuma jin kunyarka, harshen aba zai iya motsi a gabanka ba.

Sai Abu Abdullah (as) ya ce: (iadna na umarceku da abu ku aikata)

قال هشام : بلغني ما كان فيه عمرو بن عبيد وجلوسه في مسجد البصرة ، فعظم ذلک عليّ، فخرجت إليه ودخلت البصرة يوم الجمعة ، فأتيت مسجد البصرة ، فإذا أنا بحلقة كبيرة فيها عمرو بن عبيد وعليه شملة سوداء متّزر بها من صوف ، وشملة مرتديها، والناس يسألونه ، فاستفرجت الناس فأفرجوا لي ، ثمّ قعدت في آخر القوم على ركبتي .

Sai Hisham ya ce: na samu labarin abin da Amru bn Ubaida ya kasance ciki da zamansa cikin masallacin garin Basara sai hakan ya girmama kaina matuka, sai na fito na tafi wajen sa na shiga garin basara ranar juma'a na shiga masallacin garin Basara sai kawai ga wani taron mutane da ya tattaro Amru bn Ubaida yana sanye da wata bakar alkyabba daga gashi alhalin mutane suna tambayar sa sai na nemi mutane su buda mini wurin zama sai suka buda sai na zauna kan cinyata a can gefe guda. 

 ثمّ قلت : أيّها العالم ، إنّي رجل غريب تأذن لي في مسألة ؟ فقال لي : نعم ، فقلت له : ألک عين ؟ فقال : يا بني ، أي شيء هذا من السؤال ؟ وشيء تراه كيف تسأل عنه ؟ فقلت : هذا مسألتي . فقال : يا بني ، سل وإن كانت مسألتک حمقاء. قلت : أجبني فيها؟ قال : سل . قلت : ألک عين ؟ قال : نعم . قلت : فما تصنع بها؟ قال : أرى بها الألوان والأشخاص . قلت : فلک أنف ؟ قال  : نعم . قلت : فما تصنع به ؟ قال : أشمّ به الرائحة . قلت : ألک فم ؟ قال : نعم . قلت  : فما تصنع به ؟ قال : أذوق به الطعم .

Sannan na ce: yakai wannan masani, lallai ni bako ne shin kana bani damar yin tambaya gareka? sai ya ce mini: na'am sai na ce masa: shin kanada idaniya? Sai ya ce: ya dan karamin dana wacce irin tambaya ce wannan? Rta kaka zakai tambaya kan abin da kake ganin sa? Sai na ce : ni wannan ce tambayata, sai ya ce: ya dana yi tambayarka ko da tambayar taka ta kasance daga wauta. Sai na ce masa to ka amsa mini tambayar da nayi maka, sai ya ce: yi tambayar, sai na ce: shin kana da ido, sai ya ce: na'am ina da ido, sai na ce: me kake yi da shi? Sai ya ce: ina ganin mutane da ita da launuka, sai na ce: shin kanada hanci? Sai ya ce: eh, sai na ce: me kake da shi? Sai ya ce ina jin kamshin iska da shi. Sai na ce: shi kanda da baki? Sai ya ce: eh, sai na ce me kake da shi? Sai ya ce:ina dandana abinci da shi.

قلت : فلک اُذن ؟ قال : نعم . قلت : فما تصنع بها؟ قال : أسمع بها الصوت . قلت : ألک قلب ؟ قال : نعم . قلت : فما تصنع به ؟ قال : اُميّز به كلّ ما ورد على هذه الجوارح والحواسّ . قلت : أوَ ليس في هذه الجوارح غنىً عن القلب ؟ قال : لا. قلت : وكيف ذلک وهي صحيحة سليمة ؟ قال  : يا بني ، إنّ الجوارح إذا شكّت في شيء شمّته أو رأته أو ذاقته أو سمعته ، ردّته إلى القلب ، فيستيقن اليقين ويبطل الشکّ . قال هشام : فقلت له : فإنّما أقام الله القلب لشکّ الجوارح ؟ قال : نعم . قلت : لا بدّ من القلب وإلّا لم تستيقن الجوارح ؟ قال  : نعم . فقلت له : يا أبا مروان ، فالله تبارک وتعالى لم يترک جوارحک حتّى جعل لها إمامآ يصحّح لها الصحيح ويتيقّن به ما شکّ فيه ، ويترک هذا الخلق كلّهم في حيرتک وشكّهم واختلافهم ، لا يقيم لهم إمامآ يردّون إليه شكّهم وحيرتهم ، ويقيم لک إمامآ لجوارحک تردّ إليه حيرتک وشكّک ؟ قال : فسكت ، ولم يقل لي شيئآ، ثمّ التفت إليَّ فقال لي : أنت هشام بن الحكم ؟ فقلت : لا ـفرضآـ. قال : أمن جلسائه ؟ قلت : لا. قال : فمن أين أنت ؟ قال : قلت : من أهل الكوفة . قال : فأنت إذآ هو. ثمّ ضمّني إليه ، وأقعدني في مجلسه وما نطق حتّى قمت .

Shin kana da kunne? Sai ya ce: eh, sai na ce: me kake da shi? Sai ya ce: ina jin sauti da shi, sai na ce: shin kana da zuciya? Sai ya ce: eh, sai na ce: me kake yi da ita? Sai ya ce: ina banbance dukkanin abin da ya gangaro daga wadannan gabbai da mariskai. Sai na ce: shin cikin wadannan gabai babu wadatuwa daga barin zuciya? Sai ya ce: a ' a, ta kaka haka zai yiwu alhalin suna lafiya kuma ingantattu ne? sai ya ce: ya dana, lallai gabbai idan suka koka kan wani abu da suka shaki kamshin sa ko suka ji sautin sa ko suka ganshi ko dandana shi, suna maida zuwa ga zuciya, sai zuciya ta tabbatar da abin da yake yakini to kore shakka. Sai Hisham ya ce: sai na ce masa: kadai Allah ya tsayar da zuciya saboda shakkun gabbai mariskai? Sai ya ce: na'am. sai na ce: wato kenan dole dai a ce akwai zuciya idan ba haka ba gabbai ba za su samu yakini ba? Sai ya ce: na'am. sai na ce masa: ya baban Marwanu, Allah albarku sun tabbata gare shi madaukaki bai bar gabbai ba har sai da ya san musu imami jagora da zai dinga gyara da tabbatar da yakini cikin abin da suke shakku da kokwanto, amma ku gashi ya bar wannan al'umma baki dayanta cikin rudunka da shakkun su da sabanin su ba tare da ya sanya musu jagora imami ba da za su mayar da dukkanin shakkun su da rudewar su zuwa gare shi, amma kuma gashi Allah ya sanya maka imami jagora cikin gabbanka mariskanka kana komar da rudewarka da shakkunka zuwa gare shi? sai yayi shiru bai ce komai, sannan ya waiwaya zuwa gareni sai ya ce mini: amma dai kai ne Hisham bn Hakam ne ko? Sai na ce masa: a 'a-bisa kaddarawa-, sai ya ce: shin to kai dai amma daga almajiran sa kake? Sai na ce: a 'a, sai ya ce: to kai daga ina ka fito: sai na ce: daga mutanen kufa. Sai ya ce: to idan ko haka ne tabbas kai ne Hisham bn Hakam, sannan ya jawo ni zuwa gare shi ya zaunar da ni a mazauninsa yayi shiru bai ce komai ba har sai da na tashi.  

قال : فضحک أبو عبد الله  7 وقال : «يا هشام ، من علّمک هذا»؟

قلت : شيء أخذته منک وألفته .

فقال : «هذا والله مكتوب في صحف إبراهيم وموسى ».

Ya ce: sai Abu Abdullah (as) ya yi dariya ya ce: ya Hisham, wane ne ya koya maka wannan?

Sai na ce: abu ne da dauke shi daga gare shi na wallafa shi.

Sai ya ce: wallahi wannan an rubuta shi cikin suhufu Ibrahim da Musa.

ـ عليّ بن إبراهيم ، عن أبيه ، عمّن ذكره ، عن يونس بن يعقوب ، قال  : كنت عند أبي عبد الله  7 فورد عليه رجل من أهل الشام ، فقال : إنّي رجل صاحب كلام وفقه وفرائض ، وقد جئت لمناظرة أصحابک .

3- daga Aliyu bn Ibrahim daga babansa daga wanda ya ambace shi, daga Yunus bn Yakub, ya ce: na kasance wurin Abu Abdullah (as) sai wani mutum daga mutanen sham ya zo wajen sa, ya ce: lallai ni mutum ne ma'abocin ilimin kalam da fikihu da farillai, hakika na zo ne domin in tattauna da kai.

 فقال أبو عبد الله  7: «كلامک من كلام رسول الله  9 أو من عندک »؟

فقال : من كلام رسول الله  9 ومن عندي .

فقال أبو عبد الله  7: «فأنت إذآ شريک رسول الله»؟

قال : لا.

قال : «فسمعت الوحي عن الله عزّ وجلّ يخبرک »؟

قال : لا.

قال : «فتجب طاعتک كما تجب طاعة رسول الله  9»؟

قال : لا.

Sai Abu Abdullah (as) ya ce: ilimin maganarka daga manzon Allah (s.a.w) take ko daga gareka take?.

Sai ya ce: daga manzon Allah (s.a.w) da kuma wanda yake daga wurina.

Sai Abu Abdullah (as) ya ce: idan haka ne kai ka zama abokin tarayya manzon Allah (s.a.w) kenan ?

Sai ya ce: a 'a.

Sai ya ce: to kaji wahayi daga Allah mabuwayi mai girma da yake  labartar dakai kenan?

Sai ya ce: a 'a.

Ya ce: da'arka wajibi kenan kamar yadda da'a ga manzon Allah (s.a.w) take wajibi?

Sai ya ce: a 'a.

فالتفت أبو عبد الله   إليَّ فقال : «يا يونس بن يعقوب ، هذا قد خصم نفسه قبل أن يتكلّم »، ثمّ قال : «يا يونس ، لو كنت تحسن الكلام كلّمته ».

قال يونس : فيا لها من حسرة . فقلت : جعلت فداک ، إنّي سمعتک تنهى عن الكلام وتقول : ويل لأصحاب الكلام يقولون : هذا ينقاد وهذا لا ينقاد، وهذا ينساق وهذا لا ينساق ، وهذا نعقله وهذا لا نعقله .

Sai Abu Abdullah (as) ya waiwayo gareni ya ce: ya Yunus bn Yakub, wannan mutumin ya yi jayayya da kansa gabanin ya yi magana, sannan ya ce: ya Yunus ya hasara. Sai na ce: raina fansarka, lallai ni na taba jinka kana hani daga barin ilimin kalam kana cewa: azaba ga ma'abota kalam suna cewa: wannan zai jawu wannan ba zai jawu ba, wanan zai yiwu wanna ba zai yiwu ba, wannan muna hankaltarsa wannan bama hankaltarsa.

فقال أبو عبد الله  : «إنّما قلت : فويل لهم إن تركوا ما أقول وذهبوا إلى ما يريدون ».

ثمّ قال لي : «اخرج إلى الباب فانظر من ترى من المتكلّمين فأدخله ».

Sai Abu Abdullah (as) ya ce: kadai dai na ce azaba da bomi gare su idan suka bar abin da nake fadi suka tafi zuwa ga abin da ran su ke so.

Sannan ya ce mini: fita bakin kofa ka duba wane ne daga ma'abota kalam ka shigo mini da shi.

قال : فأدخلت حمران بن أعين ، وكان يحسن الكلام ، وأدخلت هشام بن سالم وكان يحسن الكلام ، وأدخلت قيس بن الماصر وكان عندي أحسنهم كلامآ، وكان قد تعلّم الكلام من عليّ بن الحسين  

Ya ce: sai na shigo da Himrana bn A'ayunu, ya kasance ya kware cikin ilimin kalam, na shigo da Hisham bn Salim hakika shi ya kasance ya koyi ilimin kalam daga Aliyu bn Husaini (as)

فلمّا استقرّ بنا المجلس ـوكان أبو عبد الله  7 قبل الحجّ يستقرّ أيامآ في جبل في طرف الحرم في فازة له مضروبة ـ قال : فأخرج أبو عبد الله  7 رأسه من فازته فإذا هو ببعير يخبّ فقال : «هشام وربّ الكعبة ».

Lokaicn da duk muka zauna a majalisin- sannan Abu Abdullah (as) ya kasance gabanin lokacin aikin hajji yana zama `yan wasu kwanani a dutse cikin gefan haram cikin hema da ka kafa masa-sai ya ce: sai Abu Abdullah (as) ya fito da kansa daga cikin hemar sa kawai sai ga wani rakumi yana ta sauri yana sukuwa ya nufo shi sai ya ce: (Hisham ne na rantse da ubangijin Ka'aba)

قال : فظننا أنّ هشامآ رجل من ولد عقيل كان شديد المحبّة له . قال : فورد هشام بن الحكم ، وهو أوّل ما اختطّت لحيته ، وليس فينا إلّا من هو أكبر سنّآ منه .

قال : فوسع أبو عبد الله   وقال : «ناصرنا بقلبه ولسانه ويده ».

ثمّ قال : «يا حمران كلّم الرجل ».

فكلّمه فظهر عليه حمران .

ثمّ قال : «يا طاقي ، كلّمه ».

فكلّمه فظهر عليه الأحول .

Ya ce: sai mukai tsammanin cewa Hisham wani mutum ne daga `ya`yan Akilu da ya kasance yana tsananin son sa. Sai ya ce: sai Hisham bn Hakam ya shigo shi ne farkon wanda gemunsa yayi layi-layi, cikinmu babu wanda bai girme shi ba.

Ya ce: sai Abu Abdullah (as) ya yalwata ya ce: (mai taimakonmu da zuciyar sa da harshen sa da hannun sa).

Sannan ya ce: ya Himranu ka tattauna da shi cikin ilimin kalam.

Sai Himran ya tattauna da shi sai ya yi nasara kansa.

Sai ya ce: ya Daku tattauna da shi sai ya tattauna da shi, sai ya tattauna da shi sai ya yi nasara kansa.

ثمّ قال : «يا هشام بن سالم ، كلّمه ».

فتعارفا.

ثمّ قال أبو عبد الله  7 لقيس الماصر: «كلّمه ».

فكلّمه ، فأقبل أبو عبد الله  7 يضحک من كلامهما ممّا قد أصاب الشامي .

فقال للشامي : «كلّم هذا الغلام » ـيعني هشام بن الحكم ـ.

فقال : نعم .

فقال لهشام : يا غلام سلني في إمامة هذا.

فغضب هشام حتّى ارتعد، ثمّ قال للشامي : يا هذا، أربّک أنظر لخلقه أم خلقه لأنفسهم ؟

فقال الشامي : بل ربّي أنظر لخلقه .

Sai ya ce: ya Hisham bn Salim tattauna da shi, sai ya tattauna da shi sai suka san juna, suka yi kunnen doki

Sannan Abu Abdullah (as) ya cewa: da kaisu Almasir tattauna da shi cikin kalam.

Sai ya tattauna da shi. sai Abu Abdullah (as) ya fuskanto yana dariya daga tattaunawar su daga abin da ya afku kan mutumin sham.

Sai ya cewa: mutumin sham tattauna da wannan yaro ma'ana yana nufin Hisham bn Hakam,

Sai ya ce: na'am

Sai mutumin sham ya ce: ya kai yaro tambayeni cikin imamanci, sai Hisham ya fusata har sai da takai jikin sa yayi rawa, sannan ya cewa da mutumin Sham, yakai wannan mutumi, shin ubangijinka shi yafi kula da halittar sa ko kuma halittarsa ne suka fi kula da kawukan su?

Sai mutumin Sham ya ce: bari dai ubangijina ya fi lura da halittun sa.

Sai ya ce: me ya aikata kan kula da su?

قال : ففعل بنظره لهم ماذا؟ قال : أقام لهم حجّة ودليلا كيلا يتشتّتوا أو يختلفوا، يتألفهم ويقيم أودهم ويخبرهم بفرض ربّه .

قال : فمن هو؟

قال : رسول الله  7. قال هشام : فهل نفعنا اليوم الكتاب والسنّة في رفع الاختلاف عنّا

قال الشامي : نعم .

Sai ya ce: ya tsayar musu da hujja da dalili don gudun kada su rarrabu kada su sassaba, shi ke harhado kawukan su shi ke daidaita karkatarsu sh ke basu labarin farillar ubangijin su.

Sai ya ce masa: wane ne hujja?

Sai ya ce: manzon Allah (s.a.w) sai Hisham ya ce: shin a yau littafi da sunna sun amfanar damu cikin kawar da sabani daga barinmu?

Sai mutumin Sham ya ce:na'am

قال : فلِمَ اختلفنا أنا وأنت ، وصرت إلينا من الشام في مخالفتنا إيّاک ؟

قال : فسكت الشامي . فقال أبو عبد الله  7 للشامي : «ما لک لا تتكلّم »؟

قال الشامي : إن قلت : لم نختلف كذبت ، وإن قلت : إنّ الكتاب والسنّة يرفعان عنّا الاختلاف أبطلت ، لأنّهما يحتملان الوجوه ، وإن قلت : قد اختلفنا وكلّ واحد يدّعي الحقّ فلم ينفعنا إذن الكتاب والسنّة ، إلّا أنّ لي عليه هذه الحجّة .

Sai ya ce: to me ya sa kuma muka sassaba ni da kai, ka nufo wurinmu daga garin Sham cikin sabani damu da shi dakai?

Sai ya ce: sai mutumin sham ya yi shiru. Sai Abu Abdullah (as) ya cewa da mutumin Sham: me ya faru da kai ne ba za kai magana ba?

Sai ya ce: idan na ce bamu da sabani na yi karya, idan kuma na ce: littafi da sunna suna dauke sabani na lalata, saboda su suna dauke da fuskoki, idan na ce mun saba da juna sannan kowanne mutum guda daga cikinmu yana da'awar shike da gaskiya idan haka ne littafin Allah da sunna basu amfanar damu, sai dai cewa ni ina da wannan hujja kansa.

فقال أبو عبد الله  : «سله تجده مليّآ».

فقال الشامي : يا هذا، من أنظر للخلق أربّهم أو أنفسهم ؟

فقال هشام : ربّهم أنظر لهم منهم لأنفسهم .

فقال الشامي : فهل أقام لهم من يجمع لهم كلمتهم ويقيم أودهم ويخبرهم بحقّهم من باطلهم ؟

قال هشام : في وقت رسول الله   أو الساعة ؟

قال الشامي : في وقت رسول الله رسول الله  ، والساعة من ؟

Sai Abu Abdullah (as) ya ce tambaye shi da sannu zaka same shi mai cikawa.

Sai mutumin Sham ya ce: ya kai wannan wane ne yafi kula da halittun sa shin ubangijin su ko kuma kawukan su?

Sai Hisham ya ce: ubangijin su ya fi lura da su daga kawukan su.

Sai mutumin Sham ya ce: shin ya sanya musu wanda zai hada kan kalmomin su ya kuma mikar musu da karkatar su ya basu labarin gaskiyar su daga batansu?

Sai Hisham ya ce: a zamanin manzon Allah (s.a.w) ko kuma lokaci?

Sai mutumin Sham ya ce: a zamanin manzon Allah (s.a.w) na ke nufi. Sannan wane ne kuma lokaci?

فقال هشام : هذا القاعد الذي تشدّ إليه الرحال ، ويخبرنا بأخبار السماء ]والأرض [ وراثة عن أبٍ عن جدّ.

قال الشامي : فكيف لي أن أعلم ذلک ؟    قال هشام : سله عمّا بدا لک .

قال الشامي : قطعت عذري ، فعليَّ السؤال .

فقال أبو عبد الله  7: «يا شامي ، اُخبرک كيف كان سفرک ؟ وكيف كان طريقک ؟ كان كذا وكذا»

فأقبل الشامي يقول : صدقت ، أسلمت لله الساعة .

قال هشام : سله عمّا بدا لک .قال الشامي : قطعت عذري ، فعليَّ السؤال .

فقال أبو عبد الله  7: «يا شامي ، اُخبرک كيف كان سفرک ؟ وكيف كان طريقک ؟ كان كذا وكذا».

فأقبل الشامي يقول : صدقت ، أسلمت لله الساعة .

Sai Hisham ya ce: wannan wanda yake zaune da ake daure kaya a zo wajen sa wanda yake zantar damu labaran sama da kasa ya gaji hakan daga babansa da kakansa.

Sai mutumin Sham ya ce: ta kaka ni zan iya sanin hakan?

Sai Hisham ya ce: tambayi duk abin da kake son tambaya.

Sai mutumin sham ya ce: ka yanke mini uzuri, yanzu tambaya na kaina.

Sai Abu Abdullah (as) ya ce: ya kai mutumin sham, shin in baka labarin yadda tafiyarka ta kasance? kaka hanyar da ka biyo ta kasance? Ta kasance kaza da kaza.

Sai mutumin Sham ya fuskanto yana fadin: na muslunta lokaci ga Allah yake.

فقال أبو عبد الله  7: «بل آمنت بالله الساعة ، إنّ الإسلام قبل الإيمان ، وعليه يتوارثون ويتناكحون ، والإيمان عليه يثابون ».

فقال الشامي : صدقت ، فأنا الساعة أشهد أن لا إله إلّا الله، وأنّ محمّدآ رسول الله  9، وأنّک وصيّ الأوصياء.

ثمّ التفت أبو عبد الله  7 إلى حمران ، فقال : «تجري الكلام على الأثر فتصيب ».

والتفت إلى هشام بن سالم ، فقال : «تريد الأثر ولا تعرفه ».

ثمّ التفت إلى الأحول ، فقال : «قياس رواغ ، تكسر باطلا بباطل ، إلّا أنّ باطلک أظهر».

ثمّ التفت إلى قيس الماصر، فقال : «تتكلّم وأقرب ما تكون من الخبر عن رسول الله  9 أبعد ما تكون منه ، تمزج الحقّ مع الباطل ، وقليل الحقّ يكفي عن كثير الباطل ، أنت والأحول قفّازان حاذقان ».

قال يونس : فظننت والله أنّه يقول لهشام قريبآ ممّا قال لهما.

ثمّ قال : «يا هشام لا تكاد تقع ، تلوي رجليک إذا هممت بالأرض طرت ،

 مثلک فليكلّم الناس ، فاتّق الزلّة ، والشفاعة من ورائها إن شاء الله»[8] .

Sai Abu Abdullah (as) ya ce: bari dai ka yi imani da Allah lokaci yake, lallai muslunci ya gabaci imani, kansa ne mutane ke gadon juna da auratayya, shi kuma imani kansa ake bada lada.

Sai mutumin sham ya ce: ka yi gaskiya, ni ne lokaci na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah na shaida Muhammad manzon Allah (s.a.w) ne, kai kuma wasiyyin wasiyyai ne.

Sannan Abu Abdullah (as) ya waiwaya zuwa Himrana, ya ce: ka gudanar da tattaunawar kalam a irin wannan gurbin sai ka dace.

Ya waiwaya zuwa ga Hisham bn Salim ya ce masa kana son gurbi amma baka san shi ba.

Sannan ya juya ga Ahwalu ya ce masa: kiyasi ribata ne, zaka rusa bata da bata sai dai cewa batanka ya fi karfafa

Sannan ya waiwaya zuwa ga Kaisu Almasir ya ce masa: kana tattaunawa cikin kalam mafi kusa da zaka kasance daga manzon Allah (s.a.w) mafi nisantarka daga gare shi, kana cudanda gaskiya tare da karya, mai gaskiya `yar kadan yana wadatarwa daga mai yawaita karya, kai da Ahwalu ma'aunai ne hazikai.

Yunus bn Yakub ya ce:wallahi nayi tsammanin zai cewa Hisham irin abin da ya gargaya musu

Sannan ya cewa Hisham baka kusa ba ka fadi kana lallankwasa kafafuwanka idan ka himmatu da kasa sai ka tashi sama, mutum misalinka zai iya tattaunawa da mutane cikin ilimin kalam, kaji tsoran zamewar kafafuwa, da izinin Allah ceto na bayanta.[9]   


[1] Alkafi: m 1 sh 77 hakama riwayar da aka amabata daban kamar yadda ta zo cikin biharul-anwar na Allama majalisi.

[2] ()  التوبة : 105.

[3] Nahlu:16

[4] Isra'i:71

[5] Tauba:105

[6] Nisa'i:53

[7] Kisas:50

[8] ()  النساء: 87.

[9] Ka koma ga sharhin littafin Alkafi cikin wannan riwayoyi masu daraja domin ka tsinkayi gwalagwalan kalam